Showing 183001 words to 186000 words out of 242549 words
a jikinsa? Salima da Maimuna suna kyautata mata amma ai har yau guminta suke ci. Su Hasina dama tun zamanin marigayiya Allah Ya jikanta suka juya mata baya. Me tayi mana da zafi Uwani? Saboda ta auri ubanmu ta haifemu shi ne laifi? Ko don ta jure wahalar gidansa domin ta zauna damu don kada rayuwarmu ta tagayyara? Kiyi tunani idan har kina da rabon jindadin duniya da lahira. Innayo jininta ne kadai bata zubar domin mu ci, mu sha kuma mu sami ilimi ba. Tun karfe hudu take tashi amma babu ita babu sake kwanciya sai wuraren shadaya ko shabiyun dare. Hannunta kullum a ruwa, ido a gaban murhu. Haba Uwani? Kamar baki rike ciki kin yi nakuda ba? UWA, UWACE komai lalacewarta. Balle kyautar Allah irin Innayo."
Bata kara tofa komai ba bayan haka ta shige daki saboda kukan da yaci karfinta. Uwani kuwa zama tayi dabas akan kujera duka jikinta babu kwari. Ta kwashi kusan minti ashirin tana juyayin maganganun Zara kafin wani irin bacci ya dauketa. Tabbas sau tari mutum yana ganin abin dake zuciyarsa ne a cikin bacci. A yadda take a zaunen ko gyara zama bata yi ba baccin nata ya dauketa zuwa duniyar mafarki mai ban tsoro. A cikin baccin take fatan Allah Ya kawo mai tashinta saboda firgicin da ba za ta ce ga abin da ya kawo mata shi ba.
*
"Shazali ya maganarmu ne? Ranar laraba muka yi da Alh. Tahir gashi har yau litinin baka ce min komai ba"
Gefen titi Shazali ya gangara da motarsa domin maganar da zai yi da Comared tana bukatar nutsuwarsa sosai.
"Ranka ya dade akwai shirin da nake yi ne. Hatsaniya ta shiga tsakanina da mutumin da nake son kawo masa ne, saboda haka sai na lallaba shi a hankali."
Tsaki Comared ya ja ya kuma kama yi nasa fada harda zagi.
"Ka tabbata yaron ya zo domin idan aka sami akasi raina da naka duk sai sun baci"
Hakuri Shazali ya bashi a ransa yana ta tufka da warwarar yadda zai yi ya sami kan Abbati cikin lumana. Aikin Comared din da ya yi masa bayani ya wuce biyawa Alhajin da zai zo bukata kadai. Aiki ne na sihiri wanda Alh. Tahir ya zata za ayi ne domin toshiyar baki (Yumna). Bai san cewa Comared tasa tukunyar yake son gyarawa ba. Sharri yake son kulla masa ya watsa hotunansa ta yadda zai rasa duk wata kwangilar dake hannunsa. Sai a bawa Comared don dama irin sana'arsu daya. Lokaci guda Alh. Tahir din ya yi musu zarra, sunansa kadai ake ji. Abotar sai ta koma murmushin gaban ido da gulmar bayan ido, batare da saninsa ba.
To shi ma Shazali burinsa ya yi amfani da wannan damar ya tozarta Abbati. Duk da cewa a gaskiyar lamari yafi jin haushin Munzali saboda yafi baki. To amma wulakantar Abbati sai tafi ta Munzali ciwo kamar yadda ya yi hasashen tonon asirinsu. Abbati dan dangi ne. Munzali kuwa da danginsa da babu duk daya a tunaninsa. Sannan son da Munzali yake yiwa Abbati zai sa yaji ciwon abin sosai. Dama ce ya samu da zai nuna musu shi din ba kanwar lasa bane. A matsayinsa na silar arzikinsu bai kamata su juya masa baya ba. Sai da suke ganiyar samun kudi kamar hauka sannan zasu ce wai sun tuba. Ko waye ya fada musu cewa shi baya son samun rahama bai sani ba. Lokacin tubansu idan ya zo ba sai kowa ya fada musu ba. Tsufansu ya ishesu sanin cewa ya kamata a koma ga Allah. Su gina masallatai su dinga bayar da sadaka. A haka zasu koma lahira kamar jarirai. (Babu bawan da Allah Ya yiwa alkawarin jinkirta masa rayuwa zuwa wani wa'adi. Lokaci yana zuwa ne ko da tsufa ko babu. Ko an tuba ko ba a tuba ba sai an tafi. Ya Rabbi Ka yafe mana zunubanmu na zahiri da badini. Amin)
Da waccan magana ya katse kiran Comared ya shiga laluben layin Abbati. Cikin sa'a kuwa ta shiga sai fatan a dauka. Abbati na ganin sunansa a jikin wayarsa ya ja tsaki ya mayar da ita aljihu. Sun kusa Jogana motar tasu ta soma hayaki suka tsaya. Abin duniya ya taru ya yi masa yawa domin ya kasa samun mota mai tsayuwa ta dauke shi. Ga yamma ta kawo kai. A gefe guda kuma ya kasa samun Munzali. Hanne da yake tunanin zata hadasu ita ma wayarta a kashe. Daga baya ne ya yi tunanin kiran Kukunsu. Cikin sa'a kuwa ya sameta. Shazali da bai hakura da nemansa ba ya dinga jin wayar tana shiga number busy.
Kalmar lafiya kalau kadai Abbati ya iya cewa ga dukkan tarin kalaman gaisuwa da kukun yake jefa masa. Jin zai fara tambayarsa mutanen gida ya yi saurin katse shi.
"Don Allah hadani da Munzali"
Kuku ya dubi hanyar bene ya ce "yau ko sau daya bai fito ba. Sannan yaki barin Qibdiyya ma ta sauko. Abincinsu ma ni ban sani ba ko sun ci don ya kulle kofarsa"
Dunkule hannu Abbati ya yi ya daddaki goshinsa cikin rashin sanin abin yi. Can dai ya ce masa yana zuwa ya kashe wayarsa. Hannunsa yana rawa ga gumin tashin hankali ya shiga scrolling din sunaye a wayarsa. So yake ya gani ko zai yi dacen samun nambar 'yan uwan Munzali amma babu ko daya. Tsoronsa kada ya dauki mummunan mataki musamman da Kukun yace yana tare da Qibdiyya. Kiran kukun ya sake yi da wata shawara ta zo ransa.
"Ka san gidan iyayen Munzali ko?"
"Na sani ranka ya dade"
"Ka je gidan ka nemi mahaifiyarsa Asabe ka fada mata. Ita zata san me ya kamata ayi kafin na iso. Ka tabbatar ita ka samu"
A kofar gidan Alh. Rabi'u kukun ya tsayar da mashin dinsa ya sauka ya dinga kwada sallama.
A cikin gidan Asabe tana kuryar dakinta abin duniya ya yi mata yawa. Zantukan Munzali basu da ma'anar da zata iya cewa ga dalilin da yasa yake rokon Qibdiyya gafara don an mata fyade. Ta so tahowa ma da ita a jiya a hana. Yau kuma yaki daukar wayarta. Daga baya ita ma bata samunsa. Ga sunan yaron da Qibdiyya ta ambata ma ya kwanta mata don bata taba jinsa ba. Shawara tayi tafi dari akan ta kira su Ummakati ta fada musu ko tayi shiru. She was never a Mom to all of them. Ta dai san wahalar daukar ciki da nakuda. Ta kuma dan san wahalar raino musamman kafin yaro ya fara zama. Daga nan kuma sai abin da hali ya yi. Allah Mai rayawa Shi ya raya mata zuri'arta cikin mugun sakaci da rashin sanin ciwon kai.
Da Innayo ce tabbas ta san da tuni ta lalubo abin da ya dace har ma ta aiwatar. Yinin ranar bata tsinana komai ba sai kullawa da kwancewa. Ga ranar da duk girman d'a yake bukatar mahaifiyarsa. Gata da rai da lafiya amma bata san me ya kamata ta yiwa Munzali ba.
*
Tashin da Uwani tayi daga firgitaccen baccinta yana da alaka da karfin sallamar Kuku. A razane ta tashi tayi hanyar kofa da sauri. Zara ta kalleta ta girgiza kai. Ita ma sallamar ce ta fito da ita.
Kallon ina-na-sanka Uwani ta dinga yiwa masa. Shi bai ma ganeta ba sai Asabe da ya tambayeta.
Juyawa tayi kamar ta koma daki sai dai ta karasa ta fadawa Asaben. Tare suka dawo bakin kofar. A gabanta ya fada mata halin da Munzali yake ciki. Cikin tsantsar rudani kuwa Asabe ta soma kuka. Ita kuma Uwani wani case ta tuna a asibitinsu inda uba ya kusa kashe 'yarsa saboda bakincikin an mata fyade a kauye. Ya ce gara ta mutu akan duniya taji wannan labari. Ba tare da tunanin komai ba sama da ran kaninta da 'yarsa ta koma daki da gudu. Mayafin dake jikin Zara wanda ta lulluba zata fito tun zuwan Kuku ta warware ta yafa. Ta ruga daki ta dauko jakarta mai dauke da kayan aikin gaggawa ta fito.
"Ki fadawa Innayo na tafi gidan Munzali"
Zara ta bita da sauri "gidan Munzali kuma? Me ya faru?"
Uwani bata ce komai ba ta fita. Asabe har lokacin tana tsaye tana koke koke bata iya cewa komai ba ga kuku. Isowar Uwani ce ma ta ankarar da its cewa ya kamata tayi wani abu.
"Malam muje don ba gane gidan zanyi ba"
Kuku ya dan ja baya "ke ce Asaben?"
Rai a bace da ganin yana bata mata lokaci ta ce "ni yayar Munzali ce. Ka wuce mu tafi"
Asabe sai ta gyada masa kai ta koma ciki da zummar dauko mayafi. Kafin ta fito sun bar wurin. Duk da tsoro irin na Uwani haka ta hau mashin din tana salati har suka isa.
I just published "38" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1133889152?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=VZ0iecln71g4e%2B3XyeweYBP%2F5nkH%2BcNoWrBHfg6iF2vPrMxcsWcPxWRResAX78c51fQElDFikz8lba2nyxXA4uHandgvdjrxFJT0p%2BYtGV68AukxrUibEQ9qpTux2mxt
UWA UWACE...38
Batul Mamman💖
Karfe goma na safe Habibu ya shigo cikin ministry da wata 'yar jaka a hannunsa. Kayan sawarsa ne da abubuwan bukata na kurkusa ya hada a ciki. Zaman Kano ba nasa bane ya sani tun ranar da Salihi ya titsiye shi. Babu shakka bayani ya kai kunnen Uwani. Sanin da ya yi mata na son kudi ba na yau bane. Abu mafi karanci da zata yi masa shi ne ta hada shi da 'yan sanda. Shi yasa zai yiwa tufkar hanci ya gudu. Ba kudinta ne kadai ya jike a hannunsa ba, harda na wasu da dama. Da ace kudaden suna da albarka a hannun macuci kuma maha'inci irinsa da tuni ya zama wani. Shekara da shekaru da 'yan dabaru yake kwatar kudi a hannun mutane ya danne. Haduwarsa da Uwani da amincinsu ne yasa ya rage rarakar aljihun wasu. Bai taba shan wahala ko ta anini ba wurin tatsarta. Ita take kawowa tana bashi, shi kuma yana gina kansa.
'Algungumi, an dai fadi ba nauyi' ya ambaci maigidanta Salihi dashi a lokaci guda yana jan tsaki. Duk shi ne ya bata komai da ya far masa kamar ita ta aiko shi. Tunda ya san gaban kansa yake yi gara ya gaggauta guduwa kauyensu har kura ta lafa. Manyansa a harkar magudi ba za su bari ya rasa aikinsa ba. Yanzu ma daya daga cikinsu ne ya ce ya biyo ya karbi rabonsa na wasu kudade da suka yi kashe mu raba da hakkin talakawa.
Hagu da damansa ya waiga don yana ji kamar ana kallonsa sai dai bai ga bakuwar fuska ba. Hakan yasa shi sakin jiki ya shiga office din mutumin. Yana rufo kofa wani masinja ya kira wayar DPO Yahaya kai tsaye ya sanar dashi shigowar Habibun.
"Ka san yadda zaka yi ka rike min shi idan kaga zai tafi har mu iso."
"Yallabai kada ku dade domin da jaka na ganshi"
"In sha Allahu ba za mu wuce minti ashirin zuwa talatin ba."
Masinja ya cika aiki kuwa. A matsayinsa me da ma'aikacin da aka fi gani tare da Habibu, DPO Yahaya yasa aka kai shi station. Bayan guntuwar tsoratarwa suka gano da gaske bashi da hannu wajen ha'incin Habibu. Ya dai san yana yi kuma kamar yadda ya dinga yi musu rantsuwa yana yawan yi masa fada. Alakar tasu ba wata mai zurfi bace sama da yawan musayar yawu game da bambancin ra'ayin siyasa.
"Muna so ka bamu hadin kai ka taimaki abokinka ya daina cutar mutane" abin da DPO din ya fada masa kenan da ya bashi lambar wayarsa.
Bai fi minti bakwai ya rage a lokacin da Masinja yake tsammanin isowar 'yan sandan ba sai ga Habibu ya fito yana fara'a. Masinja ya karaso suka gaisa ya soma jansa da hira.
Idanun Habibu akan gate yana daddaga wuya ya zaro dari biyar "sauri nake ga wannan ka sha ruwa"
"Yi hakuri ka saurareni Habibu. Matsala ce ta taso a unguwarmu."
"Ka ganni nan? Garin zan bari yau dinnan. Ka nemi gidan Dagaci ko Mai unguwa ku kashe matsalar"
Masinja bai hakura ba ya bi bayansa ya rage murya kamar sirri zasu yi.
"Na san kana dan taba harkar nan. Ka taimakeni ko wani abu ne sai na biya."
Saurin takun Habibu sai ya ragu. Masinja kuwa ya gimtse dariyarsa da yaji me yace.
"Wace irin matsala ce? Yadda na dauke ka dan uwa kaima ka san ba zan iya dauke kai akan matsalarka ba"
Masinja ya kirkiro labari ya shiga zuba masa. Wai fili ya sayar ba tare da sanin mai shi ba miliyan biyar. An gama biyan kudi amma balli na neman tashi. Shi ne yake neman mafita.
Hannu Habibu ya dora akan kafadar Masinja yana murmushin mugunta.
"Ina kudin yake yanzu? Allah Yasa baka kaisu banki ba"
A madadin amsar Masinja da yake jira sai jiniyar 'yan sanda ta ziyarci kunnuwansa. Saboda tsabar kaduwa, hannun nasa da ya dora a kafadarsa ya kasa saukewa. Jikinsa ya yi sanyi kalau amma haka ya daure domin a zatonsa motar wucewa tazo yi ta unguwar. Dif ya daina jin karar har ya samu damar sauke numfashi. A ransa yake tunawa kansa cewa mijin Uwani a yadda take fada masa yafi kama da marasa wayo. Ita kuma tunda bata san ainihin me ya mata ba da wuya tayi kararsa. Wayar da tayi masa da asubar ranar dama ita ta kara saka masa son guduwa sai kura ta lafa. Yana can yana zancen zuci sai ji ya yi an damki hannuwansa. Ya zabura ya kalli masu rike shi yaga duka kayan gida ne a jikinsu. Wannan kuwa dabarar DPO Yahaya ce domin kada Habibu ya farga ya yi tunanin gudu.
"Lafiya? Ku su waye? Satar mutane kuma da safiyar Allah a gaban jama'a?"
Daya daga cikinsu ya dauko ID card ya nuna masa "mal. Habibu, ana tuhumarka da satar kudin Uwani Rabi'u ta hanyar yaudara"
"Bangane ba!" Da ya fada a tsorace ta nuna cewa ya gane tsaf.
"Idan mun station za ayi maka cikakken bayani. Muna neman hadin kanka ko mu tafi da kai ta karfin tsiya"
Mutanen da suka fara tsayuwa kallo ya kalla sai kawai ya hakura yabi su. Bai san da sa hannun Masinja ba tunda gefe yaja ya tsaya.
Ana tafiya da Habibu station DPO din ya sanar da Salihi. Shi ne ya bukaci ya zo da Uwani domin jin ta bakinta. A lokacin ya tafi gidansu daukarta sai yaci karo da ita a bayan mashin din Kukun su Munzali. Hawa mashin ba dabi'arta bace. Ganin da ya mata ya tayar masa da hankali. Ko dai fitar da tayi ta son zuciyarta ce ko kuma ta emergency ce na abin da ya shafi wani. Zuciyarsa sai tafi karkata da tunanin farko tunda ya santa da son kai. Babu bata lokaci yabi bayansu har gate din gidan Munzali. Akan idonsa ta dira da sauri don saura kiris ta fadi ta tura karamar kofar jikin gate ta shiga da gudu gudu. Shi ma sai ya kashe motarsa ya bi kukun da sauri ganin an bude masa gate zai shiga da mashin din.
"Me yake faruwa ne a nan? Ni ne mijin matar da ta shiga yanzu Uwani."
Kuku ya ce "Alh. Munzali ne babu lafiya"
***
A cikin dakin Munzali kuwa a kwance yake yana rawar sanyi. Zazzabi yayi masa mummunan kamu. Har ta kai yana jin kamar ana kwankwatsa masa kasusuwa. Ciwon kai kuwa bai san daga wane bangare yafi sukarsa ba. Tunani barkatai sun addabi zuciyarsa. Mafi girma a ciki bai wuce jin tsoron ko tubansa ne bai karbu ba. Da tubansa ya karbu da babu wanda ya isa ya ketawa Qibdiyya haddi.
"Da tubana ya karbu da Allah Ya tsare min ke ko bana raye" ya furta a kasan makoshi yana shafa kan Qibdiyya.
Sake nanike mahaifinta tayi ta ce "Daddy har yanzu Papa bai zo ba"
Kwalla ta taho masa ya yi saurin riketa saboda kallon kurillar da take yi masa.
"Zai zo. Watarana zai zo...in Allah Ya yarda" saboda bai dade da gama wayar da ta kara masa ciwo da Baaba Mari ba.
"Daddy..."
Wata tambayar ce ya riga ya sani. Tun safe take faman damunsa. Da yace ta fita saboda ciwon kansa sai ta kulle kofar da mukulli maimakon ta bude bisa kuskure. Shi kuma azabar ciwon kai ya hana shi tashi.
"Kaina ciwo yake don Allah kiyi shiru"
Can gefe ta koma ta dauki biskit da juice wanda ya zame mata abinci tun safiyar yau din ta cigaba da ci. Wasa-wasa sai ga Munzali yana zubar da hawaye saboda ciwo. Komai ya jagule har yana tunanin rayuwarsa ce ta zo karewa. Sai dai yana tsoron tafiyar ba tare da sanin ko akwai nakasu a tubansa ba. Duk masu kwankwasa masa kofa ana kiransa yana ji amma ya kasa daga koda hannunsa ne. Ita kuma Qibdiyya bacci ne ma ya dauketa. A wannan halin Uwani ta iso gidan. Da sassarfa ta hau saman tana buga kofa amma shiru. Ana haka Salihi ya shigo Kuku yana yi masa jagora. Kiran da bugun da take yi ne ya kai hankalinsu gareta. Salihi yabi bayanta da sauri. Shi da Kuku suka hadu suna bugun kofa amma ko gezau taki motsi.
"Qibdiyya"
Munzali ya tabota da muryarsa da ta dashe bata fita sosai.
Gyara kwanciya tayi abinta ta juya masa baya. Ya sake kai hannu ya tabata idanunsa na fitar da kwallar azabar ciwon kai. Da kyar ya samu ta farka tana zuba masa magagi.
"Jeki ki bude kofa"
Zuwa tayi ta kama mukullin tana ta murda shi ba daidai ba. Hamdalar Uwani da Asabe da bata jima da isowa ba ta tsaya a dalilin rashin buduwar kofar. Salihi ne ya yi dabarar cewa a miko mukullin ta kasa.
"Na kasa cirewa" ita ce amsar Qibdiyya saboda ta kasa murda shi ya koma yadda zai fita. Sai da suka kwashe kusan minti goma sha biyar ana kwatanta mata yadda zata yi tana kasawa.
"Ina babanki?" Asabe ta tambayeta a firgice.
"Yana kwance. Kuma kuka yake yi"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. A zaton Asabe ya ma mutu. Cigaba da juya mukullin Qibdiyya tayi har ta gaji. Ta cire hannu kenan Munzali ya taso da bin bango ya bude kofar. A tare Uwani da Asabe suka tura kofar ya fado gabadayansa akan Uwani saboda ita ce a gaba.
"Munzali? Munzali tashi. Na shiga uku na lalace. Ku taimakeni"
Zantukan Asabe kenan tana faman jijjiga shi bayan Salihi ya daga shi daga jikin Uwani. Da ta tashi jakarta ta dauko a kofar dakin ta soma auna shi. Jininsa ya hau ta yadda ita kanta ta tsorata sosai.
"Asibiti zamu kai shi"
Ta ce da Salihi tana mikewa