Showing 15001 words to 18000 words out of 242549 words
gaji da barnar kudi wurin zubar miki da ciki."
Dalilinsu daya na biyewa wannan kazamar rayuwa. Uba ya mutu ya barsu da bashi babu gadon komai sai gidan da shima ya gada a wurin nasa iyayen. Danginsa sun yi kokarin taimakawa Ladidi wurin raba 'ya'yan su rike taki amincewa. Ita so tayi su dinga bata kudi bayan suma din babu mai katabus. Girman zumunci ne ma yasa su wannan yunkurin. Ta zauna babu abin da ke shigo mata sai kawai ta nunawa 'ya'yanta cewa dangin babansu basa kaunarsu ne. Ita kuma nata dangin suna kauye ba zuwa za tayi ta zauna ba. 'Ya'yan ne jarinta tunda suna da kyaun fuska da daukar hankali duk talaucinsu. Babbar bata biyewa Ladidi ba. Tafi duka kannenta kyau da kyaun hali. Aurenta tayi a Kaura Namoda tana dan aikowa Ladidi abin da ya samu. Nasima ce ta dasa dan ba a fitina sai mai bi mata ita ma ta fara yawo yanzu.
Fuska biyu ta kwararrun munafukai Nasima take nunawa a gidan. Khadija bata ganin wata kofar zargi sai gabanin dawowarta gidan tayata zama da ta fara yi mata rashin kunya. Tahir kuwa sai da yaji duk duniya babu macen da zuciyarsa ke kauna sama da ita. Da kananun shekaru ta kware a barikanci. Sai ya zo wucewa sai ta dinga bude jiki da dabara.
"Wayyo kadangare"
Ta dinga ihu watarana da Khadija ta fita cikin sauri da Farha ta kusan hadiyar kwankwalatin kwalbar fanta. Asibiti ta tafi kaita ta bar Nasima dasu Lilu a gida. Da yake makira ce tana jin dirin motar Tahir ta turasu daki. Yana bude kofar ta saki zanin tana tsalle-tsalle.
"Kadangare ne a zanina" ta ce da kukan kissa tana makale masa a jiki.
Tahir an sami abin da ake so ya matso yana cewa ta tsaya ya duba mata. Ya tabbatar Khadija bata gida tunda ta iya yi masa haka. Bai yi kasa a gwiwa ba ya biye mata tunda dama jira yake. Ranar ya fara kaita dakin Khadija yaci mutumcin aurensa a cikin gidansa. Sai da suka fito suna murmushi yake tambayarta inda Khadija take.
Kwabe fuska tayi ta soma kikkifta idanu. Muryarta ta karyar kamar mai shirin kuka.
"Tun yanzu ka fara nuna min iya matsayina."
Jikinsa ya janyota "Me nayi?"
"Yanzu yanzu fa kake tambayata matarka. Wato na gama nawa amfanin."
Ganin tana hawaye gabadaya sai hankalinsa ya tashi. Rarrashinta ya dinga yi da kalamai masu dadi sannan ya dauki kudi ya damka mata. A fakaice tayi murmushin mugunta sannan ta maida masa kudin aljihunsa.
"Ni ba kudinka nake so ba."
Wani irin dadi ya mamaye zuciyarsa jin ba shi kadai yake hauka ba. Aljihunsa tas ya zazzage ya bata duka kudaden dake ciki. Suna wannan yanayin Suhaib ya fado falon daga dakinsu yana kiranta.
"Inata nemanki Anti. Lilu ne na kasa cire masa belt ya yi kashi a wando."
Da azamarta ta mike tana murmushi "Liluna kenan. Yau dai yana min shagwaba son rai." Sai da ta juyawa Tahir baya ta cigaba da magana "Ta wata kakarmu ta ce duk yaron da ya wuce shekara guda yana kashi a wando uwarsa tayi asara."
Juyawa tayi suka hada ido da Tahir ta dora da cewa "ka san mutanenmu na kauye ba dai iya zagi ba da raina kokarin mutum ba. Shi Lilu ma da yake karami babu wani a gabansa."
Tafiya tayi ta barshi yana juya zancen a zuciyarsa. Yafi sau biyar zai iya tunawa da Lilu ke yi a wando. Amma duka lokutan dukan gaske Khadija ta yi masa. Yayyensa babu wanda ya yi haka. Sai zuciyarsa ke bashi ko ta fara gazawa a tarbiya ne.
Yana zaune Khadija ta shigo da Farha a bayanta. Da dankwalin kanta ta goyota saboda ta sha wahala. An ciro kwankwalatin da ya karce mata makwogaro sannan anyi mata allurai. Da sauri ya tashi yana tambayarta ina taje.
Wani irin kallo tayi masa na mamaki sai yaji kamar ta fahimci halin da yake ciki.
"Nasima bata fada maka abin da ya faru ba?" Ta ce tana shigewa daki ta kwantar da da ita akan gado. Ganinsa tayi a yamutse ba yadda ta barshi ba ta dawo falo tana labarta masa abin da ya faru. Tashi ya yi zai koma duba Farhan yana jin babu dadi da tsautsayin da ya sameta ya bashi kofar cin amanar mahaifiyarta. Zai daga labule Nasima ta fito tare dasu Suhaib. Khadija ta tashi ta kama kunnuwansu ta murde kowannensu ya saki kara.
"Ban hanaku tsalle akan gado ba? Kuna ganin tsautsayin da ya sami Farha baku tsoron ku fado."
Sai da gaban Tahir ya fadi ya kasa karasawa ciki. Yana jin Lilu ya fara rantsuwar basu bane ya juyo ya musu abin da bai taba ba. Marinsu ya yi duk su biyun saboda tsoron kada ta yarda dasu ta fara zargin wani abu.
"Ba zan yarda da rashin kunya ba. Maminku tana magana kuna karyata ta. Idan ba ku ba waye zai hau gadon ya yi mata tsalle? Na sake ji ko gani sai na zaneku. Ku wuce ku bani wuri."
Da kuka suka bar falon. Khadija tayi mamakin daukar zafinsa haka. Ta dade tana rokonsa ya dinga taimaka mata akan kwabar yaran idan sun yi laifi ya ki har ta hakura. Da ta biye masa da yanzu sun gama sangarcewa. Yau da laifin ba mai girma bane a idonta sai gashi ya yi musu marin da ko ita aka yiwa sai ta rike kumatu. Ba dai ta ce komai ba ta bar wurin. Da Nasima za ta tafi ta tambayeta me yasa bata fada masa inda taje ba.
"Naji kin ce Farha amma ban ji sauran maganar ba Anti. Wani abin ne ya faru?" Ta tambayeta tana rarraba idanu.
"Baki sani ba fa ki ka ce?"
"Anti ko dai nayi laifine? Kiyi hakuri."
Khadija bata ce komai ba. Sai yanzu ta tuna Nasima tana wurin abin ya faru amma bata juyo ba.
"Allah Ya kyauta" kawai ta iya cewa saboda rashin sanin matakin dauka ta bar zancen.
A haduwar Nasima da Tahir ta gaba ce tayi masa kukan da ya karyar masa da zuciya.
"Na san za ka yi mamakin ganin ni ba budurwa bace. Ba zan maka karya ba da kaina na sayar da mutumcina. Talauci da yunwa sunyi mana yawa. Babu mai son taimakonmu. Da mutane suka gane cewa zan iya komai domin ciyar da mahaifiyata da kanne shi ne maza suka fara nemana. Na san cewa kaima kana cikinsu amma ba yadda zanyi saboda albashina ba zai ishemu ba."
Daga ranar ya bude mata bakin aljihu sai yadda tayi. So yake ya nuna mata yafi sauran mazan. Kudi kam bata da matsalarsu. Tahir kuma ita take juya akalarsa. Khadija sun maida ta hoto suna badakalarsu a gidan bata sani ba. Kiyayyar da yake nunawa Nasima ta zame mata katangar hana hango komai a tsakaninsu. To gashi yanzu anyi aure!
***
"Mari kin ji labarin ana neman masu casa a gidan Sarkin Noma?"
Audugar da Mari take kadawa ta ajiye ta kalli kawarta Tasalla da murmushin da yafi kama da dariya.
"Ki bari don Annabi."
"Yasin da gaske nake. Wannan karon ina tsammanin mata sai sun cika tsakar gidan saboda alherin da ya yi bara."
Tsam Mari ta tashi ta shiga daki ta dauko mayafi. Tasalla tana ta tsokanarta wai ladan aikinta wannan karon harda amaryarta zasu ci.
"Ko Malam in fada miki sai dai kallo. Yaran nan zan rabewa in je in dubosu." Kwalla ce ta taho mata ta goge da habar mayafinta "Har mafarkin Sani nake Tasalla. Ya yi kankanta sosai da bara. Ga Abbati kin dai san halinsa. Duk inda ya shiga raina shi ake yi. Ba zan taba yafewa Mal Sa'adu ba."
Da sauri Tasalla ta dora hannu a bakinta "bari fada kar a ji. Wan mijinki ne fa."
"Wan miji ai ba uban miji bane. Don baki ji yadda nake nadamar haihuwar mazan ba. Da mata ne wa ya isa ya tura su almajiranci?"
"Kul Mari. Ba'a yiwa Allah tawaye akan haihuwa." Cewar Tasalla.
"Astangafirullah" Mari ta ce da sauri tare da yin tofi a gefe na neman barranta daga zunubin kalamanta.
Sun yi sa'ar samun gurbi cikin mata goman da ake nema suyi aikin casar shinkafa da masara a gidan Sarkin Noma. Mari kason mutum biyu take karba ta wuni tana aiki. Banda wannan ta cigaba da dinkinta duk da kuwa ba wani mai tsada bane ga bashi a wurin mutanen kauye. Haka take musu dinkin ta shafawa idanunta toka sai an biyata kudinta. Tuni tayi suna kuwa. Ana cewa bata da lamuni wurin kudi amma ta iya dinki. Duk abin da ta samu sayayya take yiwa Abbati da Sani. Yaran dake gabanta ba komai take basu ba saboda ganin suna gaban mahaifinsu.
Bayan sati uku ta nemi izinin Inuwa za ta je Zaria da Kano ganin 'ya'yanta. Shi kuma ya sanar da Mal Sa'adu. Nan da nan zance ya zagaye gidan aka yi ta aibata ta. Sauran matan babu wadda ta taba zuwa ganin nata. Idan lokacin komawarsu gida ya yi ana basu hutu su tafi su taimakawa iyayensu musamman da damina.
"Wai ke Mari kanki aka fara haihuwa ko naki kadai aka kai almajiranci? Wannan rashin ta ido har ina?" Mai bin Mal Sa'adu ya ce da ita yana muzurai.
Inna Mairo ce ta kawo mata dauki wannan karon.
"Bana son bakin hali. Kun dauke yaran yanzu meye aibunta don ta ce zata ganinsu? Na rantse da za'a jarabceku da laulayin kwana daya kafin ma ayi batun nakuda bana jin da mai yarda dansa ya matsa ko nan da zaure. Ba ita ba ma duk mai so a barta taje ta ga nata."
Ashe sauran ma suna so baki da zuciyar yi Mari ta fisu. Faccalolinta da suke da yara a wasu garuruwan kowacce sai ta fara shiri. Ba lokaci daya zasu je ba saboda kada a bar gidan babu mata. Kaya niki-niki haka Mari ta hadawa su Abbati. Don karfin hali harda shinkafa, kwan zabi da garin kunu. Da ta tashi kuma ta yiwa iyalan malamansu tasu tsarabar.
Zabinta hudu ta tafi dasu suka fara wucewa Zaria ita da dan rakiyarta dan wajen kanwarsu Inuwa. Duhun dare ya kawo kai suka isa unguwar da makarantar take. A cikin layin sun yi arba da almajirai sun fi goma. Yawancinsu duk daga bara suka dawo da abincinsu. Can gabansu suke hango kura tana tashi ga ihun yara da alama dambe ake yi.
Yayin da dan rakiyarta ya yi tsaki ita ido ta zuba tana tausayin yaran da karancin gata ya sa rayuwarsu walagigi irin haka.
Yaro daya ne a kasa guda uku na tumurmusarsa. Baka jin komai sai kukansa gami da tsinuwa da zagin da yake aika musu. Sauri Mari ta kara da niyar ta isa ta rabasu sai ga wani gardi (babba cikin almajiran) da dorina. Yana zuwa ya shiga sambada musu kan mai uwa da wabi. Ji kake taf-taf ga ihun yaran suna sosa inda bulalar ta sauka. Na kwancen da ya kasa tashi ya fi tafka. Ya kuma daga hannu zai zuba masa Mari ta gane ko waye. Babu wanda zai ce ga lokacin da ta motsa kafa sai ganinta suka yi ta duka ta rufe Sani. Bulalar a gadon bayanta ta sauka ta gantsare kwalla mai zafi tana taruwa a idonta.
"Baaba?" Sani ya ce da mamakin da ya gauraya da murna.
Da ka ta amsa shi saboda radadin dukan nan. Ya kuwa kankameta yana kukan dadi. Almajiran da suke wurin suka ruga ana rige rigen fadawa Malam abin da ya faru.
Ita dai Mari daga Sani tayi tana karkade masa jiki. Farinwata ya haska mata shi da kyau taga yadda ya rame kamar ba shi ba. Ya sake kankancewa sai kai shirim kamar ya kumbura. Lebensa sama da kasa a kumbure sannan karshen lebban ta kowane bari ga alamun ciwo. Wurin duk ya tsattsage. Su kauyawa ne amma ba kazamai ba. Zuciyarta tana kunci ta dauke shi yana ta warin rashin wanka. Nan kuma taji abu ya karci hannunta. Ta shafa kafarsa da kyau taji wani mummunan faso da ya mamaye 'yar kafar. Bata ma san ina za ta nufa ba a lokacin sai ga malamin makarantar tasu ya taho yana baza babbar riga.
"Baiwar Allah daga ina? Ance kin yi rabon fada tsakanin dalibai na." Kula ya yi da Sani da ta dauka ya rungume wuyanta da 'yan hannayensa ya daka masa tsawa "to tambadadde daga ganin mata ka makale mata. Ai sai ka sauko tunda ba uwar da ta sallamoka daga kauye bace." Ya mayar da hankalinsa ga Mari yana dan murmushi "haka muke fama fa. Iyaye mata kamar basu san zafin haihuwa ba. Yara da kananun shekaru a kawo a jibge mana. Ba kuma wani kudin azo a gani suke biya ba. Shi wannan ma dai mai idon mayun sam bai kwanta min ba. Kar ki raina kuruciyarsa hatsabibin gaske ne."
Ta so ace wadannan kalaman a kunnen Mal Sa'adu ake fadarsu ya ji da kyau ba ita ba. 'Ya'yan da suke haifa cikin gumi da jini ke irin wannan rayuwar kuma laifinsu ake gani. Zuciyarta ke bugawa da karfi tana son bashi amsa amma tana hango laifin nasu da ya fada.
"Don Allah zamu sami masauki zuwa wayewar gari." Mari ta katse surutun da yake ta yi da wannan tambaya.
Kallonta ya yi sama da kasa tare da dan rakiyarta ya girgiza kai. Haka kawai a wannan zamani da ake fama da 'yan yankan kai bai ga dalilin saukar bakuwar da bai sani ba.
"Sai dai nasa a raka ki gidan Mai Unguwa."
"Nagode, ina kayan Sani suke mu dauka?"
"Baiwar Allah wai daga ina kike ne?" Ganin karfin halinta ya yi na son satar dan mutane a gabansa.
"Mahaifiyar Sani ce daga Kirikasamma. In Allah Ya so ka bar ganin mai idanun mayu kamar yadda ka kira shi daga yau."
Kunya mai tsanani ce ta rufe Malamin. Gidansa ya tafi dasu yasa iyalinsa suyi musu abinci. Da aka kawo ko hannu bata saka ba sai da ta kula Sani yana ta kallo ta janyo kwanon. A baki ta bashi ya ci ya koshi. Ta fita wanke hannu kafin ta dawo bacci ya dauke shi. Shafa shi ta dinga yi tana hawaye. Wai wannan ne Saninta. Yaro mai kiba da kuzari duk ya lalace.
Kayan Sani duka sunyi datti ga wari. Wando da riga ta samu tun asuba ta roki sabulu ta wanke masa. Da yake ana zafi sosai kafin su tashi tafiya sun bushe. Da kanta tayi masa wanka ta dirje masa jiki. Suna shan koko taji ana cewa yaran da suka yi masa duka jiya biyu cikinsu sun kwana suna zawo. Ana tsammanin abincin da suke fadan a kai lalatacce ne.
"Sani ka ci abincin?" Ta tambaye shi hankali a tashe.
"Loma daya nayi suka kwace."
'Kemis zan fara zuwa na saya masa ja da yalo kafin muje tasha' ta ayyana a zuci. Da zasu tafi bata fasa ba ta ajiye musu tsarabar da ta kawo. Neman magani ta dinga yi ido rufe amma bata sami kemis ba sai a tashar ta sayi maganin zawo a wurin wani mai tallan magunguna. Irinsu kemis guda ne a kansu suna sayar da kusan kowane irin magani na bukatar yau da gobe. Ita ba ilimin abin ba haka zalika mai maganin ma sayarwa kawai yake yi. Haka ya hado mata magunguna kala biyar wai duka na zawo da ciwon ciki. Filagil kadai ta gane sai magnesium na ruwa da ake girgizawa kafin a sha. Sauran kuwa kafinol ne hade da boscopon da panadol extra. Burinta kada wani abu ya sami danta saboda haka kai tsaye ta bashi na ruwan.
Hakura tayi da zuwa ganin Abbati zata koma gida har sai Sani ya dan murmure. A hanya ya soma ciwon ciki yana ta amai. Daga baya sai zawo duk ya fita hayyacinsa. Shi yake ciwon amma Mari ke kuka. Sauran fasinjoji kuma suka dinga hantararsu saboda wari ya ishesu. Babu wanda ya san lalurar da ta kawosu wannan matsayi aka dinga cin mutumcin 'yan kauye a gaban idonsu.
Kafin su isa Kirikasamma Sani ya fara sankamewa idanunsa a waje gwanin ban tausayi. Mari tayi kuka har muryarta ta dashe wurin yi masa sannu.
"Baaba cikina zai tsinke ki kara min magani."
Sam ta manta da magungunan da ta saya ai kuwa ta roki ruwa a wurin wata da ta kulla a farar leda. Ta ballo bibbiyu kowanne kamar yadda mai maganin ya ce mata ta bashi.
Cikin zakuwa take tambayarsa "Ka fara jin sauki?"
"Eh" ya amsa idanunsa suna kakkafewa.
A zaton Mari bacci ne. Rungume shi tayi tana dan jijjiga shi har rai yayi halinsa bata sani ba. Ashe rabon su gana ne ya kaita Zaria. Da zasu fita daga motar wata ta ce mata jikinsa kamar ya saki.
Da murmushi ta ce "bacci ya samu."
Goya shi tayi ta dauko wasu kayayyakin. Sauran kuma dan rakiyarta ya dauka suka dauki hanyar gida a kafa. Lokaci lokaci take gyara goyon ta yi masa sannu. Rashin amsawarsa a wurinta saboda bacci ne.
Sun kusa isa gida ta hango Inuwa a majalisarsu ta karkashin bishiyar darbejiya. Mamakin dawowarta a yau yayi tunda kwana uku ta ce za ta yi. Silifas dinsa ya zura ya taso da sauri da ya fahimci goyo tayi.
"Ba dai Sani kika dauko ba Mari? Me kike so na cewa Malam?"
"Maganar ba ta hanya bace ka bari muje gida. Bashi da lafiya ba zan iya barin shi a can ba."
Dan murmushi ya yi sanin cewa ita ma akwai taurin kai. Yana son yin yadda take so amma ba zai iya sabawa yayansa ba.
"To kwanto min shi na dauke shi naga kema a gajiye kike."
Ba musu ta kwance goyon Inuwa ya tare zai saba shi a kafada yaji yanayin jikin wani iri. Mutum biyu cikin abokansa suka taso jin ba'asi ganin ana kwance goyo.
"Sani ne jikin ba dadi ta taho dashi gida." Inuwa ya fada musu.
"To kawo shi mana ka tayata da sauran kayan."
Mijin Tasalla ne Lukumanu ya karbe shi sai ya dago shi da sauri jin ya tafi baki daya. Hannunsa na rawa ya ce,
"Sani. Sani bude ido..."
Mari sai ta tsaya tana son cewa bacci yake taga duk sun rufa a kansa ana jijjiga shi. Inuwa da karfi yake kiransa jikinsa yana tsuma.
"Sai dai hakuri Inuwa amma Sani ya amsa kira."
Kalaman Lukumanu kenan da suka shiga kunnuwan Mari. Duniyar tsayawa tayi cak bata iya tuna komai sai ranar da ta haife shi. Ranar da