Showing 6001 words to 9000 words out of 242549 words

Chapter 3 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3337

ji kunyar kiranta da sunan mai-aikinta ba.

"Khadija. Suna na Khadija." Ta ce dashi muryarta a dake.

Bakinsa ya doke da sauri ya sauka kan gwiwoyinsa.

"Ki yafeni Khadija."

Ba shi take kallo ba. 'Yarta ta karshe a duniya take kalla tana nadamar biyayyarta a baya. Da bata amince ta aure shi ba da basu hada jini da mazinaci ba.

"Na yafe maka tun kafin ka roka duk da baka yi nadama ba."

"Nayi. Wallahi nayi nadama sosai."

"Baka yi ba. Na rantse da Allah da kayi nadama da baka taho da ita kawoni asibiti ba. Da bata zauna jinyata har ana cigiyar rashin zuwanta a yau ba."

Busassun labbansa ya lasa a hankali. Ya san ba za ta taba yarda ba amma shi ya san cewa ya yi nadama. Yana dai yiwa Nasima irin son da ba zai iya hakura da ita ba. Idan kurar nan ta lafa aurenta zai yi ya kama mata gida daban. Zai cigaba da zama da Khadija saboda wani sashe na zuciyarsa yana ganin girmanta. 'Ya'yan da ta haifa masa kuma duk munin halinsa yana sonsu kuma ya san suna da hakki a kansa. Muryarta ce ta katse masa tunani.

"Kafin a sallameni ka rubuta min takardar saki. Ba zan tona maka asiri ba saboda bana son duniya ta nunawa 'ya'yana yatsa akan halinka. Kai dai ka tanadi abin da za ka fadawa iyayenmu tunda karya a jininka take. Sharadi na daya ne." Kallonta ya yi "kada ka yarda ka dora min laifi a matsayin dalilin rabuwarmu. Ina fata ka fahimceni."

"Ba zan iya sakinki ba. Khadija ina sonki."

"Ka daina yiwa kanka karya akan abin da baya zuciyarka."

Zancen gabadaya baya so ayi shi a asibiti amma ya san ba shi da hurumin cewa tayi shiru. Yana son cigaba da zama da ita amma ba ya jin zai zama adalci gareta ya tursasata ta cigaba da zama tare dashi bayan yanzu ya fara son Nasima. Tunda dai za ta rufa masa asiri ya san komai zai zo da sauki. Juyawa ya yi zai fita ta kira sunansa.

"Tahir! Za ka yi nadama a nan gaba sai dai ina tsoron kada ta zo a lokacin da komai ya lalace. Ina gudun kada hakkin 'ya'yan da ka batawa rayuwa ya rataya a wuyan 'ya'yana."

Da yake maganar ta tsorata shi bai san lokacin da ya ce "wallahi ba ni na bata Nasima ba a haka na sameta."

Kallon da tayi masa ne ya sa shi jin nauyin furucinsa. Sunkuyar da kai kawai ya yi yana jiran ya ji me za ta ce sai yaji shiru. Juya masa baya tayi tana zubar da zazzafar kwalla. Ta so Tahir a lokacin da bata da zabin da ya wuce bin umarnin iyaye. Ta sadaukar da farincikinta na son waninsa saboda tsira daga azabar Allah. A yau ta rasa mahaifi da kuma igiyar auren da take jira ya datse duk a dalilinsa. Ita mai iya tsaya masa ce ya kara aure idan yana so. Shi yasa take mamakin dalilinsa na yin zina. Zinar ma ta fuskar wulakanci gareta. Kalaman mahaifiyarta take tunawa a wani lokaci da ya wuce tana yiwa kaninta fada zai tafi jami'a a wani garin.

"Zina masifa ce. Idan ka yi da 'yar wani kai ma sai ta zagayo jikinka inda za ka ji ciwo mai radadi. Ko ni, ko 'yan uwanka, ko iyalinka ko 'ya'yan cikinka"

Addu'a ta soma yi musu tana fatan Allah Ya karesu daga wannan mummunar dabi'a. Za ta sadaukar da rayuwarta wurin kula da tarbiyarsu da fatan rufowar asirin mahaifinsu. Aure kuwa ta yi ta gama. Abin da ya yi saura ba rayuwarta za ta yi amfani dasho ne wurin ganin yaranta sun sami ingantacciyar rayuwa.

Bayan kwana biyu suka sake kebewa da Tahir a dakin. Tuni tayi masa akan takardar sakin ya ce da ya saketa gara ta tona masa asiri. Amsarsa ta tayar mata da hankali ta kuma sanyata tunanin dalilinsa na sauyawa bayan da ya amince.

Yanayinta ya kalla a ransa yana yabon kaifin basirar Nasima. Yana fada mata zai saki Khadija ya aureta ta fitittike ta ce sam bata yarda ba. Nuna masa tayi duniya za ta zagesu idan suka yi haka. A ranta kuwa gudun kada ya bata rikon 'ya'ya take yi. Tafi son ayi auren a gaban Khadijan ta ganta suna masu matsayi daya a gidan. Ita ta bashi shawarar wadancan kalamai domin a cewarta Khadija za ta zauna don 'ya'ya. Tunda aka kai yanzu maganar ganinsu bata tashi ba to ya sani cewa indai akan 'ya'yanta ne za ta rufa masa asiri.

Ga zahiri ya gani. Sai ga Khadija tana kuka tana rokonsa saki kamar ba ita ya yiwa laifi ba. Da aka murda kofar dakin da sauri ta share hawayenta harda karyar ciwo ke cinta. Da wannan barazanar ya samu ya rufe bakinta har aka yi sallama. Da wani ya san abinda uban 'ya'yanta ya aikata ko da kuwa mahaifuyarta ce gara ta cigaba da zama dashi ko babu soyayya. Ba za ta so labarin gamon da tayi ya taso a lokacin da wani alkhairi ya doso rayuwar 'ya'yanta ya wargaza ba.

KHADIJA: A jerin ire-iren iyaye mata ta fado a jinsin masu shanye komai domin 'ya'yansu. Ta yarda ta fanshi zubar hawayensu ta hanyar sadaukar da farincikinta. Karesu zata yi muddin rai kada kazantar mahaifinsu ta wargaza rayuwarsu a gaba.

*****


KIRIKASAMMA
1995


Ta san ya ji ta sarai amma bata sare ba ta cigaba da binsa da roko da laluma saboda muddin ya sa kafa ya fita yau to magana ta kare. Kiran sunansa tayi da dan karfi ganin ya kusa kofar fita. Indai bukatarta za ta biya tayi alkawarin jure duk wani jan rai da wulakanci daga Inuwa.

"Malam inata magana baka ce komai ba har za ka fita."

A fusace ya juyu kamar zai mangareta ya soma fada.

"Ke dai Mari da mayya ce ki ka kama mutum Yasin sai buzunsa. Haba! Ni na taba ganin bakin naci irin wannan? To duk jarabarki sai ya tafi yadda ake tura 'ya'yan kowa."

Hargaginsa ya fito da sauran matan gidan daga bangarorinsu. Zaman kauye babu abin yi har jiran barkewar rikici suke don a bawa ido abinci. Gidan nasu kuwa an sami karuwar jama'a, kama daga matan da ake kara aurowa zuwa hayayyafar da ake yi kusan duk shekara.

"Rigimar me ku ke yi da rana tsaka Inuwa?" Mal. Sa'idu babban wa ga mazam gidan ya tambayesu amma aka rasa mai bashi amsa.

Mari sadda kai tayi kasa zuciyarta tana bata cewa hakuri kawai za ta yi wannan karon a tari gaba. Mal Sa'adu da sauran 'yan uwan Inuwa babu mai goyon bayanta. Maganar nan kuma ko Inna Mairo ba bayanta za ta bi ba.

"Kya yi shiru kuma yanzu? Ai sai ki bude baki ki fada musu abinda ki ke rokona" cewar Inuwa yana duban yayansa "wai makaranta ce bata so a tura Abbati."

"La haila ha illallahu..."

Mata sai tafa hannuwa kamar sun ji gagarumin sabo. Shi kuwa Mal Sa'adu cewa ya yi maganar ba ta tsaye bace su biyo shi sashensa.

Durkuso Mari tayi a gefen tabarmar da Inuwa ya zauna. Bata ma yi niyyar zama ba domin rashin kunya za ace tayi. Mal Sa'adu ne ya yi magana cikin jimami.

"Yanzu ke Mari karatun Muhammadiyyar ne ba kya so? To ko dai kin canja addini ne bamu da masaniya?"

Kai da hannuwa ta karkada a tare "a'a Malam. Cewa nayi a barshi ya cigaba da karatun a nan ba sai an kai shi Kano ba almajiranci ba."

Matan gidan dama ba kaunarta suke sosai ba saboda fifikon da Inna Mairo ke nunawa a kanta. Gashi tayi karatu har matakin aji uku a firamare kafin Inuwa ya aurota. Su kuwa babu arabi ba boko. Anyi musu baiko tun tana shekara goma. Sai ta tafi aikatau Dutse inda ta sami wayewar kai. Gidan da tayi aikin suka saka ta a makaranta. Sun so a barta ta karasa amma gidan su Inuwa suka ce idan bata dawo anyi auren ba a dawo musu da kudinsu. Haka nan tana ji tana gani aka rabota da ilimin da ta fara jindadinsa. Wannan ne yasa ta dage aka kai 'ya'yanta firamaren garin sannan suna zuwa makarantar allo da ta dare. Da sana'ar dinkimta da take dan samun kudi take yi musu hidimar makaranta. Su biyar ne yanzu. Abbati babba da mai binsa Sani sai 'yan mata uku. Al'adar gidan ta tura yara maza almajiranci kwatakwata bata burgeta. Ta ga yadda almajirai ke watangaririya idan sun tafi karatu, bata marmarin 'ya'yanta suyi irin wannan rayuwa.

"Lallai Mari. Ke ko 'yar kunyar nan ta dan fari ma ba kya ji har kike kallon idon Malam kina cewa a bar miki da a gabanki?" Uwargidan Mal Sa'adu ta furta da sigar nuna tayi ba daidai ba.

"Ko ma dai mene ne wannan sabon abin da ki ka zo dashi ba al'adar gidanmu bace. Zuri'ar gidan nan suna zuwa almajiranci tun talan-tale. Naki dan da bai fi na kowa ba shi ma zai je. Sai dai kuma idan zaki sake masa uba." Mal Sa'adu ya kare da tsorata ta.

Idan aka ce ta sake masa uba tamkar ana tuhumarta da laifin haifar dan da ba na sunna bane. Muryarta a karye ta bashi hakuri "Allah Yasa hakan shi ne mafi alheri."

"Karatun allo hairan ne! Abbati zai je kamar sauran 'yan uwansa ya rubuce sittin kuma ya haddace shi."

'Nima haka nake fata' Mari ta ce a ranta tana mikewa tsaye. Jiki ba kwari ta shiga dakinta tana jin kamar an zare mata laka. Wannan karon an mata fin karfi amma ba za ta yarda badi a kai Sani ba.

Kafin ranar tafiya ta shanya kanzo gari guda ta gyara masa. Man gyada ma ta soye shi da albasa ta kuma daka masa yaji. Tayi kuli-kuli, carbin malam, hallaka kwabo da duk wani abu da take tunanin zai ci daidai karfinta. Nasiha kuwa har ya soma gajiya da ji.

"Ka yiwa malaminka biyayya Abbati."

"Banda kwadayi ko dauke dauke."

"Idan an turaku bara ka ce na hana. Ga kayan abinci nan ina ta hada maka hatsi. Zan fadawa Babanka ya bawa malamin. Idan ya so in sun dora sanwa a dinga dibar maka."

"Abbati kada ka je bara fa. Daga cikin gidan wani zubin sai an zageka an zagi uwar da ta kawoka duniya kafin a baka kwantai."

"To Baaba" yake cewa ga duk nasihar da fadan nata. Har yanzu bai san ma'anar karatu da ake cewa za'a kaishi tare da sa'ansa dan yayan Inuwa ba. Yayyansa da suka tafi garuruwa daban daban yake sha'awa. Idan zasu zo suna dan kullo tsarabar birni su kawo. Kuma shi da Baaba ke son ya zama likita yanzu ne zai yi karatu na 'yan birni ya fara allura.

Mari tayi kuka sosai ranar da zasu tafi. Bai taba nisa da ita ba musamman saboda tsoron fadansa. Indai rigima ake yi da wuya ka ga Abbati a ciki. A gidan manya da yara idan ka cire mahaifansa da 'yan uwan babansa ana tsokanarsa da Abbati solobiyo. Rashin kuzarinsa yana daga cikin manyan dalilanta na son ya zauna a gida. Kazalika shi ne ya kara rura wutar kiyayyarta da zuwansa almajiranci. Banda iyayen sun riga sun farlantawa kansu kai yaransu maza akwai makarantu yanzu a garin nasu na ilimin islama.

Har soro ta fito tana kuka da zasu shiga a-kori-kurar da ta zo daukarsu. Hawaye take wani na bin wani tana ta nanata masa abubuwan da ta fada masa.

"Mu kuwa kamar tsinar namu 'ya'yan muke bamu san zafin nakuda ba." Cewar guda cikin faccalolinta.

Wata ta amshe da cewa "mu da aka jima ana daukar namu ba."

"Wai kuma a haka fa don dan fari ne. Wannan da Sani ne zai tafi sai tayi mana karamin hauka."

A gigice ta kalli amaryarta da ko haihuwar fari bata yi ba tana neman ballo mata ruwa. Ranta a bace ta ce,

"Bakin ki ya sari danyen kashi. Sani ba zai je bara ba da yardar Allah. Wannan ma don anfi karfina ne."

"Ai kuwa zan nuna miki babu dan da za ki fi karfinmu a kansa. Kai Inuwa.." Mal Sa'adu dake bayan matan ba tare da saninsu ba ya yafito kaninsa "tsayar da direban nan ka hado kayan Sani."

Ba Mari ba shi ma sai da ya razana. Sani shekararsa tara ga karamin jiki kamar dan bakwai.

Mal Sa'adu ya juya a fusace ya kira ragowar kannensa. Duk wanda dansa sai badi zai tafi ya ce a hada masa kaya yau. Sauran matan basu ji dadi bane saboda basu shirya ba. Mari kuwa da ta gama magana da kanwar Inuwa dake aure a Kazaure sai da ta kusa haukan da ake kira mata. Sun gama shiri za ta dawo ta ce a bata Sani saboda bata da namiji sai ta tura mata kudi a kaishi bodin.

A buhu Inuwa ya cusa kayansa tana kuka tana tumami amma Mal Sa'adu ko gezau. Inna Mairo ma tayi masa magana ya ce babu matar da za a auro tafi karfinsu. Idan bai yi haka ba sauran ma zasu raina mazajensu ne.

Kukan Mari a kofar gida har makota ana ji. Ana saka Sani a mota ta sauko dashi tana magiyar a barshi ta yarda a tafi da Abbatin. Ita a nufinta ko shi kadai ya yi bokon ya zama wani abu a gaba zai taimakawa yayansa. Shi kuwa Abbati da zuciyar kuruciya sai ta ayyana masa mahaifiyarsu bata kaunarsa tafi son kaninsa. Kukan shi ma ya saka ta mika hannu za ta sauko dashi Inuwa ya daka mata tsawa.

"Ki mayar dasu ko su sauko ku kama hanyar gidanku tare." Ransa ne ya baci da jama'ar da ta tara musu ana ta gulmarta wai bata da rikon addini.

Mutanenmu da matukar tsoron kalmar saki. Ba arziki ta saki yaran tana zaman 'yan bori a kasa. Tana ji tana gani motar nan tayi gaba aka tafi da 'ya'yanta. Abbati za'a sauke shi a Kano shi kuma Sani da sauran yaran a Zaria saboda can ne suke da manyan yayye.

MARI: Ga Mari ba mutuwar auren kadai take tsoro ba harda inda za ta kai yaran. Iyaye basa raye ga talaucin kauye. Idan aurenta ya mutu kannensu ma masomin tagayyarar rayuwarsu kenan. A wannan lokacin maslahar da ta hango bata wuce ta sadaukar da mafarkin cigaban manyan 'ya'yanta akan rayuwar kannensu ba.

*****
KANO

1995


"Masu gida. Magadan Alhaji. Ku zo ku dauka na gama rabawa" Asabe ta kira 'ya'yanta tana rangwada murya.

Gajeren tsaki gami da murmushi Innayo tayi ta cigaba da barar albasar gabanta. Ina abin gado a tattare da Alh Rabi'u har da mutum zai yi tinkaho? Tabbas arzikinsa ya karu a shekarun nan haka kuma tsiya ta rashin son wadata iyalinsa ta kankama. Innayo bata sake haihuwa ba tun Hasiya. Asabe kuwa ta jera maza uku bayan wanda suka yi goyo tare lokacin Hasiya. Salon kishin Asabe ya dade da dena bata mata rai. Ita bata yarda bane sai ta cusa mata haushi ta kowane hali. Innayo kuma bata da wannan lokacin. Har yanzu da ta aurar da duka 'ya'yan uwargidan Alh Rabi'u bata hakura da dena neman kudi ba. Yadda ta gina su haka take ta fafutukar gina nata. Dukkansu sai da suka gama sakandire da guminta aka yi bikinsu.

Abu daya ke yi mata ciwo a rai wanda yasa ta dada jajircewa akan 'ya'yanta. Tun lokacin bikin A'i babbar 'yar Alh Rabi'u mahaifiyarsu ta sake bayyana a rayuwarsu. Mijinta Kansila ne a lokacin suna ta damashere da dukiyar talakawa. Innayo bata son auren ta kuma fadawa A'i, amma sai ta tsallake ta sanar da mahaifiyarta Laraba. Ita kuma ta tsaya mata sun ga mai arziki. Alh Rabi'u dama tuni ya mika wuya ya yi mubaya'a ga wannan hadi. Tana ji tana gani akayi auren. A'i da kannenta suka koma jikin mahaifiyarsu. Ita dai bata fasa yi musu komai da ta saba ba amma tsakaninsu babu wannan mu'amalar ta uwa da 'ya'yanta. Komai nasu na shawara da Laraba suke yi. A ranta ta kan ce uwa uwace! Shekara na zagayowa Kansila ya biyawa A'i, Alh Rabi'u da Laraba hajji. A gabanta kannen A'i suka shigo da tsaraba mai tarin yawa ita kuwa da 'ya'yanta aka bisu da dan madina da bagaruwa. Alh Rabi'u kuwa 'yan mazansa ya gwangwaje ya bata robar zam-zam irin 'yan kulalan nan adadin 'ya'yanta.

"A sha a sami tubarrakin Annabi Isma'ila." Ya ce lokacin da ya ajiye mata a gefen katifa.

Idan ta ce wannan abu bai yi mata ciwo ba tayi karya. Ita ma za ta so nata 'ya'yan su zame mata inuwar hutawa a gaba. Auren irin su Kansila da ta san dukiyar yawanci zuwa take ta tafi da an gama gwamnatinka ne bata so. Sai ya zamana bata da dare bata da rana. Sana'ar abinci ta iya kuma ita ta kara fadadawa.

Muryar Zara ta ji wadda Hasiya take bi tana magana bakin tsiwar nan a gaba ta zumburo shi.

"Ni dai gaskiya ki canja sana'a Innayo wallahi gulmarmu ake yi a makaranta. Ko? Ko Hasiya?" Ta waiga bayanta inda Hasiya ta tsaya jikin kofa.

"Ni dai ban sani ba." Hasiya ta ce tana ja da baya gudun fadan Innayo.

Haushi ya turnuke Zara ganin Hasiya za ta bata mata shiri ta harareta.

"Banza kawai. Ke kin fi so a dinga jin tsamin geron 'yar tsala a jikinki duk safiya a makaranta"

Ita da gaske take son mahaifiyar tasu ta sami wata sana'ar ba ta abinci ba.

Sai da Innayo ta gama barar albasar ta daga kai "yau ke ce da yin danmalelen dare. Ga albasar nan ki yanka kanana Hasiya za ta karbo tumatir ki hada."

"Innayo" Zara ta kira ta kamar tayi kuka.

"Mai abinci ta fi almajira kuma ta fi mai shiga makota tana bani bani. Idan kin raina min sana'a ni ki ka raina." Ta bata amsa ko kadan muryarta bata daga ba.

Daga gefensu Asabe ta tsoma baki tana dariyar shakiyanci "sunan wani wai shi girkau. An tasa yara a gaba ana ta kone musu sinadarin kyau da wutar icce ai dole su yi bore. Shiga makota bani bani kuwa dabara ce sai mai wayo. In mutum ya isa ya gwada mana."

Innayo bata kula ta ba sai 'ya'yanta da ta bi da kallo daidai suka fahimci ma'anar kallon. Daki suka shige Zara tana botsarewa ita a dole bata son aikin.

"Tara ki nake yi Zara. Idan ki ka kaini bango kin san sauran" cewar Innayo daga bakin kofa.

Zara bata kara cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login