Showing 171001 words to 174000 words out of 242549 words

Chapter 58 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3368

da sauri. Bata son lokacin break ya yi taje ta wahala wurin neman Ayaah cikin dalibai. Idan ta isa da wuri ajinsu kadai zata nema.

Ta gama shiri ta fito Honourable ya bata kudin adaidaita suka ji sallama. Direban Minister ne wato Abdulkarim. A soro suka hadu da Honourable Habu ya mika masa wani envelop.

"Oga ya ce jiya likitan Abbas ya turo masa. Gwaje gwaje ne da ake son ku sake kai shi ayi yau dinnan. Idan sakamakon ya fito zasu gane aikin da za ayi dole sai an bude kan ko kuwa irin wanda ake soka na'ura ne tayi. Ya ce kuje kai tsaye ya biya kudin."

Honourable Habu ya ma rasa irin na'u'im godiyar da zai yi. Shi kuwa direba fadi yake ai bai ga komai ba cikin dimbin alkhairin wannan bawan Allah.

Direban na fita Ummita ta fito. Riga da siket ne a jikinta na atampa. Ta yane kanta da mayafin pashmina wanda ya sha jiki ba laifi. Sai dai a wanke yake ya kuma sha guga.

Ta hango mota a farkon layinsu ikayar inda mota ke tsayuwa amma bata yi mata kallo biyu ba ma. Kanta a kasa tana tafe hankalinta yana kan cimma titi da wuri ta sami abin hawa. Bayanta gefenta taji ana horn sai ta kara rabewa kusa da kwatar dake gefe, a zatonta ko ta tsaya akan hanyar motar ne. Sake horn aka yi ta kuma matsawa. Da aka yi na uku sai ta juya baya cike da tsiwa. Direban na bude kofa ta ce,

"Malam ko kwatar kake so na fada ne sannan ka sami hanyar wucewa?"

Ganin dan dattijon da ta gaisar dazu tare da mahaifinta sai kunya ta kama ta. Kasa tayi ta rissina mayafinta ya rufe mata gefen fuska ta sake gaishe shi tare da bashi hakuri. Murmushi ya yi don ko da ya dameta da horn din sai da Maigidansa ya ce kada ya firgita 'yar mutane.

"Shigo a rage miki hanya"

Girgiza kai tayi da sauri "Baba zai yi fada. Na gode"

Abdulkarim yaji abin da tace sai yaji ta burge shi. Idan bai yi kuskure ba ita ce Ummi babbar diyar Honourable. Bude bayan ya yi ya fito da kafarsa daya ya tsaya.

"Zo muje a fara sauke ki ina sauri ne."

Yawu ta hadiya da kyar da taga mai maganar. Sake yin kasa tayi zata gaishe shi ya ce,

"Shigo motar sai mu gaisa"

Ummita ta daburce "Allah Baba da Anti Hasiya sun hana"

Abdulkarim sai ya dauki waya ya kira Honourable Habu. Yana tsaye bai mayar da jikinsa ciki ba har wayar ta shiga. Gaisawa suka yi sannan ya kada baki ya ce,
"Tare muke da Mal. Amadu amma sai nace kada ya fada muka ina mota saboda bana son ka fito da safe haka. To yanzu mun hadu da Ummi nace ta shigo mu kaita inda zata je amma taki. A takaice dai neman izini na kira"

Honourable ya dan ji nauyi domin harga Allah baya son take dokarsa. Sai dai kuma yana kyautata zato ga Ministan. Ba wai kuma don sakar masa bakin aljihu da yayi yanzu ba.
Tuntuni bai taba saninsa da mugun hali ba. Duk da dadewarsu basu hadu ba, baya jin zai kira shi domin neman izinin cutar masa da 'ya.

Dariya ya yi ya ce "Tana karkashin ikonka babu ruwana."

Kallonta Abdulkarim ya yi tana kallon kasa ya ce "to sai ki bar kirgen kasar kizo mu tafi ya bayar da izini"

Ummita ta dan tsuke baki tana mamakin salon yadda ya yi mata magana kamar yaji haushin kin shigarta.

Daya barin ta zagaya zata shiga amma ga mamakinta sai taga kofar baya a bude. Direban ta kalla galala tana ware idanuwanta ta dan rage murya ta nuna kofar a tsorace.

"Wai nima bayan zan shiga?"

"Baki yarda da azkar dinki na safe ba kenan, ko baki yi bane kike wannan tsoro?"

Mamakin wannan Minista yana neman zauta ta. Shi da yake abokin babanta ya akayi yake yi mata magana kamar ta yiwa tsaranta laifi? Kuma ma da wane kunnen yaji abin da ta fada a hankali.

Dan murguden bakin da tayi duk akan idon Abdulkarim din. Dariyarsa ya gimtse don kuwa da gayya yake yi mata magana a haka. Baya son ta shigo a darare kamar tana tare da uba. Bashi da masaniyar ko anyi mata miji amma haka nan yake jin wani kwarin gwiwar tunkararta. Idan da mijin a hannu sai ya hakura. Bai san lokacin da dariya dai ta subuce masa bane a yayin da ya hangota ta kai hannu baki tayi tofi. Ba kunya tabi jikinta ta shafe ta kuma tofawa motar sannan ta shiga da kafar dama gami da Bisimilla da dan karfi. Har ta shiga yana dariya.

Mal. Amadu ma sai da ya dara. Ta zauna a dofane tana kallonsu. Dariyar masu kudi ma daban take, babu sauti mai karfi ko hargagi ta ayyana a ranta. Tambayar da ya yi mata ce ta maidota hankalinta

"Wai me da me kika karanta kika tofa mana ne?"

"Su Au'zu bi kalimatillahi...." Sai tayi azamar dora hannunta akan labbanta "ba daku nake ba. Tunawa nayi ban yi ba kafin na fito"

Hannu ya mika mata yana murmushi "to sai ki bani abin sadaka ladan yi miki tuni ko. Don da farko na zata mu kike tofewa don kada mu gudu dake."

Mayafi ta janyo abin da ya lura ko dabi'arta ne ta rufe rabin fuska tana dan murmushi.

"Wai ya sunanki ne?" Ya tambayeta saboda yana son sake jin muryarta.

"Ummita"

"Ummi-ta? Tawa kenan ko ta mutane da yawa?"

Hanjin cikinta taji ya yi wani juyin waina a tanda ta manta da kunya ta kalle shi cikin ido. Ba shiri ta sauke nata ta dukar da kai kamar mai shirin kwanciya akan cinyarta. Basu sake magana ba sai kwatancen da take yi har suka isa makarantar. Ga mamakinta dana Mal. Amadu sai suka ji Abdulkarim yace a jirata.

Ta kusa minti ashirin a cikin makarantar kafin ta fito a guje tayi bakin titi. Shaf ta manta da wanda ya kawota kuma yake jiranta. Hannu bibbiyu tasa tana tsayar da adaidaita sahu. Abdulkarim na ganin yanayinta harda hawaye kwance a fuskarta ya fito da sauri.

"Ummita"

Ganinsa yasa kukan nata ya karu. Ta dawo da baya suka hadu domin shi din ma nufota ya yi. Kafin ma ya tambayeta ta fada masa abin da ke faruwa.

"Ba a ga Ayaah ba. Wai ta kusa awa biyu da fita fitsari har yanzu bata dawo ba. Kuma ga jakarta a ajin. Anje duka bandakunan da lab da ko ina bata nan" shirun sakan biyar tayi wani tunani yazo mata "ko dai aljanun bandakin sun dauketa?"

"Bama mutane ba aljanu Ummita?" Abdulkarim ya tambayeta yana kada kai don kada ta saka shi dariya a halin da ake ciki "Muje bandakin mu duba. Allah Yasa dai kin iya rukiyya sai na tsaya daga bayanki ko?"

Duk da tashin hankalin da suke ciki bai hanata fassara shi a ranta ba. 'Mutumin nan ba dai bakar magana ba'. Ita da kanta kuma ta hango wautarta ta ce,

"Ko masu satar mutane" ta dan tafa hannu irin na ta canka daidai "ai fa an ga kana zuwa gidanmu shi kenan za a fara kawo mana hari."

Abdulkarim bai ma san lokacin da ya ya balla mata harara ba.

"Ji mun yarinya. Ni kuma zaki dorawa laifin?"

"To ai ..."

Kai ya girgiza kawai ya ce ta zo su koma cikin makarantar. Suna tafe zuwa ofishin Principal ta daga waya zata kira gida ya hanata. Idan sun san aihinin me yake faruwa sai su fada. A haka hankula ne zasu tashi babu sanin madafa.

A ofishin Principal din banda ita akwai malamai biyar ana ta mayar da zance. Kowa ya shiga rudani har wasu suna cewa a tashi yaran kowa ya tafi kada a hada dasu. Yana shiga mutum uku suka gane ko waye. Da radar da bata buya ba suka sanar da ragowar. Nan da nan kuwa aka dinga raba idanu tsakaninsa da Ummita wadda ke biye dashi sau da kafa. Kallon ne ya tunzura shi kafin ma ya tambayi ya ake ciki ya fara da bayanin da ya baiwa Ummita dasu kansu mamaki.

"Wannan 'yar tsohon Ubangidana ce. Mun dade da rabuwa sai kwanakin nan Allah Ya sake hadamu. Yanzu ma daga gidansa nake kuma da izininsa muka taho nan."

Principal sai ta hau borin kunya "ranka ya dade me ya kawo wannan bayanin?"

Ya dage kafadu sannan ya ce "zuciya abar banza ce wani zubin. Yanzun nan sai ta shiga yiwa mutum sake sake ta sanya shi zargi a gurbin da bai dace ba."

Kowa kuma sai ya shiga gyara tsayuwa ana gyaran murya. Bai kulasu ba ya tambayi ba'asin sanda aka farga da batan Ayaah.

Bayanin da aka yiwa Ummita aka sake yi masa. Ya gyara zama tamkar a ofishinsa ya nuna wani Malami.

"Kirawo min Maigadinku"

"Su uku ne"

"Duka su biyoka sai ku saka wasu malamai a wurin saboda kada yaran su fice"

Masu gadi duk sun tsumu kowa ya rantse bai ga fitar wani bako ba ko na dalibar da ake magana a kai. Guda cikinsu yafi kowa dagewa aka rantsuwarsa. Gashi a shekaru alamu sun nuna ya girmi wadancan sosai. Yadda ya gabatar da kansa ya sanya Abdulkarim dora masa ayar tambaya. Dalilinsa kenan ma na daga waya yace zai kira Kwamishinan 'yan sanda domin a zo ayi bincike.

Hakuri aka soma bashi ya rufe ido yana fada akan sakacinsu da amanar 'ya'yan mutane.

"Idan sun zo zasu tafi da masu gadin a kullesu na a kalla sati koda an ganta kuwa. Wannan ai sakaci ne da rashin sanin aiki."

Dan dattijon maigadin yana jin haka ya soma muzurai. Rashin fara'a da ya gani ko digo a fuskar bakon nasu ta tsorata shi. Haka kawai da iyalinsa azo a kulle shi yana zaman zaman sa. Hularsa ya cire ya dan firfita fuskarsa wadda ta soma tsatatsafo da gumi sannan ya rankwafo a gaban Minista.

"Yallabai ai ba ayi haka ba. Yarinya dai babu wanda ya saceta. Duba min nan..." Ya zaro wata kodaddiyar naira dari biyu "ka gani wani matsiyacin Alhaji ne yazo da katuwar mota ya dauketa. Wannan abar ya iya bani don na barta ta tafi da alkawarin zata dawo kafin a tashi."

Dan ofishin Principal a take ya karade da sallallamin malamai mata da fadan malamai maza. Dattijo kamar a cinye shi danye. Principal ta ce barin aikinsa yazo domin bata san tun yaushe ake haka ba.

"Wallahi Hajiya yanzu ma tsautsayi ne. Wata yayi nisa nayi haka ne da tunanin zan dan samu na cefane. Ni yarinyar ko wayewa da fuskarta ma banyi ba sosai."

Ummita dai sai kuka kawai take yayinda Abdulkarim ya ce ba zai tafi ba har sai 'yan sanda sun zo.

***

Goshi Suhaib ya dinga murzawa ya rasa wane irin tunane ya kamata yayi. Ta ina zai fara nemanta? Baya son Munzali duk da ya san 'yar yayarsa ce amma yana gudun halin da zasu shiga kafin a ganta.

"Idan ta bishi kanta ta yiwa" ya furta a zafafe. Sai dai kuma can kasan zuciyarsa ya san cewa ba zai taba iya kawar da kai ba. Haka kawai yana zamansa yarinyar tayi masa karan tsaye a rayuwa. Banda mahaifiyarsa da kanne babu wata mace da ya taba damuwa da shirginta sai wannan yarinyar mai idanu a tsaye.

Mota ya shiga ya zauna ya bar abokan aikin Danliti da mayar da zance. Kusan minti goma ya yi kansa na kan sitiyari yana tunanin mafita kafin dabara tazo masa. Waya ya dauka ya kira nambar Ayaah yana ta addu'ar ta dauka.

***

Kokarin danne tsoro Ayaah take yi amma ya bayyana karara. Ta fara nadamar biyo shi tun kafin su bar layin makarantarsu amma ta rasa bakin cewa ya tsaya ta sauka. Banda ragon azanci ta yaya ma zata je gaishe da suruka da kayan makaranta? Idan matar mai hankali ce tana ganinta karshenta tayi mata fada.

"Wai ina zamu je ne naga muna yin bayan gari."

"Walalamb'e" Danliti ya bata amsa kai tsaye.

"Walame?" Ayaah ta tambaye shi da sauri don tana jin kamar bata ji me yace bane da kyau.

Danliti ya sake maimaitawa wannan karon harda dariyarsa.
"Kada ki damu Baby. Yanzu zaki gani da idanunki."

Tun daga Hotoro ta daina gane ina suke tafiya. Ta dai ga wani roundabout daga nan suka yi hagu gefen wani gidan mai. Jikinta ya yi sanyi kalau kamar mara lafiya. Gashi yau gabadaya tsoronsa ma take ji. Suna zuwa kofar gidan zata gudu kawai. Don kada ya gane ta kakalo murmushin dole. Ana haka 'yar wayarta ta soma vibrating. Bata san nambar ba amma da sauri ta dauka. Don ta san yanzu da wuya idan ba a fara nemanta ba.

Danliti bai damu da wayar da zata amsa ba saboda ya gama yanke hukuncin cewa ko me zai faru yau sai ya kusanceta. Ikon a hannunsa yake kamar yadda ya fadawa kansa.

Da sallama ta dauki wayar, muryarta tana dan rawa.

Suhaib yana jin yanayinta wani abu ya taso masa a kokon rai.

"Ayaah kina tare da Danliti? Zaki iya magana sosai?"

"Eh amma ba zan iya ba" ta amsa masa tana kokarin kin kallon inda Danliti yake.

"Kin gane ni ko?"

"Eh"

"Good, ki saurareni da kyau kuma kada kiyi abin da zai gano ki. Mutumin da ya daukeki wallahi makanike ne yanzu ma ina garejinsu. Mutumin banza ne. Ya fadawa abokin aikinsa zai zo daukarki ya kaiki inda zai..." Sai ya kasa karasawa.

Ayaah ta sake tsorata sosai jikinta ya soma rawa. Yawu ta hadiya da kyar a hankali ta ce "ba na fada miki mumminsa zai kaini na gaisar ba? Yanzu muna hanyar gidansu ne. Kar ki bari a gane bana aji kinji"

Ba karamin burgeshi yaji tayi ba. Ga tsoron yana iya rarrabewa cikin zancenta amma a haka ta fada masa abin da ya dace ya sani.

"Na fahimta. Ki kokarta ki turo min address din inda kuke ta sms saboda kada ya gane."

"In sha Allahu. Ni dai ki dauko min jakata ki jirani a bakin gate ko an tashi."

Danliti ya dan kalleta ya murmusa yana kiran "Baby na kenan! Ki gama wayar nan ki fada min kalaman da zasu sanyaya min rai"

"Kiji min dan iska..."

Saboda yanayin da take ciki murmushi kadai ta iya yi amma duk da haka Suhaib yaji sautinsa. Shi kuwa gogan ya zata dashi take.

"Dariya ma na baki?" Suhaib ya ce yana shan kunu

"A'a. Don Allah ni dai kiyi sauri. Zan turo miki nambar registration din tawa ki cike min form din."

Kafin ya ajiye wayar ya sami kansa da cewa "Ki kula da mutumcinki Ayaah. Kada ki yarda ya taba min jikinki."

Shi da ya fada ya yi mamakin karfin halinsa sai dai kuma yanzu ba lokacin hakan bane. Haduwar kwana daya ce amma zuciyarsa taki bashi hadin kan yakiceta daga tunaninsa.

Ita ma a nata bangaren wani irin nauyi kalamansa suka yi mata. Haka nan ta cije ta sake yanko karya ta fadawa Danliti bayan ta kashe wayar.
"Wai nambarmu ta NECO ake bukata daga ofishin Principal. Shi ne kawata ta kira don kada a neme ni."

Mutumin da ko sakandiren bai gama ba sam bai fahimci karyar ba. Hankalinsa bai bashi yasa ido akan abin da take rubutawa ba. Iya abin da ta gane a hanyar da suka bi da sunan unguwar da ya fada wanda bata ma rike daidai ba ta rubuta.

Suhaib ya koma wurin sauran makaniken ya karanta musu text dinta.

"Da mamaki dai amma wannan kwatancen ya dace da hanyar gidansa. A can unguwar Walalamb'e yake da zama"

"Muje ka nuna min"

Mutum uku ne suka shiga motar. Harda shugabansu cikon na hudu. Rayukansu duka sun baci akan abin da yake yi. Ga daukar abin hawan masu kawo gyara sannan kuma ya dauki mace yana shirin bata mata rayuwa.

*
Bangaren inda suka nufa wawakeken filin unguwa ne da gidaje tsilli-tsilli basu matse juna ba. Gidajen wurin kaf babu bene ma a iya ganinta. Duk sunfi kama da gidajen gargajiya. A takaice dai unguwa ce ta masu karamin karfi sosai. Cikin Ayaah ya sake kullewa da mugun tsoro a lokacin da faka motar a kofar wani dan tsakon gida.

"Ina ne nan?" Ta dan dake ta tambaye shi.

"Gidan mai ban ruwan fulawa a gidan Mummy. Kiyi hakuri zan shiga in duba shi ne yanzu na fito"

Tunda dai bai kirata ba sai taji dama dama a ranta. Fita ya yi ya rufeta a cikin motar ya shige gidansa da sauri. Mukullin dakin Rabilu abokinsa da ya bashi aro tun jiya ya manta a aljihu yazo dauka. Sun yi da Rabilun can dakinsa dake kusa da unguwarsu Ayaah zai kaita. Kuma idan shi Danliti ya gama biyan bukatarsa da ita shi ma mai dakin zai yi.

Kafin ya fito ta sake turawa Suhaib wani sakon.

(Ya kulleni a mota wai wani wurin zamu je ba inda na turo maka ba. Don Allah kayi sauri wallahi tsoro nake ji.)

(Ki kula da duk inda kuke bi ki sake turo min. Please take care of yourself.)

Amsar ta karanta ta gyada kai kamar yana kallonta.

A ciki kuma matar Danliti da murna ta tashi tana yi masa maraba ya doka wani uban tsaki da ya saka ta ja da baya. Naira dari biyu irin wadda ya bawa maigadin makarantarsu Ayaah ya jefa mata a wulakance.

"Gashi nan na san abin da kike yiwa kenan. Ke dai a baki kudi ku ci abinci da 'ya'yanki."

Hawaye taji ya taho mata tayi saurin tarewa da hannunta. Kudin ta duka ta dauka ta ce,

"An gode. Allah amfana"

Tsaki ya sake yi mata ya shige daki yana neman wandon da ya cire jiya. Ita kuma mayafinta ta zara a kan igiya. Ta goya karamar ta rike hannun mai wayon ta fice tana ce masa zata karbo kayan miya.

"Na ajiye mota a waje ta mutane. Kada ki kuskura kije kusa da ita. Ke dawo idan na tafi sai ki fita."

Sarai ta ji abin da yace amma tayi biris ta fita soro ta leka. Abin da tayi tsammani ta samu. Yarinya ce mai fuskar kamala a cikin motar. Takaicin halinsa ya turnuketa. Babu wani bakon abu a halayyarsa da bata sani ba. Bakon abin da shi bai sani ba tare da ita shi ne a yau ta gama hadiyar bakincikinsa in Allah Ya so. Komawa tayi cikin gidan suka yi kicibis a bakin kofa. Rai a bala'in bace ya dinga yi mata masifa.

"Me yasa kika fita? Da kika fitan me yasa kika dawo?"

Hakuri tayi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login