Showing 69001 words to 72000 words out of 242549 words

Chapter 24 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3372

guguwar da ta tunkaroku da wannan niyar taku bala'i ce..."

Kwalla ce mai zafi ta cika idanun Abbati har ta soma saukowa bai sani ba. Ko gezau bai ji ba da ya ce za'a iya kawar dasu a doron kasa. Amma maganar tonon asiri ta kada hanji da hantarsa. Kafin kowa ya fado masa a rai sunan mahaifiyarsa ya soma amsa kuwwa a kwakwalwarsa. Wallahi ya gwammaci tayi arba da gawarsa da dai ta sami labarin yadda yaci zamanin kuruciyarsa da silar arzikinsa. Zuciyarta za ta iya bugawa amma ba wannan bane kadai matsalar. Yana ji kamar ko a lahira Baaba Mari ba za ta yarda ta hada hanya dashi ba bare har ta yafe masa ya sami rahamar Allah. Zinar da bata so yake aikatawa. Mafi muninta ma. Sannan ya kasance bashi da maraba da karuwa mai biyawa mutane bukata a biyata.

Budar bakinsa zai yi magana sai hawaye ya soma ambaliya a kuncinsa. Bai damu da hana zubarsu ba.

"Ni kadai zan iya zuwa?"

"Me kake nufi?"

Abin da zuciyarsa ta karanto masa a matakin karshe ya furta. Abin da yake jin shi ne karshen soyayyarsa ga Munzali.

"Sirrina iyayena kadai zai batawa rai amma kuma ba ni kadai suka haifa ba. Zuwa wani lokaci zasu iya mantawa. Amma Munzali uba ne. Ba Qibdiyya ba ina jin har jikokinta idan ta sami mai aurenta kenan sai an goranta musu."

Shazali ya murmusa yana danne dariyar da ta taho masa. A wannan fagen karan Munzali ya kai tsaiko amma Abbati ne tauraron shi ma ya sani (wa iyazu billah). Bashi da asara indai Abbatin zai cigaba da zuwa yana samun nasa kamshon kudin.

A munafunce ya ce "Ayi haka Abbati? Wahalar za ta yi maka yawa."

'Qibdiyya batayi laifin amsa sunan diyar fasiki mai neman maza ba' wata karamar murya ta jaddada masa. Sannan yana da yakinin cewa idan Munzali ne a wannan gabar abin da zai zaba kenan. 'Kila ya hada da kaiwa Shazalin naushi ma kafin ya taka martabar' wani sashen ya ankarar dashi.

Shazali shigewa ya yi gidansa bayan ya fada masa cewa gobe da sassafe zai bar garin don ba zuwa ya yi domin ayi wani nadin sarauta dashi ba. Bai damu da hana shi shigar masa gida ko jin zafin maganar ba. Masifar da ya kunna masa tafi komai daga masa hankali.

Bayan shekara da shekaru cikin jindadi da fantamawa da kudi Abbati ya sami kansa da shiga tsakar da kudi ba zai maganinta ba. Kuka ya soma a hankali har yaci karfinsa ya durkushe a wurin. Su suka cuci kansu ko rayuwar da aka jefasu a kuruciya? Sanda suka farga da illar abin kuma komai ya lalace sun saba.

Ya san bai yi kuskuren ceton Munzali ba domin shi kadai ke fada masa yaji. Tunda ya samu ya amince zasu bar komai tare bai dace ya dawo dashi ruwa ba. Bayan shi Munzali bai dauki wani abu da daraja ba sama da 'yarsa. 'Shin akwai adalci idan na bari mutumcin uba ya zuba a idon 'ya kamar yadda na kakanta ya zube a idon dansa?'

Ya furta daidai jin kunnuwansa a yayinda hawaye masu dumi suka makanta ganinsa. Runtse ido ya yi suka sauko zuwa kuncinsa.

*

Washe gari har akayi nadin a fada suka dawo nan kofar gidansu Abbati domin yin walima Munzali bai ga walwalarsa ba. Hasalima tamkar gangar jikinsa kadai ke tare dasu amma shi yana wata duniyar daban. Munzali sai ya takura shi ma fara'a ta dauke masa.

Da suka shiga ciki ne a dakin Baaba Mari danginta suna yi masa addu'a ta tuntubi Munzalin game da abokinsa.

"Kace masa ya saki fuskar don sarauta ba tana nufin dinke fuska kamar damammiyar fura ba."

Tayi ne domin ayi dariya kuma kowa ya dara banda Abbatin. Allah Yasa fuskarsa nade take da rawani sai ya dan dukar da kai saboda dariyar tasu kuka ta kusa saka shi. Gani yake idan ya yi dariya tamkar yana maraba da cigaba da wannan sabon ne. Bai yi aune ba hawayen da bashi da niyar zubarwa suka soma diga a gaban farin rawaninsa.

Munzali ya matso kusa dashi ya dago kansa sai kawai ya fashe da kukan. Wannan wace irin rayuwa ce suka tsunduma kawunansu ciki gashi fita ya zame masa matsala. Ta ina zai fara ambaton sunayen mutanen da ya sani ta wannan hanya? Waye zai yarda dashi kafin azo batun taimaka masa?

"Don Allah Baaba a dan bamu wuri" cewar Munzali idanunsa sun kada sun yi ja. Bai san damuwar Abbati ba amma ya san cewa duk damuwar danuwan nasa tasa ce shi ma.

Da kanta ta sallami matan dakin ana ta gulmar abin da ya saka shi kuka a wannan lokacin. Wasu har sun fara cewa dama akwai masu harin kujerar me yiwuwa asiri aka fara jefo masa.

Jiki a sanyaye Baaba Mari ta ce "Me ya same ka har ka ke zubar da hawaye a gaban mutane haka?"

Munzali ma zuba masa ido ya yi shi kuwa sai ya ce "Baaba ji nake dama ban karbi sarautar nan ba. Haka kawai hankalina bai kwanta ba ina ganin kamar wani nauyi na karba. Kasa daurewa nayi da na tuna abubuwan da Liman ya fada min akan hakkin mutane."

Murmushi tayi ta koma ta zauna "Nauyi ne mana Abbati. Amma da yardar Allah da kuma addu'armu za ka rike amanar da aka baka. Kai dai ka yawaita addu'a da kuma kiyaye hakkokin Allah."

Nasiha sosai ta dinga yi musu mai ratsa jiki har Munzali ya dinga jin muguwar tsanar kansa. Wannan mata mai kyaun hali ya cutarwa da d'a ta hanyar koya masa mafi munin zina. Kukan da ya dinga yi bai da alaka da zantukan Abbati don ko kadan bai yarda ba. Nasa laifin ne ya dame shi yaji kamar da biyu take magana.

Da ta kare maganarta ta sako zancen hakkin Hanne.
"Idan kun tashi komawa jibi ka tafi da matarka. Wannan zaman da take ya isa haka. Yana daga cikin dalilan da suke ta kawo rikici a gidan nan. Sannan kaje na yarje maka ka takawa Deluwa birki haka nan. Na gaji da shari'a ba gaira babu dalili."

Dan murmusawa ya yi ya mata alkawarin cika umarninta sannan suka tashi zasu koma waje. A daidai soron da zai sadasu da matasan da suka yi dafifi a waje Munzali ya ce,

"Ga fa mutanenka suna jiranka Ya Sardaunan Makaryata."

Da sauri Abbati ya dube shi sai ya ga ya dinke fuska.

"Ni kake kira makaryaci?"

"Kar ma ka fara sha min kunu don ka san gaskiya na fada. Yadda ka ninke Baaba Mari ni ba za ka min ba. Tun fa kafin aje fada nake tambayarka damuwarka kaki fada yanzu ka zo kana zancen wai maganar Liman...maganar da ko awa daya ba ayi da yinta ba."

Da yake bashi da kuzarin rigima da Munzalin sai ya bashi hakuri kawai.

"Da ciwon kai na kwana ga case din Hanne da maganar Inna Deluwa da 'Yashshafanta..."

"Duk kuma so kake na yarda da abin da ka ce ko? Zan kyaleka dai sai mun koma"

"Nagode. Kuma Allah Ya kaimu abubuwa su daidaita sai na gurje bakinka. Wai ni kake kira makaryaci. Wallahi Munzali ka raina ni. Ko rawanin kaina bai isa tsorataka ba?"

Dariya suka yi baki daya sannan Munzali ya daukesu selfies a wayarsa suka fita waje.

*
Kwana biyu da dawowarsu Kano Hanne taga canjin kulawa daga wajen Abbati. A nata tunanin ayyukan malaminta ne suke ci. A bangarensa kuwa ya zabi daukan shawarar Baaba Mari ta sauke nauyin da ya dauka na matarsa da mutane. Babu soyayyarta ko digo a ransa amma akwai kyautatawa. Yana sa ran samun canjin halayya gareta sakamakon gyara zamantakewarsu da ya dauki niyar yi. Ita din ce dai ban san alkiblar da take fuskanta ba balle ya gane inda ta dosa.

Yau da sassafe suka fita tare da Munzali duba fili. Sun yi ta tufka suna warwarewa kafin su yanke shawarar gina makarantar boko primary amma Islamic oriented (wadda tafi bada karfi a fannin addini).

Tunda suka fara tafiya Abbati ya zurfafa a tunanin yadda zai yi ya sabule ya tafi Abuja saboda kiran da Shazali ya yi masa da safe. Munzali ya gaji da janyo hira yana barinsa da zance shi kadai. Ga kauce-kauce akan maganar damuwarsa ta Kirikasamma.

"Wai kuwa ka samu ka karbi nambar Farha a wurin Mardiyya?"

Saukar guduma maganar tayi masa. Farhan da ta hana zuciyarsa sakat amma ya kasa kiranta bayan Mardiyya ta turo nambar saboda kyamar kansa da yake. Me zata yi da kazami irinsa wanda ya zama bolar masu kudi? Idan ya aureta anya bai cika mugu kuma mara imani ba? A da dai da ya zata tubansa mai sauki ne ya kudiri niyar hada rayuwarsa da tata amma banda yanzu.

Kallon mamaki Munzali ya dinga yi masa. Kwanakin nan ya rasa abin da yake damun Abbati. Kullum suna tare suna shawarwarinsu amma iyakarta kenan. Shi ya san ba Abbatin da ya saba dashi bane. Wannan bashi da aiki sai yawan tunani da damuwar da ta fito baro-baro akan fuskarsa. Ya gaji da wannan sabon yanayin da ya jefa shi wasiwasi da tuhumar kansa ko shi ya masa laifi. Tanadin da ya yi musu wanda a ka'ida zai shawarce shi ma ya kasa fada masa. Kudin da suka samo a Abuja kaf ya kwashe nasa miliyan goma harda ciko ya tura wani asibiti mai zaman kansa a kasar Italy. Asibitin ya shahara wurin canjawa mutane halittar jinsi kazalika suna da bangare guda da yake gudanar da theraphy na masu son komawa yadda suke. A bincikensa ya gano wannan bangaren zai iya taimaka musu wurin kawar musu da sha'awar da za ta iya mayar dasu ruwa. Har magana ya yi da daya daya cikin manyan likitocin asibitin domin ya samu gamsashen bayani. Akwai wadanda ake haifa saboda genetic defect su kasance a zahiri wani jinsi a badini kishiyarsa. Sai ka sami zabgegen saurayi da muryar mata yana karairaya (dan daudu). Ko mace da katuwar murya tana tafe tana bokarewa kamar wani dan ball. Irin wadannan yawanci aiki ake yi musu a kwantar da jinsin dake da rauni domin su zama abu daya. Kaso na biyu kuwa wanda a nan suka fada sune 'yan taka haye. Koya musu akayi ta karfi da yaji tun kafin ma su san ma'anar wannan mu'amala. Su ne suke iya aure har su hayayyafa sannan a gefe suna bibiyar 'yan uwan jinsinsu. Matsalar da irinsu kan samu ita ce ta sha'awar da kan taso lokaci zuwa lokaci saboda sabo. Wannan sha'awar Munzali yake son nema musu maganinta domin ya san suna da ita. A yadda ya fuskanci Farha ta tafi da tunanin Abbati ba zai so ko kadan gurbatacciyar rayuwarsu ta baya ta sami kafar nuna kanta bayan ya aureta ba.

Kiiiii ya taka wani wawan burki motar ta yi gaba kamar za ta jefar dasu ta gilas sannan ta tsaya da karfinta a gefen titi.

Sai lokacin Abbati ya yi firgigit ya kalle shi yana kuma dube dube na neman abin da ya kawo haka "lafiya? Birkin ne da matsala ko me?"

Cikin yanayin ko in kula Munzali ya ce "Ko daya. Naga ina ta magana baka ji bane shi ne nayi haka domin dawo da kai duniyar mutane."

"Yi hakuri kan nawa ne ya yi wani wuri."

Haushin boye boyen da yake yi masa ya sanya shi magana da bacin rai
"Wurin da bai kamata na bika ba bare na san damuwarka mu magance ta? Kai ni ban ma damu da na sani ba. Ba dole bane sai ka fada min komai naka tunda dan Adam yana da sirri amma a kalla ka fadawa Baaba Mari ko wani da kake ganin zai tayaka neman mafita."

Kallom tsaf Abbati ya yi masa sannan ya ce "kana nufin akwai abin da kake boye min?"

"Ai ba kai kadai ne ka san ma'anar maganar nan da ake cewa ciki ba'ayi shi don abinci ba kadai. Ka rike damuwarka a cikinka amma wallahi ka daina nunata a gabana. Ba za ka sa kullum na kebe in dinga tunanin matsalarka ba. Ga 'ya muna da ita ga kuma aure nima ina son yi. A bar mutum idan ya kebe ya yi tunanin 'yar budurwarsa mana da hanyoyin tsarata."

'Munzali kenan' Abbati ya ce a zuciyarsa yana murmushi "dan'anace ba dai zan fada maka ba. Da girmana ka dinga kokarin yi min wayo. Wannan blackmail din bai ba, ka koma inda ka koyo ka karbo kudinka."

Dariya sosai Munzali ya yi ganin ya yi nasarar dawo dashi daga ko ma ina tunaninsa ya kai shi. Dan daidaita fuskarsa ya yi ya daina dariyar.
"Maganar gaskiya ko dai har ka fadawa Farha kana sonta ne taki amincewa?"

Goshinsa ya dan matse tare da kada kai
"a'a, ni ne dai ma na fasa saboda bana jin mutum irina dake lullube da kazanta ya cancanci samun soyayyar mace irinta. Don baka ganta bane Munzali amma ko kadan babu alamun shashanci a tare da ita."

Shiru Munzali ya yi na wucin gadi har Abbati ya dinga kiran sunansa. Da ya amsa kwalla ce ta cika idanunsa har tana saukowa. Muryarsa ba rawa ya ce "Abbati za ka taba yafe min kuwa? Ni ne sanadiyar shigarka wannan rayuwar. Na cuceka na cuci kaina cuta mai girma."

Zuciyarsa radadi ta dinga yi masa ta cigaba da magana yana kuka tamkar karamin yaro.

"Na dade ina son rokon gafararka amma sai nake jin tsoron kada ka barni. Abbati ban rasa iyaye ba amma marayu da yawa sun fini gata. Mahaifana basu yi min komai ba a rayuwa sai kawoni duniya. Duk wadanda muka fito ciki daya ina jin Ummakati ce kadai rayuwarta dama-dama. Sauran kannena kowa ta kansa yake yi. Shi yasa bana kyashin basu kudi don kar su nema duk da kudin ba shi zai basu tarbiyya ba. Navso kaina daya akanka tunda nayi amfani da soyayyarka gareni muka dauwama cikin sabo..."

Kuka suke duk su biyun kowanne yana cike da nadama da tsanar kai. Ina ma ana komawa baya da Munzali zai zabi yin bara akan karbar abinci wurin Shazali.

"Ka bar kukan nan haka in sha Allahu zamu sami rayuwa mai kyau a gaba ko babu kudi."

"Wace irin rayuwa mai kyau bayan nayi sanadin abin da zai iya hanaka samun wadda ka ke so?"

Shan kunu Abbati ya yi ya ce "dalla can murya kamar kosasshen zakara ka daina kukan duk ka cika min kunne."

Kyabe fuska Munzali ya yi yana fyatar hanci da gangan "Allah sarki ashe baka tsaneni ba."

"Ban tsaneka ba amma na tsani irin wannan fyace hancin kaima ka sani. Ni ka ja motar mu tafi kar ka sakani amai." Ya dage hancinsa.

Munzali don mugunta sai ya mika masa hannu "to mu gaisa in tabbatar ina ranka ko bayan raina"

"Allah Ya kiyaye in taba hannun da aka kai hanci" ya doke hannun.

Motar tana tafiya baka jin komai sai dariyarsu da fadan da baya karewa kamar mage da bera. Munzali ya yarda damuwar Farha ce ta tsayawa Abbati shi yasa ya yanke shawarar neman Mardiyya ya aura. Da haka zai taimaka ya rabata da mamanta sannan yaji dadin cusawa Abbati Farha har sai yaga an shafa FaI just published "15" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/nvrHssbTfbb



UWA UWACE...15


Batul Mamman💖



Maula Ya Salli Wa Sallim Da'iman Abada
Ala Habibika Khairil Khalqi Kulli himi
MUHAMMADUN SAYYADUL KAWNAINI WA SAQALAIN
WAL FARIQAINI MIN URBIN WA MIN AJAMI

Oh my Master, send your salutations and blessings forever
Upon your beloved, the best of the whole creation
MUHAMMAD IS THE LEADER OF BOTH WORLDS AND OF MAN AND JINN
LEADER OF THE ARABS AND NON-ARABS AND THEIR KIN.

OUR RASUL, OUR HONOUR Sallallahu alaihi wa sallam.




***

"Dakta yaushe za ki sallami matar nan ta room 3 ne? Ba shishshigi zan miki ba amma gara taje gida ta karasa jinyar nan ko don jinjirarta. Yau kwana hudu babu wanda yazo dubiya balle a kawo abinci. Kullum sai dai ta bada naira dari biyu a siyo mata bons da ruwa."

Tafiya likitan take yi da fari amma jin abin da sub-staff (karamar ma'aikaciyar) take fadi ya dakatar da ita.

"Wace mata? Akwai mutum a room 3 ne?"

Dan zaro ido mai aikin shara da wankin bandakin tayi
"Dakta ba dai kin manta da ita ba? Haba ko da naji. Shi yasa naga ba a shiga ashe." Ta fada da tausayawa "Matar nan da ki ka yiwa dinki fa."

Hanyar dakin likitan ta nufa. Tana budewa ta hade rai gabadaya. Dakin zafi ga wani irin kuka da tun kafin su shiga dakin take ji na baby.

"Haj Zara?" Ta ce da mamaki wanda ya gauraye da bacin rai "wata lalurar ce ta sake dawo dake?"

Zara ta dan murmusa tana kokarin tashi zaune amma ta kasa. Bebi dinta tana can gefen gado babu wani lullubin kirki sai cilla kafafu take tana kukan yunwa.

"Ban tafi ba tun ranar nan ina jiran sallama" Ta ce da murmushin yake.

A harzuke likitan ta soma magana ta zura hannu cikin aljihun labcoat dinta ta dauko wayarta
"Tunda nayi miki dinki na ce miki ba zan kwantar dake ba saboda baki zubar da jinin da zaki bukaci kari ba. Ga 'yarki..."

Yarinyar ta dauka ta shafa fatarta da hannunta taji wani mugun bacin rai. Ba ayi mata wanka ba tunda tazo duniya. Layin reception ta kira ta bukaci a lalubo nambar Alh. Unais a file dinsu a tura mata.
Zara na jin haka hankalinta ya tashi. Niyarta ta zauna ranar suna ta koma nata gidan.

"Doctor da kin kyale shi. Zamu iya maneji har jibi sai na tafi." Ta ce a sakarce.

"Anya kina da hankali kuwa? Daga ke har bebinki babu wanka tunda ki ka haihu. Ance bons kike ci kullum ta ina za ta sami ruwan nono mai kyau?"

Bata san hankalin nan da sauki ba a wurin Zara. Tunda aka gyara dinki ta kwana biyu ta soma jin wani irin mugun ciwo a wurin. Idan taje fitsari da kyar take yi ta dan shafa ruwa saboda ciwo. Wuri ya ruruce saboda rashin kulawar da bai samu ba. Kwayoyin cuta na neman kama wurin (infection). Ciwon da take ji ne ya yi tsamari har yana neman taba mata kai. Kwakwkwarar hira da za ta bukaci aiki da hankali yanzu tafi karfin tunanin Zara. Sako daya take fahimta-ciwo.

Alh. Unais na amsa wayar likitan nan ta dinga surfa ruwan bala'i akan sakacinsa da lafiyar iyalinsa.

"Ka zo ka dauketa yau dinnan. Kuma a biya duka kudin kwanakin da tayi."

Ta ajiye wayarta shi kuma ya shiga wurin mahaifuyarsa ya fada mata. Haj.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login