Showing 153001 words to 156000 words out of 242549 words
illar da ya janyo min."
Mal. Sa'idu ya yi dariya
"Magana kike son yi akan zuwa almajiranci ko? Ke a dole ba za ki karbi addini a yadda ya zo miki ba?"
"A yadda yazo muku dai. Wannan fitinar da kuka farlanta bata cikin shika shikan musulunci. A takaice ma dai baku yiwa addinin komai ba sai bacin suna."
"Mari wai sai yaushe zaki daina janyowa kanki matsala da Yaya Sa'idu?" Cewar Mal Inuwa cikin fushi.
"Kila yau! Yau din da nake so kai dashi ku san cewa kun dade ana rubuta muku zunubi a matsayin wadanda suka jagoranci aikin alfashar da dansu yake yi saboda mummunar akida."
Falon sai ya yi tsit. Baka jin komai sai hawa da saukar numfashi. Kan Abbati a kasa yayinda Mal. Sa'idu yaji lokaci ya yi da zai saurari Mari. Kalamanta ba karamin zargi bane wanda yake jin dole sai da hujja za ta yi shi.
"Addinin Musulunci da kalmar Karatu ya fara zuwa garemu. Wannan yake nuni da cewa ko kadan jahilci bashi da muhalli a cikinsa. Allah ma Ya ce mu san Shi kafin mu bauta Masa. Duk musulmin kwarai bai dace ya yi gaba da neman ilimi ba."
Mal. Inuwa ya ce "to amma ai ke kina yi."
"A fahimtarku ba" ta nuna Abbati da yatsanta "ga danku nan. Kamar kowane bawa shi ma da tasa kaddarar yazo duniya amma kune sila. 'Ya'yanmu amana ne. Babu inda aka ce mu sakesu da kananun shekaru neman karatu ba tare da kyakkyawar kulawa ba. Kun turasu gidan malamai da sunan neman ilimi amma babu abinci. Yunwa ba kanwar uwar kowa bace. Idan ta taso dole a kawar da ita ko a ji jiki. Babba ma idan ka kai shi karatu babu abinci ka hada shi da jidali balle yaro. Wani sai ya wuni yana barar bai samu ba. Mutane su ci karo dasu wasu su zagesu wasu su tsine musu tare da mu iyayensu saboda sun dame su da bara. Ba dole su nemi abinci ta hanyar da ta fi musu sauki ba? Wasu su dace da halal, da yawa su fadawa haram. Hatta masu kwacewa na kasa dasu kana ganin laifinsu? Sun yi girma da bara kuma da gaske babu abincin. Sannan sun tafi babu tunanin ranakun da zasu tashi ba lafiya. Waye zai kula dasu idan suna ciwo? Wa zai basu magani? Ko kun manta ranar da na shigo garin nan da gawar Sani ba tare da na san ya rasu ba?" Sai ta fashe da kuka. A haka ta cigaba da cewa "Uwa uba baku ajiyesu a inda za a basu tarbiyya ba. Iyakarsu da malamansu a biya musu karatu su bayar da hadda. Idan sun yi laifi a zane su. To amma tarbiyyar fa? Sai abin da suka tsinta a titi? Da yawansu basu tashi sun ga jinkai da tausayi ba. Dan shekara shida yana yawo a unguwa neman abinci a lokacin muku-mukun sanyi ko damuna. Wani idan ka ganshi saboda rashin kulawa da zama cikin hazo sai dai ka dinga ja masa Innahu min Sulaimanu. Wallahi zato zaka yi aljani ne. A makarantar babu mai tausaya musu sai kalilan idan anyi sa'a. Mu da muka haifesu mun riga mun bata rawarmu da tsalle da muka rabu dasu da kuruciya. A karshe zukatansu su bushe. Idan anyi dace yaro ya zama nagari, idan ba a dace ba ya buwayi al'umma."
"Yanzu ki ka ce kowa da kaddararsa. Ni tun tasowata banda Sani da jikan Mai-adua ban taba jin labarin yaron da yaje karatu ya rasu ba. Gidan nan yara nawa muka tura kuma gasu nan duk sun dawo kamar ba ayi ba?"
Mal. Sa'idu kenan. Ya fadi haka ne ba don zuciyarsa bata soms zuwa inda Baaba Mari take son kai shi ba. Ba dai ya son ya karbi gyaran ne daga gareta.
"Ashe baka ji lokacin da nace kowane bawa da kaddararsa yake zuwa ba? Amma akwai sila. Kuma dole ne silar ya karbi sakamakon abin da ya zama tushen faruwarsa mai kyau ko akasinsa."
"Kai Abbati. Wace irin sana'a kake yi? Sata ko fashi?" Cewar Mal. Sa'idu muryarsa ta soma sauyawa daga dakiyar da yayi da farko.
Abbati bai iya amsawa ba. Ba zai iya cewa ga takamaimai abin da yake cikin zuciyarsa ba.
"Ba da kai nake ba!" Ya daka masa tsawar da zata firgita mai karamin tunani "nace wace irin sana'a kake yi?"
Baaba Mari ta daga masa hannu duk da kwarin jikinta yana ta raguwa.
Tsawar da ya yi ta bata rai itama ta koma yi masa magana tana daga murya.
"Baka da hurumin yiwa dana tsawa Yaya Sa'idu. Wannan damar ta saraya a wuyanka. Abin da ya rage tsakaninmu bai wuce ALLAH YA ISA ba. Ni da d'ana bamu yafe mak...."
"Mari!" Mal. Inuwa ya kirata da karfi.
"Kaima da ka kasa tsayawa 'ya'yanka ka tanadi amsar fitar da kai ranar lahira."
Dakin ya yi shiru na wani lokaci. Iyayen maza biyu mamakin kalamanta ya ishe su. Baaba Mari kuma ciwo ke neman dawowa sabo. Abbati ya matsa kusa da ita da sauri. Filo ya kara mata a bayanta domin ta zauna da kyau.
Mal. Sa'idu ya rasa me zai ce ya kare kansa sai "Yanzu ke da ace barinki aka yi da yaran nan za ki iya kula dasu ba tare da uba ba? Uwa ai ba ita kadai ce madogarar 'ya'yanta ba. Sannan karatun nan da kike ta suka ba shi ne yake taimaka musu wurin iya rike kawunansu a duk inda suka sami kansu ba saboda sun horu?" maganar ma a hankali ta fito.
"Rike kai..." Baaba Mari ta furta da murmushin da tun dazu take yawan yi domin ragewa Abbati damuwa "Allah bai halicci kananan yara domin su rike kawunansu ba. Da haka ne kuwa to kowannemmu zai fado daga sama idan lokacin haihuwarsa ya yi. Yaya, cikin daukar ciki da haihuwa akwai mabanbatan wuya irin wadda bakunan mata kadai ke iya labartasu. Wannan azabar mai kama da mutuwa bata taba hana uwa mai cikakken hankali son 'ya'yanta ba. Ashe baka san.." ta dubi idanun Mal. Sa'idu babu tsoro ko shayi "soyayyar uwa da 'ya'ya aya ce cikin ayoyin Ubangijinmu ba? Cikinsu ya hanamu lafiya, haihuwarsu ta gadar mana da ciwo da sauyin halitta, tarbiyarsu ta janyo mana zagi da aibatawa komai kokarinmu amma duk da haka bamu fasa son kayanmu ba. Me yasa karatu yazo mana da cewa Allah Yana kunyar wadanda bai bawa haihuwa ba? Kuma Ya umarcemu da kyautatawa marayu domin samun lada. Lallai Ubangijin da Ya samar da wannan ladan ba zai so a tauyewa uwa zamewa 'ya'yanta uwa ba. Munfi kowa son cigaban 'ya'yanmu. Idan suka zama manyan malamai sai nafi kowa cikinku farinciki. Amma zama malamin ko wani kwararre a fannin da Allah Ya dorasu yana tafe da kulawarmu. 'Ya'yanmu suna bukatarmu kafin su shiga duniya su iya rike kawunansu. Baka bani damar kulawa dasu a lokacin da suka fi bukata ta ba. Yaya Sa'idu jawabina da yawa. Gashi na gaji bana jindadi. Kuje kai da dan uwanka na barku da ...."
Caraf Mal. Inuwa ya hanata karasa magana "haba Mari karki karasa mana. Ni duk zancen ma baki fada mana me yake yi ba."
Ta kalli fuskar Abbati sai kawai ta tashi ta barsu a wurin ta shige dakinta. Shi da ta bari taji nauyin karasa labarin da kansa ya zayyane musu komai. Mahaifinsa ya dinga kukan da ko ranar da iyayensa suka bar duniya bai yi irinsa ba. Daga cikin dakin Baaba Mari tana jinsa ita ma kukan take yi. Hawaye wani yana min wani babu kakkautawa. Mal Sa'idu ne ma bata ji koda tarinsa ba sai daga baya taji alamun faduwa da kuma kiransa da karfi da Abbati da Mal. Inuwa suka yi.
***
Honourable ya kai ya kawo a dakin asibiti ya kasa zaune ya kasa tsaye har likitan da ya sake shiga ya fito.
"Baku yi min bayani ba sai shiga kuke kuna fita. Me ya sameta?"
"Alhaji muje ofis muyi magana."
'Yan matan aka bari a kanta yabi bayan likitan. Ana cewa ya zauna bai ji ba don hankalinsa baya tare dashi.
"Yallabai matarka ciki gareta na wata uku."
Cikin wani gigitaccen farinciki Honourable ya ce
"Allah Hakimu, Hasiya ke da ciki? Alhamdulillah. Allah Ka karawa Annabi SAW daraja."
"Amin" cewar Likitan "sai dai akwai 'yar matsala."
Nan da nan Honourable ya zauna hannuwansa akan teburin likitan. Murna tana neman komawa ciki.
"Zubewa ya yi?"
Gamsashen bayani likitan ya yi masa akan halin da take ciki. Mahaifarta bata da kwari ne tana barazanar zubar da cikin. Idan ba a daure mahaifar ba zai iya zubewa. Sannan tana bukatar bed rest na wani lokaci. Kuma ta daina komai har ya yi kwari a gani.
Honourable ya ce musu ya amince ayi duk abin da ya dace. Yana fitowa masallacin asibitin ya nufa ya yi sallah raka'a biyu domin godiya ga Allah. Hasiya ke rike da gidansa da sanaarta. Da ace wata biyu da suka wuce ta sami cikin nan mai matsala bai san yadda zai yi ba. Yana neman kudi sosai amma kamar kofofin samun sun toshe masa. Yanzu gashi tayi cikin a lokacin da yake da abin kula da ita. Minista Abdulkarim ya bashi kudi a hannu banda wanda ya zuba a account din asibitin da aka kai Abbas.
"Allah Ka kara mana hakuri da kaddara kowace iri."
Daga nan bai koma cikin asibitin ba. Adaidaita sahu ya tare ya ce a kai shi Dala. Sai dai akira shi duk abin da aka ga dama amma da bakinsa zai yiwa Innayo wannan albishir. Ita ce mutum ta farko da ya san Hasiya za ta so gani idan ta tashi. Kuma bai ga wanda zai yi masa tattali da jinyarta kamar mahaifiyarta ba.
***
Kankanin daki ne kamar akurkin kaji, ba taga ko daya sai kofar shigowa. Babu komai a cikinsa sai tarkacen gyaran mota irinsu spanner, sukun direba da matattun tayoyi. Iskar dakin kuwa warin fetur take da bak'in mai. Daga bayan inda aka jere wasu tayoyi suka yi tsini muryoyi ke tashi a hankali. Daya tana magiya dayar kuma tana bayar da hadin kai. Cikin sassarfa Suhaib ya shigo dakin ya isa bayan tayoyin ya leka. Mummunan gamun da ya yi bai sa shi ja da baya ba sai ma cakumo wuyan rigar namijin da ya yi.
Dani ne sanye da kayan makanikai ya yi duqun-duqun. Suturarsa da fatar jikinsa duka suna neman agajin wanka da wanki. A tare dashi kuwa ba kowa bace illa Ayaah. Fuskarta babu kwalliya amma tayi kyau. Hijabin jikinta kuwa dama shi Dani ya kamo saura kadan ya gama cire mata shi. Ya gama hillatarta da alkawarin aure idan ta yarda ta bashi hadin kai kamar yadda Suhaib yaji.
Kunnenta Suhaib ya murde iya karfinsa yana yi mata fada cikin bacin rai.
"Ban yi miki magana ba dazu?"
Ayaah ta turo baki "wai kai ina ruwanka? Kuma ba ya ce zai aureni idan Mummy ta dawo."
"Mooooommiiii"
Yaji an ce daga gefensa. Kunnen Ayaah ya saki ya juya. Yarinyar nan mai kwalliyar aljanu cousin din Abbati ya gani. Bata fasa kiran Mooomiii ba. Lilu a kusa da ita ya dinga dariya yana kiranta Iya duba duba.
*
A zabure Suhaib ya tashi daga bacci yana salati. Kansa ya yi wani irin nauyi kamar an dora masa dutse. Baccin dauke shi ya yi bai sani ba. Fuskar Ayaah ce ta zauna masa daram a kansa lokacin da ya gansu Dani zai cire mata hijabi. Murmushi take yi kamar abin da suke niyar yi daidai ne.
"You have the guts to smile (har kina da damar yin murmushi)" ya furta tare da yin kwafa ya yi wurgi da filo.
Sake kwanciya ya yi niyar yi wani tunanin ya fado masa. What if yarinyar nan ta bi mutumin yaje ya bata mata rayuwa? Daga hirarsu ta dazu ya fahimci kamar yanzu ne yake neman amincewarta.
"Wannan kanta baya ja da gani"
Tsaki ya yi ya tashi a gurguje ya zura takalmi ya fita zuwa cikin gidan. Yawancin 'yan biki sun watse tunda yau aka tafi da amarya Kaduna. Yana shiga suka yi kicibus da Mardiyya.
"Bani wayarki."
"Wallahi Ya Suhaib babu komai a ciki mara kyau."
Murmushi ya mata duk hankalinsa yana kan wayar.
"Karki damu Auta na yarda dake."
Wayar ta bashi ya laluba contact dinta. Da yazo kan numbar Ayaah da sunanta da ya zauna masa daram a ka ya ganeta. Yana wurin suka karbi nambar juna. Kallo biyu ya yiwa numbar ya haddaceta. Mardiyya tana jiran taga me zai yi sai gani tayi ya miko mata wayar.
Dakin da suka yi masauki ya koma ya samu wuri ya zauna a gefen gado. Yana danna kira ta shiga. Sai yaji wani bakon yanayi ja sarkewar harshe ya ziyarce shi. Me zai ce mata matsayin dalilin kiran?
I just published "33" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1095386077?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=wsvg1y6wjXkjc%2BsoHY%2FGAgyROXyp%2BY%2F6LAbeHHjA%2Biw0477%2B48VGV%2F8yOfEUfjTePvzgNLOgDlVDMm3xWUvdH978a2xKHrFdotfVZAjOUHbes%2FelWEJ2MliWyG77rSUB
UWA UWACE...33
Batul Mamman💖
Kunyarku nake ji wallah. Haka dai zaku dinga hakuri dani saboda Son So dake tsakaninmu. Allah Ya barmu tare har aljanna. Amin
***
"Ranka ya dade kana da bako."
DPO Yahaya ya dago kai cikin bacin rai ya kalli Sergent din da ya yi maganar a tsorace.
"Me na ce muku dazu?"
"Duk wanda yazo ace ka dan fita" ya ce sannan ya gyara tsayuwa rabin jikinsa a bayan kofa "Yallabai mun nemi ya sanar damu matsalar da ta kawo shi ya kafe lallai kai yake son gani."
Girgiza kai ya yi ya fasa yin fadan da da ya yi niyya. Yau din kamar hadin baki tun sassafe ake abu daya. Daga wannan case din sai wancan. Wani abin ma sai kayi tunanin al'ummar tamu ta rasa alkibla. Cuta, ha'inci, mugunta, magudi da uwa uba zina. Kansa ya dauki caji yana ta ciwo. Shi yasa ya bayar da umarnin ace baya nan domin ya huta. Tunda an riga an fada masa bashi da zabin da ya wuce sauraron mutumin.
Sallamar kadai yaji ya gane surukinsa, babban wa ga matarsa. Ba shiri ya mike domin nuna girmamawa a gareshi. Mutumin akwai mutumci da halin girma.
Ilai kuwa da shigowarsa kalmar hakuri ya fara amfani da ita "ayi min hakuri Yahaya. Na san aikinku babu hutu."
"Haba Yaya Salihi ai sai kasa naji babu dadi" ya amsa masa a yayinda suke musabaha.
Bayan 'yan gaishe gaishe Salihi ya zayyane masa duk abin da ya sani game da Habibu na ma'aikatar lafiya. DPO Yahaya ya dinga gyada kai har ya gama.
"Akwai wani mugun dan ta kife mai cin kudaden mutane a cikin ministry of health. Ka san ai jurisdiction dinmu ne .."
"Dalilin kenan da na kawo maka case din."
DPO Yahaya ya ce ya kwantar da hankalinsa zai bi kanun komai
"Sunan ne naji ya zo daya ina tsammanin wanda nake zargi ne. Sau biyu yana zuwa nan amma sai kaji daga sama an ce a sake shi."
Salihi ya dan cije lebe "kana nufin idan shi ne sakinsa zaka yi?"
Da sauri DPO Yahaya ya gyara zancensa domin kuwa ya jima yana son Habibu ya shiga gonar da ta kusance shi. Irin gonar da idan Habibu ya sallami na sama dashi da kudi shi kuma zai nuna bacin ransa akan rashin goyon baya daga abokan aikinsa.
"Duk yadda akayi dubunsa ce zata cika. Yaya Salihi ka dawo gobe kawai in sha Allahu iwar haka yana cell."
Shawara suka zauna yi akan yadda zasu bullo masa a saka shi fiddo kudaden Uwani. DPO Yahaya ya dan muskutu gaban kujerarsa cikin muryar da babu cin fuska a tattare da ita ya ce,
"Amma don Allah garin yaya Maman Mubashir tayi wannan sakacin? A gaskiya ko babu addini a al'adance ma banga dalilin da zaisa mace ta riki wani namiji amini idan ba shakikinta ko miji ba. Duk da na san cewa muma mazan bamu cika kyautawa ba. Idan harkar kudi ta hadamu da mace sai muyi taking advantage din kyautatawarta mu danne mata kudi. To amma duk da haka wannan ba hujja bace da za ta dinga budewa wani shirgegen kato sirrin da mijinta bai sani ba."
Salihi sai ya yi murmushi. Kafin ya tashi ya ce masa zai dauki kwakkwaran mataki akanta. Sai dai yafi kowa sanin Uwaninsa. Duka abubuwan da tayi babu guda da zai yi mata uzuri akan shi. Bata kyauta ba iya rashin kyautawa. Duk da haka gidan da ta taso ya taka muhimmiyar rawa wurin shaping din rayuwarta. Bakin halinta na rowa ba komai bane illa nason da halin mahaifinta ya yi a jikinta da kuma tsoron kada a maimaita wata Innayo din da ita.
Domin ya sami cikakkiyar yarda tsakaninsa da ita da sauyin hali sai ya nuna mata cewa ba kowane namiji bane Alh. Rabi'u. Dukiyar matarsa ba tasa bace kuma nauyin dawainiyarta da ta yaransu a wuyansa yake shi namiji. A karshe yana son ta bambance tsakanin kyautatawar da mata kan iya yiwa mazajensu domin lada da rainin wayon maza marasa tsoron Allah. Irin mazan dake sarayar da ayyukan da suka wajaba a garesu su barwa mace daga taimako. Sune suke tsorata mata da yawa su kasa taimakon mazajensu koda suna da halin yin hakan.
***
Kwalla fal idanun Innayo a lokacin da Honourable Habu yayi mata kyakkyawan albishir.
"Hasiyan ce dai da ciki ko?"
Kunyar da ya manta da ita a lokacin da ya iso gidan har ya fada mata da bakinsa ce ta kama shi. Ya dan dukar da kai yana murmushi. Ita ma murmushin ta mayar masa wanda ya koma dariyar farinciki.
"Fadi komai kan ka tsaye ai auta ce babu mai cewa mun yi rashin kunya."
Honourable dai sai dariya mai hade da kunya. Asibitin da Hasiyan take kwance ta tambaye shi sai ga Asabe a kansu kamar daga sama ta fado. Daga dakinta taji kamar suna ambaton Mariya domin 'ya' kawai taji da kuma asibiti. Bayan abin da ta gani dazu a firgice ta fito.
"Me ya sami Mariyan? Ina Munzalin?" Ta ce yayinda take waigawa hagu da dama tana dube dube.
Innayo tayi mamakin abin da ya tayar mata da hankali haka. Ba abin ta tambaya ba ta san tsaf za ta gwasaleta.
"Hasiya ce a asibiti."
"Au tooo...to Allah Ya sauwake" ta ce a sanyaye tana juyawa dakinta.
Innayo bata ma bi ta kanta ba ta shirya ita da su Salima zasu tafi asibitin. Dakinta ta koma inda ta baro Uwani tana ta kai gwauro da mari ita kadai.
"Na san cewa a karkashin wani kike nima ba zan so ki dinga yawo da aurenki ba. Amma ai ko sakon gaisuwa ga