Showing 129001 words to 132000 words out of 242549 words

Chapter 44 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3365

kiran na tarar da wani amma yaki dauka sai da ya shiga mota. Idanunsa na kallon Mal. Inuwa da Mal. Sa'adu tare da wasu kawunnan Abbatin suna ta dago masa hannu. Murmushin mugunta ya yi sannan ya amsa wayar. Shi ya fara magana bai ma saurare shi ba, kuma yana gamawa ya katse kiran.


"Zabi ya rage naka Abbati. Kafi kowa sanin cewa ina da abubuwan da zan nunawa tsohuwarka wanda zai sa ta tsine maka yau dinnan ba gobe ba. Ka fadawa Munzali na ce ku same ni a Port Harcourt jibi."


***


Awanni uku da rabi kafin waccan mummunar wayar sun zo wa Abbati da Munzali tare da masoyansu da abubuwa daban daban. Ga Abbati da Farha, wata kofa ta karin sani da fahimtar juna ce ta bude musu bayan an dawo daga daurin aure.


Sai ta kurewa Suhaib a waje yake yarda magana ta hada shi da mahaifinsa. Sai dai yau ta sha bamban da kowacce rana. Jiya bayan sun dawo daga dinner Farha ta fada masa yadda suka yi da Abbati. Shi da Mami wadda ya fadawa zancen duk sun yi mamakin jin bai yi karatu ba sai na yaki da jahilci. 


Tabbas Mami Khadija za ta so 'yarta ta auri mai ilimin boko bayan na addini sai dai kuma ta duba abubuwa da yawa. Na farko dadewar Farha a gida babu wanda ya taba cewa yana sonta (kadan daga cikin shukar Alh. Tahir da zuri'arsa suke girbewa). Yabawa da hankalinsa da mutumcin mahaifiyarsa. Sai kuma ganin girman soyayyar da Farha take yi masa. 


Dasu aka daura auren sannan suka bi su Lilu gidan Kawunsu inda aka shiryawa Ango reception. Suhaib ya hango Alh. Tahir cikin mutane. Sai da yaga ya bar jama'ar dake tare dashi ya fito daga karkashin katuwar canopy din ya bishi a baya.


"Ga bakin Farha da Mardiyya zasu gaisheka."


"Suhaib kenan. To ina kwana?" Cewar Alh. Tahir yana mai jindadin maganar da dan nasa ya yi masa ko a wane yanayi ne.


Shi ma Suhaib sai yaji kunya ya dan rissina da murmushi a fuskarsa. Murnar alakar dake tsakanin Abbati da Farha ta cire masa damuwa sosai. Wannan kuwa ya biyo bayan nishadin da yake ganin Mami Khadija tana yi saboda ganin walwalar 'yarta. Kansa ya dan shafa ya ce,


"Abba ina wuni? Ya taro?"


Bai iya boye jindadinsa ba kuwa "Lafiya kalau. Suna ina bakin? Ko na rannan ne da suka zo gida?"


Da Suhaib ya tabbatar masa su din ne sai ya ce su dan jira shi minti kadan zai je ciki ya gaisa da kakaninsu da suka zo. Sannan tunda akwai 'yan uwan Alh. Tahir din mazauna Kano, zai fi son su gaisa dashi a gabansu domin a taya shi bincike.


*


Munzali ya kasa nutsuwa da Suhaib ya fada musu zasu gaisa da Alh. Tahir da kawunnansu.


"Idan wani ya san mu ko wanda ya san mu fa?"


Ya ce jikinsa a sanyaye ga wani tsoro yana shigarsa. Idan ka cire Qibdiyya, to Mardiyya ce mace ta biyu da yake matukar so. Asabe darajar haihuwa kadai ta samu a wurinsa saboda watsi dashi da tayi.


"In sha Allahu babu komai"

Abbati ya sami kansa da karfafawa Munzali gwiwa duk da a zahiri ya fi shi jin tsoro. 


Manyan mutane sun halarci daurin auren saboda baban amaryar dan siyasa ne. Shi kuma ango danginsa manya ne a ma'aikatun gwamnati daban daban. Dole su tsorata saboda ire irensu sune abokan mu'amalarsu a baya.


*

Mardiyya ta gama shiri za ta fito su gaisa da Munzali kafin Alh. Tahir ya kirasu Mama Nasima ta tsayar da ita. Dakin da babu kowa ta shigar da ita ta damka mata wata 'yar leda.


"Yi maza ki bude ki saka kwallin kafin wani ya shigo."


"Kwalli kuma? Kinga idona fa na saka." Ta matso da fuskar gaban mahaifiyarta sosai.


Mama Nasima ta daure fuska da sauri ta kwance ledar ta miko mata abubuwan dake ciki.

"Kwallin mallaka ne. Ki saka sannan ki shafa hodar ki fita wurin Alh. Munzali."

Ja da baya Mardiyya tayi da sauri bayan ta mayar da kullin ledar tafin hannun mamanta.

"Ba zan saka ba."

Kiris ya rage Mama Nasima ta mareta 

"To shashashar banza. An fada miki mazan yanzu ana sanya a kansu ne? Tun yanzu idan bamu tashi tsaye ba kina ji kina gani wata za ta kwace shi a hannunki. Yau da sassafe Dini (kaninta) ya shigo mota domin ya kawo amma za ki fara yi min shirme."


Kwalla sai ta taru a idon Mardiyya. Tana son mahaifiyarta amma taki jinin halayen da ta tashi ta ganta a kansu. 


Mama Nasima da ta fuskanci kamar abin bai mata dadi ba sai ta wayance ta koma lallabata.

"Kafin ki fara yi min wa'azi tun wuri ki sani ba kayan boka bane. Haba Mardiyya, kamar baki sanni ba? Wannan wani malami ne wanda ya dogara da Qur'ani. Ko kasa zai buga miki sai ya kama sunan Allah."


"Mama ni dai ki daina wasa da lahirarki a kaina. Malamin Allah babu ruwansa da duba ko buga kasa."


Ba don bakunta da idanun mutane ba da  Mama Nasima ta kai mata duka don haushi.


"Baki ji na ce yana Bisimillah kafin ya fara don ya kori shaidanu ba?"


Cigaba da maganar zai iya saka Mardiyya yi mata rashin kunya wanda ba halinta bane. Sai kawai ta zabi fita daga dakin cikin kunar rai ta iske Munzali da Abbati a inda Suhaib ya ce suna tsaye. 


Tun daga nesa Munzali ya gane tana cikin bacin rai. Wurin wata mota ta tsaya ya ka a ya sameta. Yana isowa wayarta ta hau ruri. Sunan (Mama) ya gani a jikin wayar kafin tayi saurin kashewa. Murmushin yake tayi masa wanda akan ce yafi kuka ciwo. A zuciyarta kuwa tana tararrabin kada Maman ta biyo bayanta. Yanayinta na mai son boye zahirin halin da take ciki ya fi komai damunsa. Karamar yarinya ce da ta dauki nauyin saita mahaifiyarta da boye aibunta. Abin da shi Munzali mai shekaru da suka kusa rubanya nata bai yi ba duk kuwa da shawara da fadan amininsa. A lokacin da Abbati yake masa wannan fadan yana ganin tamkar bai gama fahimtar matsalarsa bane tunda ya tashi gaban uwa tagari. Sai gashi ya hadu da Mardiyya cikin yanayin dake kusanci da wanda ya taso a ciki. Kuma tana gwada sabanin abin da ya dinga yiwa tasa mahaifiyar. 


Girmanta ne ya karu a idanunsa tare da wata irin soyayya mai ratsa zuciya. Murmushi ya yi mata ganin duk ta takura kanta tana ta waige waige.


"Ashe nayi kuskuren tunanin zan zama mai baki shawara game da abin da ya shafi rayuwarki Diamond girl."


A razane ta dube shi sai ta sadda kanta kasa saboda kallon da yake mata ya nuna maganarsa ta jindadi da yabawa ce.


"Idan baka bani ba wa ka samu da zai bani?"


Ido cikin ido ya kalleta ya kuma kada yatsansa yana mai gargadinta da kada ta kaucewa kallonsa. Daurewa tayi ta cigaba da kallonsa zuciyarta tana rawa.


"Zuciyarki ce za ta dinga bamu shawara Mardiyya. Da ka nake tafiyar da personal matsalolina. Amma na gane kan yana kuskure domin a zuciya ne akwai jin kai da tausayi. Tawa zuciyar kuma karama ce akan taki ta wannan fanin. Shin za ki karbi amanar wannan bawan Allahn dake neman hasken bin iyaye ki gyara masa rayuwa? Kin amince na gabatar da kaina a matsayin manemin aurenki? Za ki iya aurena nan da wata hudu da kin kammala secondary?"


Murmushi tayi ta cukwikuye fuskarta cikin mayafi. Ga duka tambayoyinsa tana gyada kai na amincewa.


*


Farha kuwa da ledoji biyu masu dauke da abincin da aka raba na reception ta fito. An yi packaging abincin cikin mazubin roba mai kyau sai lemon ginger da zobo a robobi suma duka masu kyau da dadin rikewa. Ledar da aka saka su a ciki ta gaba sunan ango ne da amaryarsa. A baya kuwa tana dauke da tambarin /D Delight/ kwararru wajen girkin taro tare da abin sha (online cooking classes for Ramadan coming soon in sha Allah. Come and patronize Batul Mamman please.)


Abbati kadai ta hango saboda Munzali yana tare Mardiyya. Tun kafin ta karaso suke yiwa juna murmushi. 


"Ya Farha kin tayar min da duka kishina da wannan kwalliyar. Ina tafiya ki je ki goge indai ba a ciki zaki zauna ba."


Dariya tayi a hankali "so ka ke na dauka da gaske kake har na fara jin nima na isa?


Harararta ya yi da jin furucinta ta cigaba da yi masa dariya. Dolensa ya soma tayata domin  gabadaya yana neman shagala da kallonta.


"Kin yi yawa ma. Kin kuma san da haka. Fatana kawai kada Allah Ya kawo abin da zai iya shiga tsakaninmu."


"Kana ganin akwai?" Sai kuma tayi murmushi "kodayake yawancin kullum sai naci karo da sakon Malama hide my ID idan an kawo kararku."


"In sha Allahu ba zan taba yi miki abin da zaki kaini kotun social media ba." Ya furta da alamun tsoron da ta zata na wasa ne.


"Allah Yasa"


Kasa hakuri ya yi ya dora da cewa "ko kin ji wani abu nayi miki rantsuwa ko meye ya zama tarihi. Zan zame miki miji nagari in Allah Ya so."


"Allah Ya yarda" ta amsa da karamar murya.


"Da gaske nake sonki Ya Farha. Burina na zama mijin da babu abin da zaki ji a kaina ki yarda kai tsaye ba tare da bincike ba."


Kalaman nasa sun fara bata tsoro. Shi kuma firgicinsa akan tunanin idan gaskiya tayi halinta watarana ne. Rokonsa tayi da sigar da bai ga kofar kubucewa ba.


"Kayi min alkawari daya Ya Abbati..."


"Kina son wani abu ne bayan ni?"


Girgiza kai tayi tana murmushi "kwantar da hankalinka ba mutum bane."


"Au tohh. Ina jin ki. Nayi alkawarin."


"Babu zancen sirri ko rufe wani abu da zai zo tsakaninmu nan gaba. Ko aure ka ke son karawa ka fada min da wuri ba don neman izini ba sai don bani da boye boye kuma bana son ayi min."


Jikinsa ya yi sanyi kalau yaji tsana fiye da ta baya game da rayuwarsa.


"In sha Allahu irin zaman da zamu yi kenan. Kuma tunda kin amince min zan sanar da iyalina game dake tun kafin iyaye su zo."


Hira suka soma gwanin sha'awa basu ankara ba ashe Alh. Tahir ya fito kiran Suhaib domin kiransu Abbati cikin falon. Da ya hango Farhansa tare da Abbati sai da yaji zuciyarsa ta wani takure a kirjinsa. Abu ne dai bai taba ji ko gani ba tun tasowarta. Damuwar da suke da ita shi da Mami akan wannan matsala yana sa ran cewa ta kau. Tahowa ya yi garesu fuskarsa a sake ya ma manta da fushin Farha.


Ita ta fara ganinsa ta daure fuska sosai. Bata da yadda zata yi da zuciyarta akan bakincikin  hoton da kwakwalwa ta kasa gogewa. Mahaifinta dauke da kawarta akan cinya daga shi sai dogon wando da singeleti. Wannan abu har ta koma ga Allah bata jin zai taba fita daga ranta. A yadda kuma abin yake mata ciwo har yanzu ta san bata da karfin gwiwar fuskantarsa ba tare da tayi abin da za ta yi nadama a gaba ba.


Gajeren tsakin da zuciya tafi karfinta a kai ne ya fito ba shiri a lokacin da take cewa Abbati,


"Don Allah zo mu koma daga can saboda idon mutane."


Yaji tsakin sannan kuma muryarta ta sauya lokaci guda. Juyawa ya nufi yi domin ganin wanda ya bata mata rai sai yaji ta ce,


"Kar ka juya mana.."


Sai dai ya riga ya ga Alh. Tahir din wanda fuskarsa take tamkar gonar auduga. Ya juya ga Farha ita kuma tata babu annuri ko digo sai ma kwalla da ta cika mata ido. Sai yaki motsawa daga inda yake.  Yana ganin ta fara tafiya bai san lokacin da tasa muryar ta fito da sigar umarni ba.


"Dawo ki tsaya."


Sau daya ta kalli fuskarsa wadda ta sauya shi ma babu wasa ko kadan taji kafafunta sun daskare a wurin. 


Alh. Tahir yana karasowa Abbati ya durkusa cike da ladabi ya gaishe shi. Ya amsa masa tare da mikar dashi tsaye ta hanyar dago hannuwansu da suka yi musabaha. Wanda kuma Alh. Tahir din ne ya mika masa.


"Tashi tashi ai ka zama dana."


Wajen sati guda sai yau yasa Farha a idonsa. Amfani ya yi da albarkacin idon Abbati ya janyota barin jikinsa.


"Farhan Abba wato tun yanzu za ki min ritaya ko?"


Da kyar ta saki jiki ta rabu da jikinsa amma har runtse idanu tayi saboda tsigar jikinta da ta tashi. Mahaifi! Sanin mahaifinka yana zina daban da ganin mahaifinka a yanayin da ya kusanci zina. Yanayi mai nuni da cewa anyi ko ana gabar yi. Its devastating! Kada Allah Ya hadamu ko zuri'armu da mummunan gani irin wannan.


Abbati dake dariyar kalaman Alh. Tahir bai fasa la'akari da yanayinta ba. Hakan ya tuna masa da abin da Suhaib ya yi rannan a gabansu na kin zuwa gaishe shi. Ko ba a fada ba ya gane akwai matsala kenan.


"Ki bamu aronsa kakaninki da baffani zasu gaisa dashi." Cewar Alh Tahir. Sannan ya dubi Abbati "ina fata kai da abokinka da gaske kuke akan 'ya'yana. Idan akasin fahimtarmu ne a gabanku don Allah kada ku yaudaresu."


"In sha Allahu ba za mu baka kunya ba" Abbati ya furta kai a kasa.


Alh. Tahir sai ya murmusa "Allah Ya muku albarka. Bari na nemi Suhaib a waya ya shigo daku wurin 'yan uwana."


Da haka ya tafi. Farha ma sai ta daga kafa tana shirin barin wurin. Da muryar dazu ya ce,


"Farha."


Kiran ya fadar mata da gaba. Ya tuna mata cewa Abbati babba ne ta kowacce fuska akanta. Ko Suhaib bai isa ya kara dashi a shekaru ba balle ita. A hankali ta juyo suna hada ido sai hawaye ya soma gudu a kumatunta. Kallon roko da magiya tayi masa sannan ta fadesu da baki.


"Don Allah kada ka tambayeni komai."


Sai ya sami kansa da yin murmushi "bani da niyar tambaya. Amma duk da haka ina da abin cewa idan kin bani dama."


Sai ta dawo ta tsaya sosai lokaci lokaci tana goge hawayenta da bayan hannu.


"Yanzu kin ga idan ba ni ba babu wanda zai ce kin burge shi da wannan fuskar da ta baci da kwalli."


Sai da yaga murmushinta ya soma magana a nutse.


"Ya Farha darajar mahaifi da mahaifiya ta girmi komai da kowa banda da'a ga Allah da ManzonSa SAW."


"Na sani" ta ce a raunane wani hawayen yana zubowa.


"Ina mai baki shawara da kiyi amfani da wannan ilimin ki bi hanyar da ta dace ta mu'amalarki da Abba." 


Babu wasa ko damar tayi masa musu a maganganunsa. Cigaba ya yi har sai da ta fashe da kuka sosai.


"Allah SWT Ya yi mana dukkan gata da bai watso mu cikin duniya ba tare da iyaye ba. Daga Mahaliccinmu sai Annabinmu sannan iyaye a girman daraja. Allah Ya ambaci yi Masa biyayya tare da da'a ga iyaye a wurare daban daban cikin littafinsa mai tsarki. Karshe ma dai iyayen nan kin sani saboda adalcin musulunci ya horemu da kyautata musu ta kowacce siga koda mushirikai ne. Illa iyaka kada mu yi musu biyayya wurin saba Masa. Tunda sune abu mafi kusanci da suke tuna mana da Girma da Buwayar Allah. Cikin hikimarSa ya hado mutane biyu mabanbanta jinsi da komai Ya ce musu ga amanar bayiNa wato 'ya'ya. Sai ki ga mutum har sata ya kan yi domin ciyarwa ko dauke wata lalurar wannan amanar. Wani ayi ta cin zarafinsa a wurin aiki amma ya yi ta jurewa saboda albashinsa shi ne abincin 'ya'yansa. So many things dai da ba sai na fada ba. Wasu irinmu mu da bai bawa 'ya'yan ba har kuka muke muna fargabar ko girman zunubanmu ne yasa Allah bai bamu amanar bayinSa su zo a matsayin 'ya'yanmu ba..."

Kuka ta fashe dashi domin ya gama daureta da jijiyoyinta. Ta san Qibdiyya ba 'yarsa bace kuma bai ce mata yana da d'a ba. Amma da ya fada da bakinsa sai da ya tabata fiye da zato.

"Kayi shiru don Allah, za ka haihu in Allah Ya so....na fahimci kuskurena kuma Allah zan gyara."

"A yau ba gobe ba?"

"A yau ba gobe ba."

Murmushi ya yi ya ce "Allah Yasa ke dinnan rabona ce ta duniya da lahira" 

Amin ta ce yadda zai ji domin ita kam bata jin kunyar ya san cewa tana yi masa soyayya mai girma. Duk mutumin da zai gan ka a irin yadda ya ganta ya kuma zauna yana kokarin ganin ka gyara lahirarka baka da na biyunsa.

Basu gama hirar ba Suhaib ya zo suka wuce cikin falon tare da Munzali. Da wasa da dariya  dattijan suke yi musu tambayoyi har aka gangaro kan sana'a. Bakinsu a hade suka ce kasuwanci suke yi. Iyayen sun yaba da halayyar da suka gansu  a kai aka shiga barkwanci.

Wannan lokacin Shazali ya zaba ya kira Abbati. Kiran da Munzali ya fito ya same shi a mawuyacin yanayi a dalilinsa. Jijiyoyin kansa duka sun fito sai gumi da yake tsatstsafo masa saboda firgici. 

"Allah mun tuba. Allah Ka rufa mana asiri"

Kalmominsa kenan har suka shiga mota a gigice suka tafi ko sallama basu koma sun yiwa kowa ba.

"Idan ya fada mata wallahi da kyar in bata tsine min ba. Munzali yaya zanyi da rayuwata kuma? Me zai rage min idan Baaba taji wannan zancen?"

Abbati kuka yake yi. Kuka kamar karamin yaro. Irin kukan da ya manta rabonsa da yin makamancinsa. Bai hada iyaye musamman Baaba Mari da kowa ba. Ita ce mafi girman gatan da Allah Ya bashi domin ba don ita ba kila bayan waccan dabi'a sai ya hada da wasu munanan alfashar.

Munzali ma kukan yake yi ya kuma kasa rarrashin Abbati. In ta kwabewa daya ta kwabe musu ne su duka. Hanyar Kirikasamma ya dauka ba tare da tunanin komai ba.

***




I just published "28" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1069889361?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=KFjeRCEYOeCCop1KZemoqtrxbYnKdEUt%2BN3vuRslVOGHXeVyvRctm2H9e2ieXQp2h5na2H8%2FZfP%2Fo%2BHnu2uzK%2BqpwO8SvawBfcO53XyKaH3pEGnYSjnrlqziEAz69pxG

UWA UWACE...28


Batul Mamman💖




KULLU AMIN WA ANTUM BIKHAIR. EID MUBARAK✨🌙


(Yau da gobe tasa na fahimci cewa kowane littafi shi yake rubuta kansa. Marubuci zai gama tsari labari da lokacin da yake hasashen kammalawa. Amma da zarar ya dora alkalami ya fara rubutu, sai yadda labari ya yi dashi. A yadda naso da yanzu tuni na kusa gama wani labarin bayan UWA UWACE, Allah bai nufa ba. Labarin ya zo lokaci guda da jinkiri kala kala. Na gode da hakurinku tare da bibiyar lafiyata da kuka dinga yi.)


***********

Kallon jan fentin da aka yiwa alamar (×) a jikin gidanta Uwani tayi taji jiri yana dibarta. Tambayar Salihi ta dinga yi cikin sarkewar harshe kamar ya san wani abu a kai.


"Me nayi? Ina da takardun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login