Showing 63001 words to 66000 words out of 242549 words

Chapter 22 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3396

ya ce ta tabbatar shi ne abu na farko da ya fara sha bayan shigowarsa gida. Ta tabbatar wannan dai sai dai a hakura domin bata san waye zai sha ba idan an fitar. Na abincin ma a miya ta saka. Dolenta ta canja miyar don kada a sami matsala idan wasu suka ci. Tayi tsaki yafi cikin carbi tana jin haushin aikin da ya saka ta ga asarar kudi. Dadinta ma ba duka ta juye magungunan ba da ta sha bacin rai.

*
Lomar farko Abbati ya tauna kasa harda tsakuwa a cikin salad. Miyar kuwa tsabar tattasai ya yi yawa har wani daci take yi. Ga garin nasu ba wani restaurant zai samu ya sayawa bakinsa abinci ba. Allah Ya taimake shi ya riga kowa zuba abincin. Qibdiyya na kan cinyarsa zai bata sai ya ce bari ya dandana miyar ko da yaji. Munzali ya kalla yana neman ceto. Tuni ya fahimta ya karbi plate din hannun Shazali yana cewa yaji kamar muryar baban Abbati su je su gaishe shi. Audu dama bai riga ya dauka ba shi ma ya mike suka fice.

Iya Kande ta kalli yanayin Abbati ita da take da wayo kuma ta fahimci wulakancin da Hannen tayi musu kafin ya shigo dazu. Idanunsa sun yi jazur ga jijiyoyin kansa sun tashi.

"Sai hakuri baban Qibdiyya."

Murmushi kawai ya yi ya shiga daki. Wurin da ya tabbatar ba zai ji kunya ba ya je ya zauna a gefen Baaba Mari.

"Ni dai wallahi bana son wannan dabi'ar. Baka jin komai kake zama a jikina. Wannan ba sai ka sa a fara cewa rashin kunya ka koya a birnin ba."

A da idan tayi maganar sake nanikarta yake sai ta ture shi. Yanzu kuwa murmushin yake ya yi.

"Baaba ko zan sami abinci na bawa bakina?"

Bai fada ba amma sarai ta fahimci me ya faru.
"Kira Atine ta kawo abincin wurinta. Dama kannen naka sun yi muku abinci na ce su cinye kayansu kana da mata."

Maimakon ya kira Atinen wadda dan kawunsu take aure ita ma a gidan aka yankar musu wuri sai kawai ya tafi da kansa. Tayi murnar ganinsa sosai ta kinkimo kwanuka ta biyo shi.

Audu na hangosu ya baro su Munzali yazo ya karbi na hannunsa. Godiya Abbati ya yi masa ya ji dadi. A duniya bai taba ganin mutum mai saukin kai kamar Abbati ba. Ga kyau ga kudi kuma ga dangi rututu amma shi mutum ne mai yiwa kansa abu. Bai dade da fara aiki tare dasu ba ya soma zargin iyayen gidan nasa ko Sojojin baya ne (maza masu neman maza) saboda wasu abubuwa da ya gani. Har yau bashi da kwakkwarar shaida amma yana saka su a addu'a idan gaske ne Allah Ya yaye musu. Bai san kaddarar da ta kaisu ga wannan fitinar ba amma tabbas ya yarda da kyakkyawar amintar dake tsakaninsa da Munzali.

Zama suka yi suka ci suka koshi sannan suka tafi gidansa. Hanne ta burbura gyara don ba wani abin kirki tayi ba. Har dare kuwa bata ga fara'ar mijin nata ba.

Ana sallar Isha Audu da Shazali suka nemi makwanci. Abbati har lokacin yana ta kumburi akan abin da Hanne tayi musu. Munzali ya taso daga inda suka yi sallah a wajen gidan ya zauna a kusa dashi.

"Mutumina inata jira ka gama shan kunun nan mu kira 'yar budurwar nan ta Diamond plaza naga kuma abin yaki karewa. Abin takaici ban san wadda ta burgeka ba da wurinta zan garzaya da kokon bara."

Harara Abbati ya wurga masa yana dauke murmushin da ya soma jin Munzali ya gama ja masa rai akan nambar.

"Kokon bara wane iri?"

Dariya ya dinga yi masa "maida wukar idan bayi barar kai zan kawowa zuciyar ta ta."

Abbati ya lumshe idanu "sunanta Farha. Ina jin sister din wadda muka bi ce."

"Ai yarinyar ta bani tausayi. Tashi a gaban Asabe part two ba karamar jarabawa bace."

Dundu mai shiga Abbati ya sakar masa a baya ya dinga shafa bayan yana harararsa.

"Mugu kawai"

"Naji din. Tunda kunnenka baya ji mu tafi a haka. Na fada maka Asabe ba abar rainawa bace. Iyaye sun fi gaban wasa tunda sune tsananinmu na samun rahama. Kuma banda abinka duk tsiya ai ta haifeka kai kuma ka haifa min Qibdiyya."

Murmushi Munzali ya yi. Abbati daban yake har kullum. Shi ma Abbatin sai ya mayar masa yana ji a ransa ba zai taba jindadin rayuwar da babu Munzali a cikinta ba.

"Allah Ya baka hakuri Mutumina na tuba. Yanzu dai matso mu danna kira.."

Wayar da ta kasance mafarin komai!

***
"Alhamdulillah ta sauka. Hajiya ku bamu kayan baby."

Hajiyan Fatakwal ta sake fadada murmushinta sannan ta ce "Nos bani jaririn zan gyara jikana da kaina. Ita dai ga jakarta nan.."

Jakar kayan Zara ta tura mata ita da Alh. Unais aka rasa mai iya mallakar kansa. Dukkaninsu murna ta cika su yau burinsu ya cika. Ganin wannan ranar ne ma ya hana Hajiyan sake tayar da zancen maganganun da taji Zaran tayi a waya.

Nos ta koma cikin dakin haihuwar ta sami Zara tana rizgar kuka. Da gudu ta karasa gaban gadon duk da cewa ga likitoci biyu tsaye a kanta suna bata hakuri.

"Me ya faru? Ina baby din? Ko wani wurin yana mata ciwo ne?" Ta dinga jera tambayoyi ba tare da samun amsar ko daya ba.

"Ina kayan?" 'Yar dattijuwar likitan ta tambaya ranta yana baci da kukan Zara.

"Kakar ta ce a in kai mata."

Idanu cike da hawaye Zara ta dago kai ta ce "kin fada musu mace ce?"

"A'a fa. Basu ma jira ba suka ce in dauko musu."

"Na shiga uku. Doctor kin cuceni wallahi. Sau nawa kina ce min namiji ne?" Ta fada a zafafe tana wani kukan.

"Haj. Zara ni ba zan baki hakuri don nayi kuskuren fadar jinsi ba domin ba ni na halicci abin da ke cikinki ba. Kuma tun farko muna fada muku ana iya samun canji."

Zare safar hannunta tayi ta jefa a shara ta fice rai a bace. Yarinya kamar wannan za ta kawo mata raini akan abin da bata da hannu akan yiwuwa ko akasinsa.

Tana fita Alh. Unais da Hajiyan Fatakwal suka matso. Ganin ba bebin bane a hannunta sai ya zaro kudi.
"Dakta ga tukwicinki inji Imran dani babansa. Mungode sosai."

Dan dagowa tayi ta kalleshi da kyau "wane Imran din?"

'Yar dariya mai fallasa tsananin farincikinsa "jaririna na ciki"

"Oh..ashe fa Nos din bata fada muku ba. Ai mace ta haifa. Ko ba Zara Rabi'u ba?"

In sun tanka to lallai kujerun wajen ma sun tanka.UWA UWACE...14


Batul Mamman💖



*
Kafin isowarsu gida kishiyar Zara ta sanar da duka maaikatan gidan uwargidan Alhaji ta haifi da namiji. Labari da dumi duminsa yazo gareta daga wajen kanwar Alh. Unais wadda ta kasance aminiyarta cewa mace aka haifa. Dariyarta ta sha a daka harda rawa sannan ta fito rama wulakancin da Zara ta dinga yi mata da cikin.

Dama saboda doki Alhajin da kansa ya tuka su zuwa asibiti ita da Hajiyan Fatakwal bai bari direba ya kaisu ba. Hancin motarsa na shigowa katafariyar farfajiyar gidan 'yan dattijan masu aikin gidan mata suka soma guda.

"Allah shi raya Imarana magajin Alhaji Unaisu" inji mai girkin gidan.

"Aminnnn" sauran suka amsa a tare.

Hajiyan Fatakwal ta fito fuska a hade ta daka musu tsawa.

"Ku matsa ku bani wuri duk kun cikawa mutane kunne. Waye ya ce muku namiji ne?"

Sai suka yi tsuru-tsuru dasu. Hajiyan Fatakwal ta shige bangarenta ko waige babu balle ta sake kallon Zara. Jaririyar ma bata karbeta ba tun a asibitin ita suka bari ta dauko abarta. Ko tausayin yadda take daga kafa da kyar Alh. Unais bai ji ba ya ce tazo su tafi tunda kalau take. Hutun da ake yi bayan haihuwa tayi a gida don bai ga dalilin zama ba. Kasa magana tayi saboda yadda suka canja mata lokaci guda. Gashi ta sha dinki irin wanda ba a taba yi mata ba duk haihuwarta amma dole ta sauko jiki ba kwari.

Alh. Unais bin bayan mahaifiyarsa ya yi suka barta da masu aiki. Laurat kishiyarta ta dubeta ta tabe baki.

"Ya aka haihu a ragaya uwar Imran? Bari na dauko wayata don har na canja muku suna ke da maigidan zuwa Abu wa Ummu Imran."

Tana dariyar shakiyanci ta wuce. Masu aikin ma ganin kamar Alhajin cikin fushi yake sai aka rasa mai karbar 'yar. Akwatin kayanta kawai aka daukar mata.

Sai da kowa ya fice daga dakin ta kwantar da jaririyarta ta sami damar fashewa da kuka. Kirjinta har wani irin dokawa yake saboda bacin ran abin da aka yi mata tun daga asibiti har gida akan haihuwar mace. Bata yi mamakin ganin haka daga surukarta ba amma ta zata Alh. Unais yana sonta ko da bata taba haihuwa ba ma.

Cikin radadin ciwo ta tashi ta tara ruwan zafi bayan kimanin minti talatin da ganin Hajiyan Fatakwal bata shigo ba. Jikinta ya yi tsami sannan 'yar ma tana bukatar wanka.

Setin robor wankar jaririyar ta dauko ta ajiye a dakinta daga bangaren da yafi kusa da bandakin. Haka ta dinga dibar ruwa tana takawa da kyar har ta ajiye komai a wurin. Ta tashi za ta dauko bebin kafarta ta turgude ta tale gabadaya. Wata irin razananniyar kara ta saki lokacin da dinkin da tasha wuyarsa ya kece kyat! A wurin ta fadi jini na zuba cikin dan kankanin lokaci ta fice hayyacinta.

Maryama da kannenta sai karfe shida suke tasowa daga islamiyya. Basu da masaniyar Mummyn tasu taje asibiti har ta haihu. Bakwai da rabi suke tafiya makarantar boko daga can su wuce islamiyyar. Mas'uda ce ta fara shiga falon Zara daukar wani abu taji kukan jariri. Da gudu ta karasa ciki ta hango jaririyar akan gado tana ta tsala ihu ga mahaifiyarsu kwance a kasa.

Kanta tayi ta dinga jijjigata amma ta kasa tashi sai da kyar ta ce ta kira Hajiyan Fatakwal. Kafin wani lokaci dakin ya cika da 'ya'yanta sai Alh. Unais da Hajiyarsa. Masu aiki ne suka taimaka mata tayi wanka da kyar jikinta babu kwari.

Duban yanayinta Hajiyan Fatakwal tayi gami da yin karamin tsakin da ya shiga kunnuwan mutanen dakin. Zara bata da hankali a ganinta. Irin maganganunta na rannan a waya su suka tabbatar mata da haka. Tayi mata lamuni ne dama albarkacin cikin da namiji da ake tunanin za ta haifa. Amma tunda abu yazo da haka ta sami damar raba danta da bakar kadara irin wannan. Dinbin asarar da Zara ta saka Alh. Unais akan hasashen gaibu ba kadan bane. Bakin gadon ta samu ta zauna ta dora kafa daya kan daya. Hannuwanta dake dauke da zobban gwal ta dauko guda ta nuna Zaran dashi.

"Wai har yanzu baki sanar da kowa haihuwarki cikin danginki bane?"

Gabanta ne ya yanke ya fadi ta kalli Hajiyan a tsorace "zan kirasu."

"To ya dai kamata. Ba zai yiwu bane ace duk haihuwa sai dai ayi miki komai a nan. Dubi yadda ki ka fadin yanzu har dinki ya bude. Ya dace iyayenki su dinga tabuka nasu kokarin komai talaucinsu."

"Umhumm" Zara ta furta kamar taci madaci.

"Da dai nayi wa Unais magana akan daga can su samo miki mai zama har kiyi arba'in, to amma tunda ga wannan lalura da dole sai an sake miki dinki gara ki tafi gida. Kira min maman taki nayi mata magana."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Zara ta furta da dan karfi hannunta akan kirji "gida fa ki ka ce Hajiya?"

"Akwai matsala ne? Gidanku fa nake nufi."

Zara ji tayi ta gwammaci kar a turo kowa tayi aikin komai na jegonta da kanta akan dai ta koma gida. Ta zauna da Innayo a wannan dakin da iskarsa ma bata mata dadi? Tunanin kadai ya sake dagula lissafinta.

"Hajiya ki barni a nan zan iya..."

Hannu ta nuna mata fuska a hade "bana son wata magana. Ko akwai magana ne?" Ta dubi danta. Kai ya girgiza don shima haushinta yake ji "yauwa to ki shirya direba sai ya mika ki yanzu. Kar ki manta da batun dinkin dai."

Jikinta ya yi sanyin da ko baki ta kasa motsawa. Wane irin wankan jego zata je gida haihuwa ta biyar? Anya ba za a zata auren ya mutu bane?

Babu sarki sai Allah dolenta ta shirya 'yan kayanta ta lallaba zuwa dakin maigidan. Tare da Laurat ta same shi ta nuna tana son magana dashi ya ce Bismillah. Laurat ta kalla ya hade fuska kuwa.

"Kin kuma yi kadan ki zo ki sameta kiyi tsammanin zan ce ta fita saboda ke."

Laurat ta murmusa tare da mikewa.
"Kila sirri ne bari na baku guri."

"Dawo ki zauna nace."

A fakaice ta yiwa Zara gwalo ta koma kusa dashi ta zauna.

Kirjin Zara ya dinga harbawa saboda tsananin bacin rai amma haka ta danne.

"Uhmm dama cewa nayi kayan bebi din kadan ne unisex duk na maza ne. Ko za ka bani kudi...."

"Ba zan yi asara ba. Ki saka mata duk wadanda aka farke kafin na sami sararin sayan na matan"

Gyada kai tayi tana kokawa da hawayen da bata son zubarwa a gaban kishiya.
"To in dauko maka ita kayi mata huduba?"

"Idan kin je gida kakanta ya yi mata ya kuma saka mata sunan da yake so."

Hannuwanta ta dunkule har suka soma zafi saboda rashin gudun jini. So take ko ta halin yaya ta farka daga mafarkin da take yi. Lokaci guda mafarkinta ya sauya game da haihuwa. Ta saka rai za ta haihu su dawo gida miji yana nan nan da ita sai gashi ko mutum daya bai karbi jaririyar ba cikinsu. Duk rashin kunyarta bata san da idon da za ta kalli Innayo ba.

Asibitin da ta haihu ta ce da direban ya ajiyeta suna fita. Da kafarta ta kai kanta wurin likitar da ta gama yiwa rashin kunya ta nemi a dubata. Duk irin haushinta da likitan take ji sai da ta tausaya mata. Mirgina kai kawai ta dinga yi hagu da dama tana hawaye da ake sake yi mata dinkin. Azaba ce kan azaba don ta gwammace ace sake haihuwa tayi akan wannan wahalar da bata da na biyu. Ana cikin yi tana jin kukan jaririyar da har yanzu ko wanka ba ayi mata ba.

"Wai ina 'yan uwanki ki ka dawo ke kadai?"

"Wayata ce babu chaji shi yasa ban kirasu ba" ta iya cewa tana kawar da kanta don kar a gano karyarta.

Likitan bata takura ba amma jikinta ya bata akwai wata a kasa. Boye mamakinta tayi lokacin da Zara ta ajiye kunya a gefe ta roketa ta bata gado ko da na kwana biyu ne. Tunda file dinsu kudi kawai Alh. Unais yake sakawa bata da matsalar biyan kudin komai. Kudin hannunta ko dubu biyar basu kai ba saboda baya basu kudi a hannu sai dai ka gani a kasa.

***
"Wai Ayaah ta zo inji Dani."

Muryar wani dan almajiri ya karade tsakar gidan Honorable. Murja ce ta amsa masa saboda tana wanki a wurin. Dakinsu ta shiga ta sami Ayaah ta tura earpiece a kunne tana fama da koyon turanci a gidan rediyo. Makarantar gwamnati suke zuwa turancin babu sosai gashi tana son cigaba da karatu. Shi ne ta daukarwa kanta sauraron wani shiri da ake darusan turanci a gidan rediyo.

"Helflesslyyy"

"Aimlesslyyy"

"Hofelesslyyy"

Take ta maimaita kalmomin da ake fada da kokarinta na ganin ta tace turancinta. Sai karya murya take tana magana da hanci.

Duka Murja ta daka mata a cinya ta tashi a zabure.

"To tashi alhudahuda ana kiranki a waje. Ki je ki kore shi kafin Baba ya dawo wallahi"

"Daga sallama sai kora saboda ba wurinki yazo ba?" Ta maida mata a tsiwace.

"To kar ki kore shi. Ki bari Baba ya dawo ya tarar da kasurgumim kafiri a kofar gidan nan ki sha mamaki."

"Kafiri?" Ayaah ta ce tana kai hannu kirjinta ta dafe.

Murja bata amsa mata ba sai ta janyo hijabi ta dora akan rigarta ta fita da sauri. Ko ba Baban nasu ba bata so Anti Hasiya ta dawo daga wurin Innayo da ta sake tafiya yau ta ganshi. Karshenta ta fadawa baban nasu don ayi mata fada tunda ba kaunarta take ba. Tuno fadan da tayi mata rannan tayi ta dan yi murmushi. Ita bata ma san laifin da Antin tayi musu ba har ta tashi da tsanarta. Lallabawa zata yi ta soma yi mata biyayya ko don kayan daki...

Ido, baki da hanci duk ta bude tana kallon Danliti a kofar gidansu. Bai tashi zuwa kawo jakar ba sai da aka sake samun rantsatsiyar motar kece raini a garejinsu. Ya sha shadda mai kyau sai daukar ido take. Kan nan nasa a kwance luf yana sheki ya sha man alayyadi wanda ya hada da ruwan turare dan d'uri domin ya danne warinsa.

Shi da kansa ya san ya yi barna a zuciyarta saboda yadda ta kasa mallakar kanta a gabansa.

"Malama Ayaah sai ki ka ganni a kofar gidanku ko?"

Muryar da ya daddage ya kashe domin ta kara dadi ta shiga kunnuwanta wanda tsabar rudewa sai cewa tayi "cewa akayi in zo in ji Dani."

Kansa ya shafa da dan murmushi "sorry you know rannan sunanki na tambaya ban samu na fada miki nawa ba muka rabu. Suna na Abubakar amma a gida kakanni suka saka min Danliti. Abokai na kuma suke cewa Dani. Sunan nawa dai na san ba zai miki dadi ba."

"Nooo" Ayaah ta cije baki wurin fadar kalmar saboda ya gane ita ma ba baya ba a turancin.
"Sunan da dadi mana. Dad dina sunanku daya amma Hon. Habu ake kiransa shi ma."

"Nice" inji Danliti.

Jakar ya mika mata tare da zuba mata karairayin yadda ya dinga nemanta bayan ya ganta a motarsa. Abin ya so daure mata kai saboda duk lissafinta jaka tana adaidaita sahu. Za ta iya rantsuwa bata shiga da ita motar ba. Saurin kawar da tunanin tayi tunda dai ta dawo sannan ga Dani a gabanta.

"Ban san me ki ka yi min ba Malama Ayaah amma tunda muka rabu na kasa sukuni. Zuwa nayi da bakinki kiyi min bayani."

Wayyo Allah. Ko balam-balam ba za ta gayawa Ayaah kumburi ba a wannan lokaci. Tsaf ta fahimci inda ya dosa. Jirkita idanu tayi tana masa fari. Zuciyarta fes sai farinciki Allah Ya kawo mata mijin aure tayi ta bar gidan nan.

"Ni ban maka komai ba" ta fada tana dan tura baki.

Danliti ya kunshe murnarsa zai mata magana wayarsa ta shiga ringing. Saboda rayuwar karya da cutar 'ya'yan mutane da suka saka a gaba wayar mai tsada ce. Dauka ya yi ya kara a kunne maganarsa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login