Showing 81001 words to 84000 words out of 242549 words

Chapter 28 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3377

domin kwanciya Abbati bai farka ba. Suhaib ya duba wayarsa amma a rufe take bare ya dan duba sunaye. Hakura ya yi tunda Mami ta ce ya jira ya tabbatar wani nasa ya zo.

Ba jimawa da Suhaib ya ajiye wayar a kan wani tebur da ake ajiye kayan abinci na mara lafiya Munzali ya kira. Sun yi dashi zai kira shi idan ya tsaya amma shiru. Daya layin nasa wanda wayar tana mota yana shiga shi ma bai ji an dauka ba. Haka ya dinga kira babu kakkautawa saboda hankalinsa dama bai kwanta da tafiyar ba. Haka kawai tunane tunanen ban tsoro suka far masa ya kasa sukuni. Kasa zama ya yi ya tashi ya tafi gidan Shazali. Ya san da wuya ya ce masa yana gida idan kira ya fara yi.

Maigadinsa bai hana Munzali shiga ba tunda ba bako bane.

"Ka dage kafi Abbati bashi farinciki. Ina mai tabbatar maka duniya sabuwa za ka bude idan ka kama manyan nan a hannu."

Kalaman da suka sauka a kunnuwan Munzali kenan yana shirin yin sallama a budaddiyar kofar shiga gidan Shazali. A shirye yake yana takowa bakin kofar yana waya zai fita. Idanunsa na sauka akan na Munzali da yake bashi da gaskiya sai ya ja baya. Munzali kuwa ya ce da wa Allah Ya hada shi....cakumar wuyan Shazali ya yi gami da yi masa mummunar shaka.

Da ihu yake masa magana idanunsa sun gama kankancewa.
"Ina Abbati?"

"Wane Abbatin?"

Rufe bakinsa ya yi daidai da saukar naushi a bakin.

"Wane Abbati? Ni ka ke tambaya wane Abbati?"

Shazali sai ya fara kokawar kwatar kansa saboda Munzali zai iya yi masa lahani.

"Kaga Malam nima da na ce yaje Abuja ya musu bayani bai karasa ba. Dazu muka yi waya ya ce min yana asibiti wai bashi da lafiya."

"In na yarda Allah Ya tsine min. Kai Shazali! Dubeni da kyau wallahi. Munzali ne. Ka sanni ba tun yau ba. Bani da mutunci ko kadan akan abin da ya shafi Abbati. Ina yake?" ya furta a fusace. Jijiyar kansa tuni sun firfito idanu sun yi ja.

Cikin jin haushin naushin da ya masa ya ce "Dama ta ina zaka yi mutumci a kansa tunda har yanzu kana begen ku cigaba da..."

Wannan karon bai gama hada kalamansa ba wani naushin ya sauka. Munzali ta dinga dukansa a haukace yana cewa ya fada masa inda Abbati yake.

"Indai kana tunanin waccan soyayyar nake yiwa Abbati to kayi kuskure. Ni da Abbati ma'abota inuwar Al'arshi ne in Allah Ya yarda (duba hadisin Qudsi dake magana akan mutanen da Allah zai sanya a inuwar Al'arshi ranar lahira. Allah Ya amintar damu da masoyanmu na gaskiya da wannan ni'ima. Amin). Wannan shi ne tsakanina da Abbati!"

*
Karfe bakwai da rabi Abbati ya tashi. Ya farka kansa ya yi nauyi amma babu ciwo sosai. Munzali ne ya fara fado masa a rai da ya hango duhun waje. Da sauri ya shiga laluben wayarsa saboda ya san dole yana can cikin tashin hankalin jinsa shiru. Inda Suhaib ya ajiyeta ya hangota. Zai dauka Suhaib din ya dawo daga masallacin kofar asibitin.

Godiya sosai Abbati ya sake yi masa.

"Babu komai. Za ka samu ka kira wani ko?"

"Eh yanzu zan kira. Nagode."

"To ga abinci nan. Zan dawo da safe in sha Allah. Ko in zuba maka?"

Saukowa daga gadon Abbati ya yi "ka barshi naji kwari ai. Zan fara yin sallolina tukunnan."

Suhaib ya fita shi kuma ya shiga bandaki. Da ya idar da sallah ya dauko wayar domin ya kira aka yi rashin sa a chaji ya kare. Aljihunsa da inda ya ga wayar ya duba babu mukullin motar balle ya je ya dauko chaja da daya wayar. Fita ya yi cikin sa a ya sami motar an gyara mata parking. Duk yadda aka yi wanda ya gyara din bashi da nufin cutarsa. Zuwa wayewar gari idan ba a kawo ba sai ya yi cigiya. A reception din ta sake tsayuwa ya tambayi wadda take kan aiki aron waya. Mata ta hade girar sama da kasa.

"Ba sai kin bani ba. Zan fada miki nambar idan an dauka ki ce a kira Abbati ne."

Kunkuninta tayi ta gama sannan a wulakance ta ce ya fadi nambar. Bai nuna jin haushin abin da tayi ba ya fada mata ta kira. Munzali na dauka a dakile ta ce "ka kira layin nan wani Abbati yana son magana da kai."

Yana dakinsa lokacin ya rasa me yake masa dadi. A gefe ga jaka ya hada kaya da duka atm cards dinsa a ciki. Waya kuwa baya nisa da ita yana ta adduar Allah Yasa ba mugun hannu Abbati ya fada ba a hanya.

Wannan wayar ta shigo a kan gaba. Matar na kashewa ya kira hannunsa har rawa yake. Da wayar kamar bata so haka ta mika masa.

"Munzali kayi hakuri" Ya fara cewa sannan ya fada masa abin da ya same shi.

"Yanzu yaya jikin naka? Zan taho na san in sha Allahu kafin sha biyu na iso."

"Kar ka soma tafiyar dare. Bani da wata matsala yanzu."

Duk yadda Munzali ya so Abbati hana shi tahowa ta yi.

Da bacin rai karara a muryarsa ta ce "Da asuba zan taso."

"Naji. Allah Ya tsare hanya." Abbati ya amsa da murmushi.

Mai waya dai sai cika take tana batsewa wayar tasa ta kusa minti shabiyar. Da ya gama ya mika mata ta dan murguda baki. Wani murmushin ya yi sannan ya zura hannu a aljihu ya ciro dubu uku ya bata.

"Ga ladan aron waya"

Kunya ta kama ta amma bata sa ta mayar da kudin ba. Sai ma dannesu da tayi da hannu.

"Laahhh babu komai fa. Idan baka gama ba ka kira shi ma." (Kudin wayar bai wuce naira hamsin ba)

"Mun gama. Nagode"

Ya fara bin hanyar dakin da yake yaji tana cewa "ni suna na Rufaida. Idan kana so ka dinga zuwa aron wayar kafin a sallameka."

*

Da sauri sauri har yana tuntube Alh. Tahir ya nufi bangaren Mami Khadija inda aka ce masa Farha tana kwance. Ya saba duka yaransa banda Suhaib yana waya da kowa kafin ya baro office. Shi yasa babu matsalarsu da bai sani ba. Rashin miji a wajen Farha kuwa nasihun da yake mata suna matukar tasiri a ranta. Yau da bai sameta ba sai ya shiga damuwa. Idan ya kirata kiran na shiga take rejecting call din. Shi ne ya kira Sauda take fada masa bata da lafiya har sun je asibiti sun dawo. Meeting suke yi mai matukar mahimmanci amma haka ya fito ya ce gobe a cigaba.

Ya kusa kofar dakin daga bayansa yaji kira daga Mami Khadija.

"Ina son magana da kai amma a dakinka."

Kallon mara tunani ya yi mata. Wace irin magana zasu yi a kebe Farha ba lafiya
"Ko ma meye ki jira don Allah in duba yarinyata."

Hannuwanta ta harde a kirji ta ce "abu mafi muni da za ka yi mata a yanzu shi ne ka nuna mata fuskarka a yau."

A tsorace ya juyo "fada mata zan auri Yumna kika yi? Haba Khadija! Ba na ce zan yi musu magana da kaina ba?"

Gaba tayi abinta. Bashi da zabin da ya wuce binta dakinsa. Suna shiga ta ce ya dauko wayarsa ya kira Yumna.

"A wane dalili?"

"Ka kirata ko ni na kira."

Da gaske take yaga alama. Kiran ya yi ai kuwa Yumna ta dauka da salon muryar da take yi masa idan suna tare.

"Zakina"

Mami Khadija ta tabe baki "daga Diya kuma yanzu Zaki ka koma? Tafe tafe sai an sami mai kiranka kadangare."

Harara ya jefa mata ransa na baci. Zai yi magana ta karbi wayarsa.

"Yumna ki saurareni da kyau ki ji abin da zan fada miki."

Hantar cikin Yumna ta kada amma ta kasa kashe wayar. Mami Khadija ba sa'ar yinta bace. Akwai layin da duk rashin kunyarta bata isa ta ketare ba.

"Babu ruwana da abin da ya hadaki da Maigidan nan. Duk wani shirme da shiriritar da ki ke yi da rayuwarki ya tsaya kanki da abokan shaidancinki" tayi maganar idanunta a kansa. Wani irin sanyi yaji ya ratsa shi na tsantsar kunya. Amma bai ce komai ba har ta cigaba da magana.
"Ki fita harkar 'ya'yana. Babu ke babu Farha. Bana bakinciki da shigowarki gidan nan a matsayin matar aure amma muddin ki ka dasawa ranki taba min yara to ki saka a ranki ke da Tahir sai dai a titi. Bana magana biyu saboda haka don't try me."

Wayarsa ta ajiye masa a kusa dashi ta fice daga dakin. Jiki na rawa ya kuma kiran Yumna.

"Turo min abin da ki ka turawa Farha har ya sumar da ita."

"Zakina.." ta ce tana shekar kukan kissa.

"Zakin uw**ki. Ki turo min yanzu yanzu kafin na tambayeta." Ya daka mata tsawa.

Yumna sai ta rikice. Gumi ya dinga karyo mata. A haka ta tura masa video din jiki ba kwari.

Alh. Tahir zabura ya yi da ya bude. Nasa gumin tamkar an kwara masa ruwa. Yanzu ace wannan abu Farha ta gani? Mutumcinsa kaf ya zube tunda ya san cewa ta gama ganinsa a wannan yanayi. Kulle kansa ya yi a daki ya rasa tudun dafawa. Yana son Farha amma ya tabbata yadda Suhaib ya guje shi ita ma haka za ta yi.

Tun Yumna na jiran ya kirata yayi masifa har ta hakura. Bata san abin zai hada da asibiti ba. Sannan gashi a gabansa kuma da wayarsa Mami Khadija tayi mata magana. Hakan na nuni da cewa wanda take yi dominsa shi ma yana shakkarta. Status din nata dama ta rufe babu mai gani sai Farha saboda kar ta sami matsala a gida. To gashi ta sami matsala da wanda take shirin shiga gidansa.

*
Bacci rabi da rabi Farha tayi a daren ranar saboda tana rufe ido abu daya take gani a mafarki. Mami Khadija bata matsa mata da tambayar me ta gani ba. Ta dai ce mata kar ta ja da hukuncin Allah game da mijin da Yumna za ta aura. Addu'a ce kawai tasu tunda basu isa su haramta halal ba. A gefe daya ga tunanin mutumin nan na asibiti da ya addabeta. Ji take ta tsani maza babu sauran nagari tunda mahaifinta ma bai tsira daga tarkon shaidan ba. To amma ta kasa cire yanayin da ta ganshi na rashin lafiya daga tunaninta. So take taji halin da yake ciki ko za ta sami sauki a zuciyarta. Abin gabadaya sai ya dinga bata haushi. Emotions sun yi mata yawa suna ta karo da juna.

Da gari ya waye sai ta tashi da ciwon barin kai saboda rashin isasshen bacci. Mami Khadija ta bata magani tun asuba. Karfe bakwai da rabi ta gama shiri saboda tana da aji karfe goma a ABU. Direbanta har ya iso ita yake jira sai ga Suhaib.

"Ina zuwa da sassafen nan na ganka a shirye?"

"Wallahi Mami mukullin motar mutumin jiya ne na gani a aljihuna da asuba. Ya barshi a motar da na gyara masa parking ashe ban ajiye a dakin ba."

"Ai kuwa gara kayi maza ka kai masa." Ta kalli Farha wadda ana ambatonsa taji faduwar gaba "yi maza ki shirya ki bishi." Sannan ta juya ga danta "Suhaib ta sake ganin likita. Da ciwon kai ta kwana. Hawan jini yana sa ciwon kai. Bana so ya zame mata ciwo tun da kuruciyarta. Gara taje ta sake yiwa doctor din complain. Ga wannan ku tafi wa mara lafiyar dashi" ta ajiye kwandon abincin da aka hada mata na zuwa office. Damuwar Farha ta mantar da ita tasa ayi abincin safe dashi.

Cikin minti ashirin ta shirya cikin riga da sket na atampa. Hijabi mai hannu ta saka navy blue wanda ya kusa kwaurinta. Fuskarta tayi fayau babu kwalliya sai hoda da kwalli.

A mota Suhaib yake ce mata kamar ya taba ganin mutumin.

"Kamar shi ne mai motar nan na diamond plaza."

"Ikon Allah" ya dinga cewa yana murmushi "idan kuwa haka ne ai ku bashi hakuri wannan karon tunda wancan lokacin kun gudu."

Da suka shiga asibitin Suhaib sai ya wuce dakin da Abbati yake ya ce in ta gama ta biyo shi sai su gaisa. Ita ma bata sami ganin likitan ba ance sai karfe tara zai zauna. Yanke shawarar bin Suhaib ya zo ya kaita gida kawai tayi. Kila idan tayi bacci za ta ji sauki.

*
"Jiki ya yi kyau gashi har kayi wanka" Suhaib ya ce da ya shiga dakin ya ajiye kwandon hannunsa.

"Alhamdulillah. Nagode sosai da taimakonku gareni."

Munzali wanda ya iso awa daya da ta wuce ya taso ya mikawa Suhaib hannu suka sake gaisawa. Wayar matar jiya ya kira ta kwatanta masa asibitin.
"Nagode sosai. Daga yau ka zama dan uwanmu kaima. Ni sunana Munzali, kai fa?"

"Suhaib"

Mukullin motar ya mikawa Munzali yana basu hakurin mantuwarsa. Sun nuna masa babu komai har suka soma taba hira. A dan wannan lokacin ya fahimci yadda suke son juna. A haka dai kamar su ga hanjin juna da mara lafiyar da mai jinya. Sai kawai ya dinga murmushi yana kallonsu.

Su ukun suka kalli kofar dakin da aka kwankwasa gami da yin sallama da tattausar murya amma ba a bude ba.

Abbati ji ya yi duk wata na'urar jikinsa ta tsaya. Ashe dadin muryarta da yaji a waya ba komai bane. Yanzu ya san yaji muryarta domin duk wani gashi na jikinsa ya mike kamar zasu amsa sallamar.

"Yi hakuri kanwata ce. Na ce ta sameni a nan ne idan ta ga likita."

"Meye abin bada hakuri? Kanwar dan uwanmu fa kanwarmu ce" Cewar Munzali ya daga murya ya ce "shigo."

A hankali ta turo kofar kamar tana jin tsoron. Kanta a kasa ta shiga ta sake wata sallamar. Munzali da Suhaib kadai suka amsa. Abbati kuwa yawun bakinsa ma ya kafe.

"Kanwarmu ya jiki? Kin sami ganin likitan?"

Kallon mai tambayar tayi niyar yi sai idanunta suka sauka akan na Abbati. Da sauri ta kawar da kanta gefe ta amsawa Munzali wanda yake mata fara'a.

"Da sauki amma sai tara Doctor din zai zauna. Ya Suhaib ko za ka kaini gida kawai?" Ta marairaicewa Suhaib saboda a takure take jin kanta.

"Sai dai ki rakani ATM . Maybe kafin mu dawo taran ta yi"

Munzali ya kalleta ya girgiza kai "bata da lafiyan za ka kwasheta wani wajen? Barta kawai ta zauna a nan ko ka kaita gidan idan babu nisa. Amma kafin nan don Allah rakani in kama mana hotel idan akwai a nan kusa. Da alama yau za a sallamemu. Gashi bana son mu kama hanyar Kano sai ya kara jin sauki. Ni kuma ban san kan garin nan ba."

Suhaib ya ce akwai wani kurkusa dasu su je ya nuna masa. Mukullin motar da suka zo ya mikawa Farha ya ce ta jira shi a motar kafin su dawo.

Munzali ne ya fara fita sai Suhaib din. Farha ta kusa bakin kofa Abbati ya kirata. Zuciyarsa taki bashi hadin kai na kar ya kula ta.

"Ya Farha" Abbati ya furta da wata irin siga da ta tsaya mata a zuci. Tsayuwa tayi gabanta na harbawa da sauri.

"Yaya jikin naki?"

Kunya sai ta lullubeta. Shi da ya kwana a asibiti ko gaishe shi da jiki bata yi ba. Bata san me yake damunta ba. Murmushi tayi ta juyo amma kanta tana kasa.

"Ina kwana? Ya jikin? Allah Ya kara sauki."

"Lafiya kalau. Jiki da sauki. Amin Ya Rabb." Ya amsa da murmushi.

Yadda ta jero tambayoyin haka ya amsa su. Dariya hakan ya bata amma sai tayi murmushi kawai.

"Subhanallah" ya furta da sauri saboda yadda murmushin ya daki ko'ina a jikinsa.

Farha sai ta kalle shi saboda bata ji me ya ce sosai ba "Na'am?"

"Babu komai Ya Farha."

"Ka daina ce min Ya Farha."

Dumi dumi yaji a zuciyarsa. Salon maganar ya burge shi. A lokaci guda ya hau musu da zuciyarsa.
'Bata san shagwaba take bane? Anya ba kasheni yarinyar nan take son yi ba? Dama haka ake son mutum? Wannan ya zan ji idan ta ce tana sona?'

"Ka ji." Ta maimaita a zatonta bai ji bane.

"To me kike so na kira ki wanda zai kusantoki gareni ba tare da na bata miki rai ko na cutar dake ba?"

Babu wata kalma da ya fada da bata ji ba amma bata gane komai ba. Ta dai ji ya ce 'kusantoki gareni'. Sauran kuwa kamar ba da hausa ya yi ba.

"Kin yi shiru."

"Me ka ce?"

"Cewa nayi in dinga kiranki Farha-ta?" ya tsokaneta ganin ta tafi duniyar tunani.

Yana ganin yadda idanunta suka kara girma da mamaki ta yi saurin cewa "wallahi ba haka kace ba."

"Kin tabbata?" Ya tambayeta yana dariya.

Soyayyar Farha ta zame masa jinin da yake yawo a jikinsa. Anya daidai ne ya biyewa zuciyarsa?I just published "17" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/7cEOGqDTzbb


UWA UWACE...17


Batul Mamman💖




Ta san tsokana ce amma bata da karfin ikon hana zuciyarta dokawa tana wani irin tsallen murna wanda bata san ana irinsa ba. Da ta tuna tasirin da wayarsu ta farko tayi a kanta, da yadda ta jima tana jiran wayarsa har ta fidda rai sai ta zabi dakile hirar tasu yanzu. Banda Allah Ya hadasu yanzu da bashi da lafiya kila da ba za ta kuma ji daga gare shi ba. Ba abu bane da take son ta amince tayi ba amma tabbas ta kasance cikin dokin lokacin da zasu dauki hoton da ya fada. Tana tsoron sanyawa ranta abin da zai yi wuyar samuwa gareta.

Wani irin kallo tayi masa mai kama da harara sai ya fadada murmushinsa. Bata iya hararar ba da alama. Ita kuwa kunya ce ta isheta tana neman hanyar gudu.

"Baki ce komai ba. Kenan kin yarda haka na ce?"

Marairaice fuska tayi ta ce "ina da karamar lalura fa. Wani lokacin idan an yi magana sai in ji dif. Kunnuwana suna zabar abin da zasu ji. Kaga duk abin da ka ce bayan mun gaisa ba komai naji ba."

Tashi ya yi daga kan kujerar gefen gadon zai dauko wayarsa da ta soma ringing ya dakata ba shiri. A fuska ya nuna mata kamar zancen ya jefa shi cikin alhini. Nan kuwa dariya yake son dannewa.

"Da gaske Ya Farha? Allah Sarki lovely Farha. Yanzu Sweet Farha ba komai ki ke ji ba? Farhata har kin bani tausayi...."

Ciwon kan da ya kawota asibiti tun dazu ta manta dashi. Rashin kuzarin ma ta neme shi ko sama ko kasa. Da wani irin sauri ta bar dakin tana jiyo dariyarsa har cikin kokon ranta.

"Tunda idanunki kalau suke zamu dinga chatting Farhataaaa" ya dan dago murya yadda za ta ji.

Sai da ta waiga gefe da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login