Showing 39001 words to 42000 words out of 242549 words
Wannan yasa ya raina Mahaifinsa fiye da tsammani baya ganin girman sa ko na miskala zarratin, tayi fadan, tayi nasihar, ta ja shi a jiki duk dan taga ya aje wannan matsalar ta Tahir a gefe yayi masa kallon uba dan ta san sharrin da ke tattare da kin yin biyayya da kyautatawa ga mahaifa amma abu ya ci tura. Addu'a kawai take yawaita yi masa.
Babban kalubalenta a kan rayuwarsa bai wuce shaye shayen da ya sa a gaba ba domin neman saukin bacin rai. Gashi har yanzu babu alamun dainawa a tare dashi. Sa'arsu daya Ya gama makaranta har yayi bautar kasa. A lokacin Alh. Tahir yaso kwarai ya tura shi yaje yayi Masters a kasar waje amma fir taki yadda saboda ta san cewa a kan idon ta ma ya aka kare da shaye shayen balle idan yayi nesa da ita. Shima kansa baya son tafiyar, saboda gani yake babu wanda ya damu da yanayin mahaifiyar tasu sama dashi. Wannan ita ce rayuwarta da Suhaib. Tana matukar son shi, kusan ma duk cikin 'yayanta tafi nuna masa so da kulawa, saboda yadda tasan yana sadaukar da duk wani abu na rayuwarsa dan ganin murmushi shimfide akan fuskarta.
Bayan ta gama kallonsa tana wannan tunanin, ta maida dubanta ga Farha dake tahowa gare ta. 'Allah sarki Farha', ta ce a cikin zuciyarta. Yarinya kyakkyawa ga kyawun sura. Duk wani cikar zati na 'ya mace da za ayi sha'awa ace ana so kama daga kyan hali, dabi'a, yawan fara'a, ladabi da biyayya, iya girki babu ta inda Farha ta gaza. Amma har yanzu ko da wasa babu wanda ya taba sallama kofar gidan su da sunan manemin aure.
Wannan abu yana matukar damunta yana ci mata tuwo a kwarya. Ita ma Farhan yanzu take bautar kasa amma babu mashinshini kwata kwata a rayuwar ta. A duk sanda ta dubeta tana jin wani irin kunci da bacin rai a zuciyarta. Mai yiyuwa ma abin da mahaifinsu yake wa 'yayan mutane ne yake dawowa kan yaranta. Haka take yawan ayyanawa a cikin zuciyarta.
A bangaren Farha abin itama yana damunta fiye da yadda za'ayi tunani. Sai dai kuma tana nata kokarin ganin cewa iyayenta basu rage ta da komai ba ta dinga nuna hakan bai dame ta ba. Lokuta da dama takan tsinci kanta cikin kuncin rai har takai ga kwana tana kuka da tunane tunane kala kala.
Son auren bai dameta ba kamar yawan tunanin ta ina ta gaza, mene bata dashi da ya janyo mata bakin jini. Ko irin saurayi yazo taji bata so ta kora ma babu. Irin samarin unguwa ma haka ko yan class daya da zasu nuna suna sonka ko da ba da aure ba irin dai school soyayyar nan duk babu. Kawayenta su zauna ana ta hirar saurayi, haka za tayi zugum tana jinsu ba za ta iya cewa uffan ba akai. Daga karshe ma har gani suke ko ta sawa kanta boko ne ganin mahaifiyarta lecturer ce ko itama bokon ta sa a gaba. Zolayarta suka koma yi ana kiranta Farha Boko addini. Sai ta biye musu kawai aka tafi a hakan, kamar da gaske abin bai dameta bane ba ko baya gabanta. Nan kuwa tafi kowa son taji wani ya zo da kokon barar neman soyayyarta. Itama ace yau dai ta taba yin saurayi.
Bayan ita, sai da Mami tayi dogon juyi tukunna da idanuwanta sannan ta hango Lilu can tsaye da abokai. Wani murmushin takaici ta yi a ranta, wato abun da ta kwana tana yi masa fada akai har suka kwanta bacci ta bayan kunnuwansa ya wuce.
Ta rasa gane irin kin ji da masifar kiriniya irinta Lilu. Kunnuwansa kamar an cusa masa duwatsu an toshesu, baya ji kwata kwata. Fitinanne ne na bugawa a jarida. Shima duk sanda ya yi abubuwansa, Tahir take hangowa, takan ga karshen ta abubuwan da yayi ne Allah ya jarabce shi da 'ya'ya haka.
Khalil bashi da tsawo, har takanyi mamakin yanayinsa jikinsa kamar mutumin ruga. Karamin jiki gareshi babu kiba sai fadin rai da jin shi ma ya isa. Ya fi sauran 'yan uwansa kyau har mutane kan ce masa mai baby face.
Da wannan fuskar kamar ta salihan bayi yake yaudarar mutane, idan yayi abu mutane kanyi mamaki har suga kamar ma karya ne ace wai shi ya aikata hakan. Iya saninta game da halayyarsa ta san baya shaye shaye. Amma akwai hulda da abokan banza, har club yana zuwa. Ga kuma azabar son mata har mamakin sa ma ta ke, shekaru ba wani abun azo a gani ba amma idonsa idon mace sai yayi yadda yayi ya tsarata. Ko da bai fara aikata me gabadayan ba to fa ya dau hanya gadan gadan wurin gadon halin ubansa. A gida ma duk wani abu na fitina, ko abun da za ace bari ko wani abu mara dadi a to sunan sa ake ambata.
Yanzu haka da take hangoshi tsaye yake tare da wasu abokansa yana ta zuba zance daga inda take tana iya jiyo muryarsa ana shewa ana dariya. Ga gashin kan san nan yayi wani irin askin gefe da gefe anyi lowcut, tsakiya ya tara gashi kamar kan zakara. Ita dai ta san ba buzu ta haifa ba amma idan ka ganshi banbace shi da buzu tabbas zai baka wahala. Gashin gaban ne ya wani nannade ya kwanta luf luf yana sheki. Wannan ne dalilin fadan su a daren jiya. Tayi tayi ya fadacmata me yake shafawa haka, har tana ce masa idan ma relaxer ya fara sawa to Allah ya tsinewa mai kamanceceniya da mata. Sannan ta ce idan zai zo taron convocation din to ya tabbatar ya aske kansa askin mutunci.
To gashi dai yazo babu askin da alama kuwa har ya fita nuna farinciki ma yadda yake ta shewa da abokai.
Bayan shi kuma sai autar ta Sauda. Ita yanzu suke shirin gama secondary tare da Mardiyan Nasima, don tare aka saka su makaranta.
Sanda aka saka Sauda, duk da Mardiya bata kai shekarun shiga ba haka Nasima ta nace sai an sakata tsabar masifar kishi dake azalzalarta. Matsalar Sauda shi ne raina duka matan Abbansu. Bata ragawa kowa indai zai shiga gonar Maminta. Amma Allah Ya hada jininta da Mardiya. Nasima tayi kokarin ranasu har ta gaji. Sannan sabanin yayarta Farha da ta rasa manema, ita kuma har sun mata yawa. Shi yasa Allah Allah take ma ta gama makaranta ayi mata aure kafin masifar Tahir ya rabe ta. Tunda manema ne da ita ta ko ina babu babba babu yaro kowa Sauda. Ita da ta haifo su ma bata ga da me saudat din ta dara Yar uwarta ba to amma abu na ubangiji baka da ta cewa se Hamdala.
A gefensu kuwa Mardiya ce a tsaye tana murmushin yake. So take ta karaso wurin Mami amma tana jin nauyi. Sauda ta figo hannun kanwarta suka taho tare ta rungume su daya bayan daya.
Mardiya ita ce babban misali na rayayye ya fita a cikin matacce. Iyayenta basu da halin yabo ko daya amma ita dabi'unta ababen burgewa ne. Tana son 'yan uwanta da mahaifi sannan a gefe tana yakin boye mummunan halin mamanta Nasima.
Su biyar Abba Tahir ya mallaka. Ya dauki son duniya ya dorawa 'ya'yansa. Hatta Suhaib da shi kadai ya san boyayyen halinsa yana son abin sa. Duk wani so da gata da barin kudi ba ta inda ya ragesu. Tunda ya yi kudi arziki ya habbaka.
Bayan gama daukar hotuna iyalin suka hadu a motoci biyu. Ta Alh. Tahir ce ta fara fita saboda takura da ya yi da kallon da Suhaib yake watsa masa. Dayar kuwa Lilu ne ya ja su zuwa gida...
Kaddarar shekarun da Alh. Tahir ya diba yana tafka ashararancinsa da 'ya'yan mutane a yau ne za ta rabi dukkan 'ya'yansa. Domin a wannan rana ne Munzali da Abbati suka shigo garin Kaduna akan hanyaWattpad https://my.w.tt/mod4Kht3cab
UWA UWACE...9
Batul Mamman💖
***
Tun kafin ta iso bangaren da 'yan kunshin suke zama wanda yake hanyar kofar fita Anti Hasiya ta san takun waye. Sautin kwas-kwas da takalminta mai mugun tsini yake yi har tsakar kan mutane ake ji. Dunduniyar duka takalman ta cire wurin tsinin sai qusa ke kartar fasassun tiles din da aka saka a wurin . Budurwa ce da take cikin ganiyar shekarun 'yan matancinta. Tana da kyaun kirar jiki da na fuska. Kayan jikinta sun matseta don siket din sai da ta dinga tsalle tana jan shi sama kafin ya shiga. Rigarta kuwa ko anyi rantsuwa babu kaffara kana gani ka san da kyar take sauke numfashi. Ga rabin kirji duk a waje haka ma bayanta. Kanta babu dankwali sai wani yalolon mayafi sa ta yane kan dashi. Ana ganin zara-zaran kalbar da tayi da zaren lilo a cewarta shi ba haram bane.
"A haka zaki fita?" Cewar Anti Hasiya ganin tana niyar fita kai tsaye.
Maimakon amsa Ayaah gatsina fuska tayi ta nufi kofar gidan gadan gadan za ta fita. Anti Hasiya tayi murmushin takaicin wannan hali nata. Wani salon fitsara da rani bata tunawa dasu sai taga tsakar gidansu cike da 'yan kunshi. A lokacin take yunkurin taka matar da take matsayin uwa a gareta don kawai ta zubar mata da mutumci. Bukatarta ta dade da biya domin dadaddun kwastamominta kusan kowa ya san tana da 'yar da take neman fin karfinta ba don a tsaye take ba.
Murja dake gefe tana tata sana'ar ta kitso ta saki kan matar gabanta ta taso a harzuke.
"Ba dake Anti take ba?"
Ayaah tayi mata kallon raini tana jujjuya idanu "ai fa tunda ki ka fara kama matsabbai bakinki ya bude. To haka zan fita uwata ko zaki hana ne?"
Wata mata ta kada baki ta ce "ke kuwa 'yan mata idan baki ga girman yayarki ba bai kamata kiyi haka a gaban mahaifiyarki ba."
Dukan kunnuwanta tayi a tare tana murguda baki hagu da dama tare da farfari da ido kamar sabon kamun aljanu.
"Mahaifiya? Tabdi. To ni mahaifiyata tana kasa Hajiya. Wannan matar..."
"HAJARA!"
Ba Ayaah ba kusan duka matan wurin harda Anti Hasiya kuwa sai da tsawar Honorable ta kada musu ciki.
"Baki da bakin amsawa ne?" Ya sake cewa a harzuke yana tsaye a kofar da ta raba ainihin tsakar gidan da barandar da ake zaman kunshin.
"Gani Baba" ta ce da sauri lokaci guda kwalla na zubo mata.
"Share wadannan munafukan hawayen kizo ki wuce mara kunyar banza."
"Baba gidan Anti Hasina (kanwar A'i kuma yaya ga Hasiya) zani."
"Kin wuce ko kuwa?"
Bata jira ya kuma magana ba ta bi ta gefensa ta shige ciki tana kuka. Dan dukar da kai ya yi ya bawa matan hakuri.
"Ai shekarun nan sai an kai zuciya nesa. Allah Ya shirya mana zuri'a." Matar dazu ta furta da dan murmushinta.
Ciki ya koma zuciyarsa tana tukukin bacin rai. Tsakaninsa da Hasiya yafi kowa sanin cewa ba soyayya bace. Ya sakawa zuciyarsa Allah ne Ya kawota cikin rayuwarsu domin ta zame masa bangon jingina. Idan ya tuna yadda har A'i ta rasu bai taba taka kafarsa gidansu ya gaishe da Innayo ba kunya kan rufe shi. Shi yasa baya ganin laifinta da taki goyon bayan auren nasu har yanzu. A yayinda mutane da yawa marasa tawakkali zasu alakanta aurensa da Hasiya a matsayin silar karayar arzikinsa shi alkhairi ya hango. Ya sani sarai cewa ko uwar 'ya'yansa da wuya ta zauna tsahon shekarun nan tana dawainiya dashi. Ba yadda zaiyi ya raba 'ya'yansa da kakarsu Laraba da kannen mahaifiyarsu amma yana bakincikin alakarsu. Yaji dadi da sauran basa daukar zuga amma Ayaah zugar ce ta tadda hali. Da fada yana fitowa mutum kila ba za ta ganu ba yanzu. A kanta ya fara dukan 'ya'yansa amma kullum dada kangarewa take yi. Shekararta goma sha shida da watanni, yanzu take ajin karshe a sakandire.
Bayan sun shige ciki sai da Anti Hasiya ta dauki mintuna kafin ta ita cigaba da zanawa matar gabanta lalle. Lokuta marasa adadi ta kan ji kamar ta yiwa Ayaah dukan tsiya amma sai ta daure. Maraicinta take dubawa da kuma sanin cewa duk ranar da ta kai mata hannu akwai yiwuwar ta karairayata. Bata iya fushi ba sam. Sai ta dade tana tara mutum kafin ta dauki mataki. Abu na biyu kuwa bai wuce fargabar da take fama da ita akan kalaman Innayo ba. Tana yawan fada mata cewa yadda su A'i suka watsa mata kasa a ido ta tabbatar da wuya idan ba haka su Ummi zasu yi ba. Gashi ita bata haihu ba ma balle tasa rai da samun mai jinkanta a gaba.
'Ba duka aka taru aka zama daya ba. Dan da zai ji kan mutum ba lallai ya fito daga cikinsa ba.' Haka take yawan fadawa zuciyarta.
Daga karfe uku ta rufe karbar 'yan kunshin ranar. Sai bayan la'asar ta gama ta shiga ciki tayi wanka. Ummi tayi abinci ta ci sannan taje ta duba Abbas. Yana yawonsa ko ina sai dai kwakwalwar ce ta dan tabu. Maganarsa ta hankali bata tsayi yake komawa shirme. Kwanakin nan yana yawan tashi da ciwon kai irin wanda yake yi tun bayan hatsarinsu. Ganin har lokacin yana kwance ta koma dakin Honorable.
Kudin da take tarawa ta dauko. Dubu hamsin ne da 'yan kai suka rage bayan sun sayi kayan abinci sannan ta biyawa Ayaah kudin NECO da WAEC. Dubu shabiyar ta cire zata kaiwa Innayo washe-gari. Wata shabiyar din ta bawa Honorable a kai Abbas asibiti. Ashirin din kuma zata rike goma sai goman kai ta siyo kayan lalle. Dama haka take yi duk karshen wata ta raba musu ribarta.
"Hasiya ki bar kudinki. Na yiwa wani abokina dan majalisa magana zai bamu tallafi akai Abbas asibiti a duba shi sosai."
Kin karbar kudin da ya miko tayi, "ka fara kaishi ko magani su bashi na saukin ciwo kafin tallafin yazo."
Da kyar ta samu ya karba a daidai lokacin da suke jin ihun Abbas din cikin azabar ciwo. Da gudu-gudu Honorable ya fita ya samo mai adaidaita sahu suka kaishi asibiti. Sai karfe tara na dare aka sallamosu.
Kafin su dawo saurayin Ayaah ya kawo mata ziyara. Tunda babu idon babba a gidan tayi shiga irin wadda take so ta fita ba tare da sauraron gargadin Ummi da Murja ba.
"Wowwww baby so ki ke ki kasheni ne da wannan kwalliyar? Kin san ina matukar son kwalliya. Ganinki haka ya cire min duk wani bacin rai da na taho dashi." Ya ce tana isowa jikin motarsa.
Kanta taji yayi gingirin ya kara girma saboda tsabar dadin da taji da yabawarsa. Hankalinta kwance ta gillo masa karya da suka soma hira saboda yadda da soyayyarsa da tayi.
"Babanmu ya ce ka fito."
Sarai ya fahimceta sai ya bagarar ya gyara tsayuwarsa.
"In shigo dai ko Baby?"
Kallonsa tayi da rashin fahimta ta ce "ka shiga ina?"
"Oh, ba kina nufin na shiga ciki mu gaisa bane?"
Da saurinta ta gyara masa "nufina ya ce ka turo ayi magana saboda asa rana."
Rabeel sai ya mike tsaye da kyau yadda za ta ga tsayinsa ya daure fuska yana jera mata tambayoyi "amma ba dai ce masa kika yi mun tsayar da maganar aure ba ko? Yaushe muka hadu? Ke da kike karatu me zaki yi da aure?"
Tsoron kar shi ma ya kufce kamar sauran yasa ta kwantar da murya tana bashi hakuri
"Dama ba wai auren za a daura yanzu ba. Kawai dai don ya san da kai ne kafin na gama makaranta."
Kofar motarsa ya kama zai shige yana sababin da ya kwana biyu yana neman damar yi. Ya gaji da gafara sa bai ga kaho ba. Ta kware wurin kwadaita masa jikinta da irin shigarta amma taki bari ya dara daga rike mata hannu. Ya zata a waye take yazo kwasar ganima ashe kidahuma ce. Ga damar sulalewa ya gudu ya samu ba bata lokaci kuwa ya cafketa.
"Yadda bana son a katsewa kannena mata karatu kema ba zan katse miki ba. Na zata Baba zai yarda kiyi zurfin ilimin da zamu yi alfahari dashi ni dake da 'ya'yanmu amma na fahimci ba haka ba. Tunda da wuri yake son aurar dake gaskiya ki nemi wani."
Hankalin Ayaah in yayi dubu to duka ya mike tsaye. Bata da burin da ya wuce tayi aure ta bar gidansu. Gwaggo Laraba dama ta fada mata Anti Hasiya ce ta hana Murja da Ummi aure sannan sun kasa shiga jami'a. Daga mai dinki Ummi sai Murja dake kitso. Ga babansu ta hana arziki ya zauna masa domin ta juya shi. Shi yasa ita ta dage da karatu sosai don ta sha alwashin shiga jami'a. Abin kaddara duk kokarinta bata ci kwalifayin (qualifying) ba shi yasa Anti Hasiyan ta biya mata kudin NECO da WAEC. Ta fara murna wannan saurayin sun yi wata biyu shi ma yana shirin subucewa.
Murmushi ta kirkiro na dole ta ce "Lahhh, wasa fa nake maka. Baba so yake na zama likita ma."
Ai kuwa ya hade girar sama da kasa
"Ayaah ni kam ba zan iya hada inuwa da makaryaci ba. Kamar baki san haramcin karya ba ki kalleni ki yiwa mahaifinki karya da sunan wasa?"
Hawaye ta soma tana bashi hakuri ya shige motarsa yaja. A ransa yana cewa ta fiye bakin naci. Tun satin farko da yazo ya fahimci ita aure kawai take so.
"A nemi wani wahalallen ba ni ba" ya ce yana dukan sitiyari.
Kamar kiftawa da bude ido Ayaah ta neme shi ta rasa. Kuka sosai ta fashe dashi tana mai gasgakata Gwaggo Laraba. Lallai bokan Anti Hasiya ya iya aiki. Yanzu yanzu ta fito yana dariya amma ko rabin awa basu yi ba ya tafi.
Rabeel bai zame ko ina ba sai gidansu abokinsa Danliti wanda ya bashi aron mota. Waya yayi masa ya fito karbar makulli.
"Amma Rabilu yau kayi sauri ko baka sameta ba?"
Dariya ya yi sannan ya kwashe yadda suka yi da Ayaah ya fada masa.
"Kuma sai ka barta?" Cewar Danliti da mugun mamaki.
"To zama kake so nayi a sani auren da ban shirya ba?"
"Kai dai gaula ne. Irinsu ai da sa musu rai da aure ake moresu. Yarinya danya shakaf kamar wannan ka tsallake ka barwa wani?"
Maganar ta shigi Rabeel ya cije yatsa yana maganar 'yan tasha yadda ya saba "ban yi tunani ba Yasin. To yanzu meye shawara?"
Danliti ya lashe lebensa na kasa "sa'arka ta kare saura tawa.