Showing 213001 words to 216000 words out of 242549 words
ta ce "don Allah rakani baiwar Allah."
"Wancan kofar ce" Farha ta furta da sauri don bata son shiga.
Daddy ya dubeta da shanyayyun idanunsa na 'yan duniya ya ce "ki taimaka ki rakata zan koma in shigo da mota naga maigadin ya fito"
Yawu Farha ta hadiya ta kalli gate din. Tabbas maigadin ta gano yana yiwa dan saurayin da bai fi Lilu ba inkiya da ya zo zai bude masa gate. A gefe guda Umma Lami ta cigaba da sharar hawaye. Ba yadda ta iya dole ta taka kafafunta inda take ganin kamar bai kamata ta je ba. Shi kuma Daddy da yake bai san me ya faru ba ga kyakkyawar fuskar Farha da ta hargitsa tunaninsa tuni ya shigo da motar ya take musu baya. Umma cewa tayi babu lafiya a gidan Munzali. Tunda bai manta yanayin da suka riski gidan da ya kai Zakiyya ba sai bai alakanta abin da barnar da ya aikata ba.
***
"Mu baka fada mana su waye bakin ba."
Alh. Rabi'u ne ya yi tambayar yana mai yiwa Mami kallon kurilla.
Tashi tsaye Abbati yayi ya ce masa "Munzali zai yi muku cikakken bayani" sannan ya yiwa Hanne da iyayensa nuni da kofar dakin da suka fito "mu shiga ciki mu basu wuri."
Wani irin abu mara fasali ne ya sami damar tokare wuyan Munzali da jin furucin Abbati. Gwiwa a sake yana jin jiri na dibarsa ya sami wuri a kusa da Suhaib ya zauna. Falon baki dayansa daga iyayensa har na Abbatin suka shiga cikin rudani. Ba don komai ba kuwa sai kasancewar ba a taba ji ko ganin gilmawar wani abu makamancin wannan a tsakaninsu ba. Ko sallamar su Farha babu wanda ya ji sai idanu da aka kafe Abbati da Munzali dasu.
"Da me kake so naji Abbati?" Munzali ya dago kai yana dubansa ya yi masa tambayar a zuciye.
"Da abin da ka ke jin kai kadai Allah Ya bawa wuyan dauka mana" shi ma ya mayar masa da amsa cikin fushi.
Dama ya san dole ran Abbati ya baci. Amma bai yi zaton abin ya yi masa zafin da zai tona musu asiri a gaban kowa ba. Muryarsa yaji ta karye, kuka na barazanar kwace masa. Idan Abbati ya fita daga rayuwarsa tabbas rayuwarsa za ta tawaya. Rabuwarsu bata da muhalli a kowace mahanga ya dube ta.
Tashi ya yi ya karasa har inda Abbati yake tsaye ya ce "A waje na b'ata maka rai, don me za ka kawo maganar gaban iyayenmu?"
"Saboda su shaida cewa ..."
Katse shi ya yi kafin ya kai karshe ya ce "kalamaina kuskure ne kuma kai ma ka sani. Ashe ban kai matsayin da za ka yafe min idan nayi maka laifi ko da ban baka hakuri ba?"
Yadda murya da yanayin Munzali suka sauya a lokacin da ya yiwa Abbati wannan tambaya sai da ya sanya kwalla zuwa idanun duka matan wurin. Harda Asabe kuwa domin jikinsa ya nuna asalin sallamawa ga abin da yake neman fin karfinsa.
Gorin haihuwa akwai ciwo. Takalmin wanda bai haihu ba baya taba yiwa wanda ya haifa daidai. Shi yasa fahimtar halin da zukatansu suke shiga a lokacin da aka goranta musu yake da matukar wahala. Ciwon yana ninkuwa ne a yayinda gorin ya fito daga bakin wanda kake tunanin matsalarka tashi ce. Shi yasa duk dauriya irin ta Abbati ya kasa hakura. Wani kuskuren yinsa ma babban kuskure ne!
"Fadin abin da yake zuciyarka ba shi ne laifin ba. Zuciyata ta kasa nutsuwa da tunanin kila na saba yi maka wasu abubuwan da suke sa kayi tunanin don ban haifa bane nake aikatasu."
Magana Mal. Inuwa ya so yi sai Mal. Sa'idu ya hanashi. Ya kuma nunawa kowa alama da hannu akan kada su shiga wannan rigimar. Baaba Mari kwalla kawai ta dinga sharewa. Tsaftatacciyar alaka ma ba a rabata da sharin shaidanu daga aljanu da mutane balle kuma tasu. Tausayi suka kara bata ta kuma godewa Allah da bata gaggauta rabasu kamar yadda tayi niyya ba. Maganar da Munzali ya yi a wannan gabar wadda ta tab'a zukatansu ita tayi sanadiyar dawo da zaman na abin da aka yi dominsa tun farko.
Da idanuwansa wadanda suka kada kamar garwashi ya dubesu ya ce "bani da wata kalmar kare kai ko ban hakuri da zan fada maka. Idanuna ne suka rufe dazu har nake ganin kamar ciwon da nake ji baka jin irinsa shi yasa ka kasa fahimta ta. Sai yanzu na gane cewa a cikin komai akwai hikimar Ubangiji. Ya bani haihuwa amma bana cikin mutane masu bin komai cikin lumana domin samun maslaha musamman akan abin da ya shafi wadanda nake so. Sai Ya hadani da kai. Ya baka nutsuwa da hangen nesa domin ka nuna min hanya idan na makance. Abbati wannan bai isheka dalilin yafe min ba? In kuma ba za ka yafe ba ai ka san cewa baka da ikon rabani dasu Baaba. Saboda haka duk abin da ya shafi Qibdiyya dole ne su sani."
Kallo sai ya koma kan Abbati. Murmushi ya soma yi wanda yake tafe da dariyar farinciki. Ba yace ga kalmar da ta haska masa zuciya ba a zantukan Munzali. Ya dai san kawai komai ya wuce har kasan zuciyarsa.
"Baka ce komai ba?" Munzali ya tsokane shi shima yana dariya.
Hankalin kowa sai ya kwanta har nutsuwa ta maye gurbin tension din da ya gauraye da iskar falon.
Kujerar da Munzali yake shi ma Abbati ya zauna suka saka Suhaib a tsakiya. Da Abbati zai fara yi musu bayani sai murmushin fuskarsa ya bace sai damuwa da alhini.
"Jarabawa ce Allah Ya dora mana irin wadda bamu taba tsammani ba ko a mafarki. An wayi gari an sami wani mara tsoron Allah ya raba Qibdiyya da mutumcinta."
Da wanda ya sani da wanda ya sami labari yanzu baki dayansu sai da suka ambaci kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Gumi kamar ruwa a take ya fesowa Daddy. Cikinsa ya kulle yayinda ya fara tunanin hanyar gudu. Yadda yake rarraba idanu yana cilla kai kamar kadangare ne ya dauki hankalin Farha. Ita da shi daga bakin kofa dama suka tsaya. Abbati ne bata son ya ganta shi kuma mara kunyar karyar Munzali yake gudu saboda karonsu na dazu.
Duk wata alama ta rashin gaskiya da firgici ta nuna kanta a tattare dashi. Wannan yasa Farha taji wani abu ya darsu a ranta. Suna jin an fara tambayar waye ya yi sai taga ya juyo da sauri da nufin fita. Ta kalle shi ta tabbatar bata yi kuskuren ganin tashin hankali mara misaltuwa a tare da shi ba. Alamun rashin gaskiya sun dabaibaye fuskarsa ta yadda mutum ba zai fassara tashin hankalinsa da damuwa akan yarinya ba kadai. Ba tare da dogon tunani ba kawai tayi shahada tayi abin da zuciyarta ta raya mata. Qibdiyya ta kwallawa kira wanda hakan ya yi sanadiyar da kowa ya kallo bakin kofar.
Qibdiyya dake zaune a jikin Zakiyya daga kai tayi ta hango mai kiran da na kusa da ita. Nan da nan tayi mummunar razana. Farha ta dad'a samun yakini akan zarginta. Daddy bai yi aune ba tayi saurin rufo kofar ta rike hannun taki matsawa. Ai da ya fahimci me tayi bai san lokacin da ya yi wasu kwararan taku biyu ya isketa ba.
A wajen Qibdiyya zaman da akayi da zantukan da suke yi babu wanda ta fahimta. Abu daya ne ta sani shi ne yawan tambayar da aka dinga yi mata akan abin da yake mata. Shi yasa tana hango shi ta soma kuka tana cewa
"Ban fada ba Uncle Daddy. Don Allah kada ka yanka min Mummy da Daddy da Papa" ta dubi Munzali wanda ya yi mutuwar zaune da idanuwanta wadanda suke nuni da jigatar da tayi daga jiya zuwa yau ta ce "Daddy kaima ai ban fada maka ba ko? Kaima haka ko Papa" ta kare tana duban Abbati.
"Baki fada ba Mamana" Abbati ya amsa da kyar don magana ma baya son yi. Shi da Munzali da Lilu da uwar gayya Zakiyya duk kofar suka nufo cikin sauri.
Daddy yasa karfinsa zai ture Farha ya fita ita kuma taki sakin hannun kofar.
"Ki bani wuri kafin nayi miki lahani"
Ya yi maganar a fusace yana mai dunkule hannu zai kai mata naushi a inda ya san za ta wahala. Jikinsa ko ta ina rawa yake saboda tsoro. Fuskarsa duk ta canza ta rikice da fargaba. Amma ko gezau taki saki. Tunda Allah Ya kubutar mata da kani tana jin abu na karshe da za ta yi shi ne bayar da gudunmawar kama ainihin mai laifin.
Hannun nasa ya kusa sauka a cikinta don har ta runtse idanu taji shiru. Tana bude ido taga Abbati ne ya rike hannun naushin. Munzali kuma ya sauke masa wani wawan mari wanda sautinsa ya karade falon. Yayinda Lilu ya janyeta zuwa gefe. Zakiyya kuwa da babu wanda ya kula kujerar dinning table ta kinkimo. Munzali na sauke hannunsa ta rotsawa Daddy kujerar a kansa. Ta gaban kansa inda ya tara wata uwar suma a dukunkune kamar mahaukaci sabon kamu ya dinga tsarto da jini. Durkushewar da yayi da jinin dake zuba basu sa taji sassauci ko digo a ranta ba. Shi yasa ya sake daga kujerar za ta kuma buga masa.
"Kada ki yi kisa 'yar nan. Ki bari a bi komai cikin lumana"
Ashar ta debo za ta saukewa mai ambaton lumana bayan abin da aka yiwa gudan jininta sai tayi ido hudu da Mal. Inuwa. Albarkacin furfura da yaci yasa ta saki kujerar ta kara fashewa da kuka. Ganin yadda falon ya koma da sauri Baaba Mari ta dauke Qibdiyya ta koma dakin da suka fito.
Duk wannan abin da akeyi ashe Lami suma tayi tun yunkurin Daddy na farko wurin fita. Mami Khadija tana tsakar godiya ga Allah da Ya wanke mata d'a tun kafin ayi nisa ce ta fara lura saboda a kusa da ita take zaune. Kanta ta gani ya langabe gefe guda ta rufe idanu. Da hanzari ta tabo Asabe wadda daga gani ta fahimci 'yan uwa ne saboda kamanninsu. Ita kuma da kuka ta hau ihu tana kiran sunan kanwarta.
Da kyar aka samu ta dawo hayyacinta. Tana bude ido ta yunkuro ta zauna kowa yana yi mata sannu. Mutum guda ta nema da ido tayi sa'ar gani, wato Zakiyya. Ta isketa tayi kuka har ta gaji. Fuskar nan ta cabe da hawaye da majina.
"Matso" ta kirata da hannu.
Zakiyya na matsowa kuwa ta cire hannu ta tsinketa da mari.
"Baki da hankali ne Lami?" Asabe ta furta da mamakin wannan hukunci "ga wanda za ki mara can fa" ta nuna Daddy a zaune a kan kafet da jini a fuska.
"Ita zan mara Yaya Asabe. Zakiyya zan fara hukuntawa domin ita ce silar komai."
"Umma ni kuma?" Zakiyya
Mami Khadija na jin haka sai ta mike. Duka 'ya'yanta ma suka tashi. Baaba Mari ma ta ce da Hanne ta samo abinci ta biyota ciki a bawa Qibdiyya.
Umma Lami ta gyara zama ta hanyar sauko da kafafuwanta daga kan kujera ta ce "ina za ku? In kowa zai fita ke Hanne da wannan budurwar..." Ta nuna Farha "ku dawo ku zauna. Abin da zan fada zai iya amfanarku tunda baku wuce shekarun haihuwa ba". Ko ba a fada ba a kallon fuska kawai mutum zai karanto ciwon da yake cin zuciyar dattijuwar nan.
"Zakiyya kin cuceni kin cuci kaninki da 'yar cikinki. Komai lalacewar dan iska a kullum yana kokarin yin abinsa ne a nesa da gida. Ma'ana cikin gidansu ko inda idon sani zai iya gani. Amma yau a dalilin sakacinki irin wannan kwad'on mara dadin ambato ya faru a tsakanin zuri'ata"
Hakuri 'yan dattijan suka dinga bata ta girgiza kai tana cije baki.
"Gado ne kadai Allah bai shardanta tsakanin Daddy da Qibdiyya ba. Banda shi duk wani hukuncin da ya hau wuyan mahaifinta na halacci da haramci shi ma yana kansa. Wane irin hakuri zan yi? Wallahi da ganin irin wannan bakar rana gara ace mijina na kama da mace akan gadona."
Mami Khadija taji gabanta ya fadi domin kalaman karshen sun ratsa ko ina a jikinta. Ji tayi kamar da ita matar nan take.
Zakiyya kuwa cikin kuka ta ce da maihafiyarta "Mene ne laifina Umma? Ta yaya bacin rayuwar Qibdiyya zai zama laifina alhalin ni ba mazinaciya bace?"
Numfashi mai tafe da zazzafar iska mara dadi Umma Lami tayi fashin baki akan bakincikin da ya sark'esu muddin rai.
"Zakiyya kowane bawa bai isa ya tsallake kaddararsa ba ni na san wannan. Na kuma yarda kaddarar yarinyar nan kenan. Matsalar shi ne ke kika zama silar tabbatuwar kaddarar. Akan mutuwar aurenki kin zo kin ce Munzali yana yi miki boye-boye. Don kin matsa da tambaya ya koroki gida. Amma ni nafi tunanin shegiyar kyuya da gandarki ce ta kashe miki aure. Babu abin da yake kayatar dake sama da danna waya, kallo da bacci. Sau nawa Qibdiyya za ta dinga kwala miki kira daga bandaki kiyi ta jera mata ina zuwa akan uzurin banza? Ko kin manta ranar da kika bari har bayangida ya soma bushewa a jikinta saboda bana nan. Sai da na shigo nace miki zai maidota gidan ubanta?"
"Naji ban kyauta ba amma Umma meye hadin laifina da abin da Daddy yayi?"
"Son zuciya. Yawan fadan da nake yi miki sai ki ka mika masa matsayinki na uwa. Daga bata abinci aka koma cire uniform da sakawa (bata san idan bata gida harda tsarki da wanka Zakiyya take saka shi ba). Ko shi ya kawota duniya ai akwai abubuwan da basu dace uba ya yiwa diya mace ba. Kuna son haihuwa amma ba kwa jure raino. Da yawan matan da irin haka yake faruwa da yaransu idan an bi sila baya rasa nasaba da sakaci ko yaya ne (Ban ce duka ba! Mau'du'in labarinmu yana magana ne akan sakacin). Muna cikin zamanin da uba mahaifi yake iya ajiye mutumcinsa ya taki tsatsonsa mace ko namiji. Kinga kuwa halin ko in kula ba na uwa bane. Sai kin yi da dukkan gabbanki ki kuma hada da tsananta addu'a wadda bana jin ke kina ma tunawa da cewa ya kamata ki dinga yiwa 'yarki. A soyayyar baki da daukarta a hoto ki ka fi kauri."
Dukar da kai Zakiyya tayi yayinda kukanta ya kara tsananta. Tabbas mahaifiyarta ta fadi gaskiya. Kuma ita shaida ce cewa indai ta gani sai tayi mata fada akai.
"Baki yi mana adalci ba Zakiyya. Abu irin wannan ya faru amma na rasa kukan me zan yi? Sannan ina ji ina gani dole in cigaba da kwana gida daya da wanda ya yiwa jikata haka tunda nice uwa a gare shi. Duk bacin ran da zan shiga ba zan iya korar shi daga gida ba kada yafi haka lalacewa."
Maganganun Umma Lami sun bawa kowa tausayi harda masu kuka. Musamman Farha da Hanne wadda ta kara tsorata da sharrin kyuya. Daga nan iyayen suka saka baki aka jajantawa juna.
Wadannan zantuka musamman na Umma sun tsayawa Munzali kwarai a zuci. Kansa ya kara dorawa laifin abin da ya faru. Ya kuma gaskata cewa lallai bawa bai isa ya yiwa Mahaliccinsa wayo ba. A lokacin da rayuwa take gara musu, suna tsaka da samun kudi kamar ruwan sama ya aureta bisa umarnin Asabe. Na farko babu soyayya sannan sam aure baya gabansa. Saboda haka ba shi da lokacinta. Tun tana kuka da korafi har ta saba. Waya da tv suka zama abokan hirarta. Ga masu aiki har biyu ya dauko sannan ga kudi baya yankewa. So ya yi ya dauke mata hankali da jindadin duniya. Sai dai bata jima ba cikin rayuwar ba-cas-ba-as ta gaji ta sake kafa masa kahon zuka. Shi ne dalilin sakin. To ashe da wannan sabon na rayuwar da ya koya mata ta tafi. Gashi 'yarsa ce ta kwana a ciki. Shi yasa da ya kalleta yaga yadda take zubar da hawaye ta bashi tausayi.
Kallonsa ya mayar ga Daddy ya hadiyi yawu da kyar.
"Tsakaninka da Allah tun yaushe ka fara bata Qibdiyya?"
Amsar tambayar famin ciwo zata zama shi yasa Abbati ya nemi dakatar dashi.
"Munzali.."
Runtse ido Munzali ya yi ya gyada kai alamun ya hakura da tambayar sai ya canja wata "Me yasa sai ita? Ya aka yi ka iya keta haddin yarinyar da idan kaf matan duniya sun kare ba za ta taba halatta a gareka ba."
"Ku yafe min" ita ce kadai amsar da ya iya hadawa da busassun labbansa.
"Kada ka yaudari kanka. Duk fadin duniya babu wanda ya isa ya yafe maka a madadin Qibdiyya. Ka roki Allah tsahon kwana domin ka roketa da kanka."
Daga wannan bai sake cewa komai ba ya tashi ya bawa su Mami hakuri sannan ya fita daga bangaren. Sam zuciyarsa babu dadi. Yana son ya hada Daddy da hukuma a sauya masa kamanni amma cikin ransa yana jin kamar bai cancanci yin haka ba. A matsayinsa na uban Qibdiyya wanda jirwayen kazantar rayuwarsa yabi 'yarsa ina shi ina ganin laifin wani?
Gwiwoyi a sake Umma da Zakiyya suka tashi zasu tafi. Baaba Mari ta riko hannun Qibdiyya ta damkawa Zakiyya tare da cewa,
"Ki tafi da ita domin yau tafi bukatarki akan kullum"
Da zasu fita ne Qibdiyya ta ce "Papa ina wayar da na baka?"
"Subhanallah" ya furta da sauri don shaf ya manta ta bashi waya ta ce ya kira. Aljihunsa ya laluba ya daukota ya kunna. Cikin sa'a ya samu akwai chaji. Ya duba wurin sunaye yaga 'Alhajina' da wannan ya yi tunanin ko waye kila yana da alaka da mai wayar sai ya kira.
I just published "45" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221355822?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=vwihQZy0W9YXQvP7R%2FtMltmxa%2F15b2tHeN1txxBjr5ZBvikcf3aylzrsi7bsEL83RMwgrLdcJNzrbHKFPZyf7VdK9pZmM8onmizYpGjR2yXyiR2cyhJyZU8jw%2F6BvX%2B%2B
UWA UWACE...45
Batul Mamman💖
Da shigar kiran ko dan sautin nan na alamun ta shiga da mutum yake ji idan tana ringing bai kare ba aka dauka.
"Abdul?" Abbati ya ji an ambata da muryar da ake iya gane tana cikin tsananin tashin hankali.
"Ba Abdul bane. Na sami..."
Katse shi Alh. Sadisu ya yi cikin matsanancin bacin rai ya ce "Waye kai? Ina dana? Wallahi duk inda kuke a kasar nan sai an nemo min ku"
Duk inda aka yi shi ma dansa Shazali ya dauka, Abbati ya ayyana a ransa. Tunanin hakan yasa shi kashe wayar ya duka a gaban Qibdiyya ya ce ta fada masa a yanayin da ta baro mai wayar cikin dabara.
"A gidan da