Showing 162001 words to 165000 words out of 242549 words

Chapter 55 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3407

wuce ya soke auren ba ya cigaba da yawonsa. Wanda kuma duk ya yi zina da ahalin wani shi ma sai anyi da nasa.

A gefe guda kuma mahaifiya ga Lilu mace ce tagari. Uwa ce da ta amsa sunanta wurin tarbiyya da yawan yiwa 'ya'yanta addua. Ga Ubangijin da take mikawa lamuranta Mai ji ne ga kukan bayinSa. Al Hayyu, Al Qayyumu ba zai bata kunya ba.

Gamu ga Sarkin da baya saba alkawari. Mahaliccin da Adalci ya kasance cikin suffofinSa. Duk da cewa labari ne amma ina son tunatar damu uwaye karfin addua. Tabbas alkawarin Allah na dawowa mazinata da sharrinsu ta hanyar da zasu koka ba zai tashi ba. Sannan kuma adduar Uwa ta gari ga 'ya'yanta wannan kaifiyan ce.

Indai haka ne kuwa to lallai Alh. Tahir sai ya yi kuka akan sharrin da aka yiwa Lilu. Sannan Mami Khadija sai ta kara mika wuya ga Allah a yayinda Ya kubutar mata da danta daga dabaibayin da bai isa ya kwance ba.

Ya Rabbi ka karawa Annabinka daraja, Ka azurta shi da kololuwar daukaka. Amin.




***
Mami Khadija kiran Lilu tayi bayan ta rufe kofarta. A zatonta Alh. Tahir ya bar wurin ashe yana tsaye. Kafafunsa sun yi masa nauyi ya kasa dagasu. Lalacewarsa bata yi kamarin da zai iya cigaba da jure juya baya daga tsatsonsa ba. Bazuwar zancen nan zuwa kunnuwan ragowar 'ya'yansa ba karamar barazana bane ga mutumcinsa a idanunsu. Shi kuwa zai iya komai domin kare wannan martabar. A tsarinsa miji ko mata kada ya fishi girman masauki a zuciyarsu. Yana son ya zama babban amininsu kamar yadda suka faro tun kuruciya. Wannan dalilin ne ma yasa Farha da Lilu suka ji ciwon laifin nasa fiye da yadda zasu misalta. Muryar Mami yaji cikin dakiyar da ya saba gani a tare da ita tana magana da Lilu.

"Ina ka tafi?"

Bai ji amsar ba sai abin da ta mayar masa. Yadda tayi magana babu alamun wasa ko wargi. Umarni ne take bayarwa domin ta kare dan nata.

"Yana daga cikin rahamomin Ubangiji garemu da Ya halatta mana yin abota. Lokuta da dama suna maye gurbi ko ma su fi family dinmu tsaya mana akan matsaloli. Sai dai kuma ba kowacce irin matsala ya kamata a fadawa aboki ba. Wani abin sirrinka ne har lahira. Idan yau kaje wurin abokai da damuwar nan har ka fada musu komai ka cuci kanka. Ba kai kadai ba hatta 'yan uwanka ka tozartasu a idon duniya. Saboda haka duk mummunan sirrinka da Allah bai tona ba kada ka zama mai fitar dashi. Zai zama tamkar ka cakawa kanka wuka ne da kanka. Shi mahaifi sutura ne ga zuri'arsa. Abu kadan idan ya faru wanda ya dauke uba daga muhallinsa a wurin 'ya'ya sai kaji ana kiransu 'ya'yan mace. Kuskure guda daya tak zasu aikata sai a kusa shekara ana goranta musu duk don babu uba kuma babu madadin uban. To ina ga kai da kanka ka tona halin naka? Abokanka karshenta suyi maka tayin kayan maye. A halin da kake ciki na san karba zaka yi"

Shiru suka yi na 'yan dakiku kafin Mami Khadija ta ambaci alkunyarsa wadda mutane suka bar kiransa da ita.

"Khalil?"

"Na'am" ya amsa da muryar da ta makale a makoshi saboda damuwa.

"Ina fata sunanka zai jagoranci hukuncin da za ka yanke domin ni kam bani da sauran abin cewa gareka. Banda iyayena dominku nake komai. Don Allah kada ku sa bayan kukan miji na dora da na 'ya'ya."

Lilu sai ya fashe da kuka. Mami Khadija ta dinga rarrashinsa da kalmomi masu dadi. Ba don gargadin da tayi masa ba tabbas idan yaje wurin abokan nasa sai ya farkewa mahaifinsa laya. A ganinsa hakan ba zai zama komai ga mutumin da bai iya daraja kansa ba. Ya manta bayan shi akwai 'yan uwansa. 'Yan uwan ma mata masu rauni. Gashi babu wadda tayi aure. Wane dan mutumcin ne zai so auren 'yar mutumin da aminiyar 'yarsa take ikirarin yayi mata ciki?

Da wannan tunanin ya sauyawa shawararsa akala. Alwala ya dauro ya sanya dogon wando da tsaftatacciyar jallabiya ya dauki littafi mai tsarki ya soma karantawa.

(Babu wani abu mai canja kaddarar bawa ko ya sassauta ta kamar addua. Duk takun da bawa zai yi domin kusanta kansa da Mahalicci, Sarkin da bashi da wa'adin zamani zai zo gareshi da fiye da wannan.)

***

Shi kuwa Alh. Tahir kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ya bar kofar dakin. Kamar da wasa haka ya shigo tariyo wasu kazaman mu'amala da ya yi da mata daban daban. Tunanin kuwa yayi sanadiyar radadi mai azaba a cikin zuciyarsa. Yana cike da tsoro matuka a wayi gari duka 'ya'yansa suna yi masa kallon fasiki. Wannan rana ya tabbata zata fi kowacce muni a gareshi. Ba zai jure kallon kyama irin wanda Suhaib da Farha suka bishi dashi ba daga dukkansu. Shi bai ma san soyayyarsu tayi masa irin wannan kamun ba sai yau. Har musu ya yi da zuciyarsa akan cewa yanzu son da fargabar kiyayyarsu ya ninku sau adadin da bai sani ba a ransa. Zazzabi ya soma ji tun kafin ya isa nasa bangaren. Tunani ya sha masa kai bai ga isowar Suhaib gabansa ba sai muryarsa wadda ta dawo dashi hayyacinsa yaji.

"Ina son zuwa Kano gobe in sha Allahu."

Alh. Tahir ya ware idanunsa sosai da son dawo da nutsuwarsa jikinsa. Bashi da lokacin zurfafa tambaya ko binciken me dan nasa zai je yi a Kano daga dawowarsu yau. Ya dai aminta dashi ya san ba shashanci ne zai kai shi ba. 'To ma idan shashancin ne ai a wurinka ya gada' wani sashe na zuciyarsa ya tuna masa.

Shi dai Suhaib yanayin sanyin da ya gani a wurin mahaifin nasa ya bashi mamaki. Domin Alh. Tahir mutum ne mai yin komai da kuzari. Sai ya sami kansa da kasa sharewa.

"Abba lafiya dai?"

Alh. Tahir yayi murmushin jindadi har hakoransa suka fito. Yau shi ne Suhaib yake nuna damuwa akan damuwarsa.

"Lafiya kalau. Kaina ke ciwo shi yasa ma na dawo da wuri. Anjima kazo in kara maka guzuri"

"Na gode. Kuma Allah Ya kara sauki" cewar Suhaib yana yin gaba.

Wurin Mami Khadija ya wuce don baya son sai dare yaje yace zai yi tafiya da safe.

Tunda taji sallamarsa bata yarda ya karaso dakin ya sameta a yanayin da take ciki ba. Fuska ta saki har ya shigo ya fada mata zancen tafiyar. Ba karamin dadi taji ba kuwa saboda ko kadan bata so ya fuskanci abin da ya faru. Tafiyar tasa tamkar rage karfin rikicin da take gudu ne. Dagula komai zai yi da fushinsa da zuciya.

"Allah Ya kiyaye hanya. Kwana nawa zaka yi?"

Suhaib wani irin kallo ya yi mata na rashin gamsuwa. Maminsa mai bin kwakkwafin yara normally cewa zata yi me zai je yi.

"Mami lafiya kuwa? Ko baki da lafiya?"

Fahimtar inda ya dagota da tayi yasa ta nemo murmushi ta dora akan fuskarta.

"Wai don kaga ban tambayeka komai game da tafiyar ba?"

Kai ya gyada kawai yana yi mata kallo na son gano inda baraka take idan akwai ta.

Murmushi ta sake yi sosai ta ce "jikina ne ya bani kamar surukata daga Kanon zata zo. Ko dai wurinta zaka je ko kuma idan ka tafi yau zaku hadu."

Suhaib dai bai san kujerar da Ayaah ta samu a zuciyarsa ba amma kalaman Mami sun saka shi jin kunya. Shi din ba ma'abocin harkar mata bane saboda tsoronsa na zama tamkar babansa. Faffadan murmushin kama kai ya shiga yi gami da susar keya.

Mami Khadija ta mike cike da farinciki tana dariyar da ta bayyana hakora.

"Hasashena ya zama gaskiya akwaita kenan. Alhamdulillahi. Na santa?"

"Nifa Mami ki ma daina wannan batu don ban girma ba."

Kallon ka-ma-rainani tayi masa tana cewa "to bari nayi addu'a ga wadda zaka je wurinta din. Allah Ya kawo mata santalelen miji wanda zai aureta nan ba da jim...."

Abin da yayi a lokacin har ya koma dakinsa yana mamakin kansa. Katse addu'ar Mami ya yi da saurinsa yana mai bata fuska.

"Ba amin ba."

Ta dage gira tana leken fuskarsa da yayi kicin kicin da ita.

"Koda kaine mijin?"

Shi ma sai sannan ya gano tasa katobarar. Gaggawar fita daga dakin nata ya yi cike da jin kunya yana cewa ba abin da take zato bane.

Sai da ta tabbatar ya fita ta iya sauke ajiyar zuciya. Farha ce kuma a ranta yanzu. Yarinyar tana da dauriya fiye da zato da tsammani. Da ta matsa mata da tambaya tabbas ta sanar da ita cewa har yanzu bata ji daga Abbati ba. Bai daga wayarta ba sannan kuma bai nemeta ba. Hankalinta taji ya tashi da tsoron kada zuwansa rayuwar Farha ya zama tamkar lasawa yaro zuma a baki. Da ace abin da ya saka shi komawa gida ya girmama bata jin mahaifiyarsa zata boye mata lokacin da suka yi waya. Tunanin ba zai fissheta komai ba shi yasa ta fita zuwa dakin 'yan matan.

*

(Allah Ya zama gatanka akan duk abin da baka da iko akansa)

Sakon sms da Farha ta turawa Abbati kenan taji an murda kofar dakinta. Mami Khadija ce ta shigo da sallama. Farha tayi saurin gyara zama daga kashingiden da tayi.

"Ya naga kowa ido biyu ne? Na zata zan sameku duk kun kwanta saboda sammakon da akayi."

Dan murmushi Farha tayi tana cewa kwanciyar zata yi yanzu. Mami sai ta sami wuri a bakin ta zauna.

"Farha" ta kirata a tausashe. Ba da baki Farhan ta amsa ba, sai dai ta tattaro hankalinta da nutsuwa ta mikawa mahaifiyarta. Mami Khadija ta cigaba da magana "kafin faruwar abin nan, ina nufin tafiyarsu gida babu shiri ranar da suke ganawa dasu Abbanku kun samu sabani ne?"

"A'a Mami" cewar Farha tana danne kwallarta. Kewa da damuwa akan rashin sanin halin da Abbati yake ciki sun yi mata yawa. Karfin hali da dauriyar tata sun kai makurarsu.

"Ki kwantar da hankalinki ki kuma yawaita addu'a. Ba komai da muke so bane alkhairi a garemu. Miji kuma babu matar da zata auri wanda ba nata ba" da dan sauri Farha ta dago ta dubeta tana son ta ce ita dai Abbatin kadai take so amma ta kasa. Mamin ma dai murmushi tayi "ke dai ki kasance mai mika wuya wurin karbar kaddara. Mijinki da yardar Allah wanda zaku kama hannun juna ne har aljanna. Bana miki fatan haduwa da abokin rayuwa wanda zaki so tatayyarku ta kare a duniya kadai."

Farha ta san da wa Mami take shi yasa ta dinga zubar da hawaye. Duniyar gabadaya sauki ne da ita amma mazauna cikinta suyi ta jajibowa kansu matsaloli ta hanyar sabon Allah.

A daren ranar Jiddo ta kira Danliti ta fada masa Suhaib ya karbi nambarsa a wurinta. Ta kara da cewa bata san manufarsa ba saboda haka tana mai gargadinsa da ya yi taka tsantsan. Ya kuwa yi mata alkawarin kiyayewa.

Sai dai kuma ta riga ta makaro. Tun bayan komawar Suhaib dakinsa ya kira shi. Sauya murya ya yi yadda ba zai saurin gano shi ba ya ce kwatancen garejinsu yake nema.

"Kwanaki mun zo tare da wani abokina daga Abuja har ka bashi nambarka. Na shigo gari ne mota take ta bani matsala. Idan zan sami gyaran da wuri ina son kawo maka ita gobe."

Kalmar Abuja kadai da Danliti yaji tasa shi bayar da cikakken kwatance harda wata nambar idan bai same shi a wannan ba. A gefe guda kuma maganar Jiddo ta sanya shi yiwa Ayaah mugun tanadi. Indai akwai wata alaka tsakaninta da Suhaib da wannan shirin nasa zai bakanta masa rai. Ita kuma ya zama ladan bata masa lokaci kamar bata san me ya kawo shi ba tun farko.

***

Duk wani taimako da Uwani zata iya bawa Qibdiyya tayi a lokacin wanda bashi da wani yawa. Mafi a'ala a kaita asibiti wurin kwakrarren likita domin a dubata yadda ya dace. Shawarar da ta bawa Munzali kenan bayan sun fito daga dakin.

Kai ya gyada mata ba tare da ya iya magana ba. Zazzabi yake ji yana bin lungu da sako na jikinsa kamar ana gasawa akan garwashi. Numfashi da iskar da yake fesarwa ta baki ta hanci duk zafine dasu. Daki ya nuna musu a kasa ya ce idan zasu kwana ne ga wuri nan idan sun idar da sallar magariba. In kuma zasu tafi ne shi ma ga kudin mota don ba zai iya tuki ba. Ficewa ya yi daga gidan bayan ya yi tasa sallar a daddafe yana taku kamar a iska saboda rashin nauyin jiki yaje kofar gidan Abbati. Shi kadai kawai yake son fadawa abin da yake faruwa domin ya dauki mataki. Don sai yanzu ya kara yarda cewa Abbatin ya fishi tunani. Duk inda ya laluba sai yaga kamar idan ya taba Lilu sai ya kashe shi. Ya san zafin fyade tunda Shazali ya yi masa a shekarun da suka fi na Qibdiyya ma. Ya san ciwon da rai ke rikewa a yayinda ya san cewa shi ne sanadiyar dulmiyar wani a aikin sabo. Wannan ya tilasta masa yin sanyin da yake ganin yanzu ba muhallinsa bane. Salamar da ya san Abbati zai cusawa ransa ko yaki ko yaso ya tattaro ya sanyawa zuciyarsa. Saboda idan bai nutsu ba yana da yakinin cewa sai ya yi abin da zai yi nadama a gaba. Gara ya nemi uban Qibdiyya ya nemi shawararsa kafin ya zartar da nasa hukuncin. Ya debi kusan mintuna goma yana sallama da kwankwansa kofa kafin Hanne ta bude masa. Yadda ta bude kofar da dankwali a hannu zai sanar da duk wanda ya ganta cewa daga bacci ta tashi. Yatsina fuska tayi da ta ganshi taja guntun tsaki. Murmushi mai ciwo ya yi mata. A ransa yake jin kinsa da take yi tuntuni ba zai rasa nasaba da kasancewarsa sanadiyar bata rayuwar mijinta ba.

"Don Allah kin yi waya da Abbati? Na neme shi na kasa samunsa."

"Rabona dashi tun ranar asabar da kuka fita tare" ta bashi amsa tana cika tana batsewa. Ganin bai ce mata uffan ba ya juya zai tafi sai ta ce "kayi ka gama munafurcinka na son saka shi ya min kishiya. Ta Allah ba taka ba."

Bai ko waiga ba balle ya kalleta. Yana ji ta buga kofa da karfinta kamar za ta balleta. Gida ya koma ya shige daki bayan sallama da su Uwani sun ce ba zasu kwana ba. Asabe ta so ya bata Qibdiyya su koma ya ki. Bayan tafiyarsu ya karbi abinci a wajen Kande ya bawa Qibdiyya. Yarinyar jikinta duk yayi sanyi ta kasa sakin jiki tayi wasa saboda yanayin da taga babanta. A jikinsa kawai ta sami wuri ta kwanta tayi lakwas.

Munzali ya dinga kallonta yana kara tsinewa Shazali. Ya kuma kara tsanar Alh. Rabi'u wanda sakacinsa ya zama masomin lalacewar tarbiyar gidansu. Duk abin da ya samesu da shi 'yan uwansa babansu ne sila. Sakarwa iyalansa mata ragamar gidansa da hadasu da nauyi da hakkokin da ba nasu ba shi ne matakin farko na tabarbarewar lamuransu. Tsatson Innayo sun dace da uwa ta gari amma halin uba ya zama jirwaye ga tarbiyar irinsu Uwani. Shi kuwa da 'yan uwansa da basu yi sa'ar uwa ba sai dukan ya zame musu biyu.

Waya ya dauka ya sake kiran Abbati duk da bai sa ran cewa za a amsa ba. Jikinsa yana bashi cewa Abbati yana cikin koshin lafiyar jiki. Sai dai bashi da tabbacin ta ruhi. Washegari litinin dama ya yi niyyar binsa idan shirun ya yi yawa. Ya tabbata sirrin boye ya riga ya fito fili. Wannan lokacin ne Abbati yafi bukatarsa. Su Baaba Mari zasu yafewa Abbati idan suka ji cewa shi ne ya fara saka shi a wannan hanyar zasu dauki laifin su dawo masa dashi.

*
A cikin halin ciwo Baaba Mari take sosai don sun sake komawa asibiti. 'Yan uwa da basu san me yake faruwa ba suna ta al'ajabin wannan abu. Ace mutum kamar Abbati ya kasa kai mahaifiyarsa babban asibiti a halin da take ciki. Tun ana kananun maganganu da safe har aka fara tararsa gaba da gaba ana fada masa zuwa yamma. Kannensa ma sai da suka nuna bacin ransu sosai. Ya rasa inda zai saka ransa yaji dadi. Ciwo yana cinta amma ta ce indai ba halal ya nemo ba ya barta ta mutu ta huta.

Wuraren Isha sai ga Mal. Inuwa ya shigo dakin kamar an koro shi. Kullin leda ya dauko daga aljihun 'yar sharar jikinsa ya mikawa Abbati.

"Ga wannan dubu talatin da hudu ne mu mayar da ita babban asibiti."

Da kyar Baaba Mari ta iya bude idanunta ta dube su. Mal. Inuwa yana ganin fasalin kallon mai kama da na tuhuma ya hau rantse rantse. Yanzu tsoron bacin ranta yake yi da gaske.

"Gonarmu da wajen gari na sayar. Da shike ba girma gareta ba shi yasa bata yi kudi sosai ba. Nan an warewa duka 'ya'yan Malam (yan uwansa da suka hada uba) kasonsu. Wannan ne nawa." Ya sake nuna ledar.

Da Abbati ya karba sai da yaji kamar bai taba rike rabi rabinsu ba a rayuwarsa. Kudi dai ya baya miliyan biyar baya a asusunsa na bankin da atm din yake jikinsa a yanzu haka. Da za a tara abin da ya tara da kadarorinsa shi ma ba zai ce ga adadin abin da za a samu ba. Sai dai duk wannan arziki tubalin toka ne. Kwakkwarar iska guda ta hure komai saboda haram dama bata da nauyi. Da zarar mutum ya dauki damarar rabuwa da ita indai da zuciya daya ne to tafi komai saukin saukewa.

Suna shirin tafiya don har an samu musu mota kwatsam sai ga Mal. Sa'idu a kofar dakin yana sallama. Kallon kallo aka soma tsakanin Abbati da kannensa. Dame kuma yazo?

Mal. Inuwa ne ya leka sai dai bai jima ba ya dawo yace Abbati yaje.

"Gani"

Leda sak irin ta hannun Mal. Inuwa ya mika masa. Da ace hankalin Abbati a kwance yake da yaga yadda tsufan kawun nasa ya sake bayyana. Ya zabge sosai a tashin hankalin kwana daya. Allah Ya ragewa aya zakinta akwai hannunsa dumu dumu a cikin rayuwar duka 'ya'yan gidan. Ba don haka ba da tuni ya lakabawa Baaba Mari laifin bata danta. Kila ma zuwa yanzu duka gidan da garin sun gama ji har an karar da tofin Allah tsinen da za ayi masa. Da yake shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login