Showing 90001 words to 93000 words out of 242549 words

Chapter 31 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3374

tayi daban daban. Jambakinta kuwa purple ne an zagaye shi da jar jagira. Abin dai sai godiya kawai. A son ranta Abbati ya karbi tukin sai ta shiga gaba. Sauran su taru a motar Buba. Deluwa da Baaba Mari suna motar Munzali a baya. Abbati yana gefensa suna ji ya gama waya da Suhaib wanda ya ce su je asibitin Doctors Haven yana jiransu a waje. Da isarsu kuwa suka hango shi a mota ya tayar su kuma suna bin bayansa.

Maganar Munzali game da kayan jikinsa ta dawowa Abbati ya dubi Munzali wanda hankalinsa yake titi don kada Suhaib ya bace masa. Yadi ne a jikinsa wanda yasa domin tsokana ga Abbati.

"Idan mun je ka zauna a mota kawai"

Munzali ya karkace kai ya ce "saboda?"

"Saboda na isa. Ko so ka ke a dinga yabonka shigarka ace tawa bata yi ba?" ya bashi amsa.

Dan waigawa baya Munzali ya yi ya ce da Baaba Mari "ki shiga tsakanina da mutumin nan. Cin zalina yake yi duk sanda ya sami dama."

Dariya suka bata ta murmusa "haka dai ku ka iya kamar kananan yara."

"Haba Baaba ina da kamar Qibdiyya ki ke ce min yaro?" Inji Abbati

"A baki ba! Kodayake gara ma kai wannan karon. Kai kuwa Munzali dama taraka nake yi. Kai baka mayar da mahaifiyar Mariya (sunan gaskiyarta take kiran Qibdiyya) ba kuma baka nemi wata ba..."

Caraf Deluwa wadda tun dazu take neman shiga hirar ta ce "shi ma Abbatin ai sammakal. Har ma gara Munzali tunda ya ajiye kwai duniya ta shaida. Kai kuwa ka ajiye juya a gida bata komai sai ta ci ta sha tayi kashi. Ai Mari aure ya kamata ya kara ko Allah zai sa ya sami magaji."

"Ku ne 'yan birni. Me ya kamata mu kaiwa mutanen nan ne a matsayin tukwicin kyautatawarsu?" Baaba Mari tayi tambayar ga 'ya'yanta tana mai kawar da kai ga maganar Deluwa a karo na uku. Ranta yana baci ne idan tayi maganganunta to amma bata son ta biye mata. Yin hakan zai zubar musu da kima a idanun 'ya'yansu da wadanda suke tare. Ba ta son tayi abin da ko da wasa Buba zai gorantawa Habi idan sabanin yau da gobe ya hada shi da ita. Sannan ga Munzali da uwa uba 'Yashshafa wadda tayi imanin komai rashin kan gadonta, idan taga ana saitawa mahaifiyarta zama sai taji babu dadi.

Abbati ne ya amsa mata da cewa sai dai su ajiye musu kudi tunda sun riga sun biyo bayan Suhaib babu damar tsayuwa. Ita kuma ta ce ba kowa ke karbar kudi ba siyayyar za ta fi. Basu ankara ba suna shawara sai gani suka yi Suhaib ya saka trafficator ta bangaren dama. Munzali sai ya ce mata kada ta damu in Allah Ya yarda zasu kawo tukwicin ko ba yau ba.

Deluwa aka hangame baki da kofofin hanci ana kallon tafkeken gida irin wanda bata taba gani ba. To Baaba Mari ma dai sai da taji faduwar gaba. Masu kudi irin haka ne suka taimakawa danta. Anya in sun san cewa su kauyawa ne zasu kallesu ma kuwa?

"Baaba fito mana"

Muryar Abbati ce ta katse mata tunanin da bata san ma ta dulmiya a duniyar yinsa ba. Shi ma kuma suna fitowar hada ido suka yi da Munzali kowanne ya jinjina kai. Basa bukatar furta zantukan da zukatansu suke yi. Maganar daya ce tak. Gidan nan yafi karfinsu.

*

"Ya Farha sun iso."

Cikinta ya sake bada sauti bayan na farko da ya yi lokacin da taji an bude gate. Waskewa tayi don jikinta har wani dan rawa yake yi kamar mai shirin kamuwa da masassara.

"To kuma sai aka ce idan sun zo ki fada min? Bakin Mami ne ki je ki sanar da ita mana."

Sauda ta kama dariya "gani nayi wai kin sha wahalar yi musu girki."

Farha ta sha kunu "to biyana za su yi?"

"Eh mana. Ko dan murmushi aka cillo miki na san za ki kwana kina juyi." Tana kare magana ta fita da sauri kafin Farha ta iskota.

A can waje bangaren da aka yi domin ajiye motoci Mama Nasima ce za ta shiga motarta. Mardiyya tana gefenta ta dauko mata jaka. Suna wurin su Abbati suka shigo. Suhaib ya ajiye motarsa a inda ya saba sannan ya tafi inda suka tsaya baya kadan dashi suna jiransa. Kamar da wasa Mama Nasima ta kalli bakin da take tunanin na makiyarta ne sai idanunta suka sauka akan Munzali sannan Abbati.

Motar da bata shiga ba kenan ta bude baki ta soma cewa "Alh. Munzali" kamar ita ta rada masa sunan.

Su duka suka waiga har ta karaso wurin tana kallon mutanen da suka zo tare.

Kan Mardiyya ta dungure wadda tana jin ta kira sunan Munzali hankalinta ya tashi ta biyo bayanta.

"Wai yarinyar nan sai yanzu take fada min kuna tafe kuma harda manyanka. Shi ne fa na fito da kaina zan tarbeku." Ta dubi su Baaba Mari jikinta a dan sanyaye da yanayinsu da ya fallasa rangwamen wayewa a tare dasu. "Sannunku da zuwa Inna." Suka amsa fuska a sake don basu san wurin wa suka zo ba dama.

Mardiyya tayi karfin halin cewa "Mama ba fa..."

"Wuce muje ki hado musu juice sannan ki dora abu mai sauki (bata taba daukar mai-aiki ba saboda gudun kar a ramawa kura aniyarta)."

Duk abin da ake yi Munzali kallon Mardiyya yake wadda idanuwanta suka cicciko da kwalla. Tana magana hawaye na kokarin sauka.

"Mama kinga tare da Ya Suhaib..."

Munzali sai ya girgiza kai da sauri saboda fahimtar halin da mahaifiyarta ta sakata. Irin wannan ai ba bakonsa bane tunda ya tashi a gaban Asabe.

"Abbati ku je da Suhaib zan shigo daga baya."

Mama Nasima ta yamutsa fuska tana hararar Suhaib "au, kun sansu ne?"

Hanya kawai Suhaib ya nunawa su Abbati "Bismillah muje."

Abbati sai ya kalli Mardiyya ya yi mata alama da tayi murmushi ga Munzali nan. Murmushin kuwa tayi ya hado da zubowar hawaye.

"Mama muje dama zan kawo miki karar Diamond girl"

Munzali ya ce domin kawar da hankalin Mama Nasima daga kansu Abbati. Ai kuwa ya yi nasara domin yana kiran 'yarta Diamond girl ta soma dariya.

"Yaran yanzu ba kwa kunyar kowa. Duk da dai kamar ma zamu yi sa'anni da kai Alhaji. Amma babu komai. Aure babu inda ba ya kai mutum. Abbanta ya girmeni sosai. Kusan kamar kai da ita."

Kallon ban hakuri Mardiyya take yi masa. Shi kuma ya nuna mata ko kadan bai shiga damuwa ba. Da ido kadai yake karfafa mata gwiwa har taji saukin zuciyarta akan abin da mahaifiyarta tayi. Basu sani ba ashe kallonsu Mama Nasima take. Ta sake kallon motar da Munzalin ya tuko taji sanyi a ranta. Watanni kalilan suka ragewa Mardiyya da Sauda su gama secondary. Ranar jarabawar karshe in sha Allahu za ayi kamun 'yarta. Aurar da ita zata yi ga kamilallan mutum ko hankalinta ya kwanta. Bangaren zuciyarta da bai manta rayuwarta da ta mahaifin Mardiyya ta baya ba yana cike fal da tsoron kada wata rana kaddara ta giftawa tilon 'yarta.

Suna shiga falonta ta yar da mayafi akan kujera ta fada kitchen. Sai lokacin Mardiyya ta iya yi masa magana.

"Ni wallahi ban ma san me zan ce maka ba. Don Allah kayi hakuri."

Kashe mata ido ya yi fuskarsa a sake ya ce "Kar ki damu Diamond girl. Ina jin fa gara wannan maman tamu akan wadda na baro a Kano."

Abin sai yaje mata bambarakwai. A iya saninta mahaifiyarta ce kadai me wannan halin.

"Da gaske?"

"Zan kaiki ki ganta sai ki tabbatar."

'Yar dariya tayi, yaji wani irin sanyi a ruhinsa sai da ya kai ga lumshe ido. Kamar da wasa ya cewa Abbati zai nemeta sai dai bai taba zaton zai ji komai a ransa ba game da ita. Ya zata tausayi ne kawai...

"Ka kaini ka ce mata wa? Bamu da 'yan uwa a Kano na san ma Abba ba zai bari muje ba."

Muryar Mama Nasima suka ji tana cewa "kina nan kin saka shi a gaba da zance maimakon ki biyoni kitchen ko? Wannan ni kike son ki tozarta a zaci ban miki tarbiyya ba. Alh. Munzali sai kayi hakuri fa. Matar taka akwai kuruciya ga autanci yana damunta."

Tamkar Mardiyya ta nutse a kasa don kunyar mahaifiyarta. Sai gashi Munzali ya kara mata da cewa "kinji Mama ta bada amsar idan na kaiki Kano da wane suna zan gabatar dake ga iyaye da 'yan uwana."

*
"Sannunku da zuwa. Sannunku. Ku zauna don Allah"

Mami Khadija kenan take yiwa su Baaba Mari barka da zuwa cike da fara'a da kyautatawa. Baaba ta saki fuska ita kuwa Deluwa duk ta gigice da sanyin falon. Haushin shareta da Baaba Mari ta dinga yi ya bace a lokacin. Suhaib take kallo tana sake kallon zinariyar 'yarta wani abu yana darsuwa a zuciyarta.

"Shafa'a (tana jin kamar idan ta kara 'tu' din sunan zai yi kauyanci) koma motar ki shigo da kwanukan da suka yi ta mana hidima dasu mana."

'Yashshafa ta tashi ta fara zumbura baki sai ji tayi Deluwa ta ce da Suhaib "Sha'aib rakata kaji dan albarka."

Abbati ya harbo jirgin ya ce 'Allah Ya 'yantani' a ransa sannan ya mike kafin ta sake magana.

"Muje na tayaki."

Deluwa ta hade rai kamar ta rufe shi da duka. Sanda taso ya kula 'yarta yaki, yanzu ta sami wani zata cusawa yana neman hana ruwa gudu.

'Yashshafa tayi waje tana ta karairaya sai ka rantse kugunta bai zauna daidai ba. Abbati ya tabe baki yana dariya a ransa. Banda rigimar Deluwa daga ganin mutum ta fara tunanin hada shi da 'yarta. Kafin ta karasa kunyatasu gara ma suyi su bar gidan. Sai da suka isa jikin motar Suhaib ya fito ya karbi mukullin motar Abbati dake asibiti. Lilu zai dauko a gidansu abokinsa sai ya kai shi ya dauko motar. Bakin Abbati baya gajiya da yi musu godiya. Bayan ya tafi ne ya mikowa 'Yashshafa tissue.

"Goge fuskarki kafin mu koma. Da ace naga wannan adon bararojin tun kafin mu fito ba zan yardi ki biyomu a haka ba."

"Ni dai gaskiya Yaya Abbati ka bar min kayana ina so. Duk wata mace da ta amsa sunanta yanzu sai da me-uf (make up)."

Magana zai sake yi mata kawai ya hango Farha ta fito daga wata kofa da bata da nisa da wadda suka fito. Doguwar rigar atampa ce a jikinta sai mayafin mai kauri wanda ta dora a ka ba tare da ta saka dankwali ba. Bata san ya ganta ba tayi saurin buya a bayan wasu fulawoyi masu tsayi da suka cike tazarar dake tsakanin bangarensu da na Mami Khadija.

Kwando daya ya mika mata ya ce "jeki, iyaka dai duk wanda ya yi mafarkin fuskarki a gidan nan yau alhaki a kanki."

Tana soma tafiya ya hango Farha ta kuma lekawa sannan ta buya a zatonta tare zasu koma ciki. Har ya lallabo ta gefen bangaren Mami Khadija ya tsaya a bayanta bata sani ba. Kallonta ya dinga yi kamar babu kowa a duniya sai su kadai.

Farha da bata san yana wurin ba ta sake lekawa sai bata ga kowa ba. Sauke ajiyar zuciya tayi kanta cunkushe da tarin tambayoyi. Bata san ma'anar wannan bakon yanayi da take tsintar kanta game da Abbati ba. Sai tuhumar zuciyarta ma da take yi wurin azalzalarta da yawan tunaninsa.

Kafa ta daga za ta bar wurin ta bangaren nasu dakin Abbati ya yi mata magana da sauri.

"Abin da muke buyarwa din har ya tafi ne?"

Ba karamin tsorata tayi ba harda ja baya. Tabbas taji kamshin turare mai ratsa zuciya amma bata kawo cewa a bayanta mai shi yake ba. Ga kunya ga kuma mamakin yadda yazo wurin bata sani ba, basarwa tayi ta ce masa,

"Me kake yi a nan?"

Takowa ya dinga yi a hankali zuwa inda take. Ta rufe ido har ya karaso domin tamkar a tsakiyar kanta take jin sautin duk takunsa.

"Naga kin buya ne shi ne nima na taho kar abin da kike gudu ya kamani."

Tura baki tayi don ta boye kunyar da ta kama ta ta ce "babu abin da nake gudu ni."

"Da gaske? To ko ni ki ke kallo?"

Ba shiri ta daga kai ta zuba masa kyawawan idanunta "me zai sani kallonka?"

Hannuwansa duka biyu suna aljihun wando, ya jikina da bango ya dubeta da kyau kafin ya ce

"Nima haka nacewa kaina. Me zai sa ki kallona?"

Karkata kai tayi ta dan kalli yanayinsa da ido daya sai taji babu dadi.
"Wai haushi kaji?"

Shi da zai yi fushin wasa tana neman saka shi dariya. Da kalma daya ya amsa mata kada dariyar ta subuce masa
"Eh"

Farha ta sake ware idanu wanda ya fahimci tana yin hakan cikin mamaki ko tsoro. Yadda yake ji a ransa a lokacin zai iya rantsuwa babu wanda ya taba son wata mace kwatankwacin yadda yake jin Farha a ransa.

"Fushin gaske ko na wasa?"

Ya marairaice mata fuska "na gaske mana. Abbati bashi da abin da zai sa Ya Farha ta kalle shi ai dole in ji babu dadi."

"Ni yaushe nace maka haka?" Ta fada hankalinta yana neman tashi. Abbati kuwa kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda ya amince ba haukansa yake shi kadai ba.

"Kin yarda ni ki ke kallon? Uhmm?"

Yadda ya tsareta da ido sai taji kamar tayi tsuntsuwa ta bar wurin. Motarsu ta nuna da hannu ta fice daga wurin yana bin bayanta.

"Motar nan nake kallo ina tunanin kafin ku fito na zo na dauki hoto..."

"Cewa za ki yi baki manta alkawarinmu ba. Ina fata baki manta ba?"

Ko kadan bakinta da zuciya basa son yi masa musu. Sai dai bata saba ba sannan tana jin kunya. Kofar bangaren Mami ta kalla ta ce,

"Zan kirga goma duk wanda ya fara fitowa shi zai daukemu. Idan na gama ba a fito ba sai dai ka hakura."

"Na yarda. Bari na taya ki kirgawa."

Idanunsu akan kofar ta fara kiran 'daya' yana tayata. Suna kaiwa shida ya ce a sake wai da sauri take yi. Haka nan ta amince saboda bata son ta fara bada kanta a gabansa. Ta fahimci nan gaba kadan za ta kasa jurewa rashin kallonsa da ta tilasta kanta.

"Daya, da digo daya, digo biyu, digo..."

"Wannan kirgen naka ya sunansa?"

"Farhan Abbati style" ya fada kai tsaye yana yi mata wanu irin kallo. Kai ta sunkuyar ba tare da ta bashi amsa ba. Ya kawo ido ya zuba mata yana ta doka murmushi.

"Yaya Abbati ka zo in ji Mooomina"

'Yashshafa ce ta fito tana wannan tafiyar irin ta wanda ya sha da kyar daga kamuwa da cutar shan inna. Haushi ya kama shi na yadda ta bata daddadan moment dinsa da Farha.

"Mominki kuma 'Yash..."

"Shafa'a. Suna na Shafa'a" ta gabatar da kanta ga Farha da sauri kafin ya karasa fadin sunanta.

Abbati ya kada kai ya ce "to Shafa'a wace momin ke kirana?"

Ta san ya gane yake son bada ita a gaban wannan kyakkyawar matar.

"Moomina dai da muka zo tare."

Sai ya yi kamar lokacin ya fahimta "Au wai Gwaggo Deluwa?"

'Yashshafa ta juya a fusace ta bar wurin tana buga kafa don takaici.

Farha sai da tayi dariya sannan ta ce masa "baka kyauta ba. Ka fahimceta amma ka nuna baka gane ba?"

"Laifin naki ne don ke take son burgewa. Haka kawai muna 'yan kauyenmu don ta ganki ta fara kiran Innarta da Moomi" ya kuma fada yadda 'Yashshafan take cewa.

Farha dai hannu ta sa ta kare bakinta tana dariya kasa kasa.

"Kana da abin dariya" ta ce a hankali da suka shiga falon Mami Khadija daga bakin kofa.

"Zan yi komai domin ganin dariyarki Ya Farha. Idan kin bani damar zama abokin raba duk wani yanayi da za ki tsinci kanki daga yau har karshen rayuwarki ga mahaifiyata can..." ya nuna Baaba Mari wadda suke hira da Mami Khadija tamkar sun dade da sanin juna "zuwanki gabanta ku gaisa shi ne zai tabbatar min da cewa wannan Ya Farha Farhata ce"

A hankali ya yi maganar daidai jinta domin ita ce a gaba yana biye da ita a baya. Kalamansa sun fito da sigar roko, tararrabin rashin samun karbuwa da zallar soyayya. A duniyar Farha bata taba shiga yanayi makamancin wannan ba. Idan haka ake soyayya bata fatan ta sake yiwa kowa bayan Abbati. Wucewa ciki tayi ba tare da ta juya ko ta amsa masa da baki ba. Maimakon ta wuce ta damanta inda zai fi saurin sadata da Baaba Mari sai ta zaga ta hagu. Abbati yaji kamar ana ajiye masa duwatsu a zuciyarsa don tsoro. Sai da ta gama ja masa rai sannan tayi takun karshe ta zube a gaban Baaba Mari.

Sama sama yake jin muryoyinsu suna gaisawa. Farinciki ya mamaye zuciyarsa har yana neman yi masa yawa. Inda ya tashi ya je zai zauna waya ta shigo masa. Bakuwar namba ya gani ya dauka da sallama. Muryar wani da bai gane ba yaji.

"Idan kai ne Abbati ina tare da matarka ta ce sunnanta...ke ya ma sunanki?"

"Hanne" ya ji muryarta tar tana bada amsa.

"Yauwa Hanne. Wai wayarta babu chaji tana nan tashar Kawo ka tura a daukota. Sannan ta ci shinkafa da miya a wurin Esther, ni kuma ta sha lemo da ruwa a shagona. Kudin da ake binta dubu daya da dari uku ta ce za ka biya."

Ransa in ya yi dubu kuwa ya baci. Me yasa za ta wulakanta shi haka? Banda tahowa ba da izininsa ba harda cin abinci a tasha...kuma bashi!

Tashi ya yi bayan ya fadawa mutumin cewa gashi nan zuwa.

"Ina za ka je mu da muke jiranka mu kama hanya?" Baaba Mari ta tambaye shi.

"Wane irin kama hanya ko ruwa baku sha ba balle aci abinci? Don Allah ku zauna. Sauda duba ki gani idan plates din zasu isa." Inji Mami Khadija tana tashi.

Sai Abbati ya mata bayani a takaice "Baaba ku zauna Hanne zan dauko a tasha wai yanzu ta iso. Idan na dawo sai ku fito mu tafi." Ta gane ransa a bace yake sai ta ce masa sai ya dawo. Ta san zai yi mata bayanin komai idan sun kebe.

Yana daf da fita Mami Khadija ta ce "ba dai wata 'yar uwar taku bace ta iso? Allah Yaso baku kama hanya ba da kunyi sabani."

Deluwa fadi ba a tambayeka ba tayi tsagal ta ce "matarsa ce."

Bai gama fita ba saboda haka yaji abin da ta ce. Tsayuwar dole ce ta kama shi ya waigo a hankali yana neman idanun Farha domin ya gane tasirin maganar aurensa gareta.

***

Anti Hasiya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login