Showing 195001 words to 198000 words out of 242549 words
aka yi masa shi ne cewa yau da yamma mutumin da zai zo suyi abin zai yi tafiya zuwa wata kasa. Shi kuma Comared a cewarsa wai shi kadai ya sani wanda zai rike musu sirri a kankanin lokaci. Sannan tunda shi din bai saba ba dole aka nemo masa kwararre. Har zuciyarsa yake kyamar wannan abu to amma idan ya tuna da kalaman mahaifiyarsa akan auren Yumna sai yaji wani irin kwarin gwiwa. Ko ta wane hali sai ya kifar da maganar aurenta sannan yaci mata mutumci akan wulakanta shi da tayi a gaban 'ya'yansa. Allah wadaran bariki. Banda haka me zai sa yarinyar da take durkusawa har kasa ta gaishe shi ta koma abokiyar sa'in'sarsa? Har ta kai yana fada tana fada. Yau da ta halali ya nemi aurenta komai son da yake mata ya san dole ta bashi girmansa na mijinta kuma sa'an uban da ya haifeta.
Suna hanya da direbansa ya kira Mami Khadija ya fada mata aikin da zai yi a Kano ya dawo yau. Zai fara zuwa duba Suhaib da sun shigo gari sannan ya wuce. Tana jiran ya fara ajiye wayar bayan tayi musu fatan sauka lafiya su duka sai taji ya fara cigiyar 'ya'yansa.
"Bani su mu gaisa" ya tambaya da dan jin nauyi.
"Lilu yana tuki, Farha kuma tayi bacci" ta kashe wayarta bata jira taji me zai ce ba.
Su biyun duka sai suka juya bayan motar inda take zaune ita kadai suna kallonta. Ta dauke kai abinta ta lumshe idanu tana 'yan tunane tunanen da suka zame mata jiki. Idanunsu da ta dinga ji jifa-jifa yasa tayi dan murmushi ta bude nata a kansu. Ba shiri suka mayar da kallonsu gaba lokaci guda.
"Lilu rami kake son tura mu ne kake kallon baya haka?"
Kai ya shafo da 'yar dariya "wane ni in kai Ya Farha rami saurayinta yasa a kulleni?"
"Dama ka gama raina ni shi yasa ka rasa amsar fada sai wannan" cewar Farha tana kai masa duka shi kuma yana karewa.
"Bana son ganganci ana tuki."
Nutsuwa suka yi na dan lokaci kafin Lilu ya soma magana.
"Wai Mami musulunci ya wajabtawa mata zama da miji mai bin mata ne?"
Gaban Farha ya fadi da tsoron kada Mami ta zata ita ta sanar dashi abinda ta sani. Ta kalle shi ta kalli Mamin a fakaice. To shi ma din bakinsa ya rufe da hannu saboda shirmen da yake tunanin ya yi na maganar a gaban Farha.
Yadda suka koma kallon kallo suna tuhumar juna da ido sai kawai Mami Khadija ta ce "don Allah ku rike sirrin nan kada ya kai kunnuwan Sauda da Mardiyya. A kalla ko su biyu ne a samu su dore da yiwa mahaifinku kallon nagartaccen uba."
"Ya Suhaib ya sani?"
Farha ce tayi tambayar sai dai kafin ma taji amsar Mami ta fahimci ya sani din. Biri yayi kama da mutum. Tsahon lokaci suna mamakin rashin shakuwar babansu da babban wansu duk yadda Abban yake da jan yara a jiki. Abin ya dade yana damunsu. Ashe ba a banza ruwa ya yi tsami ba.
Tunda Mami Khadija ta rufe ido bata kara cewa dasu uffan ba. A tunaninsu tayi bacci ne shi yasa suka fadawa juna abin da suka sani. Farha harda kwalla. Tana jinsu suna ta maganar mutum mafi soyuwa a garesu a 'yan kwanakin baya da sigar kyama da bakinciki. Me yafi wannan tashin hankali da ciwo a wurin uwa? Ashe zaman da iyaye suka tursasata ake yi masa kallon rufin asirin miji fanko ne? Da ta bar gidan sun yi nesa dashi da matukar wuya su san halinsa. Ko sun sani ba zai musu ciwo kamar yanzu ba da suke rayuwa tare suna yi masa kallon nutsatstse. Da karshenta yana nan da darajarsa ta uba.
Duk lalacewarsa mijinta ne shi dai uban 'ya'yanta. Babu yadda za ayi uwa tayi maraba da raini ko tsana ta gifta tsakanin mijinta da 'ya'yansu. Uwaye da dama sun sadaukar da manyan burikansu domin 'ya'yansu su tashi a happy home. Ayi ta jure mugun halin miji domin kada gurbin mahaifi ya sami tawaya a rayuwar yara. Ita dai sadaukarwar bata yi mata rana ba. Amsa sunan matar fasiki mai gadara da sab'on Allah ba hakuri bane....!
(Ya Rabbi kada Ka jarabcemu ko mazaje/matayenmu da alfasha. Wadanda Ka hada da fasikai Ya Allah Ka basu ikon daukar matakin da zaka yi farinciki dasu rana gobe kiyama. Amin)
Hukunci ta yanke a take a zuciyarta. Wannan karon babu gudu babu ja da baya.
***
Karfe bakwai Abbati ya gama kimtsa dan abin da ba a rasa ba mallakinsu a dakin asibitin. Munzali ya kafe kai da fata ba zai kuma kwana ba. Jinyarsa ta ruhi ce ba gangar jiki ba. Idan zai sami nutsuwa a zuciyarsa babu abin da zai hana lafiyarsa dawowa.
Sai shadaya da kwata da likitoci suka zo round aka sallamesu. Tare suka tafi gida da Innayo, Salima da Uwani. Sai kuma Salihi wanda shi ma da wuri ya iso saboda kwana da suka yi da fargabar halin da Qibdiyya take ciki. Asabe bata zo ba suna gida ita da Zara saboda Abbati yace ta zauna a gida a matsayin tana kula da Qibdiyya.
Da suka fito zasu tafi ya kasance inda Abbati ya ajiye motarsa da tazara da inda Salihi ya aje tasa. Abbati sai ya ce su Innayo su shigo motarsu. Idan gida zasu koma zai kai su. Baya suka fara shiga sai ga Salihi ya zo bangaren da Uwani take ya yi mata magana.
"Muje ina son magana dake."
Tsuke baki tayi sai da Innayo ta leka tayi mata kallon da ya sanyata bin sa babu shiri. Munzali yana fama da kansa amma hakan bai hana shi yin dariya ba.
"Wai ni Uwani yaji tayi ne kamar wata karamar yarinya?"
"Kaima ka fada Munzali. Sai kun taru kun sauke mata Al-Qur'ani izzu sittin ina jin."
Dariya aka sake yi yayinda Abbati ya tayar da motar suka wuce gidansu kai tsaye. Munzali ya tambaye shi me zai hana su fara sauke su Innayo maimakon yaje Rijiyar zaki sannan ya koma Dala. Motar sai tayi dif na takaitaccen wa'adi kowa yana tunanin amsar da ba za ta fallasa abin da suke kokarin boyewa ba. Abbatin ne ya amsa masa da cewa zai taho da Asabe dasu Ummakati tunda basu sami zuwa asibitin yau ba. Cike da farincikin hangen nesan amininsa Munzali ya yarda da amsar har ma ya murmusa.
Da isarsu gidan bayan maigadi ya bude gate suka ga mota a ajiye a kusa da bangaren Munzali. Su Innayo basu shiga cikin gidan ba amma Abbati ya bi bayan Munzali har cikin falo. Zaune a ciki kuwa ba kowa bane illa Daddy da Zakiyya suna gaisawa da Kande mai kula da Qibdiyya. An janyo centre table gabansu inda Kuku ya ajiye musu kayan motsa baki.
Daddy yana shan juice sai wani gadara da fizgar kai yake irin na matasa masu zafin kai ko gaishe da maigidan bai yi ba. Abbati kuwa gabansa ne ya buga sosai har sai da ya dafa kujera yana mai fargabar ko Shazali ya nemi Zakiyya ne.
Munzali bai bi ta kan Daddy ba don sam baya son girman kan yaron. Amsa gaisuwar Zakiyya ya yi tayi masa sannu da jiki tunda taji labarin rashin lafiyarsa a wurin masu aikin gidan.
"Amma dai bana jin dubani kika zo yi ko?" Ya tambayeta bayan ya zauna.
Abbati ya cigaba da tsayuwa a bayan kujera yana jiran jin amsarta. Maganar da Zakiyyan tayi masa maimakon amsa tambayar Munzali kusan kara tsorata shi tayi.
"Abbati ina kwana? Ya wajen Hanne?"
Bakinsa yana sarkewa ya ce "lafiya kalau"
Dan dukar da kai tayi saboda jin kunyar rashin hakurinta da zargin wani abu ta ce "dama naga har an koma makaranta ne baka dawo da Qibdiyya ba"
Nasa gaban ne ya fadi yanzu. Ya kalli Abbati a fakaice ya daure ya daidaita fuskarsa don kada ta gane da matsala. (Fyaden da yake tunanin Lilu ya yi mata)
"Saboda yanayin jikina Asabe ta dauketa..."
Daddy ya katse masa magana da sigar izgilanci yana tabe baki.
"Asaben ce za ta wani iya kula da ita?"
Duk wanda yake falon harda Zakiyya yaji rashin dacewar furucinsa da sigar da aka furta shi. Munzali yaji bacin rai sosai akan hakan. Ko hauka take baya jin ya dace dan kanwarta ya yi magana irin haka a kanta. Cikin fushi ya nunawa Daddy kofa yana fada.
"Malam get out! Idan bata ci darajar komai ba a wurinka ai taci ta zama silar mallakar motar da kake karade garin nan da ita. Bayan kuma ka san na saya ne don ka dinga kai min 'ya makaranta. Ko an fada maka ban san irin yawo da gangancin da kake da ita wanda ni ke biyan kudin gyara ba? Duk kuma a cikin alfarmar Asabe da tasa ni auren yayarka?"
Kafadarsa Abbati ya dafo "ya isa haka ba lafiya gareka ba"
"Don Allah kayi hakuri" cewar Zakiyya a tsorace da fadan nasa.
"Ya fita kawai za a kawota da weekend. Sai ki fadawa makarantar zata yi fashin sati daya."
Rashin kunya Daddy yaso yi musu sai dai dukkaninsu sun yi masa kwarjini. Yanayin jikinsu ma ba daya ba. Ya san uwa da ubansa zai ci la'ada waje idan ya kara magana. A hanyarsa ta fita ne dai ya yi magana da kunkuni ya ce,
"A jikin 'yarka zan fashe"
Kalaman sun sami nasarar shiga kunnuwan Abbati. Matsalolin gabansa basu hana shi juyayin maganar a zuciyarsa ba a hanyarsa ta kai su Innayo gida. Dukanta zai yi?
*
Bakin Uwani bushewa yayi har ta rasa yawun hadiya da Salihi ya ajiye motarsa a jikin katangar police station ya ce ta fito. Hannunta yana rawa ta murda hannun kofar ta fita ta fara bin bayansa. A daidai gate din da zasu shiga kafafunta suka yi mata nauyi saboda tsabar tsoro. Jiki a mace ta coje a wurin don ji take kamar ta kwasa da gudu. Muryarta ta fito kamar mai shirin kuka ta nuna kirjinta da rawar jiki.
"Karata kayi? To me nayi maka? In kana so na dawo gidanka ai ka san umarni kadai zaka bani ba sai ka hadani da hukuma ba."
Kiris ya rage ya kwashe da dariyar kalamai da yanayin fuskarta. Kuma don karfin hali so take ta nuna masa cewa bata ji komai ba.
"DPO ne yake son ganinki"
Habar mayafinta kamar yaji me aka ce ta sabule ta rasa yadda zata gyara shi tsabar firgici. Da kansa ya saita mata mayafin a kafada yadda zai zauna ya ce "muje"
Suna tafiya mayafin ya kara cirewa ta dube shi idanunta suna shirin zubar da kwalla.
"Da ka fada min inda zamu zo ai da na saka hijabi. Ko babu komai zan shiga da mutumcina" a fusace ta wurga gefen mayafin kafadarta tare da cewa "in zaka zauna ka zauna ko in cireka kowa ya huta"
"Ina ruwan mayafi za a huce a kansa"
Allah ne Ya taimake shi yana gaba da ita da tuni ta ga dariyar da yake dannewa. Maganar da ya yi ce ma ta kara kular da ita.
Yawancin 'yan sandan da suka tarar a wurin counter sun gaishe shi da girmamawa saboda DPO Yahaya ya fada musu cewa surikinsa ne tun zuwansa na farko. Uwani bata sami sukuni ba sai da suka shiga cikin ofishin DPO din taji yana gaisheta tare da kiran Salihi da yaya.
"Bari nasa a kawo shi" cewar DPO bayan sun gama gaisawar.
Ba a jima ba kuwa sai ga wani dan sanda ya taso keyar Habibu wanda alamu sun nuna anyi lugude da jikinsa. Yana ganinta ya sunkuyar da kai don ya sha gargadi akan ko hada ido ya sake yi da ita sai an masa fin dukan yanzu. Ita kuwa mamaki ne sosai ya kama ta.
DPO Yahaya ne ya yi magana domin warware mata me yake faruwa.
"Kin san wannan mutumin?"
"Eh" ta amsa da baki tare da gyada kai.
"Good. Kamar nawa ne kudinki da yake hannunsa?"
Tunda ta fahimci ba tuhumarta aka zo yi ba sai ta hau lissafi. Akwai kudin kujerar Hajji, kudin sallamar agent, kudin hotel din da za a kama mata a Makka da Madina (bata san cewa duk a cikin kudin da ta bayar ake cire na kujera dana masauki ba), kudin fili, kudin masu gini ma ta hannunsa suke bi, kudin sallamar dillalai....
Lissafi ya dinga tafiya a yayinda ta cigaba da fadin nawa ta bawa Habibu. Da aka tambaye shi bai musa ba.
"Sai kayi musu bayani game da komai kamar yadda kayi mana."
Kai ya dukar ba don kunya ba sai tsoron hukuma. Da farko babu batun dukansa a lissafinsu. Sai da ya yi kokarin sayesu da kudi domin a kashe maganar. Sannan ne suka nuna masa cewa akwai bambanci tsakanin 'yan sanda da muna 'ya'yan sanda.
"Kudin Hajji babu su gabadaya nayi amfani dasu, filin da kika yi gini kuma ku biyar na sayarwa wurin. Ban san waye ainihin mai wurin ba ma. Sannan..."
Gajiya tayi da jin bayanin nasa mai neman sanya mata hawan jini ta ce "ya isa! Ya isheni haka. Allah zai saka min."
Ta dubi DPO Yahaya ta dan rissina kai tayi masa godiya sannan ta tashi ko bangaren Salihi bata kalla ba. Da sauro ya tashi ya bi bayanta.
Daga kafa kawai take tana saukewa ba tare da sanin ina ta nufa ba. A zuci take kukan bakinciki. Tanadin da ta soma tun ranar da ta fara daukar albashi ya rugurguje. Darasin da ta kasa tsayuwa ta koya yau duniya ta fahimtar da ita a cikin 'yan tsirarun dakiku. 'Duk gudun mutum ba zai wuce kafafunsa ba'. Babu wani bawa da ya isa ya tsallake kaddararsa. Talauci da babu take gudu kuma gashi sun zo sun risketa. Kai ta girgiza ta gyarawa kanta da cewa taje ta riskesu dai. Aikin da take takama dashi bata san makomarta ba akan shi. Kudi kuwa yanzu da matukar wahala ta fito da dubu hamsin indai ba motarta za ta sayar ba. A karshe dai mutum biyun da take ta kokarin ta wuce a rayuwa su ne dai suka rage wadanda zata koma garesu. Uwa da Miji.
"Shigo mota mu tafi."
Gefenta ta kalla inda Salihi yake binta da mota ta kawar da kai. Ransa ya baci ya daga mata murya.
"Meye haka kike yi ne kamar wata mara tawakkali? Ki zo mu tafi nace."
Ba musu ta zagaya ta shiga. Suna tafiya tana goge hawayen da yake ta yi mata zarya a kumatu. Sai da ya saita motar yadda za ta iya shiga gida sannan ya yi mata magana. Muryarsa ba da karfi ta fito ba kamar dazu amma tana iya gane zancen nasa ba da wasa yake so ta dauke shi ba.
"Ke ba Innayo bace. Bana jin har abada za ki taba zama ita. Mutane masu irin zuciyar mahaifiyarki kalilan ne"
Daga kai tayi ta dube shi sai taji a karon farko bayan wasu shekaru wai tana jin nauyinsa. Salihi ya yi mata kwarjinin da ko zamanin samartaka bata jin ta taba jin haka a kansa. A dole ta mayar da kanta kasa ta cigaba da sauraron shi.
"Ni ba mahaifinki bane. Ban taba aibata miki uba a gabanki ko bayan ido ba amma na san halinsa gaba da baya. Ta yiwu bisa kuskure na taba yin wani abu da yasa kika ji kamar tarihin iyayenki zai maimaita kansa a naki gidan auren..."
"A'a" ita ce amsarta da sauri.
Dan murmushi ya yi ya nuna mata kofar gidansu.
"Ki je ki roki gafarar Innayo gwargwadon girman laifukanki. Idan kin tabbata ta yafe miki ki kirani zan zo na daukeki mu koma gida"
Kama kofar tayi za ta fita ta dawo ta kuma zama cikin rashin kuzari.
"Za ta yafe min kuwa?"
Dariya ta bashi ya ce "zan iya rantsewa ko yanzu ma ta yafe tun kafin ki roka. Ai ba ita bace abin ji ba, ni ne."
"Au, baka yafe min ba?"
"Kin rokeni ne?"
Fuskarsa a sake take. Hakan ne ya bata damar yin murmushi ita ma. Jikinta a sake kamar burodin da ya tsumu cikin ruwan shayi ta bude motar ta shiga gida.
***
Tunanin Abbati akan manufar kalaman Daddy ya katse a lokacin da Innayo ta soma labarta masa abin da ya sami Ayaah da suka isa gida. Rokonsa tayi da su sake yiwa Suhaib da iyayensa godiya. Ta sanar dashi cewa Munzali bai sani ba. Kuma taki fada masa ne saboda halin da suka riske shi a ciki a asibiti. Amma don Allah tana so kada Abbati ya manta wurin yi musu godiya. Hakan zai sa suji cewa lallai sun ji dadin abin da dansu ya yi musu. Ya soma mamakin inda suka san juna sai ta fada masa zuwansu duba Qibdiyya harda babarsu. Murmushi mai ciwo ya sami kansa da yi. Halin Mami da 'ya'yanta na karrama mutane abin yabawa ne. Zai so ace ya hada zuri'a da wadannan kamilallun mutane. Ina ma kaddara bata riga fata ba? Da ace shi ma mai tsafta ne kamarsu da zai yi duk abin da ya dace domin samun amincewarsu wurin bashi 'ya.
Yana ajiye su ya kira Shazali ya nemi ya bashi adireshin inda zasu hadu.
"Da azahar nace maka zamu hadu ba yanzu ba" yace da shi a gadarance.
"Allah Ya kaimu azahar din."
Danne zuciyarsa ya yi wurin bayar da waccan amsa. Baya son ya nuna tsantsar damuwa da tashin hankalinsa a zahiri. Abu ne mai sauki Shazali ya yi amfani da wannan damar ya wulakanta shi. Gashi bashi da juriyar wulakanci. Karshe idan abin ya kare da rikici sune zasu kwana a ciki tunda Qibdiyya tana hannunsa.
Maganganunsu da Innayo ya tuno yaji ya kamata ya kira kamar yadda ta bukata. Akalla ko godiya ne ya yi.
***
Cije lebe Mami Khadija tayi a yayinda ta gama sauraron bayanin Suhaib game da Danliti. Wayarsa da ya karbo ya mika mata bayan ya budo mata chats dinsa da Jiddo.
"Mami" ya ambaci sunanta a tausashe saboda yadda ya fuskanci abin data gani ya tabata.
Sakin fuska tayi ta kai hannu kan bandejin da aka nade masa kafa.
"Allah Ya baka lafiya Suhaib. I am proud of you. Ka tseratar da mutumcin wata kaima in sha Allahu babu mai taba mutumcinka dana 'yan uwanka ."
Kawar da zancen take son yi sai dai ko kadan bai yi niyyar barin maganar haka ba.
"Mami jiya kusan kwana nayi ina neman fatawar da ta tilasta miki zama da ...."
Bata bari ya gama magana ba ta dakatar dashi da hannu a lokaci guda tana mikewa.
"Zanyi abin da ya