Showing 24001 words to 27000 words out of 242549 words
mara dadi. Kina iya kokarinki wani ko wata azzalumi makiyin Allah zai koya musu mummunar dabi'ar nan tun da kuruciya..kada ki raba kan 'ya'yanki saboda mugun zargi amma kuma kar ki yarda ki shantake kina musu kallon basu san komai ba Tunda uba zai iya yiwa 'yar cikinsa ciki ta haihu to ki kaddara KOMAI IS POSSIBLE. Allah Ya karemu daga sharrin yai da gobe.)
Daga wasan doki Abbati ya danne Hanne. Bata san me yake yi ba illa kashedin da yake ta nanata mata. Idan ta fada sai ya yanke mata baki.
Suna wannan yanayin hankalinsa ya yi gaba sai ga matar guda cikin kawunansa ta kawo kai. Sai da gabanta ya fadi da ganin halin da yaran suke ciki. Amma saboda bakin hali da kishin faccaloli bata yi musu magana ba. Shi kuma bai ganta ba. Lallabawa tayi ta koma ta kira kawayenta cikin matan gidan. Su hudu suka dawo suna kallonsu suna sallallami.
"Ai sai ku kirata tazo tagani. Tana can gaban Malam ana rokon kar ya koma ita da kawarta. Ashe 'ya'yan iska suka ajiye mana a gidan."
'Yar aiken Jummai ta kira
"Zo ki ga Hanne."
Yadda tayi maganar Mari ta fahimci babu lafiya. A wurinta da na kowa ne kuma ko wane yanayi Hanne ke ciki ba sai mahaifiyarta ce kadai ya kamata ta gani ba. Idan abun taimakawa ne ta taimaka mata.
Kusan duka matan gidan ta gani a tagar dakin bayan. Jikinta sai ta hau rawa ko buhu ne ya fadowa Hannen. Da gudu ta tafi dakin kai tsaye Jummai na biye da ita. (Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ya Allah kar Ka taba nuna mana 'ya'yanmu a cikin wannan yanayi. Ya Allah Ka tsare al'urarsu daga alfasha ta fin karfi ko ta ra'ayi. Amin).
Abbati ta gani dare-dare akan Hanne yana mu'amala da ita cikin kwarewa. Kunnuwan Mari suka toshe bata ma ji ihun da Jummai ta saka ba. Idanunta suka makance. Jininta ya hau duk da ba asibiti taje ba domin duniyar cak ta tsaya mata. Bata san da yadda aka yi ta isa garesu ba sai sautin maruka kawai da suke tashi.
Finciko Abbati tayi waje tana kai masa duka kamar an aikota. Magana take yi amma baka gane jumla ko daya saboda harshen ma ya harde. Hawaye kuwa ya sa ko ganin inda take kai dukan bata yi. Amma duk da haka soyayuar danta tana nan cikin zuciyarta domin ita din uwa ce mahaifiya gareshi!
***
Daga shafi na gaba in sha Allahu zamu hadu da taurarin wannan labari a shekara guda.Wattpad
https://my.w.tt/8NYyQD7zf9
UWA UWACE...6
(Da dadi ko ba dadi)
Batul Mamman💖
Tun ana jin ihu da magiyarsa har muryar ta dauke sai nishi kawai yake fitarwa . Sai da ya kusa daina numfashi Mari ta barshi. Ita ma din gefe ta samu ta tsuguna tana nata kukan. A hankali ta daga kai ta saci kallonsa da ta daina jin nishin nasa. Duk tsiya duk lalacewa Abbati jininta ne, danta ne wanda take yiwa soyayyar da bata da kalmar kwatance.
"Dan iskan yaro. Wallahi bari Malam ya zo komawa zai yi inda ya fito don bai isa ya zo ya lalata mana 'ya'ya ba"
Muryar Deluwa ce ba wata ba. Tana fara magana sauran ma suka dinga tofa nasu ana ta kwashewa Abbati albarka. Jummai ta bar wurin tare da Hanne ta tafi dakin Inna Mairo. Abin da ya faru din ya girgiza Innar ta taso da kyar saboda ciwon kafa na girma ta taho bayan. Abbati ta gani a yashe kamar gawa ga matan gidan ana ta zage-zage. A can gefe kuwa Mari ce ta zuba masa ido. Lafiyarsa take son tabbatarwa amma tana tsoron nuna tausayinta gareshi a ce bata damu ba. Ajiyar zuciya ta sauke da taga Inna Mairo ta iso wurin.
Abbati ta duka ta tayar yana numfarfashi ta gallawa Mari harara. Fada ta soma yi mata cikin bacin rai.
"Kisan kai ki ka yi niyar yi ko me? Zo ki kama min shi a kaishi daki." Da sauri kuwa Mari ta taso.
"Inna da kanki?" Cewar daya daga cikinsu tana matsowa gabansu za ta daga shi.
"Ban son munafurcin banza da hofi. Kafin nazo da tana dukan nasa akwai wadda ta hana ne?"
Deluwa ta tabe baki "yo Inna me zai sa mu hana uwa yiwa danta hukunci?"
Ko ta kanta Inna Mairo bata bi ba ta nuna Abbati "Mari dauki danki muje dakina."
Soyayyar uwa akwai ban mamaki! Mari so take danta ya shiryu. Tana son fahimtar dashi munin laifinsa amma hukuncin tana yi ne ba don tana so ba. Uwaye su kan yiwa 'ya'yansu hukunci mai tsauri wani zubin har ya zarta laifinsu domin kada a ga gazawarsu. Sau tari suna daukar wannan matakin ne domin a zuciyarsu suna hangowa 'ya'yan ceto daga wadanda suke wurin. Abin da Inna Mairo ta hango kenan wanda su Deluwa basu gani ba. Ta san cewa babu horon da uwa za ta yiwa danta ba tare da ya yi mata ciwo fiye da dan a zuci ba. Sannan su ma 'ya'yan zukatansu sun fi nadama da jin kunya idan hukunci ya tafi tare da tausayawa ko da ba daga mai horar dasu ba.
Kunyar ganin Jummai a dakin Mari taji sai kawai ta sake shi don kada taga kamar bata damu da laifinsa ga Hanne ba.
"Jummai don Allah kiyi hakuri" ta ce muryarta na rawa.
"Ba komai fa Mari kar ki damu." Ta mayar mata amma ko ido ta kasa hadawa da ita. Ba laifin Mari bane ta sani amma 'yarta kuma fa? Ba don an gansu da wuri ba kila barnar da zai yi sai tafi haka.
Muryar Mal. Sa'adu suka ji a kofar dakin yana doka sallama.
"Ina yake tsinannen yaron nan?"
Inna Mairo ta zaga wurin girki da kanta za ta dora ruwan zafin gasa masa jiki. Bata ji zuwan Mal. Sa'adu ba. Shi kuwa don kada su bata masa lokaci sai ya sa kai cikin dakin ya janyo Abbati waje.
"Shegantakar da kake yi kenan Abbati? To Yasin ba dai a gidan nan ba. Daga yau idan kaga mace ma sai ka sauya hanya matsiyaci."
Kausasan kalmominsa sun yiwa Mari zafi. Bata ki a hukunta shi ba amma da wannan sigar ba. Kara kuntata kawai zuciyarta take yi da takaicin silar lalacewarsa. Kofar dakin ta fito tana gani ya jefawa manyan 'ya'yansa Abbati ko kula da rashin karfin jikinsa bai yi ba. Dukan da Mari tayi masa kadai ya jigata shi. Yaran kuwa kamar jira suke suka dinga tafkarsa da tsumagiyar darbejiya. Abbati sai gurnani yake a wahale don kukan ma yaki fita.
Zuciyar Mari ta dinga harbawa da tsoron kar shi ma yabi Sani. Da tafin hannunta ta toshe baki saboda kada sautin kukan da ya taho mata ya fito. Tana ji tana gani ake yiwa danta dukan-kawo-wuka. Tabbas ya yi laifi amma duk wurin aka rasa mai taimakonsa saboda ba nasu bane. Da abin ya yi yawa saboda dukansa suke babu digon tausayi tana gudun kar ayi masa lahani cikin kuka ta ce,
"Malam na hukunta shi. Yanzu na gama dukansa."
A harzuke ya mayar da dubansa gareta "ni kike fadawa haka? Ni za ki cewa kin hukunta shi?"
"Nufinta a dena dukar mata da. Ai idan baku yi da gaske ba ma ina tsammanin yana daf da komawa dan mace duk da ubansa yana raye." Cewar Deluwa don ta kara zuga shi.
Kafa daya daga cikin 'ya'yan nasa ya daga zai saukewa Abbati a ciki sai ga Inna Mairo ta dawo. Da karfinta ta ce "kwarankwatsa dubu idan kafarka ta same shi sai na tsinewa ubanka gashi nan" ta nuna Mal. Sa'adu "kuma duk ku bar min wuri taron marasa mutumci. Indai mugunta da bakin hali abin yi ne don Allah kar ku fasa." Ta juya ga amaryar Mari "ke kuma da hankali ya isheki da suna dukansa ke ya kamata ki agaje shi ki dauke shi."
Sum-sum matan suka fice aka bar Mari hannunta har kaikayi yake tana son juya Abbati taga yanayin da yake ciki amma ido ya hana. Mal. Sa'adu yana yiwa Jummai tambaya game da halin da Hanne ke ciki sai ga Inuwa a guje da fatanya a hannu.
A kan dansa ya sauke ido ya tafi da zafin nama zai taba shi Inna Mairo ta hana. Ta san zance ya kai gareshi ne yazo dukansa.
"Don Allah Inna ki barni na zane masa jiki gobe ma ya kara..."
Tsakin da Mal. Sa'adu ya buga ya janyo hankalinsa.
"Da raina da lafiyata kake tunanin ba zan hukunta shi ba har sai ka zo? Kodayake kaima gara kayi masa naka domin ya san girman laifinsa."
Ran Inna Mairo ya kai kololuwar baci da yadda Mal. Sa'adu yake nuna rashin mahimmancinta a wurin tana matsayin mahaifiyarsu.
"Ku kashe shi ku huta tunda ban isa ba."
Kamar ya yi kuka Inuwa ya ce "amma Inna har nawa Abbatin yake da za'a ce har ya san mace?"
Juyo masa da Abbati tayi ya ga yadda fuskarsa ke fitar da jini kuma ta fara kumbura sai jikinsa ya yi sanyi.
Zama suka yu jigum sai tashin sababin Mal. Sa'adu har Inna Mairo ta gasa masa jiki. A dakinta ya kwanta zazzabi ya rufe shi. Mari ko dakin bata shiga ba ta zauna a waje har lokacin bata bar hawaye ba. Ana la'asar duka mazan gidan suka hallara a bangaren Inna Mairo. Ita ta soma magana a matsayinta na babba a gidan.
"Kun ga illar wannan almajirancin da karfi da yaji ku ka kakabawa 'ya'yanku yinsa ko?"
"Gidan nan kowa ya san kin fi son matar Inuwa saboda ta dan zauna a birni. Banda haka Inna ba sai kin kushe lamarin addini ba don ki goyi bayanta."
Mal. Sa'adu ne ya yi wannan maganar da gatsali. Kannensa kansu sun yi mamaki duk da ba tun yau yake kokarin nuna ya fita matsayi a gidan ba tunda shi ne namiji.
Da yake mace ce mai saurin fahimta kuma kamar Mari ta jima abubuwa da dama na rayuwar bahaushe musamman na karkara yana damunta, sai kawai ta girgiza kai.
"Malam ni fa ba matar ubanka bace, haihuwarka nayi saboda haka ba zan yarda ka fada min bakar magana a fakaice ba."
Maganar ta dan dake shi sai dai nuna hakan zai iya sakawa kannensa su fara bijirewa umarninsa.
"Gaskiya ce kawai na fada miki. Tunda dai mune maza ki bari muyi magana mu shawarta yadda zamu bullowa lamarin nan."
Shiru tayi na wani dan lokaci sannan ta tashi jiki a sanyaye. Ta san haka suka tashi suna gani iyayensu mata basu da mahimmancin da ya wuce yi ko bari a idon mazajensu. Shi yasa idan sun girma suke raina uwayensu su kuma taka matansu. Sa'adu ya dade da rainata tun mahaifinsu yana da rai. Idan tayi magana ya ce jarumin namiji kenan. Kirjinta ke suya da bakincikin rayuwar da tana da yakinin idan an kokarta za'a iya wadda ta fita dadi. Za ta bari suyi shawararsu ko don kada sauran masu jin maganar tata cikin kannensa su ga suna sa'in'sa suma su bi sahu.
Bayan tafiyarta Inuwa ya yi tsalle ya dire cewa Abbati ya gama karatu a Kano. 'Yan uwansa kuma suka dage suma sai ya koma domin ba zai zauna ya lalata musu nasu yaran ba.
Tabe baki Mal. Sa'adu ya yi har suka gama gardamarsu sannan ya kwalawa Mari kira. Tana fitowa ya ce ta je ta taho da Abbati. Yaron ko tsayuwa akan kafafunsa ya kasa amma haka ta kawo shi ta zaunar.
A zuciyarsa yake jin haushin kowa musamman Mari da ta bari aka sake yi masa duka. Idan ita tayi bai ga dalilin da zai sa ta bari ayi masa dukan da ya kusa ajalinsa ba. Duk yadda zai yi ya bar Kirikasamma zai yi don yanzu ya fahimci bashi da masoyi sama da Munzali. Shi ne farkon wanda bai hada jini dashi ba amma ya damu da damuwarsa. Kamar daga sama kuwa yaji Mal. Sa'adu yana tambayarsa a ina ya koyi wannan dabi'a.
Bai yi wata-wata ba ya ce "Nan."
Inuwa ya zabura ya ce "Nan? Nan garin kake nufi?"
Kai ya gyada da kyar. Muryar Mari ya ji tana kuka a kusa dashi.
"Karya yake Malam. Da a garin nan ne da na dade da sani. Ka yiwa Allah da ManzonSa ka bar shi a gabana."
Basu san bata bar wurin ba sai yanzu. Mal. Sa'adu ya ce da Inuwa ya koreta daga wurin ko kuma shi ya tsame hannu daga abin da ya shafesu. Da rawar jiki Inuwa ya ce ta tafi.
Gani tayi shirunta babu abin da zai haifar sai karin cuta ga danta. Tana mikewa ta hau masifa tana zubar da hawaye.
"Babu inda zani. Haba! Da me kuke so naji ne? Wallahi Allah a Kano aka lalata yaron nan. Idan ya koma Allah kadai Ya san abin da zai zama kuma. Don Allah Malam ka barshi a gida mu saka masa ido."
Galala suka tsaya kallonta kafin Mal. Sa'adu ya yi gyaran murya bayan ya tashi tsaye fuskarsa a hade.
"Inuwa zabi yana gareka. Ko mutumcin gidan nan da addininka ko matarka amma Billahillazi yau dinnan sai ka zabi guda."
Ya girgiza matuka ya kalleta tana tsuma da mugun bacin rai. Ta gaji ta kai makura akan mulkin Hitilan da Mal. Sa'adu yake gwada musu a gidan.
"Mari ki bashi hakuri."
"Ba zan bayar ba! Idan da wanda ya cancanci a bashi hakuri to a bayana yake." Sai kuma muryarta ta karye " Haba Maigida? In rasa Sani wannan kuma ya dawo a haka sannan ka ce in bashi hakuri? To hakurin me?"
"Inuwa matarka bata da kunya."
"Ba dole danta ya yi iskanci ba tana da irin wannan halin."
"Dole ka rabata da 'ya'yanka."
Shawarwarin sauran 'yan uwansa kenan da basu son abin da zai batawa Mal. Sa'adu rai har ya yi fushi dasu. Shi kadai ke sakawa da hanawa a gidan.
Kallonsa suka dinga yi ana jiran jin me zai ce.
"Ki je gida na sake ki saki daya."
Kirjinta ne ya hau dukan uku-uku amma a haka ta kama Abbati za ta tafi bangarensu daukar gyale.
"Sakar min da."
Kallo mai tsayawa a rai ta yiwa Abbati. Kallon da zai yi ta tayar masa da tsigar jiki saboda tarin ma'anoninsa har a shekaru masu zuwa. Za ta iya dafa Izu sittin cewa karya yake yi a Kano ya koyo abinsa. Tun yanzu saboda wasu dalilai ya zabi komawa can akan zama da ita. Duk wani fadi tashinta yau ya katse shi a dalilin haduwa da Munzali.
Murmushin biyan bukata Mal. Sa'adu ya yi. Yau dai ga karshen rashin kunyar Mari. Ba a taba surukar da take turjiya akan umarninsa ba sai ita. Idan ta zauna sauran ma zasu koyi bijire masa. Yanzu kuwa ko ta wane hali ba zai taba bari Inuwa ya dawo da ita ba.
Kafin Magariba ta fita zuwa gidan wani kawunta a garin Maigatari. Inna Mairo har kuka tayi ta umarci Inuwa ya mayar da ita amma yaki saboda maganar Mal. Sa'adu tafi ta kowa.
Bayan sati biyu su Abbati suka koma Kano. Inuwa ya sani ba sai an fada masa ba cewa rabuwa da Mari kuskure ne sai dai kuma ya yarda cewa hana almajiranci sabawa addini ne. Wanda baya son addini kuwa ba abokin rayuwa bane. Shi da 'yan uwansa suka dunguma Karkarna gidan Jummai. Mal. Sa'adu ya sake baiwa mijinta hakuri akan abin da ya faru.
"Kuma matsawar ina raye yana kawo girma za'a daura musu aure. Kai Inuwa ka rubuta ka ajiye. Abbati ba shi da mata sai Hanne."
***
"Wai Ladidi tace ki dafa mata shinkafa da miya, sannan ki tura a sanar da ita da wuri don bata so ya huce."
Kalaman Jiddo kenan ga Nasima tana fada mata sakon mahaifiyarta. Sakuwarta ce sai dai ba ciki daya suka fito ba. Jiddo 'ya ce ga yayar Ladidi daga garinsu Soba. Dan kudin da ake ganin ta fara kamawa tun bayan auren Nasima da Tahir shi ne aka turota cin arziki. A haka duk wani aikin wahala ita take yi musu a gidan.
Kallon wulakancin da ta saba ta yiwa Jiddo, tana jin kamar ta sa hannu ta mare ta saboda takaicin da take kwasa na Ladidi a 'yan kwanakin nan. Ta tsiro da wata sabuwar dabi'a ta cewa anan gidan za ta dinga cin abincin rana. Da ace da hali ma ba dan Tahir ya kan dawo da wuri ba to na dare da na safe ma nan za ta so ta dinga ci. Ita dai ta zauna a saka mata kaset a bidiyo tana kallo tana kwasar gara, ta ce a miko mata wannan a miko mata wancan. Cikin bacin rai Nasiman tace mata
"ki gayamata cewa nima fita zanyi idan na dafa zan aiko mata dashi gida."
Nan Jiddo ta juya ta fice. Ba jimawa ta dawo, tace ladidi tace a bar mata makulli idan ta gama zata tafi da makullin gida idan yaso Nasima in ta dawo sai ta biya can gidan ta karba. Takaici ya sake kama Nasima, tayi kwafa ta tashi ta shiga kitchen ta dauko wata tukunya ta mikawa kanwar tata.
"Gashi nan ki kai mata, ki ce jiya nayi amma na manta ban sa a firij ba shine tayi tsami. Ta saka kanwa in ta gyara miyar, ta dafa shinkafar da zataci."
Tana gama fadar haka ta dangwarar mata da miyar ta koma ciki abinta. Shiru shiru da Jiddo taga bata fito ba ta zari tukunyar miyan ta kama hanyar gida.
Ba dai haka taso ba amma haka nan ta karbi tukunyar rai a bace. Taci burin zuwa gidan Nasiman, gashi akwai wuta taje tai kallo tana cin abincinta a karkashin fanka. Da ta kai tukunya kitchen ta bude taga nama zuqu zuqu hankalinta gaba daya ya tashi, nan da nan ta jiqa kanwa ta gyare miya ta dafa shinkafa ta zauna ta ci. Saboda bakin hali ma bata rage wa kowa cikin yaran nata ba. Ta cinye abincin ta tas, naman ma bata bar musu ba.
Sai dare tukunna cikinta ya soma ciwo, yanata kulululun kuka, kafin asuba tayi gudawa ya kai sau goma. Garin Allah na wayewa, ta sake tura Jiddo a fadawa Nasima bata da lafiya azo a kaita asibiti.
Zazzafan bugun da ake yiwa gate din ne ya tashi Tahir a firgice daga bacci ya fita kofar gida. A nan ya tarar da kanwar Nasima suna magana da Mallam Ado maigadi. Bayan ta gaishe shi ta sanar da shi abun da