Showing 168001 words to 171000 words out of 242549 words
kama ya rabasu da yatsun nasa. Sau daya ya murda su duka suka ji sautin budewar kofar. Mubashir dake faman gumi zuwa yanzu ya sake kama hannun kofa wannan karon. Shi fa burinsa ya bar gaban uban ko ta wane hali. Saboda shi da kansa ya san cewa bai taba yin laifi kwatankwacin wannan ba, shi yasa hankalinsa gabadaya ya tashi. Gani yake suna hada ido zai gano duk abubuwan da suka wakana a wurin party din.
"Irin wannan patin kuke kira till dawn ko?"
Shiru babu amsa daga Mubashir kuma har yanzu hannunsa yana jikin hannun kofar amma ya daina murdawa.
"Ban hanaka zuwa ba jiya bayan na gama jin shirinka da wani a waya."
Ras, ras, ras...haka gaban Mubashir ya cigaba da faduwa yana sauraron mahaifinsa a tsorace.
Salihi ya daure zuciyarsa iyakar dauriya saboda warin hayaki iri iri da yake ji a jikin Mubashir. Da wahala idan bai sha kayan maye ba ko tarkacen hayakin. Sassauta murya ya yi sai ka rantse kuka ne zai kwace masa a kowane lokaci.
"Tsakaninka da Allah Mubashir idan ka kwatanta abin da akayi a wurin da kaje da tarbiyar addini da ma maslahar zamantakewar dan Adam kana tunanin Annabin Rahama zai yi maraba da kai?"
Fada, mari, zagi, tsinuwa ko duka sune abubuwan da yasa rai dasu. Ko kadan bai yi zaton wadancan kalaman ba. Daga kai ya sami kansa da yi ya kalli babansa. Duk wani zafin kai na matasa sa'anninsa sai ya kufce masa. Rashin kunyar da aka koya masa koda zata baci irin yanzu yaji babu guda da zai iya. Allah SWT Yafi komai da kowa. Sunansa kadai da aka ambata gami da kwallar disappointment a idanun mahaifinsa sun dagula masa lissafi. Ba yadda ya iya dole ya girgiza kai a matsayin amsa ga tambayar da aka yi masa. Ta yaya ma zai yaudari kansa yace inda yaje bai sabawa musulunci ba?
Kogin tunanin da ya fada da mabambantan yanayin dake bayyana a fuskarsa kowace dakika sun sanyaya ran Salihi. Alamu ne na cewa tarkonsa ya kama kada. Da shirinsa ya shigo dakin Mubashir domin yana fata yau ta zama rana ta farko kuma ta karshe da irin wannan fadan zai shiga tsakaninsa da dansa. Wayarsa ya kunna har yanzu suna tsaye a bakin kofar ya kunno abin da yake so ya nuna masa. Bidiyo ne wanda ke nuni da jama'a suna jam'in sallah. Bayan kamar sakan goma anyi kabbarar dagowa daga sujjada amma wani matashi a sahun gaba bai tashi ba. Koda aka sallame aka duba ashe rai yayi halinsa. Mutane suka yi ta kabbara da ambaton Innalillahi.
Mubashir bai san lokacin da ya soma kuka wiwi ba yana cewa,
"Baba kaga fa ya rasu"
"Kamar haka ne ajali ke riskar kowane bawa a lokacin da bai yi zato ba. Da ace naka lokacin yayi a jiya karshenta da sai dai yanzu a kirani inda kaje party ace inzo in karbi gawa" tsigar jikin Mubashir ta tashi da tunanin hakan kawai.
Salihi kuwa dafa kafadarsa ya yi suna fuskantar juna.
"Abin tunani shi ne da ace kaine na cikin bidiyon nan da kila har nima na koma ga Allah ina bada labarin mutuwarka. Kai nayi imani 'yan bakinciki sai sun mutu saboda sun san cewa nayi babban rabo. Ranar lahira mune 'yan hura hanci saboda nayi dacen samun dan da Allah Yake so har ya karbe shi a sujjada. Haka zaka karbi cetonmu ka kaimu aljanna idan ayyukan alkhairinmu sunyi karanci" Sai da ya ja numfashi sannan ya dora da "da kuma ace ka mutu a wurin patin haka zanyi ta boye fuska kada idon sani su ganni. Kuma ina mai imani da cewa zan dawo gida nayi ta gillawa mutane karya. Ba zan taba yarda a san a inda ajali ya riskeka ba. Kaga anyi biyu babu. Ka tafi a banza ka bar ubanka zai tafi a hofi tunda ya zama makaryaci"
Jikinsa Mubashir ya fada yana kuka duka jiki na bari. Salihi ya dinga bubbuga masa baya da rarrashi. Sai da ya kula nutsuwa ta zo masa sannan ya yi masa tambayar da ta zo masa a ba zata.
"A ina ka sami kudin da kayi waccan soyayyar? "
***
Bacci mara dadi Uwani tayi sakamakon abubuwan da suka faru a gidan Munzali jiya. Da suka dawo gida tare da Asabe tayi mamaki sosai da Innayo bata tambayeta daga ina suke ko dalilin fitarsu tare ba. Kalmar 'kema 'yarki ce' da Munzali ya yi amfani da ita lokacin da yake cewa ba zai roketa rufin asirin Qibdiyya ba tayi mata karan tsaye a wuya. Makomar rayuwar yarinyar a gaba ya sanyata cikin damuwa. Shikenan rayuwarta ta baci tun yanzu? Sai kuma nata 'ya'yan da basu wani dameta ba suka fado mata. Anya ta ma san wani abu cikin rayuwarsu sama da dan abin da ba a rasawa? Irin abin da kowa ma zai sani muddin ya zauna dasu. Ita dai a matsayinta na uwa ba za ta dorar da komai ba. Babbar 'yarta Amira ta tuna. Yarinyar da har almajiri take sawa yi mata tsarki lokacin da take karama saboda bata son tashi daga kemis dinta. Sai ta bawa almajirinta mukullin gidanta ya tafi ya gyaro mata jiki su dawo. Kudi ne kawai a gabanta sannan bata son mai aiki mace don kada ta dauke hankalin mijinta. Ta biyun kuma Anisa a lokacin tata kuruciyar wani kanin Salihi da yake karatu ta sakarwa ragamarta. Sai da Salihin ya yi mata tatas lokacin da ya farga. Idan ma da mugun nufi kila har anyi an gama. Yaran basa kaiwa shekara biyar take barinsu su fara wanka. Saboda ita ce Uwani ina kika fito neman kudi, ina zaki neman kudi. Mubashir ne ma ya dan samu kulawa a matsayinsa na dan fari kafin ta gaji ta watsar. Duk wannan tunanin sai ya kare a inda take ganin cewa ai kudi take nema musu.
'Kudin da baki iya kashe musu' zuciyarta ta tuna mata.
'Kudin da suke neman salwanta a banza?'
Kamar an tsikareta haka ta tashi firgigit ta janyo wayarta. Nambar Habibu ta dannawa kira ta kara a kunne. Ta shiga har ta katse bai dauka ba. Ta cigaba da gwadawa missed calls sun kai goma zai gani amma duka shiru. Lokaci ta kalla sai taji bari tayi masa uzuri kila bai tashi ba. Nan kuma ta canja akalar kiran ga Salihi. Kiran yaje gareshi lokacin da Mubashir cikin kuka ya fada masa da kudin wa yayi sayayya. Sam bata yi la'akari da cewa yanzu ake sallar asuba ba. Kudadenta kadai take tunani.
Yana amsa kiran Uwani ta hau fada kamar ta ari ba. Bakinta yana kumfa saboda tsabar bala'i amma ko jan numfashi ta gaza yi.
"Wallahi Salihi ka fadawa matarka ta dawo min da kudadena da sarkoki. Ba yau muke tare da kai ba na san baka taba daukar min komai ba idan baka dashi. Ka fada mata ta dawo dasu idan ba haka ba police station zan kai maganar nan su kwatar min hakkina"
Ba speaker Salihi ya saka ba amma yadda Uwani take daga murya babu abin da Mubashir bai ji ba. Jikinsa sai ya sake yin sanyi. Kunyar mahaifinsa ta sake lullube shi. Hannu yasa ya karbi wayar ya kara a kunnensa.
"Umma ni na dauki kudin da sarka sai dai abin da ya rage babu yawa."
Yana gama magana ya mikawa Salihi wayar ya shige bandaki. To shi ma dai Salihin bai ce komai ba ya katse kiran ya fita yin alwala.
Uwani tafi minti biyar a zaune da waya a hannu. Ta san waye Salihi. Ta san abin da zai yi da wanda ba zai yi ba. Sanya Mubashir karbar laifin da ba nasa ba baya cikin abin da zata taba yarda zai yi. Idan ta kure zai iya karbar laifin amma ba dai yace wani ya karba ba.
'Mubashir?' ta dinga maimaita sunan a zuciyarta kamar yau ta fara ji.
"Kai! Ina! Sata?"
"Idan kin gama surutan ki tashi kiyi alwala ko ki rufe mana baki muyi sallah a nutse"
Juyawa tayi taga Innayo akan abin sallah. Bata san lokacin da ta shigo ba. Da azamarta ta tashi amma ta kasa fita yin alwalar. Kanta ya dauki mugun caji ne yana daf da bugawa. Yadda zuciyarta take zafi ko duka aka yi mata da itacen darbejiya ba za ta ji wannan radadin ba. Ayi maka gagarumar sata kuma ka gane dan cikinka ne ya aikata? Kamar sakarya haka ta dan tsaya galala da ta tuna yace abin da ya rage saura kadan. Tuntuni satar bata wani dameta ba saboda tasa ran Ummule ce. Ko ana tsiya tsiya sai ta fito da kudin domin kararta zata yi. A kwato mata kudinta sannan a nunawa Salihi kuskuren tunanin zai iya mata kishiya ya kwana lafiya. Jikinta, zuciyarta, ruhin dake rike da ranta da ma tunaninta a take suka koma na kankanuwar yarinyar dake tsananin bukatar mahaifiyarta. Ji tayi kamar an mata tsirara duk sanyin duniya ita yake duka. Uwa ce kadai zata fahimceta ta suturta ta. Aikin da take takama dashi karshenta sun rabu kenan, kudin da ya rage dan cikinta ya sace. Kudin Hajji kuma wani sashe na zuciyarta mai dan hankali ya dage akan ta nemi Habibu komai rintsi. Zargin da mijinta yake masa ya sanyata wasiwasi. A zatonta a dake ta soma magana, bata san tun a kalmar farko komai nata ya ruguje ba.
"Kiji wani abin mamaki Innayo. Sata aka yi min ta kudade masu yawa da 'yan sarkokina wai amma Mubashir yace shi ne. Ni kuwa me nayi masa da zai min sata irin wannan? Na wahala sosai ina hada kudin nan" sai hawaye sharrrr kamar famfo.
"Allah Ya kyauta. Matsa zan tayar da sallah."
Uwani ta girgiza kai ta dafa kafadun Innayo "baki gane ba Innayo. Ba labari nake baki ba ya faru ne a gaske. Kudin nan dashi nasa ran biyan KNUPDA su sakar min gidana. Bani da komai duk na kashe a gini da biyan Hajji. Wurin aikin ma sun dakatar dani saboda mugunta irin ta masu kudi."
Salima da Zara duk sun ji maganganun Uwani. Salima sai ta kasa hakuri ta shiga dakin. Da Innayo suka hada ido saboda ta juyawa Uwani baya tana share tata kwallar. Kwalla ce ba ta tausayin Uwani ba kadai harda ta kara ganin girman Allah. Soyayyar 'ya'yanta bata hanata hango cewa abin da ya sami Uwani harma da matsar bakinta ta tonawa kanta asiri duk yana cikin sakayyar Allah ba. Irin wannan lokacin take ta jiye mata. Halin rayuwa ya juyo wanda zaisa ta dawo gareta ba domin Allah ba.
Kai Salima ta girgiza mata don ta daina hawayen sannan ta da daga hannuwanta sama tana dariyar takaici.
"Allah Ya jikan Hasiya ba don ta mutu ba. Ta ce Allah Ya hadaki da babun da kike yawan kira watarana. Yau gashi kun gamu har ta fara saka ki kuka. To kadan ma kika gani wallahi" tayi kwafa da karfi "Baki ga komai ba. Uwa? Ke har kina tunanin kin ci bulus kenan akan hawayen Inn.."
"Salima ya isa!" Innayo ta fada tana riko hannunta.
Hannun ta janye ta cigaba da tsayuwa a gaban Uwani.
"Ki barni in sauke mata kafin Hasiya taji banyi komai ba tayi min Allah Ya isa."
"Nace ya isa haka. Idan kuma kema shaidanun ne dake shi yasa ku ke neman hanani yin sallar asuba to Bisimillah"
Bayan tafiyar Salima har Innayo ta idar da sallah Uwani tana tsaye. Da gaske kanta ya rikice har bata iya gane mai yake faruwa a kusa da ita. Zuciyarta ta kasa rabe mata tsakanin sace kudin da wanda ya sata wanne yafi dimauta hankalinta. Kai a takaice ma duk wani labari mara dadi da ta samu game da dukiyarta sai yanzu ya yi zaman dirshan a kwanyarta kamar wadda ta farka daga magagin bacci.
*
Da Innayo ta idar da sallah ta zauna tana addu'o'inta amma hankalinta yana kan Uwani. Abin da take gani shimfide akan fuskarta yafi karfin damuwa sai dai a kira shi tashin hankali. Tausayinta ne ya tsirga mata. Sai kuma kamar wadda aka girgiza tayi kokarin kawar da tausayi daga zuciyarta. Uwani ce fa! 'Yar cikinta wadda ta wahaltawa amma ta dinga wulakanta ta. Kalmar wulakanci ita ta dace da duk abubuwan da ta dinga yi mata a baya. Ta tuna mugun ciwon hakorin da idan ya tashi sai ta kusa fitsari a jikinta. Amma Uwani ta rufe ido tace bata da kudi. Kuma taki kaita ganin likita don kada a alakantasu da juna. Duk wata soyayya da uwa zata yiwa da itama tana yiwa Uwani, amma hakan ba zai sa zuciyarta ta kankare mikin da ta bar mata ba. Ba za ta taba yi mata baki ba amma ta san cewa lokaci zai musu alkalanci. Tana so Uwani ta rarrabe tsakanin zare da abawa, me yiwuwa hakan zai sa tayi hankalin da ta jima tana yi mata fata. Da wannan ta mike domin tunaninta ya karkata zuwa ga autarta magamin kukanta. Hasiyatu mai zuciyar zinare. Hasiya takwarar Asiya matar da ta gagari shaidancin Fir'auna. Jarumar matar da ta zama majinginar Annabin Allah Musa AS. Ita Innayo taga ranar sanyawa yaro sunan magabatan kwarai. Ta kasance cikin farinciki domin kuwa da kyawun hali da addu'a gashi matsalolin gidan Hasiyan sun kau. Suna cikin ganiyar samun rufin asiri, ana saka rai da samun lafiyar Abbas, gashi zuciyar Ayaah ta karkato daga hudubar shaidan. Sannan uwa uba ga rabo Allah zai basu na zuri'a.
"Salima idan kin sallami 'yan makarantar (yan matan 'ya'yanta) nan ki zo ki tayani yiwa kanwarki dambu."
Zara sai tayi saurin tashi ta goya 'yarta "Kawo in yi mata Innayo."
"Yi zamanki kada ki kwasar mata sanyi sanyin safiyar nan"
Kwance goyon tayi ta kwantar da ita a kusa da Salima.
"Gata nan bari inje in taya Innayo aiki"
Bata jira cewarsu ba ta fice. Tana isa rumfar da suke amfani da ita a matsayin madafi ta dinga share kwallar dake bin idanuwanta. Ita Zara me zata ce da duniya banda NAGODE. Ta koyar da ita darasi mai wuyar fassara. Mijin da take takama dashi har take wulakanta mahaifiyarta dominsa ya juya mata baya. A zahiri ya nuna mata har yanzu yana sonta. Amma ko kusa yaki sab'awa mahaifiyarsa akanta. Yaki kawo mata 'ya'yanta sannan yaki sanyawa jaririyarta suna. Innayo ce ta tsaya mata har tayi masa magana akan haka. Wayarsu ta karshe da ita bayan ta gama sauraron bayaninsa abu daya ta fadawa Zaran wanda ya sakata zubar da kwalla.
"Biyayya yake yiwa mahaifiyarsa wadda komai rashin dadinta gareni da tawa 'yar dole muyi hakuri. Ita Uwa ta wuce tunanin duk mai tunani. Allah ne kadai Ya san fadi tashin da tayi dashi kafin ya kai yanzu. Idan na ce ya sab'a mata dominki ina ganin ban yi musu adalci ba. Ki mikawa Allah lamuranki ki zuba ido ki ga yadda Ubangiji Yake shigarwa bayinSa fadan da yafi karfinsu"
Da yammacin ranar Innayo tayi sadakar kosai tayi tawassuli dashi akan nemawa Zara zabin alkhairi.
Kukan da tayi a ranar ko digo bashi da nasaba da halin da take ciki da mijinta. Hawayen na nadama ne da dana-sani. Sai kuma tsantsar godiya ga Allah da Ya ara musu rayuwa ita da Innayo din. Dole ne tayi amfani da wannan damar ta daidaita da mahaifiyarta.
Bata ji isowar Innayo ba sai muryarta da taji tana cewa "kin tuna lokacin da ake cewa kin fi kowa iya girki a gidan nan? To kiyi mata farfesu da naman kazar can na firij, ni kuma zanyi dambun. Duk na wanda tafi ci to mai shi tafi iya girki sai a daina cika mana baki."
Zara ta juyo da murmushi mai hade da hawaye. Innayo din ma da guntuwar kwallarta domin kuwa ta dan jima tana kallonta.
Abin da ba kasafai mutanen da suke yi ba Zara tayi a lokacin. Rungume Innayo tayi tana cigaba da kukanta. A haka take magana da dusashshiyar muryar da ta cakude da kuka.
"Don Allah Innayo ki ce kin yafe min. Ba wai don na koma gidansu Maryam ba. Sai don kawai wannan kullutun hakkin naki da na daukarwa kaina ya sauka daga kirjina"
Ta dago kai tana mai nuni da kirjinta.
"Na sani sarai cewa ban kyauta ba amma kaina na yiwa ba ke ba. Don Allah ki yafe min."
Innayo ta dan tura baki duk ta rikice da kunya "to cikani don Allah kada a ganmu"
"Sai kin ce kin yafe"
"Zara zan ci kaniyarki fa. Cikani nace"
Zara ta cikata tana dariya kasa kasa.
"Baki ce komai ba."
Innayo ta numfasa tana kallonta tana girgiza kai tare da murmushi.
"Indai nice ki sani cewa hatta waccan yayar taku mai rangwamen tunani na dade da yafe mata. Babban burina dama bai wuce ku fahimci kuskurenku ba. Wallahi Zara ba kudinku nake so ba. Ku din da na haifa a halin maraici ba uwa ba uba ku nake so."
Kwalla ta sake taruwa a idon Zara. Innayo kuwa sai tayi gaba ta fara tattaro abubuwan da take bukata na girki. Yau dai gidan Hasiyan zata je da kanta ba aike ba.
Da suka gama Maimuna ce ta daukar mata kwandon da aka zuzzuba abincin. Kiranta tayi a waya tace ta nemi izinin mijinta yau sai gidan Hasiya. Zara da Saliman sun so zuwa ta hana. A cewarta bata son yawo kawai don suna gida. Wuraren shabiyu suka fita.
***
Awa guda da fitar Ayaah, Hasiya ta kula da 'yar pos dinta a inda ta durkusa ta zuba mata kunu. Dauka tayi ta bude taga 'yan kudaden da basu kai dari uku ba a ciki. Ta san ba za su wuce kudin motarta bane ta manta a gida. Idan kuwa haka ne in ba a kai mata ba karshenta ta dawo a kafa ko ta kare da rance. Wannan ma bai dameta ba sai da taga takardar da Ayaah ta nannade kudin WAEC dinta a ciki dubu sha biyar. Daren jiya Honorable ya bata saboda yau din ne rana ta karshe da zasu biya. Duk da tana jin jiri haka ta daddafa bango ta tashi tana kiran Murja da Ummita.
"Don Allah wata cikinku ta zo tabi Ayaah makaranta da pos dinta da ta manta."
Murja ta ce yanzu suka yi waya da wata mata zata zo kitso. Ummita na jin haka ta san ita ce mai zuwa. Hanzarin shiga wanka tayi ta fito ta shirya