Showing 177001 words to 180000 words out of 242549 words
yi masa akan wurin aiki. Wajibi ne uwa ta matsu da son jin silar rayuwa irin tasa. Ga gida ga motoci ga kudi kamar bai san ciwonsu ba. Samarin garin da dama idan sun kawo kawunansu ko iyayensu sun musu jagora akan ya saka su a hanyar sana'arsa sai da ya cikasu da kudi. Ana karbe kudin zaka ga mutum ya ja gefe an koma kasuwanci ko a cinyesu a banza. Ya gode Allah da ya kasance ba shi da alhakin sanya d'an kowa a layinsu. Da yanzu bai san yadda zai yi da lodin zunubai ba. Ga nasa da yake fatan samun gafara ga na wasu da babu lallai su so tuba.
Kan kasaitacciyar kujerar kushin din dakin da aka yi domin kwanciya ya tafi ya kwanta rigingine. Tunani bai barshi ba har ya luluka yana tuna masa yadda aka yi suka kawo zuwa yanzu. Yayinda Munzali ya zama mukullin bude masa wannan duniyar, shi Abbati, shi ne ya fara mayar musu da ita sana'a a lokacin da Munzali ya kwanta ciwo. Shi ne ya nemi Shazali wanda ya kaishi wurin wani babban mutum.
Tunanin komai da kowa ya yakice ya sanya kansa a faifan zuciyarsa yana tuhuma. Shin yana wannan dabiar ne a matsayin sana'a ko matsayin namijin da yake jindadi mu'amala da jinsinsa? Amsarsa ita ce zabi na biyu. Hakika ya yi mugun sabo da wannan dabi'a wadda ta sanya har yanzu sha'awar mu'amalar ta kan taso masa. A kalla kusan bayan kwana bibbiyu ko uku ya kan sami kansa a mugun yanayin son wannan abu. Yana jin wahala har ma ya kai ga siyan magani don wani zubin ko bacci kasawa yake. Haka kuma take a wurin Munzali shi ne ma dalilinsa na biya musu makudan kudade domin samun lafiya. Matsalar irin wannsn zinar ya wuce mutum ya tashi watarana kawai yace ya tuba. Ita jiki take bi tana yi masa illah. Idan bukatarta ta taso mutum dole ya nemi hanyar biyanta ko ya wahala. Allah ne shaidarsu amma rabonsu da neman juna tun gabanin ciwon Munzalin. Shamaki ne Allah Ya saka musu sannan Ya maye musu zukata da tsaftatacciyar kaunar juna domin lokaci irin wannan.
Duk wannan abu zuciyarsa bata fasa fada masa cewa shi din har yanzu namiji bane. Soyayya dai ta zuciya da zuciya Farha yake yiwa. Tunaninta kadai sai da yasa tsigar jikinsa ta tashi. Yana sonta da dukkan abin da zuciya za ta iya bawa wanda take kauna. Burinsa na duniya akan mace ahi ne ya mallaketa a matsayin matar aure. A wayi gari wasu yara suna kiransa Baba suna kiranta Mama. Duk mazan da yake mu'amala dasu kallon maza yake yi musu. Mata kuma suna nan a mata. Bai taba sanya kansa a ajin 'yan daudu ko wadanda suke karyar cewa da son jinsinsu aka haifesu ba. Shi lafiyayyen namiji ne wanda ya mayar da kusantar maza 'yan uwansa sana'a. Idan babu namiji zai rayu sarai da mace sai dai kawai illar wancan abu zai dinga damunsa kafin Allah Ya yaye masa jarabar. Infact yana daga cikin dalilansa na cigaba da zama da Hanne duk irin rashin dadin zamansu kuwa. Tuntuni auren ya wuce na umarnin Mal. Sa'idu, domin kuwa a irin kudinsa da ya saketa idan har da mai ce masa don me ba zai wuce Baaba Mari da Gwaggo Jummai mahaifiyarta ba. Sauran kowa so yake ya zo ya auri tasa 'yar. Abin da ya hada auren nasu ma tuni an manta dashi. Shi da ita suna zaune ne kawai saboda auren rai gareshi. Babu soyayya, babu shakuwa sannan babu damuwa. Gara ma shi yana bata kulawa domin sauke nauyin hakki. Ita kuwa tsakaninta dashi bai wuce kudi idan har ta neme shi. Ga misali yanzu rabonsa da gida tun asabar daga zuwa daurin aure. Amma har yau ko flashing bata yi masa ba.
A kasalance ya tashi ya shiga hada kayansa na sakawa a wasu manyan akwatuna. Ya zabi aikin ne domin rage radadin rashin Munzali da Qibdiyya. Sai dai ko kusa bai sami abin da yake so ba. Komai ya taba indai nasa ne to Munzali ma yana da irinsa sak. Haka ya gama loda kaya masu muguwar tsada a jakunkuna da akwatuna ya jeresu a gefe. Sai da ya gama da nasa ya soma tunanin ta ina zai fara sabuwar rayuwa? Duk abin da ya mallaka da kudin zina mafi muni ne don haka dole su rabu. To yanzu me zai ce da duniya? Yaya mutane zasu kalle shi? Da ya dauki aniyar sauya rayuwarsa sai ya ga ashe abu ne mai matukar wahala. Ashe rayuwar da ya bari lokacin yana dan shekara goma sha biyu sai bayan shekaru ashirin da hudu zai cigaba da ita. Abbati almajiri ne zai taso ya dora rayuwarsa daga inda Abbatin Munzali ya yi masa katsalandan. Abin da wuya....da matukar wuya. Shaidan ya shiga kai kawo wurin nuna masa tarin kalubalen da zai fuskanta da zarar ya sanya kafarsa a waje. Ya shawarta zuwa ya baiwa Baaba Mari hakuri akan ta barshi da iya abin da ya tara yafi a kirga amma ya fasa. Dukiyar ta haram ce. Indai ba yana so daga shi har mata da 'ya'yan da yake fatan haifa a gaba su zama cikin wadanda Allah ba zai ji kukansu ba dole ya hakura. Shaidan din yana nan amma so da addu'ar uwa sun yi matukar tasiri a zuciyarda da gaske Allah take fuskanta. Faduwa ya yi cikin sujjada domin neman karfin zuciya daga Sarkin dake jujjuya zukatan bayi.
"Ya Rabbi kada Ka barmu. Idan Ka barmu munyi asara. Allah Ka haska min hanyar da zata bulle dani kamar yadda nake fatan Ka haskawa Munzali. Duk wani abin da zai lullube mana zuciya daga barin yi maka da'a Ya Allah Ka nesantamu dashi. Ya Allah Ka jagoranci sabuwar rayuwarmu kada Ka kunyata tubanmu a duniya da lahira. Ya Allah Ka rufe sirrinmu kada Ka bari mu tozarta a idon duniya."
Adduarsa kenan. Kuma ya yita cikin kuka da kankantar da kai hade da yakinin ganin kudurar Ubangiji akan lamarinsu. Abin da Allah Ya hukunta ba zai wuce bawanSa ba. Abin bukata bai wuce tsayuwa akan imani da kyautatawa Allah zato ba.
Yana tashi sai ga wayar Baaba Mari. Sarkin da baya bacci Ya juya zuciyarta. Hakika tun bayan fitarsa da abin da Munzali ya ce ya sami takwararta sai ta rasa sukuni. Hukuncinta na rabasu tun farko domin su jidadin tuba yana nan. A matsayinta na uwa dole ne tayi duk wani abu da ta san cewa zai taimakawa danta ya tuba. Tabbas d'a na kowa ne to amma fa game da naka Allah zai fara tambayarka ranar lahira kafin na wani. Sannan yana daga cikin sharudan tuba da aka koyar da ita a Islamiyya, bawa ya nesanci wurin da yake aikata wani sab'o, ko ya canja abokai ko abin da zai kusanta shi da hakan a yayin tuba. Shin ta so kanta kenan don tana nemawarwa danta tsira daga azabar wuta? Kwalla mai zafi ta silalo mata ta share. Zuciyarta a kuntace take. Lallai ita Mari tafi uwar da 'yarta take yawon karuwanci shiga tashin hankali. Luwadi? Luwadin da Allah Yasa aka kife al'ummar Annabi guda a sanadinta amma ace dan da tayi rainon cikinsa ta haifa kuma ta shayar ita ce sana'arsa?
Kaico! 'ya'yan mutane da suke cikin wannan mummunar rayuwa ba zasu kirgu ba. Wadanda suka shigeta a matsayin sana'a ko hanyar jindadi a sanadiyar almajiranci sun ninka masu shiga a gaban iyayensu. Babu dalili komai dadin bakin mutum da za a fada mata wanda zai sa ta taba goyon bayan a cigaba da tura yara almajiranci. (Wannan gaba zaman fayyace halin da almajirai suke ciki zai iya cinye ragowar labarin namu. Na dai yi imanin cewa mun sani ko mun saba jin labarai marasa dadi akan yaran da suka tsinci kansu a nesa da iyaye da sunan neman karatu. Fatanmu Allah Yasa masu ruwa da tsaki su kawo gyaran da ya dace game da rayuwar al'ummar nan a kowane fanni.)
Munzali! Matsayin Munzali ta tuno a wurin Abbati ba rawar da ya taka a rayuwarsa ba. Lokuta babu adadi Abbati zai turo mata katin waya ko da tana dashi ya ce don Allah ta kira Munzali.
"Ki yi hira dashi Baaba irin ta uwa da danta. Ki dinga yi masa fada kina bashi shawara. Yana bukatar hakan."
Tun tana kiran bayan Abbati ya saka ta har ta koma yi a karan kanta. A duk lokacin da ta kira sai ta kara jin kaunarsa a zuciyarta. Yaro ne mai saukin kai ga wanda ya fahimce shi. Mutum ne shi wanda yake fama da k'ishin (thirst) uwa a rayuwarsa. A hirarrakinsu yana bude mata sirrinsa da damuwa akan gidansu. A dalilin haka ta yi yunkurin hada zumunci da Asabe amma abin bai yi nisa ba. Lokacin 'ya'yan nasu basu yi kudi kamar yanzu ba. Asabe ta dinga yi mata lakabi da Uwar Almajiri. Ko a waya suke gaisawa da wannan sunan take kiranta. Da aka yi masa haihuwa ya sanyawa diyarsa Mariyatul Qibdiyya kuwa kiranta tayi ta ci mata mutumci. Bata fadawa kowa ba har Abbati amma ta janye jikinta. Sai dai abin da ya sami takwararta ya mata karan tsaye. Fyade ta furta kazamar kalmar a raunane. Tufka da warwara basu barta ba sai dai tunaninta ya tsaya wuri guda. A takaice raba Abbati da Munzali ba zai zama mafita ba. Hadasu da nuna musu hanya a tare shi ne jigo.
(Wato 'yan uwa na fa sha korafi akan dalilin sanya Baaba Mari ta umarci Abbati da rabuwa da Munzali. Da yawa basu san manufar yin haka ba. Na so nuna muku hukuncin farko da iyaye kan zartarwa yaransu ne a duk lokacin da aka sami bullowar mummunan hali. Za ka sami uwar abokin barawo da son raba danta da barawon harma tana ikirarin zai bata mata d'a. Sau tari bata ma san cewa nata shi ne ya bata na wani ba. Illar rabawar musamman ga masu wayo shi ne su dinga haduwa a bayan idon uwa. Idan da zata zurfafa tunani sai ta gano matakin farko shi ne ta kokarta wurin taimakawa duka yaran da suka yi tarayya a barna. Ita da iyayensu su hada kai su gyara. A inda aka kasa samun haka sai guda daya ta gwada. Sai taga hakan ya kasa zama maslaha sannan ta canja tsari. Idan zamansu tare da fadan da nasihu yaki aiki sai a shigo da shawarar rabuwarsu. Wannan shi ne abin da naso nunawa da hukuncin farkon. Wallahu Ta'ala A'alam)
"Zo ina son ganinka"
Da sauri ya mike domin ya zata jikin ne. Ya sameta a zaune a dakinta ita kadai. Ta nuna masa wurin zama da hannu.
"Abbati na baka amanar kanka da ta Munzali. Na yarje muku zamewa juna jagora a kokarinku na inganta tuba. Na amince ku hada kai ku nemi taimakon Allah akan umarnin da na baku na rabuwa da duk wata dukiyar haram. Wallahi Abbati albarka ba za ta bi ku ba alhali kuna ci kuna sha da kudin zina. Rayuwarku za ta tafi akan tsarin da zai haskaka zukatanku ne a lokacin da ku ke cikin halalinku komai kankantarsa. Ita haram banda tarin zunubi harda kuncin zuciya take sakawa."
Ko kusa bai zata abin da zata fada masa ba kenan. A bazata mafi girma kalamanta suka dirar masa. Hawaye ya cika idanunsa har ya zubo a lokacin da ya matsa ya kama hannunta ya rike cikin nasa.
"Allahu Akbar. Allahu Akbar. Baaba kin sani cewa ban taba kokwonta akan Sarautar Allah ba amma yau na kara imani. Na roki Allah kuma hakika Ya taba zuciyarki. Na gode. Mun gode"
Hancinta ta ja ta hanyar shaka alamun kukanta bai kare ba ta murmusa.
"Allah Ya karawa Annabinmu SAW daraja."
"Amin"
"Ka bar duk abin da kake yi ka tafi Kano domin Munzali yana bukatarka. Ni shaida ce ba don matsalar da ta taso ba da tuni ya biyoka."
Abbati yaji gabansa ya fadi "akan Qibdiyya da ya ambata ne?"
Baaba Mari ta gyada kai.
"Fyade aka yi mata"
"La haula wala quwwata..." Abbati ya ce a yayinda ya yi wata irin mikewa cikin mummunan tashin hankali.
"Ka nutsu domin a yanzu kai ne kwakwalwar tunaninsa. Idan kaima ka makance babu lallai ku iya daukar matakin da ya dace. Ka tafi Allah Ya tsare."
Cikin minti goma sha biyar har ya isa tasha. Wurin mutum uku ya biya domin motar tayi saurin tashi.
****
Ana amsa sallamar Suhaib Ayaah ma sai tayi cikin muryarta da ta dusashe saboda kukan da tayi. Ba a amsa ba. Sai dai cikin abin da bai fi sakan biyar ba ilahirin jama'ar dake cikin gidan
Honourable a wannan lokaci suka tsaya a bakin kofa. Sunan Ayaah kawai ake kira ana kukan murna da hamdala. Jikin Hasiya ta fada tana kuka sosai. Kukanta ya tayar musu da hankali. Farincikin da suke yi na ganinta ya koma alhinin jin daga ina take da kuma abin da ya sami suturar jikinta.
Honourable kurawa Suhaib ido ya yi yana neman fassara yanayin da ya gansu a ciki. Matashi mai jini a jika sanye da 'yar singiletin da ta bi jiki da damatsansa. Ga 'yarsa ta suturta jikinta da rigar da ya yi imanin ta matashin ce. Me yake faruwa? Gabansa ya shiga faduwa yana fatan ba abin da yake tunani bane.
"Ya kamata mu zauna aji me yake tafe da yaron nan ko?"
Larai ce tayi magana tana janyo Ayaah daga jikin Hasiya ta rungume. Gani take ta fi kowa damuwa da son jikokin nata na wurin marigayiya A'i.
Ita dai Ayaah hawaye kawai take yi tare da yayyenta Ummita da Murja har suka shiga cikin dan falon da ba zai dauki mutanen gidan ba. Basu san me ya sami kanwar tasu ba amma hankalinsu a tashe kamar na kowa. Mazan duka suna waje. Honourable wayar Abdulkarim ya kira ya fada masa dawowar Ayaah tare da tsawaita godiya akan taimakonsu da ya yi.
Zamansu Ayaah ke da wuya sai ga Anti Hasiya da kwanukan abinci. Murja ce ta karbi tray din ta ajiye a kasa ita kuma ta koma kusa da Ayaah ta zauna. Tana zaman Ayaah ta dora kanta a cinyarta ta cigaba da kuka. Kasa daurewa tayi ta biye mata suna yi tare har sai da Innayo tayi magana.
"Kun bar mutum a waje kin zo kin sakata a gaba da kuka maimakon ki rarrasheta."
Larai ta harareta saboda so take ace ita ce mai rarrashin. Bata son duk wani abu da zai nuna Innayo ko Hasiya sun fi ta sanin me ya kamata akan jikokin. Sai cewa tayi,
"Wani irin rarrashi a wannan yanayin da ake ciki? Ai ki barta tayi kuka ko zata sami sa'ida."
A tsakar gidan kuma Honourable ne ya ce da Suhaib idan babu damuwa ya zauna zasu yi magana. Bai yi mamakin jin hakan ba shi yasa ya zauna akan tabarmar dake shimfide a wurin. Honourable ya shiga falon ya ce don Allah su fito waje amma yana son a dan jira zuwan Abdulkarim. A ganinsa yadda ya kokarta masa yau dinnan ya kashe duk lalurar gabansa ya dace shi ma ya san me ya faru. Ita dai Ayaah ji tayi kamar wata igiya ta kwance daga wuyanta zuwa kafafu. Yawun bakinta duk ya kafe ta rasa na jika lebenta ma. Rawar jiki kawai take yi saboda firgici. Da Salima ta kula da yanayinta sai ta yiwa Honourable magana cikin hikima. Mutumin da yake a tsorace bai dace idanu su yi masa yawa ba a irin wannan lokacin. Tana gudun tayi musu karya saboda rashin sakewa. Shi yasa taga gara ace mahaifinta ne kawai da Hasiya.
"Inaga duk abin da za a tattauna gara ayi a nan. A kira saurayin da ya kawota ya shigo ciki sai mu baku wuri."
Larai da 'ya'yanta sun so kin tashi sai dai Salima bata barsu ba. Musamman ma dai 'yan uwan nasu. Ai kuwa ta hau fada akan cewa a madadin uwa tafi kowa cancanta da zaman jin bayanin Ayaah da bakonta.
"Don Allah mu koma dakin yaran nan tunda ya dan fi yin ciki. Sai kuyi shawarar a can ko don bakon da bamu san ko waye ba."
Honourable ne da kansa ya yi magana saboda ya san halin Larai. Jan zance zata yi, gashi shi kuma a matse yake yaji bayani.
Da suka fito Hasiya ta nunawa Suhaib kofar falon ta ce ya shiga suna zuwa. Suna zuwa Honourable ya ce da Hasiya, Innayo da Larai zasu zauna da yaran. Sai Abdulkarim idan ya iso. Daga jin haka Larai tayi gaba tana mitar ai 'ya'yan cikinta ya kamata ya kira ba Innayo ba. Babu wanda ya ce mata komai a cikinsu. Suna zuwa bakin kofar Abdulkarim ya yi sallama ya shigo gidan suka rankaya ciki tare.
*
Suhaib ya shiga ya sami Ayaah tana faman goge hawaye da rigar jikinta-rigarsa! Haka nan yaji hakan ya zo masa a matsayin kusanci da ita. Kasa yi mata magana ya yi bayan sallamar da ya yi sai kallon yadda ta take kuka.
A nata bangaren kuma ganinsa yasa taji wani kwarin gwiwa fiye da farkon shigowarta. Wasu hawayen ta goge ta dago kai ta dube shi.
"Don Allah ka rufa min asiri kada ka fadawa su Baba abin da ya faru. Ban san me zasu yi min ba."
Kwayar idanunta wadanda suka yi jazur gami da kankancewa Suhaib ya kalla ya dan yi murmushi.
"Kada ki firgitani yadda kika firgita kanki mana. Nace ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita in sha Allahu"
Amsarsa bata bata nutsuwar da take nema ba domin ba abin da take muradi ya fada ba. Jikinta duk ya yi sanyi ta marairaice fuska.
"Kenan fada musu gaskiya zaka yi?"
"Banda gaskiya babu wani abu da zai fitar dake. Me zamu ce a matsayin dalilin da ya hadamu har na kawoki gida? Banga wani abu da zamu fada wanda zai gamsar damu kanmu ba balle su."
Bata hakura ba ta ce "Iyayena zasu ji kamar naci amanarsu. Don Allah..."
A tausashe ya ce "I will be here Ayaah. Zan yi musu bayani yadda zasu gamsu in sha Allahu."
Abubuwa taji suna shiga zuciyarta daga sautin kalaman har zuwa sakon da suke tafe dashi. Hankalinta ya dan kwanta amma tsoron bai barta ba. Turo baki tayi ganin magiyarta taki tasiri cikin