Showing 84001 words to 87000 words out of 242549 words
gefe don ma ta tabbatar babu wanda ya ji abin da ya ce. Butterflies din da take ji ana cewa suna yawo a ciki lokacin da mashin so ya harbi zuciya suka kai mata farmaki. Har ta isa motarsu gabanta yana faduwa sannan tana murmushi.
Zamanta ke da wuya Suhaib ya kirata yana tambayar ko likitan ya iso.
"Ka manta ance sai karfe tara?"
"Hala bacci ne ya daukeki a motar? Duba wayarki."
Hannu ta kai ta rufe bakinta "ahhh" ta ce da mamaki. Tara da minti ashirin. Bata san minti nawa tayi a dakin Abbati ba. Gani take kamar suna fita ita ma ta fito.
Abbati bai san lokacin da murmushinsa ya kara cika annurin fuskarsa ba. Shi kadai a daki bakinsa yaki rufuwa. Sake kiransa aka yi ya duba yaga Mal. Sa'idu ne. Yana amsawa yaji ya ce.
"Kirani" da sigar umarni.
Shi yake saka masa kudi amma baya taba kiransa. Kullum haka yake yi idan yana bukatar magana dashi.
"Gwoggwonka Deluwa ta ce tun jiya take kiranka baka amsa ba kuma baka bi kiran ba."
Girgiza kai Abbati ya yi. Mal. Sa'idu ya dawo da gadara da umarninsa kansa kwanakin nan. Da dai sai lallabawa saboda abin hannu. Bai san me ya faru ba abin ya canja zani.
"Ina asibiti a kwance ne."
"Ai hoo..amma dai tunda ka iya amsa wayar na san jikin da sauki."
Muryar Deluwa ya ji tana cewa "kayi sauri kayi masa maganar"
Shi kuma Mal. Sa'adu ya ce "anjima zaka tura tasha a dauko 'Yashshafa. Yanzu za ta taho ta dinga kamawa 'yar uwarta ayyukan gida tunda ita ba haihuwa take ba balle ta sami mataimaki."
Maganar ta daure masa kai sosai. Yanzu ya fara fahimtar sabuwar gadarar kawun nasa. Ya san ba zai taba yarda ba ace 'Yashshafa ta zo. Amma a haka ana magana da iko dole ya amince. Ransa a bace kuwa ya ce
"Kawu nace maka ina kwance a asibiti. Sannan a Kaduna nake ba Kano ba. Ku kira Hanne ta tura a daukota."
Yana kaiwa nan ya katse kiran ya bar Mal. Sa'adu da waya a hannu.
"Wai a kira Hanne shi ba ya gari" ya ce da Deluwa da ta dame shi da tambaya.
"Shi ba zai je ba? Malam ka ga illar saken da ka yiwa yaron nan da ya yi kudi ko? Yanzu waye zai kira Hanne taje ta daukota?" Sai kuma ta zauna dabas a gefensa "Malam ita ma Hannen motar gareta? Ya sanar da kai kafin ya saya? Kaga irinta ko? Allah kadai Ya san me da me ya mallakawa yarinyar nan." Sai da ta dan dakata taga yanayin tasirin maganarta a fuskarsa sannan ta cigaba da cewa "kar ka ga kamar na damu ko bakinciki. Ko kadan ba shi bane a raina. Danku ne Abbati. Yana ta faman hidima babu magaji ga raini da tayi masa. Na tabbata babu mai bashi kulawa sama da jininka. 'Yashshafan dai ita ce daidai dashi."
"Ki barni dasu daga shi har Hannen da iyayensu babu wanda ya isa ya ketare maganata. Zan daina yi masa sako-sako saboda ya gane kudinsa ba zai sa na karbi raini ba."
Dariya tayi muryar nan ta fito kamar ta-macen kozon kwad'o.
"Me zai hana kawai a samo mota ko Buba (mijin Habi kanwar Abbati) ya kaimu kuma ba za a biya shi ba tunda Abbatin ne ya saya masa yake haya. Kaga ni da 'Yashshafa da uwarsa sai mu je can inda yake asibitin? Dole ya karbe mu da kyau darajar Mari. Daga can sai mu tafi Kanon. In mun kwan biyu mu taho mu barta a can har su saba?"
"Ku tafi ku kadai. Mari ba kirki gareta ba. Da wuya ta bari a bar 'Yashshafa a can."
"Ai kuwa dole mu hada da ita. Shakiyin yaro ne kana ganinsa ba karamin aikinsa bane yasa a juyo damu muna isa."
Wuka da nama ya bar mata a hannunta. Tana tashi taje ta samu 'Yashshafa har ta gama shiri. Fuskar nan ta dau kwalliya kamar fatalwa za ta zance. Sanar da ita canjin da aka samu na tafiya tayi sannan suka rankaya bangaren Baaba Mari.
*
Bata dade da dawowa daga makarantar islamiyar da ta shiga ba ta matan aure. Ajinta daya amma bata damu ba. Ta mayar da hankali sosai wurin neman ilimi. A karatun da take ne ta fahimci ashe ba karamin jahilci suka rayu ciki ba. Shi yasa ta tasa 'ya'yanta a gaba da izinin mazajensu suke zuwa. Abbati ya gyara sorayen da ake karatun saboda ba ginanniyar makaranta bace. Dalilin zuwanta makarantar ne yasa ta tashi tsaye akan yiwa 'ya'yanta addu'a musamman Abbati. Ta rasa menene game da sana'arsa ya tsaya mata a wuya. Daidai da rana daya bata taba jin gamsuwa game da arzikinsa ba. Dare daya Allah kan yi bature inji Hausawa. To amma komai yana da sila. Silar arzikinsa kuma bata sani ba!
Yau sun dawo da wuri saboda hutun da aka basu na sati biyu. Ta kama hijabi za ta cire kenan taji muryar Deluwa tana kuka. Labule ta daga za ta duba suka ci karo tayi baya.
Kuka Deluwa take harda majina "mun banu mun lalace. Mun shiga ukun mu. Wayyo Allah.."
"Lafiya Deluwa? Ba kyau irin wannan kukan fa. Mutuwa aka yi ne?"
'Ai fa tunda kika fara zuwa makarantar nan muke ganin sanabe' ta ce a zuci. Sai da ta fyace hanci babu dadin sauraro sannan ta ce
"Abbati ne."
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Hanjin cikin Baaba Mari ya cure wuri guda saboda fargaba. Jikinta duk ya saki. Deluwa ta dinga dariya a zuci.
"Mari kar ki sume min mana. Rashin lafiya ce ta kama shi yana wani asibiti a Kaduna. Ki shirya don Malam ya ce yanzu zamu tafi."
Tafiya yanzu yanzu daga jin labarin rashin lafiya? Sai hankakinta ya kara tashi. Takalmin da ta cire ta mayar ko hijabin islamiyar bata cire ba ta fito. Tana son kiran Abbatin ma amma babu kowa kusa da zai nemo mata nambar a kira. Ita kuma ba iya karatu tayi ba.
Mal. Sa'adu ya sanar da mutanen gidan halin da ake ciki. Da Baba Inuwa ya ce zai bisu sai ya ce ya bari tunda ga Buba tare dasu. Su ma ya amince su tafi ne saboda ganin hankalin Baaba Mari ya tashi. Tana ji tana gani yayi wannan karyar amma sai ta kyale tunda bata san manufarsu ba. Ta nemi su Atine su biyo su Mal. Sa'adu ya ce wai za a takura mazajensu. Sai kawai Buba ya ce da Habi ta taho su tafi tare. Su Deluwa dai ba haka aka so ba amma gudun kar a gano su ko ace menene dalilin tafiya da 'Yashshafa sai ta kama bakinta.
Cikin awa daya suka dauki hanyar Kaduna. 'Yashshafa doki da murna kamar bakinta ya yage. Deluwa tamkar mai zuwa Makkah. Banda garuruwan kusa dasu bata taba zuwa ko'ina ba. Kanon ma Allah bai yi zata je ganin daular Abbati ba. Baaba Mari da Habi ne kadai cikin damuwa sai Buba.
Sun sha tafiya kamar ba za ta kare ba. Jikin kowa ya yi la'asar. Wuraren tara na dare suka iso garin Kaduna. Sannan ne kuma Deluwa ta ce 'Yashshafa ta kira mata Hanne.
"Latso min ita inji ko tayi mana girki. Yunwa nake ji kamar naci babu. Duk 'ya yame yamen da muka yi a hanya ba rikeni suka yi ba."
"Gida garesu a nan din da zata yi girki? Ba suna asibiti ba?" Cewar Baaba Mari.
"In basu da gida ba sai ta aika a siyo ba. Ni naga sai wani gani-gani kike min don na taho duba danki."
Baaba Mari sai ta ki magana. Ko babu komai Buba surikinta ne.
"A wane asibitin yake na tambayar mana kwatance?" Inji Buba
Deluwa ce ta amshe da cewa "yanzu dai ai kya bari a kira Hannen ko?"
Ita Baaba Mari ba waya. Habi ma babu duk sun barosu a gida. Abbati ya yi ta kiranta amma dama bai yi niyar fadin yana asibiti ba kada hankalinta ya tashi. Kullum dai suna waya shi yasa yayi ta kira bai samu ba. Ya nemi Atine ita ta fada masa suna hanya. Ita ma din sai yamma ya kirata. Ransa ya yi matukar baci kuwa.
"Akan me zai taso min uwa tayi wannan doguwar tafiyar? Yanzu ina zan kaisu su kwana? Me zasu ci?"
Yake ce da Munzali cikin bacin rai. Gashi bai samu sallamar ba ance sai gobe saboda ya kara hutawa. Tun yamman suke kiran Buba basu samu ba saboda rashin network a hanya har dan cajin nasa ya kare.
'Yashshafa ce ta kira Hanne. Tana zaune a falo ta ajiye tray din kayan marmari tana dauka ta yanka da 'yar wukarta ta kai baki. Bata san nambar ba haka nan ta dauka tana yatsina.
"Hello"
Deluwa ta ce "ke ni ba shalo ba gaya min sunan asibitin gamu nan mun shigo gari. Kuma da uwarmijinki muke a tanadi abinci ko don ita."
Hanne sai ta mike tsaye da sauri.
"Gwaggo Deluwa wane asibitin?"
"Kuji min lusara. Inda mijinki yake kwance mana."
"Kai Gwaggo Deluwa ko dai kun yi batan kai ne? Shi fa ya tafi Abuja tun jiya."
"Da ya tafi baku yi shalo dashi ba?"
"Ya kirani dazu ya ce min baya jindadi to amma ban ji batun asibiti ba."
Deluwa an sami yadda ake so "an gaisheki tinkiya uwar tambele. Mijinki ya kwan a gadon asibiti baki sani ba. Ya kira ya fada miki baki bada hankali kin saurara ba. Ungo 'Yashshafa latso min Abbatin"
Hanne na jin sunan 'Yashshafa bata san lokacin da ta kifar da farantin gabanta ba. Wato da ita aka tafi bayan ta gama sanin kudirinsu. Abbati ta kira harda kukanta.
"Wallahi gobe zan taho nima. Ai dazu baka ce min kana asibiti ba-"
Kashe wayarsa ya yi saboda takaicinta. Yana cikin fada mata ta ce wai tayi baki daga makota. Kafin ya farga ta katse kiran kuma bata sake a bi ta kansa ba. Deluwa tasa aka kira shi ya ce da Buba ya sami mai adaidaita sahu ta musu jagora zuwa asibitin.
Tun yamman Munzali ya kama musu dakuna a guest inn din da Suhaib ya nuna masa. Sannan ya siyo abin ci da abin sha ya ajiye musu. Suna isowa shi ya fita ya biya mai adaidaita sahun sannan ya kaisu dakin da Abbati yake.
"Sannunku Baaba kun sha hanya."
Murmushi tayi "kai ma kana ta fama da jinya Munzali. Allah Ya kara hada kawunanku."
"Amin amin. Ai Yaya Munzali ba daga nan ba." Cewar 'Yashshafa wai ita mai abokin miji.
Ganin alamun wahala, yunwa da gajiya a tattare da Baaba Mari ya sa Abbati jin kwalla a idanunsa. Tsanar Mal Sa'adu kuwa ta karu a ransa. Banda son zuciya ba maza ne ya kamata su zo ba idan ma sai an taho?
"Ina bayi (toilet) yake ne? Marata cike take taf" Deluwa ta ce tana dukawa saboda matsuwa. Munzali ya nuna mata kofar ta fada a guje.
"Baaba ya hanya? Habi harda ke a wannan wahalar?" Abbati ya ce yana kirkiro murmushi.
"Alhamdulillahi. Ya jikin naka?"
"Da sauki."
Zai fara korafin zuwansu ta girgiza kai sai ya yi shiru. Bai yarda ma sun dade ba yace su tafi masauki.
Deluwa na jin haka ta kada baki ta ce "To ke 'Yashshafa a tafi dake kuwa ke da ki ka taho jinyar dan 'uwanki?" Ta dubi Munzali " A gida baka ga kuka ba duk tabi ta tayar da hankalinta. Indai da wurin kwanan mata tayi zamanta don na san kukan za ta dameni dashi cikin dare. Ni kuwa na gaji ina bukatar hutu...hehhhehh" tayi wata dariya mara fasali.
Tsabar takaici Baaba Mari sai cewa tayi "Munzali zo ka kaimu. Ke ma Deluwa idan nan za ki kwana sai ku kwana tare da ita."
Fita tayi kawai Habi ta biyo bayanta. Deluwa jiki a sabule ita ma ta fito. Tana kuma ji Abbati ya ce da 'Yashshafa "ke ba za ki tafi ba sai na zo na sameki a nan wurin?"
Turo baki tayi irin na marasa kunya, ya yunkura kamar zai taso ta fice da sauri. Abin nasu yana neman wuce gona da iri ya koma hauka. Wace irin kwakwalwa ce da Deluwa da za ta ce 'yarta ta kwana jinyarsa kamar a garin mahaukata? Ko Habi ai ba za ta kwana ba balle ita.
Daki guda Munzali ya kamawa Baaba Mari. Habi da Buba daya sai su Deluwa a guda.
"Nima daya nake so don 'Yashshafa bata iya kwanciya ba duk sai ta bubbuge mutum." Ta ce dashi fuska a hade.
Da yake shi ma kwararre ne sai ya miko mata hannu.
Diriricewa tayi ta kalli Baaba Mari sannan ta ce masa "Me za ayi?"
"Kudin dakin da zan kama miki za ki kawo. Dubu ashirin da biyar ne kwana daya."
Sai ta hau hargagi don a bar maganar "Ashirin da biyar? Dakin aljannah ne? Barshi kawai zan kwana da Mari."
"Ita Baaba umarnin Abbati nake bi. Ya ce ta kwana daki daya saboda an saka ta tafiyar dole."
Babu wata magana da suka yi da Abbati. Hasali ma bai san komai game da inda ya kama musu ba. Sanin halinta ne yasa ya zabi raba musu wurin kwana.
Ba dai haka taso ba don tana tunanin ko abincin dakin Baaba Mari yafi wanda aka ajiye musu shi yasa taso komawa can. Tunda babu fuska sai ta rungumi abin da ya samu. Da Munzali ya koma asibitin yana bashi labarin yadda suka yi da ita suka dinga dariya.
"Amma wane daki ne dubu ashirin da biyar? Babban hotel ne?"
"Guest inn ne. Dubu goma ne fa"
Dariya suka sake yi sannan Abbati ya bashi labarin hirarsa ta dazu da Farha wadda bai samu sun yi ba saboda jin tahowar su Baaba Mari.
***
"Yaushe rabonki da hutawa Hasiya?"
Honourable ne ke maganar yana bubbuga mata kafadunta da suka rike saboda dukawa yin lalle.
Murmushi tayi. Ita kanta ta san cewa ta gaji. Yau ciwon wuya, gobe kafada, jibi kai. Ga rashin isasshen bacci. Tana tsakar fama da zuwa gida saboda lamarin Zara yau kuma manemin Ummita ya aiko cewa iyayensa zasu zo sati mai zuwa. Ita da kanta take ganin cewa da gaske sawun Innayo take bi. Wahala da fadi tashi tun farkon aure. Kila gobe hutun yazo, kila kuma wahalar goben tafi ta yau. Allah Masani. Ta dai san ba kowa ke da rabon jindadi a wannan rudaddiyar duniyar da zunubi ya yi mata kanta ba. Fatan bawa bai wuce samun dacewa da cin jarabawa a duk yadda tazo ba.
"Ina hutu ga mai shirin aurar da 'ya?"
Sai yaji nauyi a zuciyarsa. Tunda ta aure shi take wahala da 'ya'yansa ba gajiyawa.
"Ina jin kunyarki Hasiya. Abin da ki ke kawowa domin tafiyar da gidan nan yafi nawa yawa. Sai yanzu nake sake ganin wauta ta. Dama ance don tuwon gobe ake wanke tukunya. Ban san a gaba zaki maye gurbin A'i ba. Lokacin da nake da wadata ban damu da me yake faruwa a gidan nan ba balle na gyara. Allah Yasa Innayo ta yafewa A'i.."
"Ta yafe mata tuntuni."
"Nifa? Ni da ban san girmanta ba sai da na aureki. Gashi ko da wuka ba zan taba barinki ba" Dariya maganar tasa ta bata suka yi tare.
"Allah Ya yi miki albarka maman Ayaah."
Kallon yanayinta ya yi ko za ta canja fuska sai ya ga ta sake murmushi.
"Mun zama abin tsokana ko?"
"Ai na rasa me ya kamata muyi mata kuma ta dawo hanya. Ina jiye mata kar tayi irin nawa. Sai a gaba idan Allah Ya sanya samuwar farincikinta a tattare da wani abu naki tazo tana bin bango yadda nake yi a gaban Innayo."
Hasiya bata da zabin da ya wuce bushewa da dariya. Ranar har suka kwanta tana tsokanarsa da Honourable Mai bin bango. Yana jindadin ganin ya faranta mata saboda iyakar abin da yake iya yi mata kenan. Akwai abin da yake ta fafutukar samu. Ba dai ya son fada mata ne kada ta saka rai kuma bukata taki biya. Gobe zai koma wurin mutumin ko za a dace.
*
"Dama kira nayi mu gaisa." Ayaah ta ce da karamar murya tana wani murmushi tamkar yana ganinta.
Danladi ya yi juyi akan katifarsa yana harba kafafu cike da farinciki. Dama shi kadai ne a gidan matarsa ta tafi unguwa. Saboda haka zai sake ya gillawa Ayaah karya son rai.
"Thank you Ayaah. Wannan wayar ta shigo a lokacinnda nake tsananin bukatar mai sauraron damuwata ya bani shawara."
Daga magana kawai ta fuskanci rauni da damuwarsa ta yanayin fitar muryarsa.
"Me yake faruwa."
Numfashi ya ja da karfi wanda ya sake dagula mata lissafi.
"Amanata zan baki Ayaah. Ban san me yasa nake jin zan iya yarda dake ba."
Kamar za tayi kuka don yanayinsa duk ya karyar mata da zuciya ta ce "ba zan cutar da kai ba Danny. Ka fada min abin da ke damunka."
Sake salon muryarsa ya yi yadda ya san zai kara janyo tausayinsa gareta sannan ya ce
"Bana jindadin aurena Ayaah. Auren soyayya muka yi amma na rasa kulawa ta kowacce fanni" ('yan mata a kula!)
'Yar dariya tayi. Wannan mata tamkar tana share mata waje ne. Tunda ita bata iya rikon abin da take dashi ba kwatarsa a hannunta ba zai mata wuya ba. Wayancewa tayi taki nuna maitarta a fili.
"Ku fa maza haka kuke. Baku da aiki sai korafi akanmu. Ni dai ina bayan Antina don na san ba za tayi laifi ba"
"Don dai baki san zaman da muke bane. Duk girman gidan nan kishi ya hanata daukar maaiki. Ita kuma taki gyarawa. Abinci kuwa tafi ganewa na siyo a waje. Rabona da cin abincin gidan an kwana biyu. Yanzu ma ta fice tun safe ko ruwan zafi bata bar min ba. Kodayake laifin Mum ne. Tun muna yara an cika mana gida da Kuku masu aiki. Da ace ta koya mana duk da muna maza hakan ba za ta faru ba. Da Mum tana da rai wallahi babu macen da ta isa ta tauye min rayuwa haka."
Ayaah sai kwallah, sai kuka wanda Danny ya zaci duk a cikin tausayinsa ne. Nan kuwa mahaifiyar da bata gama sani ba take tunawa. Karyar Danny sai ta kara masa kusanci da zuciyarta domin ba karamin tausayi ya bata ba.
"Yanzu kana nufin baka ci abinci ba tun safe?"
"To me zan ci? Ga freezer cike da nama. Na kasa cire ko kulli daya da sai ki koya min yadda zan yi ko dan peppersoup ne."
"Ba don kada ka ce nayi maka shishshigi ba da nace ka zo bayan kafin Isha. Sai dai kuma ban sani ba ko kana iya cin abincin