Showing 45001 words to 48000 words out of 242549 words
ko namiji da kuma wanda ba nasu ba. Suna iya mu'amala da kowanne su jidadi. Abbati da Munzali sun kasance cikin wannan jerin. Sabo yasa basu damuwa da mata, ba wai don matan sun daina daukar hankalinsu ba.)
***
Kayanta ta rage ta saka wata doguwar rigar yadi mai laushi sannan ta fito falonta inda aminiyarta a wurin aiki take zaune. Da fara'a ta sake tashi a karo na biyu ta rungumeta.
"Congratulations Dr. Khadija."
"Godiya nake Assistant Prof. Zuwaira" ita ma ta kirata da nata mukamin suka dara.
Suna zama Dr. Zuwaira kamar yadda kowa ya santa a wurin aiki ta mike " 'yar uwa guduwa zan yi fa tunda naga tare da maigidan ku ka dawo. Dama makara nayi ban samu na zo miki a makaranta ba na ce bari na biyo gida."
Dan bata rai Mami Khadija tayi "ba za ki zauna walimar da 'ya'yanki suka shirya min ba? Saboda ita mutane da yawa basu je Zariyan ba. Ana la'asar za a fara."
"Zan dawo Doctor. Babban abin da ya kawoni akan maganar gidan nan ne. Na san kin ce a yau dinnan za ki yi masa idan ya kawo zancen komawarku sabon gida." Da tausayi ta kalli kawarta da ta dauka tamkar kanwarta "Khadija fight for your marriage don Allah kada hakurinki na shekaru ya tashi a banza. Ki duba ki gani ido rufe nake neman aure da shekaruna da komai saboda shi ne babban martabarmu."
Murmushin takaici Mami Khadija tayi idanunta na cikowa da kwalla. Ba don suna shigowa gidan motar Dr. Zuwaira ta shigo ba da tuni kila ta karbi takardarta a hannun Alh. Tahir.
"Magana fa nake kin tafi duniyar tunani"
A gajiye da lamarin aurenta ta soma magana.
"Kin san komai Anti Zuwaira. Abin da na kasa fadawa 'yan uwana ban boye miki ba. Don Allah kada ki shiga sahun masu bawa mata shawarar zama da mazinaci."
Kwalla ce a idanuwanta. Kuka take son yi ko zata sami sassauci. Ta wahala matuka kafin ganin cikar burinta. Aiki ba dare ba rana har ta tara isassun kudi tayi gini a nan cikin Kaduna. Gidan da Alh. Tahir ya kama mata haya a Zariya tun lokacin karatunta har ta soma aiki ya dade da saya. Da sunanta ya saya ya bata takardun gidan. Wanda ta gina yanzu zai wadace su ita da 'ya'yanta har suyi aure. Daki hudu ne. Mazan kowa daya sai matan a guda ita ma a daya. Takaicinta daya ta gama ginin daidai lokacin da shi ma Alh. Tahir ya gama tsantsara gida na kece raini. Kafin yasa ranar tarewa take so ta karbi takardarta ta bar shi da matansa na aure da 'yan matansa na titi.
"Khadija" Anti Zuwaira ta kirata a hankali da sigar laluma "idan kun rabu kin san da wa zaki hadu a gaba? Yawancin maza haka suke sai dai na wani yafi na wani. Ga 'ya'ya har hudu tsakaninku. Me zaki ce musu shi ne silar rabuwarku? Abin da hakuri bai bamu ba Khadija rashinsa ba zai bamu ba. Na isheki misali. Tun da sauran kuruciya na fito amma miji yaki samuwa. Ke banda tsoron Allah da sai na fada wani hali. A yadda nake ji yanzu ina dana sanin kai kararsa har aka rabamu."
Khadija ta dakatar da ita da cewa "dukan Anti Zuwaira? Yanzu har kina nadamar fita daga gidan wanda ya miki dukan da ki ka kusa rasa rayuwarki?" Da dan karfi ta ce "ba dole maza suke cigaba da cusgunawa mata ba. Suna yi muna turewa kawai saboda kar a kiramu zawarawa ko a rabamu da 'ya'ya."
"Khadija wace uwa ce mai hankali zata so barin 'ya'yanta a gidan da ita ta kasa zama?"
"Haka ne. Nima zamansu nayi domin dasu ya yi min barazana a lokacin."
Anti Zuwaira ta ce "yawanci duk hakurin da muke yi kenan. Fight to save your marriage and your husband."
Kuka mai ciwo Mami Khadija ta fashe dashi tana jin zuciyarta tana tukukin bacin rai "wane auren? Wane mijin? Anti da idanuna ba labari ba na kama shi da Nasima. Har yau ..." ta fada tana dukan kirjinta dake suya "ban manta da hoton da na gani ba. Zama gida daya dasu muna kallon juna tsayin shekarun nan ya isheni bala'i. Ko matarsa ce na fada musu daki ya ya zanji ballatana mai'aikina yarinyar da ta bada shawara aka cire min mahaifa! Bai kuma tsaya nan ba na kuma same su suna rigima akan kanwarta da ya kai daki. Gasu nan duk ya ajiye a gidan amma har yanzu bai daina yawon bin mata ba. Mutumin da ya ce ya ji ya gani akan sabon Allah din ne zan wahalar da kaina wurin kwatowa? To na kwato shi daga hannun wa? Shi ne fa wanda ya kamata a dinga neman tsari da haduwa dashi. Na riga nayi masa alfarma a idon 'ya'yansa. Banda Suhaib babu wanda ya san halinsa a cikinsu. Rashin abin rike kai da 'ya'ya ke sa mata daurewa suyi ta zama to Alhamdulillah naci moriyar wannan zama. Wai Anti har kin manta silar haduwa da dalilin amincinmu? Kin san komai Anti Zuwaira ki daina bani shawarar cutar kaina. Kaddara ta riga ta hada jinina da nashi mun haihu amma wallahi ina tsoro. Ina matukar tsoron hakkin 'ya'yan mutane kada ya bibiyi 'ya'yana da Mardiyya. "
Jinjina mata Anti Zuwaira tayi domin ta san cewa Khadija jarumar mace ce. Wata biyar da fara aikinta a jami'ar ABU suka hadu a masallaci. Allah sai Ya hada jininsu daga gaisawa suka kulla zumunci. Lokacin graduation din Sauda da Mardiyya daga JS3 Alh. Tahir ya shirya musu gagarumar walima a gida. Anti Zuwaira ta sami zuwa da 'yan matan 'ya'yanta su uku. A ranar Alh Tahir ya kyalla ido yaga babbar mai suna Siyama. Bai san 'yar waye ba shi dai ya ganta a wurin taro. Sai da ya san yadda ya yi ya nemi nambar wayarta. Yarinya ita ma bata san waye ba ya soma kiranta a waya da fuskar soyayya. Tafiya na gaba ya fito da maitarsa fili ya dinga tura mata kazaman sakwanni. Da yake Allah Ya kareta kuma akwai tarbiyya da kanta ta nunawa mahaifiyarta. Ita kuma ta kwafi nambar tunda bata tare da mijinta washegari a wurin aiki ta nunawa Mami Khadija. Hankalinta duk ya tashi tana tsoron kar a bata mata 'ya.
"Ta wace hanya ya kamata mu bullo masa? Idan wani abu ya sameta ta ina zan fara? Ka kwashi shekaru kana tarbiyya da tattali wani mara tsoron Allah Ya wargaza maka."
Tausayi ta bawa Mami Khadija domin ta shaida jajircewar Anti Zuwaira wurin tarbiyar 'ya'yanta.
"Bani nambar na kira shi."
"Keeee, raba kanki. Wai baki ga messages din da nayi miki forwarding ba? Mutumin nan da gani kwararren dan iska ne. Da aurenki kada matsalata ta janyo miki jangwam."
"Tsorata shi zan yi in ce mun yi bincike a kansa zamu turo masa 'yan sanda idan ya sake kiranta."
Kamar da wasa ta saka nambar a wayarta. Suna bai fito ba tunda Alh. Tahir bai taba kiran matansa da layin ba.
Ringing biyu ya dauka a zatonsa cikin 'yan matan da yake bawa nambar ce.
Kashe murya ya yi yana wani jan haruffa irin na kwararrun 'yan bariki "Hello baby girl."
Bata gane shi ba a lokacin ta ce "babar Siyama ce yarinyar da ka ke ta yiwa barin kudi. Idan baka rabu...."
Maimakon ya ja bakinsa ya katse kiran saboda mamaki da kaduwa sai cewa ya yi "Khadija?" Da ainihin muryarsa.
"Abban Suhaib?" Ita ma ta ce nata mamakin ya ninninka nashi. Anti Zuwaira sai ta matso kusa da ita. Jikinta ya yi mugun sanyi kamar anyi mata wanka da ruwan kankara haka. Kukan ma da take jin zai kawo mata salama kasawa tayi.
"Abban Suhaib abin naka har ya kai kan 'ya'yan kawayena?"
"Tsaya kiji Khadija" ya ce a gigice.
"Kaji tsoron Allah kada watarana abokan shashancinka su turawa naka 'ya'yan irin kazantar da ka turawa 'yarta. Ka kiyayi ranar da zaka ji inama baka zo duniya da lafiya ba bare ka dinga lalata 'ya'yan mutane." Kif ta ajiye wayar.
Anti Zuwaira ta matso kusa da ita a tsorace "mijinki ne? Babansu Farha ne?"
"Shi ne" ta ce a hankali sai ta yunkura kamar za ta tashi ta fadi yaraf a kasa. Anti Zuwaira taga tashin hankali muraran a ranar. Ta zata Mami Khadija ta cika ra dinga girgizata. Ganin abin yafi karfinta ta fita ta kira abokan aikinsu. Basu jima ba aka kawo ambulance daga asibitin koyarwa na Shika. Ma'aikatan su ma da fari sun zata ta rasu sai daga baya ta numfasa da karfi.
Shabe-shabe da hawaye Anti Zuwaira ta rungumeta tana kuka. A asibiti likita ya ce jininta ya hau sosai saura kadan ta sami stroke (mutuwar barin jiki).
"Kar ki bari ciwo ya kassaraki Khadija. Idan kina da damuwa ki fada min, ko bani da maganinta da shawara zan tayaki jimami. Barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Ki dinga fadar damuwarki don Allah."
Cikin kuka Mami Khadija ta ce "damuwar ina auren mijin da bai dauki zina a bakin komai ba saboda rashin tsoron Allah?"
Ita kuka Anti Zuwaira kuka. A ranar suka kulla aminta. A yau kuma Mami Khadija ta gama shirin ba za ta kara kwana a gidan Alh. Tahir ba da aure ko babu.
***
Hasiya ce mai zuwa duk satin ta duba lafiyar Innayo. Bata tafiya sai tayi mata miyar sati da girkin da zata ci ranar sannan ta gyara mata daki ta wanke bandaki. Ba don Innayo din bata son ganin su Ummi ba da su ne zasu dinga yi mata aikin. Salima da Maimuna kuma kamar hadin baki kananun 'ya'yansu ne mata. Manyan duk maza ne. Na Uwani da Zara kuma sai sallah sallah suke zuwa. Munzali ya yi gyara a gidan yanzu kowace mace tana da bandaki a cikin dakinta. Asabe bakincikin kamar ta mutu da ya ce zai hada da bangaren Innayo. Gori kuwa har ta gaji da damuwa ta saba.
Kwana na uku kenan ciwon hakori ko bacci baya barin Innayo. Tunda Hasiya bata zo ba ta san cewa dole matsala ce ta taso mata. 'Tana can tana bautar 'ya'yan miji' ta ce a zuciyarta. Wayar da Hasiyan ta saya mata ta dauka ta kira Maimuna da sanyin safiya.
"Shallo, shallo Memuna kina jina?" Ta ce da kyar hannunta dafe da mukamukinta bangaren dake ciwo.
A dan tsorace saboda ganin wayar ta sammako Maimuna "Innayo ina kwana?"
"Lafiya kalau. Ina mazajen nawa marasa cefane?" Ita ma ta amsa murya a sake.
Da dai Maimuna ta tabbatar ba matsala bace sai ta saki rai suka gaisa sosai. Da tayi tunanin ko wani abu mara dadi ne ya faru a gidan. Suna gama gaisawar dama shiri take ta ce
"Innayo Doguwa zamu tafi yanzu. An yo waya Iya (surukarta) ta zame a bayangida"
(Nima ciwon hakori nake Memuna) Innayo ta furta a zuciyarta. A zahiri kuwa addu'a da fatan sauka lafiya tayi mata. Suna gamawa ta kira Salima. Mai rakata asibiti take nema cikinsu.
Mijinta ne ya bata wayar tana gaban murhu sai fama da hayaki take za ta dumama tuwo.
"Ungo Innayo ce ke kira. Ki dauka ki tambayeta dubu goman da na ce miki. Banza karbi mana."
Tsuke baki Salima tayi domin idan tayi magana kuka ne zai taho. Sosai Hasiya ke taimakon 'yan uwanta da mahaifiyarsu sai dai samun nata ita ma ba wani mai yawa bane. Ita Salima ta san yanzu Innayo da Hssiyan ta dogara. Mijinta kuwa kamar an kwashe masa albarka. Aure har yau bata taba jindadinsa ba saboda mahaifinta bai saya mata mutumci ba. Ta kuma kasa fadawa Innayo saboda kada ta cigaba da tayar mata da hankali.
Murya can kasa ta amsa wayar bayan ya zungure mata keya "Innayo..."
"Ya naji muryarki a shake Salima?" Ta amsa a firgice.
"Da ciwon kai na kwana. Yanzu ma nasha magani amma bai sauka ba."
Mijin nata yana jin mai take cewa ya damki dankwalinta wanda ya hada da gashinta ya matse iya karfinsa. Haushi kamar ya rufeta da duka saboda taki nema masa kudin zuwa caca.
"Sannu Salima. Zan fita idan na dawo zan biyo gidan naki."
Uwani da Zara ne suka rage bata kira ba. Gabanta har dan faduwa ya yi da tayi tunaninsu. Ita ta haifesu amma kalaman da suke yi mata ke sa bata yawan kiransu. Duk da haka a gefe suna nan cikin zuciyarta. 'Yan uwan Innayo mata kaf suna kauyensu a karkashin karamar hukumar Garunmalam. Akwai kadan cikin 'ya'yansu dake aure ko kananan sana'o'i a Kano. A ganinta nemansu su rakata asibiti tamkar kwayewa kanta baya ne.
Wurin Alh. Rabi'u taje neman kudin ganin likita ya ce babu. Kudin da Hasiya ta bata satin da ya wuce tayi barka dasu. Don kokari sai ta bayar da duka ta ce wai gudunmawar 'ya'yanta ce.
Ba za ta iya zama da ciwo ba. Ruwan alwala ma da ya shiga bakinta da asuba ta kusa sakin fitsari saboda azaba. Shiryawa tayi ta tafi asibitin Sir Sunusi inda Uwani ta kai matsayin Metron (matron) a bangaren karbar haihuwa. Fatanta dai Allah Yasa tana nan tayi mata jagora bangaren hakori a duba mata.
Nisan tafiyar zuwa asibitin wanda yake kan titin Hadeja daga unguwar Dala sai mazauni ko wanda ya san Kano zai gane. Adaidaita sahu ta shiga ya cajeta kudi mai tsoka kuwa saboda nisa da goslow. Yana sauketa a bakin gate ta tambayi bangaren haihuwa guda cikin masu gadin ya nuna mata. Tana tafe tana jin yadda duk taku daya sai kunnenta ya amsa na bangaren hakorin.
Wasu nurses ta gani su hudu a bakin kofar wurin ta duka ta gaishesu saboda ganin girman masu farin kaya da mutanenmu ke yi.
" 'Ya'yan nan don Allah Uwani nake tambaya. Wata 'yar jika-jika. Ta ce min a bangaren nan take aiki."
Zaro idanu suka yi suka hada baki wurin cewa "Matron Uwani bala'i"
Daya ta ce "Iya in dai mai haihuwa ki ka kawo gara kawai ki bi tsarin asibiti kar ki daka Metron dinnan."
Innayo taji jikinta ya yi sanyi da kalaman da ake fada game da 'yarta. Ta tambayesu "akwai matsala ne ta bangarenta?"
"Ai ba kya ji mutuwar sarki a bakinmu ba. Zamu fada mata idan mun ganta" suka yi gaba abinsu.
Zaman minti ashirin a karkashin zafin rana da azabar ciwo Innayo tayi kafin Allah Ya kawo Uwani daga dakin hutunsu.
Taku daidai take yi cikin kasaita ta yatsina fuska ta ce "Wace ce aka ce tana nemana?"
Innayo ta daga kai da kyar. Bata san da yadda za ta kwatanta ciwon da take ji ba. Hasiyanta bata san da ciwon hakorin ba. Ita kuma taki fada mata saboda ta san irin nauyin dake wuyanta.
Uwani na ganinta ta karaso da sassarfa. Idanunta basu gane mata canjawar fuskar mahaifiyarta saboda kumburi ba. Ita dai kada wani ya gansu tare duk masu tsoronta cikin abokan aikinta su rainata.
"Innayo lafiya? Me yasa ki ka zo nan maimakon ki kirani a waya."
"Wurin hakori zaki kaini Uwani. Kwana biyu ko runtsawa bana iyawa."
Murya a sama sama Uwani ta ce "ni dai da kin kirani. Nan fa wurin aikina ne. Muna ta kokarin dakilar da neman alfarma da abokan aikinmu kan yiwa 'yan uwansu yanzu ni kuma zaki sani."
"Nima ba alfarma nazo nema ba. Wurin za ki rakani sai ki kara min kudi saboda sayen magani da ganin likita. Mai adaidaita baki ga yadda ya cajeni ba ya cinye kusan rabin kudin komawa gida gashi na so biyawa duba Salima"
Dariyar takaici Uwani tayi "Innayo kenan. Ki ce kudi ki ka zo karba. To ni wallahi haka na fito sikau don ko na man mota ma sai na ranta. Wata ya yi nisa."
"Uwani" Innayo ta kalleta ido cikin ido wanda hakan ya dan razanata "idan nayi miki baki wallahil azimu sai ya biki. Na bi uwata har ta koma ga Allah. Don Ya jarabceni da haihuwarki ba zan butulce maSa ba. Ke dai ki kiyayi hudowar rana da faduwarta. Shiga ki kawo min kudin ganin likita shashashar banza."
Tunda ta taso kusan yau ta taba jin Innayo tayi mata fada na gaske. Ranta a jagule ta koma ciki ta dauko dubu hudu ta kawo mata.
Ita kuwa Innayo sai taji tsoron kar fushinta ya zama silar mummunan abu ya sami Uwanin. Fatan shiriya ta dinga yi mata a zuci da cewa ta yafe mata. Tana bata kudin ta ce
"Allah Ya yi muku albarka Ya shirya min ku."
Juyawa tayi ta tafi Uwanin ta biyota ta ce "koma bakin aikinki gida zan koma."
Da yake bata da tunani sai ta koma tana fadawa kanta ai dai tayi nata kokarin. Innayo kuwa karkashin wata bishiya ta samu ta zauna ta kira Hasiya.
A duke take kan Abbas yana amai amma ganin wayar ta Innayo ce ta amsa da sauri.
"Hasiya"
Sai kuka.
Anti Hasiya bata san dalilin kukan mahaifiyarta ba amma tana jin kukan ita ma ta fara.
"Innayo gani nan zuwa. Daina kukan. Me ya faru?"
"Ki zo inda yayarku take aiki."
"Gani nan" ta ce tana mikewa tsaye a gigice.
(Uwa ta kira ki ta ce yi min kaza sai ki ji a ranki ta takuraki. Bata san uzurinki ba. Ko ta manta aure ki ke kina karkashin ikon wani? Allah Sarki...ita ma baki san uzurinta ba. Kila a wannan lokacin ke dai ce za ki iya kawo mata agaji. Kila kuma kulawarki take mararin samu. Kila kunya take so ki fitar da ita. Kila ajizancin da aka san dan Adam dashi ne ta gwada a kanki. Kila...Kila...ita dai uwa uwace ko da ta buzuzu ce.)
Idan kin karanta wannan post din yau za ki biyani da dayan abu biyu rak. Ki kira mahaifiyarki ki gaisheta ki yi mata kyakkyawar addu'a taji dadi. Idan ta rigamu gidan gaskiya ki yi mata addu'a sannan ki hada da sadaka.
She deserves the best you can offer!
#UWAUWACEI just published "11" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/RpX6BXVbqab
UWA UWACE...11
Batul Mamman💖
Astagfirullah wa atubu ilaika.
La'ilaha Illa Anta Subhanaka Inni Kuntu Minazzalimeen.
Allahumma Inna Nas'alukal Afeeya
***
"Abu, Abu...KE ABU"
Da dan karamin gudu Abu mai'aikin Zara ta shigo dakinta ta sami wuri ta dan durkusa. Kafin ma ta soma yi mata fadan da ta saba ta ce,
"Ayi hakuri muna gyaran bangaren Hajiyan Fatakwal ne ban ji kiran da wuri ba."
Maganar kuwa ta sake fusata Zara wadda ke zaune akan gado ta dora kafafu akan filo saboda taruwar jinin da suke yi "amma ai kin san yau ba girkina bane saboda haka ba aikin bangarena bane gyara mata wurin zama."
Gyada kai Abu tayi bata