Showing 66001 words to 69000 words out of 242549 words

Chapter 23 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3360

fita da sigar rarrashi ga wanda ya kira shi. Ayaah ta kusa kuka da hirar tasa tayi gaba ta gane da wa yake magana.

"Kiyi hakuri ba dadewa zan yi ba."

"Ba shekaranjiya na tura miki 50k ba?"

"To, to...naji kiyi hakuri. Yadda ki ke so Honey haka zan turo." Ya dan saurara kadan sannan ya ce "har dubu dari biyu? Ok zan miki transfer."

Wayar ya tura aljihu idanunsa a kanta yana murmushi.
"Sorry wife dina ce."

"Ok" ta amsa da yanayin ko in kula.

Muryarsa a sanyaye ya ce "Ku mata sai da lallabawa. Bakwa son gaskiya ko kadan. Da an so nuna muku laifinku sai ku hau bori."

"Wasu matan dai ba duka ba"

Dariya ya yi "dama kun saba karewa juna."

Wata wayar ta sake shigowa ya dauka murya a sake.

"Gambo ka siyo min abincin?"
"Yauwa dama cewa zan yi ka biya Yahuza suya tsire ka siyo na dubu biyar saboda tayi baki kuma bata yi girki ba. Abincin kuma duka friedrice mai hantar nan suke so plate takwas. Sai coleslaw da lemon kankana."

Yawun Ayaah ya tsinke saboda tsabar yadda ranta ya biya har kamshin abincin kwakwalwarta ta zayyano mata.

"Sorry fa na cika ki da waya. Yau Madam dina ke jin rigima shi yasa nace ku mata sai da lallabawa."

Daga iya bayaninsa ta fahimci kamar baya jindadin abin da matar tasa take yi masa. Ga kudi zai tura ga abinci zai saya. Kuma a haka aka sake masa flashing ya dauka ya sake bata hakuri yana cewa yanzu zai tura. Danne danne ya yi a waya ya sake yin alamun kira ya ce ya turo. Da ya gama gabadaya ya sake fuskantar Ayaah.

"To Malama Ayaah ni zan gudu gashi baki bani amsar tambayar da nayi miki ba."

Wayarsa ce ta hau ruri ba kakkautawa tana soma magana. Da sauri ya dauka ya sake bada hakurin cewa gashi nan zuwa.

"Madam ta matsa kambon zan tafi sai na sake kawo miki ziyara."

Ranta bakikkirin da takaicin wannan mata mai hana ruwa gudu ta ce, "tafiya ko ruwa baka sha ba?"

"Kar ki wahalar da kanki akwai a mota."

Wata wayar ta shigo wannan karon daga garejinsu. Dauka yayi abokin aikinsa na sanar dashi mai motar yazo dauka amma an fada masa anje testing. Hakuri ya kuma bayarwa yadda ba za ta gane ba. Bayan mutumin ya ajiye wayar ya cigaba da magana ba tare da ya cire daga kunnensa ba.

"Don Allah kiyi min tuwon ko leda biyu ne."
"Haba Honey. Ko baki da lokacin yin miya ni dai kiyi tuwon zan yi miyar da kaina ko in ci da mai."
"Babu komai Allah Ya kaimu weekend din."

Ayaah taji tausayin Danliti kamar tayi kuka sannan ga mamakin saukinsa. Ji yadda yake bin matar tana wulakanta shi. Idan ita ta same shi ba zai rasa komai ba. Samun kanta tayi da tambayarsa.

"Tuwo ka ke so ne?"

"Na cire rai Madam ta gaji."

Ayaah taji kamar ta nemota ya shako wuyanta. Sosai take jin tausayinsa. Ji wannan bata show ta hana shi hira da ita ma. Tayi sa'a ya karbi nambar wayarta dai. Yana tafiya don karfin hali ta ce,

"Idan na shigo gidan nan sai kin raina kanki."

Shi kuwa Danliti yana haduwa dasu Rabilu ya labarta musu yadda suka yi.

"Irinsu zuma ne da wuta ake cinsu. Na darsa mata tausayina da yawan arzikina ga hakuri. Indai ba fyade kake son yiwa mace ba to da irin haka sai kayi mata wayo ta kawo kanta har ta roki kayi eh ya ne..."

Dariya suka kwashe suna tafawa. Danliti ya kira matarsa da ko shekara basu yi ba ya kasheta da kalaman soyayya da alkawarin taho mata da tsire saboda laulayi da take.

"Mugu dan masara. Ka gama da wata ka koma lallaba ta gida." Inji Rabilu

"Ta gida ce dahir kaji. Wadannan kawai a samu garabasa ne a wuce wajen. Bari ma na tashi sai gobe."

***

"Haba Malam. Wannan irin sakin baki tun ban kira ba." Cewar Munzali yatsansa na laluben nambar Mardiyya "idan ka fiye washe baki zan fasa kira sai gobe. Ina tsoron kar ka zubar mana da girma garin rawar kai"

Ba don yana tsoron kar Munzali ya yi masa sanadin rasa abin da zai hada shi da Farha ba da a take zai rama. Kwafa ya yi kawai.

"Fadi ko kaji dadi" Munzali ya sake kokarin tunzura shi.

Abbati ya nuna masa gidansa ya ce "Ka kira ko ka kwana a waje yau. Ai dai ka san wancan gidana ne."

"Gidan Hanne da 'Yashshafa ba."

Karar da wayar ta soma yi alamun kiran ya shiga ne ya dakatar da Abbati daga bashi amsa.

Mardiyya na taya Sauda tsifa kiran ya shigo. Har yanzu basu san me yake faruwa a gidan ba sama da abin da Suhaib ya fada musu. Wayarta da Saudan ke dannawa ta hau kuka ta mika mata. Ganin bakuwar namba sai ta dan jinkirta dauka har ta kusa katsewa.

"Salamu alaikum" ta ce da siririyar muryarta.

Munzali ya dan numfasa kafin ya amsa da murmushi "amin wa alaikum salam. Diamond girl ce?"

Mardiyya ta tabo Sauda ita ma ta taso don jin waye mai kiran.

"Diamond girl kuma?"

"Eh. Mardiyya wadda muka hadu farkon satin nan a Diamond plaza Kaduna."

"Waye don Allah?" Ta tambaya duk da ta so gane muryar. Sai dai bata fatan wata matsala ta taso sakamakon tsayuwarsu yin hoto a jikin motarsu.

Abin da ta guda ne ya faru taji ya ce "dama ranar da ku ka yi hoto a jikin motarmu yayana yana ciki. Shi ne ya ce na kira ki zai yi miki magana. Shi ne ma dalilinmu na biyoki shagon."

Mardiyya taji cikinta ya kulle. Daga daukar hoto abu na neman zame musu matsala kamar sun saci motar.

Jiki a sanyaye ta ce "Hoto ne fa kawai muka dauka."

"Mirror din bangaren direba yana rawa, motar ma a gareji ta kwana."

Abbati ya zungure shi da gwiwar hannu yana balla masa harara "Sannu kanya uwar zuba. Haka kawai ka ke yi musu karya"

Sai da ya toshe kan wayar sannan ya ce "ka kyaleni nayi yadda nake so. Kai dai ba Farha kake nema ba? To za ka samu in sha Allah."

Cigaba ya yi da wayar sai yaji murya daban tana cewa "daga cin arziki sai ku ce an taba mirror? Ko an gaya maka ba za mu iya biya bane"

"Ke kuma ya sunanki?"

"Sauda" ta amsa a tsiwace "ai ba mu ya kamata ku nema ba. Mu ma muna da yayye sai mu hadaku dasu."

Munzali ya kunshe dariyarsa. Da gani 'yan matan a tsorace suke amma suna gudun nunawa don kada matsalar ta girmi yadda take yanzu.

"Zan ma fi son haka. Hadani da babba sai na bawa yayan nawa."

Kashe wayar Sauda tayi ta rike haba
"Mardiyya me yasa kika basu nambarki?"

"Biyoni suka yi" ta iya cewa ba tare da tayi bayanin abubuwan da Mamanta tayi musu ba. Duk lalacewarta da kunya ta dinga kwaye mata baya.

"To mu kaiwa Ya Suhaib?"

Mardiyya ta mike da sauri "kina bashi zan tafi na kwanta. Haka kawai ki sa ya shekara yana yi mana mita"

Dariya suka zauna yi wayar ta kara shigowa. Da sauri suka kaiwa Farha a kitchen. Takaitaccen bayanin kiran suka yi mata sannan ta amsa wayar da sallama. Sunanta Munzali ya tamnaya tana fada ya maimaita da cewa,

"Ya Farha" kamar yadda yaji Mardiyya ta fada kafin ta bata wayar "ga yayana Abbati" ya karawa Abbati a kunne ya tashi.

"Ya Farha" Abbati ya ambaci sunan a kasalance.

To ita dinma kamar kannenta taji tsoron wannan binbini.

"Yanzu shi kaninka da ya hadamu da kai ba arziki bane ace yana da motar da za a dauki hoto a jikinta?"

Murmushi ya yi yana jin jikinsa sakayau kamar zai tashi sama.
"Ni ban ce daukar hoton laifi bane."

"To menene? Su Sauda sun ce wai mirror yana rawa. To ko dai motar gidanku ku ka dauko ta sami matsala ku ke neman kudin gyara a jikinmu? Ko irin 'yan karyar nan ne masu aro mota su je burge 'yan mata? Duk fa mun san halin ire-irenku."

Sosai yadda take magana ya sanya shi nishadi. Jinginar da kansa ya yi da bayan bishiya yana sauraron muryar dake zagawa sassan jikina.

"Da gaske Ya Farha."

"Ka dena ce min Ya Farha ni ba yayarka bace."

"Allah Ya Farha?" Abbati ya kuma fadan sunan da 'yar dariya.

Ita ma Farha sai ta sauko da ta fahimci kamar zolayarta ma yake yi.

"Ya sunanka?"

"Kina iya kirana Abbati."

"Sai dai in ce maka Uncle Abbati. Wai don Allah me yasa ka kira kanwata."

"Neman rigima kawai Ya Farha. Yadda motar ta burgeku shi ne na fito ko Allah zai sa nima na burgeku ayi hoton dani sai kawai ina bude kofa ki ka gudu." Yana son ya kara da cewa ta gudu da zuciyarsa ya fasa. Ba yanzu ba. A gaba kadan za ta gane matsayin da ta taka farat daya a zuciyarsa.

"Idan na baka hakuri magana za ta wuce? Idan aka ji a gida fada za'a yi mana."

"Tun ranar ma na hakura Ya Farha."

Dan hade fuska tayi ta ce "nifa ko rabin shekarunka ban yi ba ka ke ce min yaya."

"Kin sanni ne? Ko kin san shekaruna?"

"Na ganka lokacin da ka bude motar."

"Wane irin mutum ki ka gani?" Ya tambayeta da dan tararrabi a muryarsa.

"Mai kyau" ta ce kai tsaye.

Zuciyarsa dokawa tayi da abin da bai san sunansa ba. Dumi ne ya lullube shi tun daga tsakar kansa har tafin kafa. Ita Farha tunda take bata taba hira makamanciyar wannan da saurayi na shi yasa take fadin duk abin da yazo bakinta. Kalmar karshe ce dai sai da ta fito ita kanta taji nauyinta. A karon farko taji kunya ta mamayeta. Harshenta ya yi nauyi a bakinta da kyar ta juya shi ta sake hada wasu kalmomin da suka fito kamar mai rada.

"Ba haka nake nufi ba."

"Bani da kyau kenan? Allah Sarki Abbati..." ya furta yana mayar da muryarsa irin ta mai shirin kuka.

Da sauri Farha ta ce "kana da kyau mana."

"To za ki yi hoton dani? Please Ya Farha."

"Idan Allah Ya sake hadamu." Ta ce tana murmushi sosai.

"Zai hadamu. Ina ji a jikina in sha Allah idan na sake zuwa Kaduna zan nemeki ki cika alkawari. Wace kala ki ka fi so?"

Duk da ta soma rikicewa sa zantukansa amma ta bashi amsa.
"Orange"

"Ina fatan ganinki cikin kaya masu wannan kalar a haduwarmu ta gaba. Mu kwana lafiya Ya Farha."

Da kyar ta iya cewa "Allah Ya bamu alkhairi."

Kafin ya ce Amin ta kashe wayar. Juyawa tayi za ta bar kitchen din ta hada ido da kannenta sun zuba mata nasu idanun.

"Ya ku ka kare ne Ya Farha?" Cewar Sauda tana kanne ido.

"An kare a matakin ina karbar wayar nan in tura number dinta mana" Mardiyya ta bata amsa.

Kasa ce musu komai tayi kuma bata ji tana son hana a tura nambarta ba. Bata san me take ji ba har suka fice suja barta. Haka ya karasa daren har ta kwanta tana tariyo hirarsu tana murmushin da bata san dalilinsa ba.

Could this be love knocking at her door?

Da ta kwanta ranar mafarkin Abbati ta dinga yi a daidai lokacin da ya bude motar nan ya fito suka gudu. Bambamcinsa da haduwarsu ya zahiri shi ne (Ya Farha) da ya dinga kiranta...

*

Bacci yaki zuwa kamar yadda Shazali ya yi niyya saboda aikin tunani da ya bawa kwakwalwarsa. Neman hanya yake komai kankantarta da zai dauwamar da su Munzali akan sana'ar da ya zama sanadin fadawarsu gareta. Abbati bashi da hankali da har zai tunkare shi da maganar tuba. Dariya ce ma ta taho masa da ya tuna yanayin fuskarsa a jiya da ya fada masa. Idan sun san wata basu san wata ba ai. Shi mutum ne da zai iya komai domin biyan bukatarsa. Da ya ce zai biyosu nadin sarautar tudun dafawa yazo nema kuma ya dace da samu.

A sanin da ya yiwa Munzali tun kuruciya ya fahimci shi yaro ne da ya rasa sa ido da kulawar iyaye. Sai aka yi sa a sakacinsu ya cire masa tsoron sab'a musu da kaunar faranta musu. Yana da yakini mai girma cewa ko a gaba kwai ya fashe daga Munzalin har iyayensa ba za su ji ciwo kwatankwacin na Abbati ba. Sudaddiyar habarsa da babu alamun gashi ya shafa, murmushi na mamaye fuskarsa.

Ya shiga har falon uwar Abbati. Kirjinsa har dokawa sai da ya yi saboda tsantsar haiba da tawali'u irin na matar. Bai hango komai tattare da ita ba sai kyawun hali saboda yadda ya kula mutan gidan suna shiga taitayinsu a gabanta. Kudin danta zai iya saya mata rigar mutumci amma bai isa ya saye shi duka ba. Dole ne ma kyawawan halayen da a haduwar farko ya tsammaceta dasu su taka tasu rawar.

Mahaifinsa kuwa tare suka yi sallar magariba da isha'i a masallacin kofar gidan. Bai yi masa kama da mutane masu hayaniya ba. Ya dai karanci akwai shakuwa irin ta uba da babban dansa a tsakaninsu. Shi ma din zai iya cewa ba kudi kadai ya kawo musu wannan jituwa ba. Uban yana kaunar dansa.

Kuskuren iyayensa daya. Almajiranci da suka tura shi!

A gefe guda kuma ga kawunnai da 'yan unguwar da zai rantse da Abbati zai tsaya takarar siyasa baya jin za a sami kuri'ar wata jami'ar daban da tasa daga garesu. Karara ake ganin yadda kowa yake kaunarsa.

He has everything to loose idan asirinsa ya tono. Kwafa Shazali ya yi ya zauna jiran shigowarsu. Lokaci bai tsawaita ba Munzali ya shigo falon zai wuce dakin da ya zama nasa duk lokacin da suka zo tare. Bai kula da Shazali a falon ba saboda an kashe fitila mafi haske sai wata mai dan duhu daga can gefe. Hankalinsa yana can duniyar tunanin samun masoyiya da Abbati ya yi. Dadi yake ji tare da fatan Allah Ya daidaita zukatansu ita ma ta so shi. Da sai tafi kowace mace dacewa da mutum mai kyaun hali da iya kulawa da wanda yake so. Gashi ta zo a daidai lokacin da zasu gyara rayuwarsu. Babu abin da zasu ce da Allah sai godiya. Yana shiga daki ya yi shirin bacci don ba zai jira shigowarsa ba balle su tsaya hirar da zai shiga hakkin Hanne.

Rabin awa da shigowar Munzali sannan Abbati ya shigo. Fuskarsa bata yi kokarin sakaya farincikin da ya lullube zuciya da ruhinsa ba. Hirarsa da Farha ya dinga tariyowa yana murmushi shi kadai, sai ka rantse hirar soyayya ce. Karon farko a rayuwarsa da yaji zuciyarsa tayi nauyi saboda cika da soyayya irin wadda ta halatta tsakanin masoya. Feeling ne da yafi karfin kwatancen baki ko rubutun alkalami. A gareshi Farha tamkar numfashi take tun yanzu. Yana ji a jikinsa ita din alkhairi ce mai dorewa a rayuwarsa. Zai yi bakin kokarinsa su gyara rayuwarsu shi da Munzali domin tsaftatacciyar rayuwa yake yi musu fata daga wannan lokaci.

"Abbati in babu damuwa ina son magana da kai."

Muryar Shazali ce ta katse masa tunanin da yake neman kaishi duniyar taurari shi da Farha. Cak ya tsaya ya juya bangaren da ya ji muryar domin da fari bai kula yana wurin ba. Wayarsa ya miko masa ya karba sai dai ko sakan talatin bata yi ba a hannun nasa ya saketa a kasa a gigice.

"Shazali meye wannan?" Ya furta a hankali baki na rawa.

Guntun murmushi ya yi kafin ya ce "Abbati ne da His Excellency gwamnan..."

Toshe masa baki Abbati ya yi da sauri yana cewa "Baka da hankali ne? Gidana ne nan fa akwai mata ta a ciki."

"Oh haka ne fa" Shazali ya ce da sigar shakiyanci "gudun kar ta ji ta fita ta tona maka asiri a gidanku sai ka bani aron lokaci muyi magana."

Da wani irin yanayi mai ban tausayi ya nuna kansa "Ni za ka yiwa haka? Shike nan mu fita daga waje" Abbati ya ce yana yin hanyar kofa a yayinda duk wata na'ura mai sadar da sako a jikinsa ta dauki zazzafan caji.

Abinka da kauye goma saura na dare amma kusan babu kowa duk an shige gida.

"Menene ma'anar wannan vidiyon? Jiya baka nuna min komai na rashin dadi ba har na baro gidanka" Abbati ya tambaya suna tsayuwa a bangaren hagu da gidansu jikin wata bishiyar dabino.

"Saboda ban riga na fahimci sagegeduwar da kake son ku yi min bane. Abbati kai da Munzali ba za ku iya barin sana'ar nan ba. Nayi magana da Mr. Lewis abin ya wuce tunaninka."

Bai sani ba da kirjinsa da zuciyarsa waye ya kumbura. Shi dai ya ji kamar baya iya jan numfashi saboda takurar da kirjin ya yi gabadaya. Yawun bakinsa ya kafe da kyar ya iya tambayarsa cikakken bayani. A take Shazali ya hada masa kaso sittin na gaskiya ya gwama da kaso arba'in na karya aka tashi dari.

"Jiya kana tafiya na fadawa Mr. Lewis yadda muka yi da kai. Idan da kaji irin masifar da ya dinga yi min da barazana sai ka tausaya min. Abbati da manya kuke mu'amala. Mutanen da suke juya kasar nan tamkar kwallon wasan yara. Kun gama sanin sirrinsu kila harda wanda bai shafi abin da kuke yi tare ba. Shi ya turon bidiyon nan da wasu ma na Munzali"

Jikin Abbati ya soma sanyi domin ya fara dauko hasken inda maganar ta dosa.

"...janyewarku a yanzu da kuke ganiyar samun kudi da yin suna a tsakaninsu ba komai zai harfar ba sai zargi inji Mr. Lewis. Mutanen nan zasu iya tunanin ko abokan hamayyarsu a siyasance ko kuma ta bangaren kasuwanci ne suka biyaku domin ku tona musu asiri. Idan kuma gajiya kuka yi to ka sani sune a sama. Gajiyawarsu ce gajiya ba taku ba. A takaice ina jiye muku tsoro domin tabbas rayuwarku tana daf da zuwa karshe" dan shiru ya yi yana nazarin Abbati wanda banda bugun zuciya komai ya tsaya masa.
"Maganar daya ce wadda gudun faruwarta ya kawoni gareku yanzu. Zaku iya daina amsa kiransu to amma wallahi babu abin mamaki idan aka ji kun yi hatsari ko gobara an sallaci gawarku. Ko kuma wadannan bidiyon su zaga danginku. Kar kaji haushina. Turo ni akayi na yi muku barazana idan ba haka ba harda ni zata kwabewa. Kuma yau ko mutuwa kuka yi sirrin nan dole ya fito domin maganar gaskiya mutanen nan suna da makiya. Kuma makiyan nasu da hannunsu yawanci wurin fitar musu da sirri. Wannan bidiyon ma a wurin mai kawo abincin hotel din da kuka je aka samu. Na san ka fi Munzali nutsuwa shi yasa na zabi fada maka. Abbati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login