Showing 87001 words to 90000 words out of 242549 words

Chapter 30 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3362

talakawa."

Danladi ya yi wata super a katifarsa ya kankame waya. Wannan yarinyar ba zai dauki lokaci wurin samun kanta ba.

"Ayaah kar ki wahalar da kanki."

"Sai dai idan ka raina abincinmu."

"Zan zo Ayaah. Thank you very much."

Ranar Murja ce ya kamata tayi girkin dare amma Ayaah sai ta ce za ta yi. Naira dubu biyu ta fitar cikin kudin hular turban da ta fara sayarwa ta je tayi cefanen kayan miya. Ta hado da kayan salad da balangun dari biyar wanda ta boye cikin riga. Sannan ta biya wani shago can hanyar titi ta karbo bashin foodflask mai kyau guda daya dan madaidaici. Irin mai mazubin miyar nan a ciki.

"Ayaah yau take sallah ne? Ina kika sami kudi nan haka?" Ummita ta tambayeta da ta ganta tana gyaran kayan miya.

"Wallahi ribar huluna ne nace yau dai bari muci dadi."

"Allah Ya amfana Ayaah Ya karo ciniki."
Hasiya ta ce da taji me suke tattaunawa.

"Amin" ta amsa ta cigaba da aikinta sai kuma ta ce "uhmm Anti in debi shinkafa ko na dafa taliya?"

"Duk wanda ya yi miki. Shinkafar tana da dan yawa za ta ishemu girki uku ma." Da zuciya daya taji dadin sauyin da ta gani wurin Ayaah. Ba wai na siyan kayan miya ba. Yadda take magana da girmamawa babu wannan tsiwar.

Daren ranar shinkafa da miya suka ci harda salad. Honourable ya bayar aka siyo kifi kowa yaci. Abinci yaji maggi kowa ya dinga santi. Yana tafiya sallar Magariba ta dauko flask din da ta zubawa Danladi abincinsa ta watsa balangun a cikin miyar. Yanka daya kawai ta jefa a baki ta maida yawu. Salad din ta zuba a farar leda don kar ya jike akan shinkafar. A bakar leda ta saka ta daure ta kai soro ba tare da kowa ya gani ba ta ajiye can jikin bango. Wurin da duhu babu wanda ya lura.

Ta san mahaifinta sai bayan isha zai dawo shi yasa ta ce ya zo kafin ishar. Ana idar da magariba kuwa taji wayarsa. Sulalewa tayi don kowa yana daki wasu ma basu idar ba. Ta dauki ledar ta mika masa.

"Naga duk ka fad'a."

Ya yi murmushi mai ciwo kamar gaske "ba dole ba. Damuwa ce tayi min yawa harda irin wadda bai kamata na fada miki ba. Sunan ina da aure ne kawai Ayaah amma gwauraye da yawa sun fini gata."

Sai taji kamar tayi kuka. Ga mutum cikakke ya sha kananan kaya da gani masu tsada ne. Soronsu kuwa sai kamshi yake kamar anyi barin turare amma rayuwar gidansa ba dadi.

"Ka kara hakuri komai mai wucewa ne."

Flask din ya dan jijjiga yaji da nauyinsa. Yawunsa ya tsinke tun bai bude ba. Ji yake kamar ya tashi sama ya ganshi a dakin Rabilu inda zasu ci su gyatse kafin ya tafi gida. Surutan tausayin da Ayaah take masa duk suka gundure shi. Ana idar da sallar ishar taji anyi sallama ta sallame shi. Bata sa rai sosai ba amma a zatonta zai bata tukwicin wahalarta.

"Karshenta sai ya dawo da filas din zai min kyautar godiya" tace da kanta lokacin da take komawa cikin gida.


I just published "18" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/thKZS9SmObb



UWA UWACE...18



Batul Mamman💖


Allahummagfir li hayyina wa mayyitina....
A madadin daukacin 'yan group din UWA UWACE muna mika sakon ta'aziyyarmu ga 'yan uwanmu da suka yi rashin iyaye. Meena Parrot (mahaifi) da Amina Abdullahi Shu'aib (mahaifiya). Muna rokon Allah Ya jikansu Ya kyautata makwacinsu. Mu kuma Ya bamu kyakkyawan karshe.
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~Amin


***

"Habibu ya maganar Agent dinnan? Naga har yanzu baka ce min komai ba."

"Uwani kenan. Tsakaninmu da watan Hajji akwai watanni 5 kwarara."

Hankalinta bai kwanta ba. Ta gaji da gafara sa bata ga kaho ba. Wata uku da bayar da kudinta na kujerar Hajji amma har yau bata ga komai na shaida ba. Habibu mutuminta ne tun farkon fara aikinta a asibitin. Shi yake mata shige da fice duk lokacin da aka turo mata transfer ta cigaba da zama a Sir Sunusi. Ta riga ta kafa ta tsare. A nan take cin kasuwarta. Sai mace ta haihu ta ce ta tafi gida za ta zo tayi mata dinki mai kyau a can.

"Yawancin yaran nurses dinnan duk lalata muku jiki suke in an zo wata haihuwar sai an kara budeku. Indai ba ni nazo karbar haihuwarki ba kada ku yarda ayi muku dinki ko kun karu. Ga nambata ki nemeni da an sallameki sai ki kwatanta min gidanki nazo nayi miki. Dubu shabiyar ne amma ina miki rantsuwa mijinki ma sai ya gode min ba ke ba."

Tsarin hudubarta kenan tun a wurin awo. Irin matan da ta yiwa dinki a gida basu kirguwa. Da yake kuma ta kware din sai matan suke turo 'yan uwa da kawayensu. Kasuwa ta bude mata sosai a waje. Manyan mata ko basu haihu ba suna neman Metron Uwani ta gyarasu. Ana iya cewa wannan shi ne babbar silar samun kudinta fiye da na aikin asibitin. Matan masu kudi tana yi musu suji dadi ayi mata ihsani mai tsoka. Ga karbar haihuwa da take yi a waje. Duk wata Nos da ta san sirrinta ta nemi tona mata asiri bata kara sati biyu Habibu zai tsaya har sai an yi mata transfer.

"Yanzu sai yaushe zan sa rai? Gobe sunan kanwata. Kuma a son raina inje musu da zancen Hajjin yadda duk wani dan bakinciki sai dai ya hadiyi zuciya wallahi (tana fada, fuskar Hasiya take hangowa)"

"Kice dai 'yan bani na iya basu barki ba har yau."

Nan ta labarta masa haihuwar Zara da komai. Sirrinta da na 'yan uwanta da ya sani wani ma ya tabbata ta manta anyi.

"Ina kuma shi na gaban motar" ya tambayeta mijinta yana kyalkyala dariyar raini gareshi.

Uwani ta yi guntun tsaki, "wa yake ta wannan? Wai ni zai kalla ya ce in biya kudin makarantar yara bashi. Ya kwashe kudi yana ta uban gini, bayan na san karshenta da amarya zamu tare. Gani mahaukaciya in biya a gaba mu zo muna babatu. Nima kuma ba kudin nan gareni ba."

"Uwani sarkin babu. Ki daina kiranta wallahi kada ta shammaceki."

Harara ta doka masa "Allah Ya kiyaye. Ni babu ai garkuwa ce a wurina. Masu saka ido akan arzikin da Allah Yayi min sai dai su gaji su mayar da kwadayinsu."

"Allah Ya bar min ke Matron...au, au, Hajiya Uwani ya kamata na fara kiranki fa."

Wata shewa tayi cike da jindadi ta sabi jakarta.
"Don Allah Habibu ka maida hankali in zo na fara shiri. Bana so a fara bita ina gida."

"Kwantar da hankalinki Hajiya Uwani. Bana kam sai dai na ce Allah Yasa maqabuliya ce."

Tana tada mota ya buga uban tsaki ya gyara kwanciyarsa akan benci kasan bishiya. Shegen kudin nata ma ko albarka babu. Ko da wuka ba ya ce ga wani abin azo a gani da ya yi dasu ba sun bi ruwa sun bi iska. Rigima bata kisa bare ya tsorata ranar da kwai zai fashe.


***
Washe-garin zuwan su Baaba Mari Kaduna Mami Khadija ta sake aika abinci asibiti. Banda wanda su Farha suka tafi dashi da safe Suhaib ya kai na rana. Sannan yaji Abbati da Munzali suna tattaunawa game da tahowar su Baaba Mari. Iya abin da ya fahimta shi ne 'yan uwan Abbati sun taho kuma bashi da kowa da zai saukesu a nan. Ya koma gida da niyar fadawa Mami Khadija amma bata dawo daga wurin aiki ba sai bayan isha. Ta biya gidansu ne akan shirin bikin autansu da ake yi. Tana dawowa ya fada mata.

Kallonsa tayi da kyau ta kada kai "yanzu Suhaib maimakon ka kirani tun dazu sai yanzu da dare ya yi?"

"Yanzu ban burge ba? Cewa za ki yi nayi wauta ko?" Ya tambayeta yana tsuke baki.

Dariya tayi kafin ta amsa masa "ta ina ka burge? Kuma banda wauta da ka kirani ai zan ce ka tuntubesu ko suna bukatar taimako. Ba ka ce ka karbi nambobinsu shi da dan uwansa ba? Kira dayansu mu ji me zamu iya yi musu."

Da ya kira Munzali ya sanar dashi ya kama musu dakuna a Guest Inn din da ya raka shi da safe. Sannan ya riga ya sayi abinci. Suka yi sallama cikin aminci suna masu nanata godiyarsu a gare shi.

Mami Khadija tana da wani ajin da safe ranar, saboda haka sammakon tashin Sauda tayi. Mardiyya ta kwana a bangaren Nasima, dama ta saba yi mata haka tun a wancan gidan. Idan ta je wurinta kusan raba dare suke tana bugun cikinta domin ta san me da me Mami Khadija da 'ya'yanta suke ciki. Tunda da wayonta sai kawai take biye mata tayi ta hada mata zantukan da basu da kan gado tana fada.

Tsomen doya da kwai Sauda tayi wanda ya gajiyar da ita saboda yawansa. Mamin tasu tayi farfesun kaza sannan mai-aikinta ta dafa tea aka zuba a flask din gida sai na asibiti da na 'yan uwan Abbati. Ga kuma bread an hada musu dashi.

Bayan sun gama a gajiye Sauda take cewa "Mami wai waye a asibitin ne? Jiya da shekaranjiya ma an kai ga na yau kamar masu tarbar baki."

" 'Yan uwanki basu fada miki mutumin da suka gani a asibiti mara lafiya ba?"

Da dokinta ta ce "Sun fada ban san shi ake kaiwa ba" sannan ta hau bata labarin abin da ya faru kafin ta dawo gidan "Ai jiya kafin ki dawo ne Ya Farha ta fada mana ashe wanda muka yi hoto jikin motarsu ne a plazar su Mama...Mami zo ki ga ihu wurin Ya Lilu wai mutumin ya burge shi."

"Rabani da wannan mashiriricin. Karasa hada kowanne yadda na nuna miki ki taso Suhaib tunda shi ya san dakin da mara lafiyar yake."

Tsabar son ganin kwaf Sauda ta ce "Mami ki ce yaje dani don Allah. Sai na daukar masa basket din."

"A dawo lafiya. Idan ki ka yi masa rawar kai ya make ki" Mami Khadija ta furta tana yin gaba ta fita daga kitchen din.

Kafin goma na safe sun kai abincin dakin Abbati wanda ganin Suhaib ya saka masa rai da sake ganin Farha. Da ya ga fuska daban bai nuna rashin jindadinsa ba sai aikin godiya. Haka kuma Munzali ya musu rakiya har dakin Baaba Mari.

Wannan abu ya yi mata dadi fiye da zato da tsammani. Ta dinga yi musu kyawawan addu'o'i. Wani bangare na zuciyarta yana haska mata cewa karshenta Abbatinta mutumin kirki ne sabanin zarginta. Mutanen kwarai basa rasa mataimaki a inda basa zato.

A matsayinta na uwa haka yafi komai yi mata dadi. Babu mai son rab'a danta da mummunan abu ko yaya yake sai dole. Babu wata uwa dake duka ko yiwa danta fada domin rashin so. A takaice ma tsabar soyayyar ke janyowa mu dinga kwab'ar 'ya'yanmu domin su zama nagari. Habi ta saka ta dibar musu abincin sannan ta ce ta kai ragowar dakin su Deluwa. Sai da suka ci suka koshi sannan Munzali ya daukesu suka tafi asibitin. Suna zuwa ana sallamarsa.

"Baaba za ki iya sake kwanan inda na kai ku jiya ko mu kama hanyar Kano idan mun yi azahar?"

Munzali ne ya tambayi Baaba Mari bayan sun gama gaisawa da Abbati an harhada kaya.

"Mu tafi din dai zai fi."

Deluwa taji zai bata mata shiri don so tayi su kara kwanaki ko biyu ne ta cusawa Abbati 'Yashshafa kafin su tafi Kanon. A gidansa Hanne za ta iya hana ruwa gudu.

"Kai dai wannan yaro da zakalkalewa ka ke? Ai dai ka bari wadda ta fika iko dashi tayi magana?"

Baaba Mari sai ta dauke kai kamar bata ji ba, su ma sai suka yi yadda tayi din.

"Kafin mu tafi din zai kyautu muje gidan wadannan bayin Allah muyi musu godiya. Bai dace su biyomu karbar kwanukansu ba." Ta ce da Munzali.

A ransa Abbati yake cewa kamar ta shiga zuciyarsa ta san abin da yake tunani.
"Kayan shimfidar ma duka nasu ne."

"Allah Sarki. Mutanen kirki basa karewa a duniya."

Deluwa ta jinjina kai bayan sun gama kwashe komai suna shirin shiga mota ta soma sababi. Habi da 'Yashshafa suna motar Buba. Ita da Baaba Mari ne zasu shiga baya a ta Munzali.

"Dole ki wulakantani mana Mari. Baki da laifi tunda ni na nace sai nazo duba danki. Wannan cin kashin da ki ke yi min Billahillazi kaf sai na fadawa Malam" ta kare tana yi mata kashedi da hannu.

A karo na biyu Baaba Mari ta sake bawa banza ajiyar Deluwa ta ce "Na san halinka da nawa idan ka so Abbati. Don Allah ka hanzarta yin wanka ka kimtsa yadda zamu je mu kama hanya da wuri"

Munzali sai ya kama murmushi. Da can ma Abbati komai nasa da shiri cikin tsari yake yi ballantana yanzu da zasu je gidansu Farha. Waya ya daga ya kira Suhaib ya fada masa. Sai kuma ya roke shi idan zasu iya ajiye motar Abbati a gidansu. Sati mai zuwa su zo su dauka saboda ba ya son Abbati ya gwada tuki mai nisa da fitowarsa daga asibiti.

*
Mami Khadija ya fara kira ya fada mata bakin da zasu yi. Tana hanya don goma ta fito daga aji kuma bata zauna ba ta taho saboda maganar bikin gidansu. Farha ta fara kira bayan sun gama magana ya fada mata karfe nawa zasu iso.

"Idan kina jin kwarin jikinki yau kisa hannu a hada musu abincin rana. Aikin zai yiwa Sauda yawa a kankanin lokaci. Mardiyya kuma tun jiya na kula da take taken Nasima saboda haka kar ki kirata har ta sami yadda take so ayi rigima. In kuma ba za ki iya ba sai a siyo musu kawai."

Bata san cewa kafin ma ta gama bayaninta ba Farha ta mike tsaye. Wannan yanayin na farinciki mara misaltuwa ya mamaye kirjinta.
"Zan iya Mami. Sai kin iso. Allah Ya kiyaye hanya."

Babu sauran ciwo bare damuwa. Dakin Sauda ta wuce ta tasota. Karatu take yi na gwajin da take dashi washe-gari litinin.

"Ayyaaaa Ya Farha test gareni. Yaushe zamu gama nayi karatu? Ni wallahi ban iya komai ba kar naci zero."

"Yi zamanki. Amma wallahi ki baza kunnuwa don Mami tana hanya. Kina jin motarta ki taho kitchen."

Sauda tayi mamakin wannan abu. Yau yayarta da kanta take gudun dan tayi? Ba wai kyuya gareta ba amma bata son shiga kitchen ita kadai. Ko baka tayata da komai ba ta dinga jin motsi ko a ayi hira. Sai kuma ta tuna hasashensu ita da Mardiyya akan wanda Munzali ya bawa wayarsa rannan. Mutumin da Farha ta ce mata shi ne mara lafiya. Shu'umin murmushi tayi ta wurgar da littafin tana dirowa daga gado tabi bayanta. Zaman daki bai kama ta ba indai akwai wainar da ake toyawa tsakaninsu gara ayi a gabanta. Akan hanyar zuwa kitchen din ta turawa Mardiyya text ta tsegumta mata.

(Ki kirani idan sun zo please)
Ta tura mata amsa idanunta akan Mama Nasima. Fatanta kada a sami akasi akan fitar da ta ce zata yi. Ta kasa gane yawan tambayar da take yi mata yau akan Yumna kawar Farha.

A zuciyar Mardiyya bata kaunar wannan hali mai kama da gulma na mahaifiyarta. Kafin ta girma duk abin da ta tambayeta take fada mata. Sai ta kula idan ta so takalar Mami Khadija rigima da wannan take amfani tayi ta sakin maganganu. Mamin ta gane abin da Nasima take yi amma bata taba nunawa yaranta su guji Mardiyya ba. Suhaib har CID ya saka mata lokacin wanda akan idonta Mami tayi masa kaca-kaca. Da shekarunta suka karu tayi hankali sai ta fahimci illar abin da take yi ta daina.

Duk lalacewar Nasima a tata zuciyar wannan karon ba da gulma take tambayoyin ba. Laluben hanya mafi sauki da za ta fadawa 'yarta auren da mahaifinta zai yi take. Yaran duka suna son babansu a iya saninta. Wannan labarin ba komai zai yi ba sai wargaza farincikinsu. Sannan tana sane da yadda Yumna ta zame musu makusanciya a dalilim Farha. Bata sani ba ko ita ma Farha tana yawo. Kada ya zamana an koyawa 'yarta bata sani ba. She was just being a Mom a yau. Sai dai rashin sabo da rashin kyawun zuciya tun farko yasa ta kasa gabatar da niyarta.

*
Zuwan Sauda yasa aikin nasu saurin karewa. Tuwon shinkafa Saudan tayi ita kuma Farha hadaddiyar miyar agushi. Lilu ya siyo frozen springrolls da samosa aka soya da kuma lemuka. Sai kayan marmari da aka hada fruit salad.

A gurguje Farha ta shiga wanka. Kafin ta fito Mami Khadija ta dawo taje ta duba inda aka tanadi kayan tarbar bakinsu. Komai ya yi yadda take so domin 'ya'yan nata ba daga nan ba.
*

"Kai Mutumina, wannan kamshi kamar gaisuwa zamu je kai wa ba godiya ba?"

Abbati ya cigaba da fesa turare yana murmushi kafin ya bawa Munzali amsa.

"Sa ido sana'ar su waye ma?"

"Zagina za ka yi saboda ka warke?" Cewar Munzali yana tasowa ya karbe turaren ya shiga fesawa "wai ma da kananan kaya za ka je gidan surukai?"

Abbati ya kalli kayan jikinsa ya dan hade gira. Jeans ya saka baki da jar riga shirt. Agogonsa na fata da takalmi covershoe duka bakake.
"So ka ke ka rage min farincikin da nake ciki shi ne za ka fara korafi akan kayana?"

"Rashin dacewa na gani. Tunda babu a kayanka idan ka amince kawai mu wuce Kano sai mu dawo daga baya idan an sami lokaci..."

Sauran maganar tasa bata sami fita ba a dalilin kansa da Abbati ya taho shi kuwa ya ja da baya yana dariya. Sauran kiris su fara halin nasu na kokawa kamar yara Buba ya kwankwasa kofar.

"Baaba ta ce in duba ku taji shiru."

Sai da Abbati ya harari Munzali sannan ya bude kofar yana cewa "ka ci sa a."

"Kai dai ka ci sa a ba don haka ba yau da sai nayi maka John Cena (sunan dan wasan wrestling ne) a gadon baya."

Yana fadin haka ya fice da sauri suna dariya harda Buba da yawan tsokanar junansu ke matukar burge shi.

Kamar yadda suka dawo masaukinsu haka suka sake shiga mota da kayayyakinsu yanzu. Habi da 'Yashshafa suna motar Buba. Habi tayi shigarta fes ita kuwa yallab'iyar kwalliyarta ta rambada tayi bajau. Banda uwar hoda da foundation wanda suka mayar da ita mutum mutumi ta kawo wata foundation din mai haske ta zana tun daga tsakanin girarta har karshen karan hanci. Irin abin nan da masu make up suke yi domin a karawa hanci tsini. Sai fuskar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login