Showing 186001 words to 189000 words out of 242549 words
tsaye. Ko tunanin daga ina yake ma bata yi ba. Shi da kukun dai suka saka shi a motarsa. Asabe, Uwani da Qibdiyya kuma suka shige bayan mota.
Hayaniyar fitarsu ce ta taso Hanne har ta leka ta taga. Akan idonta aka sanya Munzali a mota. Jiki na rawa ta sami abin fadi ta dauko wayarta ta kira Abbati. Rabonta dashi tun yana shirin tafiya daurin auren kanin Mami Khadija. Tunda akwai kudi a hannunta bata ga dalilin kiransa ba. Shi ne mai kokarin kiran duk inda yake koda sau daya ne a rana saboda hakki. Neman kudi kadai ke sanyata kiransa. Yau da yake gulma ce sai bata ji kyashin kiran ba. Yana dauka ta saki baki ko tauna magana babu.
"Yanzu naga an dauko Munzali an saka shi a mota kamar matacce"
Razanar da yayi zai rantse ko tonuwae asirinsa bata sa yaji makamanciyarta ba.
"Me kika ce?" Ya tambayeta da muryar da take fita kamar ba tasa ba.
Sai kuma ta dan yi jim da ta hango wautarta "bani da tabbas fa"
Kashe wayarsa ya yi ya sake kiran Kuku. A nan yaji cikakken bayani. Tashin hankalinsa ba zai misaltu ba. Allah Yasa lokacin suna Jogana. Daga nan tafiyar bata da yawa sosai za a shigo garin Kano.
Bayan minti arba'in Abbati ya shiga wani babban asibitin kudi wanda suke zuwa tare da iyalansu shi da Munzali. Sai dai ya daki gurbi domin kuwa ba nan aka kai shi ba.
*
Bangaren A & E na asibitin Sir Sunusi Salihi ya nufa. Sai lokacin Uwani ta farga da ina suke. Kaddara za a kira shafewar tunaninta a game da hukuncin da CMD ya yanke mata har aka shigo. Ta dade da gane hanyar nan din Salihi ya dauko tun a baya amma tunanin an dakatar da ita daga aiki bai zo ba sai yanzu. Da ta fito daga motar sai taji kafafunta tamkar ba za su iya daukar nauyin jikinta ba. Shi kuwa Salihi tunda bai san halin da take ciki ba sai cewa yayi,
"Shiga kiyi musu magana mana a zo a dauke shi. Idan ke ki ka shiga na san ba za a bata mana lokaci ba"
Sati biyu da suka gabata da ita ce ta shiga tana da yakinin cewa a lalace mutum biyar su biyo bayanta. Idan kuwa aka san cewa kaninta ne to Allah kadai Ya san irin kulawar da zai samu. Sai gashi a dalilin son zuciyarta yau ta zo amma tana kunyar shiga. Labari ya risketa daga masu kiranta jajen gaske da na karya cewa kowa ya san an dakatar da ita.
Matron Uwani Rabi'u sananniya ce a asbitin sosai. Akwai kwazon aiki da shige shige. Ga masifa kamar da Alh. Rabi'u aka gina asibitin. Shi yasa ta tara makiya da yawa masu son ganinta a kasa. To yau ga ranar. Taimakon wadanda take nunawa dagawa ne zai sa kaninta ya sami kulawar da ta dace.
"Matron Uwani me kike yi a nan?"
Da sauri ta juya suka hada ido da wata Matron din. Kallo daya ta yiwa Munzali ta dubi matar.
"Wallahi kani na ne babu lafiya. Yana bukatar emergency care."
"Ai kuwa nan dai cike yake da jama'a saboda an kawo masu accident."
"Innalillahi. To don Allah Matron ki taimaka min don yanayinsa ba zai yiwu mu fita dashi ba"
"Sai dai ki fara kulawa dashi kafin likita ya zo"
Har ta fara murmushi ta sake tunawa da suspension dinta. Amma haka ta daure tabi bayanta tana cewa su shigo dashi. Da gaske wurin a cike yake. Wheelchair (kujerar guragu) wani sub-staff (karamin ma'aikaci) ya kawo za a dora shi sai yaja baya da ya hada ido da Uwani tana kokarin sokawa Munzali allura a hannu inda za a kara masa ruwa.
"Matron? Ko ba Matron Uwani bace?" Ya furta da karfi har aka fara kallonsu.
"Nice. Don Allah yi sauri ka kawo ya zauna"
Mutumin ya dakata yana yi mata kallon biyu-ahu
"In baki kiyi aiki aji dadin korata?" Ya kara daga murya ya kira Matron din da ta shigo da ita wurin yana cewa " da alama dai baki san an dakatar da matar nan har na tsahon wata shida ba ko? To wallahi babu ruwana don dokar daga sama aka aiko da ita.
Uwani ta kalli Munzali ko tsayuwa ya kasa yi. Yana tsakiyar Salihi da Asabe ne sun rirrike shi yana neman faduwa. Harbawa zuciyarta ta kama yi ta dubi mutumin rai a bace.
"Wannan ba patient din kowa bane nawa ne. Kanina ne wallahi. Don Allah ka bani kujerar a zaunar dashi"
"In na baki Allah Ya tsinan..." Ya tabe baki "ko doka bata hau kanki ba Matron wallahi yau dai sai dai wani ya taimaka miki. An fada miki na manta tarin rashin mutumcin da kika yiwa matar kanina a labour room ne? Ga kuruciya gashi haihuwar fari ce amma kika dinga yi mata tsawa kamar wata baiwar da kika saya da arha."
Daga bandakin bangaren emergency din wata dattijuwa mai aikin shara da wanke bandakuna ta fito. Duk zancen da ake yi taji kuma ta kara da nata.
"Ashe ba ni kadai matar nan ta yiwa diban albarka ba. Nifa matar makocin dana aka kawo sai a baranda ta haihu. Kememe Matron Uwanin nan ta dage sai an biya kudin gado wai na gwamnati sun kare saura na kudi. Yaron wajena yazo muka tafi nace mata nima nan nake aiki sai cewa tayi wai tayi ragin dari biyu albarkacina. Su biya dubu tara da dari takwas."
"Uwani Rabi'u ake fada muku. Matar da ta kasa biyawa uwar da ta haifeta kudin ganin likitan hakori? Nan asibitin suka zo babarta ko bude baki ta kasa amma Uwani ta ce bata da kudi. Kai ranar naga rashin mutumci ajin karshe. Wallahi sai da na godewa Allah da bai bani haihuwa ba. Da haihuwar dan da ba zai ji kanka ba gara kayi ta shafa fatiha."
Uwani ta juya suka hada ido da daya daga cikin nurses din bangarensu na haihuwa. An kirata ne saboda cikin masu hatsarin harda mai ciki.
Muzanta da tozarci irin wanda ko a labari bata taba ji ba ne suka saukar mata. Idanu sun fi a kirga a kanta. Ciki harda na Salihi da Asabe. Ga maganganun 'yan kallo harda majinyata ana zundenta tana ji. Jikinta a take ya yi sanyi kalau kamar an jefata a ruwa. Gumi ne kawai yake karyo mata sakamakon zafin da take ji yana bin jikinta. Ta kuma kasa yin motsi don ji take kamar an zare mata laka. Kai ta sunkuyar kasa ta dunkule 'yar robar daure hannun wanda za a sakawa allurar karin ruwa a hannunta da karfi. A hankali ganinta ya ragu a dalilin kwallar da ta cika idanun. Hannu taji a kan na damanta an riketa ana jijjigawa.
"Mu fita mu nemi private hospital (asibitin kudi)"
Da kyar ta iya daga ido ta kalli Salihi sai ta mayar da kanta ga Munzali. Idanunsa ne suke yin luuu yana shirin suma. Ganin haka bata san lokacin da ta dauko wayarta ta duba nambar Barr. Umma Jibril. Ringing hudu ta amsa kiran.
"Matron Uwani?" Ta ambata cike da mamaki.
Yawu Uwani ta hadiya mai daci. Bata manta da haushin matar da take ji ba da yadda ta rufta ta a gidanta da sunan dinki za ta yi mata. Bacin ranta ba wai don tana tantamar rashin gaskiyarta bane. Ta san ita din mai laifi ce sosai. To amma yadda aka bi aka kunyata ta duk da ba a gaban mutane bane ya tsaya mata a rai. Ga matsalolin daban daban da suka kunno mata kai lokaci guda. Amma hakan bai hanata jin cewa Barr. Umma ita kadai ce hope dinta ba a yanzu. Muddin ta tsaya girman kai ta ce su tafi wani asibitin Munzali zai iya shiga mawuyacin hali fiye da yanzu.
Barr. Umma sai ta ce "Ko ba Uwani bace?" Da taji shirun ya yi yawa.
"Nice" ta amsa da sanyin murya tana kallon kaninta. Kanin da ba wani abu na zumunci da zata ce ya taba giftawa tsakaninsu tun kuruciya. Sai gashi a yau tana jin damuwarsa ta danne tata. Ga ciwo ga maganganunsa da bata gane ba sannan ga babbar lamari game da 'yarsa....'yarmu ta gyara a zuci.
"Hajiya don Allah ina rokonki da ki taimaka ko na yinin yau ne kisa CMD ya janye dokar suspension dina"
Karaya da nadamar da ba a son bayyanawa Barr. Umma take ji daga muryar Uwani. Da yake ba halinta bane sai ta kasa jan zancen ta hanyar nuna mata dama rana irin yau sai ta zo dole.
"Me yake faruwa?"
"Kanina ne muka kawo gashi babu wanda zai iya duba shi a emergency saboda yawan patients. Ki taimaka min don Allah."
Yau wai ita Uwani ce take magana da roko har tana jin taruwar kwalla a idanunta. Ina zuwa taji Barr. Umma ta ce. Ba a yi minti goma ba aka kira babban likitan dake emergency din. Da kansa ya zo inda Uwani take kai gwauro da mari ya mika mata dan akwatin awon bp.
"Ki daukar min duk wani relevant detail ki fara kara masa ruwa kafin na gama da wadanda suke kan layi."
Murmushin da yafi kama da dariya gami da fitowar kwalla duka suka sauko mata a lokaci daya. Asabe tana ta hamdali yayi da Salihi ya karbe wheelchair din da sub-staff din nan yaki basu da farko ya zaunar da Munzali. Ita kuma ta kama hannunsa ta dauki bp. Sakamakon da ta gani ya tsorata ta sosai. Lokuta kalilan ta taba ganin wadanda jininsu ya hau haka a bangaren haihuwa. Zafin zazzabin shi ma ya haura ka'idar da aka saba. Da taimakon Salihi ta samu ta saka masa ruwa shi kuma ya rike ledar saboda stand din ma babu a kusa. Tayi masa allurai da duk wani agajin da ya dace da halin da yake ciki.
Bayan ta gama iya nata ta ruga duk infa likitan nan ya saka kafa tana biye. Bata so ya manta da dan uwanta akan layi. Da ya ce a miko wani abu sai tayi azamar yi duk don idan yazo kansu ya kyautata. Asabe tana tsaye rike da hannun Qibdiyya amma idanunta suna biye da duk takun Uwani. Sanda kwalla ta silalo mata ita kanta bata sani ba.
"Innayo bata yi asarar haihuwa ba" ta fada da raunanniyar murya.
Salihi ya gyada kai a inda yake tsaye yana kulawa da Munzali wanda bacci ya fara daukarsa. Uwani baudaddiyar mace ce. Shi kan shi bai taba zaton akwai ranar da zai ga tambarin mahaifiyarta a tattare da ita ba. Indai mara kirki wanda ya amsa sunansa mutum yake nema to lallai in yazo kan Uwani ba zai matsa ba. Zai ce ya sami abin da yake nema ne kai tsaye. Inama Innayo tana kusa ta ganewa idanunta.
***
"Mami zani Kano gobe in sha Allah"
Wayar da aka yi mata daga Kanon ta fasa amsawa ta kalli Lilu da sauri.
"Wani abin ne ya faru?"
"Ya Suhaib ne ya buge a kafa ba zai iya tuki ba"
"Kada ka boye min komai Lilu" ta furta cike da tsoro.
Murmushi ya yi kawai ya kira Suhaib a wayarsa ya bata. Da kansa ya fada iya abin da zai iya. Kofar daki ya daka ya bugu a kafar. Hankalinta ya dan kwanta amma ta san Suhaib da dauriya akan abin da yake ganin zai janyo mata damuwa. Ga Lilu kuma shi ma bata jin yana cikin nutsuwar jan mota shi kadai har Kano.
"Zan bika amma ka san ni ina son sammako"
Dage gira ya yi harda 'yar dariya "dan farin kuma Mami? Ai na zata za ki daure har ya iso gida"
" Fita ka bani wuri" ta ce ita ma tana dariyar.
Fitarsa keda wuya ta kira Alh. Tahir ta fada masa abin da ya sami Suhaib. Izinin tafiya ya yi mata. Ya kara da cewa shi ma jibi abu mai mahimmanci zai kai shi Kanon. Su jira shi sai su dawo tare.
Da ta ajiye wayar kwakwalwarta aikin tunani ta shiga. Lamarin 'ya'yanta yana matukar damunta. Kowa da irin tasa damuwar. Yanzu da tace tana son zuwa Kano bata ce ga dalilinta ba. Indai buguwa ce tabbas abu ne da zata iya jiran a dawo mata da Suhaib din gida. To amma zuciyarta ta gaza sukuni. Kanon dai take son zuwa.
I just published "39" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1133889480?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=6I7qwMcRV%2FprvkCAkOvGj81Y%2BmQoj3hi1UT3OuzitQizPjHSDqCAybTI7a5GOCA3ThRlgbmz%2BAmhOE1LwaV8L5ikM6vN4nYTiiRNW6SjyqWr0FoHDqOW%2FWW1CPbmrqkE
UWA UWACE...39
Batul Mamman💖
Su Innayo basu san wainar da ake toyawa a gidan ba sai da suka dawo ita da Salima. Tambayar inda Uwani ta shiga ta yiwa Zara ta fada mata duk yadda suka yi har fitarta.
"Ban san me yake faruwa ba amma tana fita Asabe ma ta fita"
Dama da tunanin halin da ta bar Uwanin a gida ta wuni. Wannan labari sam bai mata dadi ba. Duban 'ya'yan nata tayi ta ce daya daga cikinsu ta kira mata Uwanin a waya. Salima ce ta kira da aka amsa ta mika mata.
"Ban hana ki fita ba Uwani?"
Fita tayi daga dakin da aka kwantar da Munzali don kada ta tashe shi daga bacci. Kofar ma a hankali ta rufeta sannan ta ce,
"Muna asibiti da Munzali an kwantar dashi"
"Me ya same shi?"
"Bayanin ba zai yiwu ta waya ba Innayo"
Muryarta babu wannan gadarar da ta saba da nuna isa. Kamar ma da sigar rarrashi Innayo take jin amsoshin Uwani. Da taji a wane asibiti suke sallar magariba kawai tayi ta sake tashi. Sai da Salima tayi da gaske wurin hanata fita bata ci komai ba. A lokacin ne ta fadawa Zara abin da ya faru da Ayaah. Suka gama jajantawa sannan suka fita zasu tafi asibitin. Wannan karon dai Zara sam taki yarda su barta a gida. Ciwon dan uwansu da zai kai Uwani asibiti ko biyanta zai yi ba abin rainawa bane. Innayo ta girgiza kai kawai don bata ga alamun zata ji maganarta ba suka tafi.
Basu wani sha wahala ba suka iso dakin da Uwani ta kwatanta musu. Mamakin ganin Salihi a wurin ne ya kama Innayo. Ya gaisheta da fara'arsa sannan ya bata kujerar da yake zaune.
Sai da ta zauna sannan ta kalli inda Asabe take tayi lakwas. Ta kira kannin Munzali namijin mai suna Bature akan yazo ya kwana amma kememe yaki. Uzuri mara tushe ya dinga bata. Dama rabonta da ta sanya shi a ido an tasarma sati. Da dai rabon kudi yake ba zai yi fashin zuwa. Ummakati kuma mijinta yace dare ya yi za su zo gobe, duk da lokacin da aka fada mata shida bata karasa ba. A gidanta autarsu mace ta tare saboda kwadayi. Gashi mijin Ummakati yana mata kulle. Sai abin ya shafi kanwar da ya kula tana yawo. 'Ya'yan Innayo mata wadanda kullum take aibatawa tare da yi musu kallon rashin galihu sune a tare da ita.
"Asabe ya mai jikin?"
"Da sauki, gashi ya sami bacci."
Dakin sai ya yi shiru tunda hirar kirki dai bata taba hada duka mazaunan cikinsa a lokaci guda ba. Uwani waya take yi da wata mai shara tana bata sautun irin abincin da za a siyo da adadin mutanen dakin. Jin haka Innayo ta ce,
"Mu kam a koshe muke"
"Sai a tafi dashi gida. Guda bakwai za ki karbo kinji" ta karkare wayar tana duban Qibdiyya wadda ke faman matse kafa.
"Kina jin fitsari ne?" Ta tambayeta. Da ka ta amsa don ta matsu sosai.
Tashi tayi domin ta kai ta sai Asabe ta riga. Dakin ya zame mata kamar akurki. Kwarjinin Innayo da zuri'arta yasa ta kara jin kanta kamar wata 'yar kora. Suna fitowa taji ance,
"Barka da dare Asabe"
Sakin fuska tayi da ganin fuskar da ta sani.
"Barkanmu dai dannan. Shiga ciki ga dakin da aka kwantar dashi."
Qibdiyya da ya gani tare da ita ya jefa tunaninsa a mizanin aune-aunen hanya mafi saukin bullewa. Babu bata lokaci kuwa ya cafki damar da ta zo gareshi da gaggawa.
"Ina zaki je ne?"
Hagu da damanta ta dinga kalla ta ce "wallahi inda zan sami piya wata (pure water) nake nema wai fitsari Qibdiyya take ji"
Dan waro idanu yayi "babu bandaki a ciki ne?"
"Ka san bangaren maza ne bai yiwuwa na shiga"
"Haka ne. To bari na dauko miki a mota"
Ya dan soma tafiya kenan ya tsaya.
"Qibdiyya zo muje ki rakani"
Wai aka ce tsaytsayi baya wuce ranarsa sannan mai halo baya fasawa. Asabe ta manta da halin da Qibdiyya take ciki har ta iya bari wani namijin ya tafi da ita mota. Sai da suka fara tafiya kawai taji kamar an sharara mata mari ta dawo hankalinta. Da gudu tabi hanyar da taga sun yi sai dai har ta isa wurin motocin babu shi babu alamunsa. Kin yarda da tunanin dauke mata jika tayi ta koma ta tsaya a inda ya barta tana jiransu.
Bata jima ba kuwa su Innayo suka fito. Uwani ce karshen fitowa tana yiwa Nos din da ta rakosu godiya. A ka'ida tun shida ya kamata 'yan dubiya su fita. Amma ganin dan uwanta ne shi ne aka barsu.
"Ina Qibdiyyan?" Zara ta tambayi Asabe tana gyarawa Salima goyon jinjirarta.
"Ina fitowa naga wani abokin Munzali. Shi ne ya ce zai dauko piya wata a motarsa"
"Abbati ne?"
Innayo ce tayi tambayar. Kafin ma ta karasa Asabe ta girgiza kai.
"Sunansa Shazali. Su kan dan zo gaisheni tare dashi jifa-jifa"
Sai suka tsaya aka koma shawarar zuwa a dauko kukunsu Munzali ya zo ya kwana dashi. Minti shabiyar, talatin, talatin da biyar...a daidai mintuna talatin da bakwai da tafiyar Shazali da Qibdiyya sai ga Abbati ya fado gabansu kamar an jeho shi.
"Ina Qibdiyya?"
*
Awa daya da rabi kafin zuwan Shazali asibiti gidansu Abbati ya fara zuwa. Rashin samun kowannensu a waya ya kawo shi gidan babu shiri. Kwana daya ya rage a lokacin da Comared ya bashi gashi ya kasa samun su. Yana zuwa maigida ya sanar da shi an kai Munzali asibiti. Hankalinsa kuwa ya tashi domin ya tabbata idan Munzali yana asibiti ba makawa Abbati ma yana can. Kenan ba shi da abin da zai tilasta musu zuwa don ko yafi kuda naci bai ga dalilin da zai raba Abbati da asibiti idan Munzali yana kwance. Wautar saurin tonawa Abbatin asiri da ya yi a wurin Baaba Mari ya gani. Ganin abubuwa suna neman rikice masa sai ya tambayi wani asibiti ne. Idan ya yi sa a suka fada tarkonsa na tsoron watsuwar sirrinsu a duniya kila ko Abbatin shi kadai ya je.
Kuku ne ya kira Uwani domin