Showing 42001 words to 45000 words out of 242549 words

Chapter 15 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3353

Can zani na gwangwaje son rai..."

"Wannan yarinyar kamar kifi ba bari zata yi ka mori komai ba."

Danliti ya shige motar da ya gyara zai mayar gareji kafin ubangidansa ya fahimci bata kwana a can ba "muje ka rakani na mayar da motar nan na baka satar ansa domin gaba."

***
Jirgin Abuja su Munzali suka shiga. A can suka dauko motarsu wadda suka ajiye a gidan shakatawar daya daga cikin mutanen da suka ziyarta a Lagos. Babu bata lokaci suka kamo hanyar Kano saboda shirin bikin nadin sarautar Abbati sati mai zuwa.

"Wai kuwa ya maganar mai yiwa Qibdiyya alkyabba ne? Ka tabo shi mana muji idan ya gama mu tsaya a Zariyan" Abbati ya tambayi Munzali suna daf da shiga Kaduna.

Da sauri Munzali ya dauki waya ya kira mutumin da ya bawa aikin dinkunansu shi da Abbati da 'yarsu. Telan kwarrare a dinkuna irin na kayan sarauta. Kwatanta musu wata plaza ya yi mai suna Diamond plaza.

"Kwananmu hudu da kama shago a nan mun baro Zariya. Ban fada maka bane Alh. Munzali saboda idan na gama da kaina zan kawo muku Kanon."

"Ka gama na Qibdiyya? Babanta ya dameni wallahi." Munzali ya ce yana dariyar hararar da Abbati ke jefa masa.

"An hada komai saura takalman."

"Zamu biyo"

***
Sau biyar Mardiyya tana kin daukar wayar Mamanta Nasima saboda tsoron me zata ce mata. A na shidan sai ta tura mata text wanda yasa da kanta ta kira a tsorace.

(Idan baki dauka ba zamu hadu ne a gida. Shashasha mara mutumci.)

Ringing din farko Mama Nasima ta dauki wayar ta fara surfa mata zagi.

"Saboda baki daukeni a bakin komai ba ki ka shirya ki ka bisu ko? Tun ranar da babanki ya fada ban ce babu inda zaki ba?"

Mardiyya sai ta wayance kamar bata ji me ta ce ba "Mama muna hanya"

Rai a bace ta ce "Au, baki ma ji me na ce ba kenan. To ki ce su saukeki a shago yanzun nan."

Mardiyya ta kashe wayar ta taba Sauda dake gefenta.
"Mama tana nemana a shago."

Sauda ta dan zura kanta gaban motar ta ce "Ya Lilu don Allah mu biya shagon Mama a ajiye Mardiyya."

Bai so ba sai dai kuma Mardiyya tafi karfin haka a wurinsa. Tana kaunar 'yan uwanta suma suna sonta ciki kiwa harda Suhaib.

"A ina yake?"

"Diamond plaza" Farha ta bashi amsa.

U-turn ya yi ya koma titin da suka baro domin sun bar hanyar plazar a can baya. Farha ce ta kira Mami Khadija ta sanar da ita inda zasu fara zuwa ta ce babu matsala. Ta ma jidadi domin abin da take son yiwa Alh. Tahir zai fi a bayan idon 'ya'yansa.

Suna shiga harabar plaza din Lilu ya hango wata jar mercedes benz ya daki sitiyari yana dariya.

"O.M.G! Wayyo Ya Suhaib mintsine ni na farka."

Suhaib ya girgiza kai yana dan murmushi "kana da matsala Lilu. Yanzu zaka yi sauri mu ajiyeta ne ko mota zaka tsaya kallo?"

Kallon rashin yarda da maganar da ta fito daga bakinsa Lilu ya yi masa.
"Mercedes benz E class, E dinma 350. Ya Suhaib dream car dina ce fa kake yi mata kallon raini."

Su Farha dake baya suka bushe da dariya don Lilu kamar zai yi kuka.

"Tunda dai iyakarka da ita bai wuce dream din ba ai shi kenan." Ya zura hannu ta taga ya dagawa motar da ta sha tint glass hannu "ke dream car Lilu na gaisheki."

"Ya Suhaib ka sace min gwiwa. Burina na mallakin motar nan kasa kafa ka dagargaza da wannan abin da kayi."

'Yan matan suka cigaba da dariya yayinda Lilu yake ta mita kamar ya ari baki. Kusa da motar yaje ya yi parking yana cewa sai ya shafata ko za ayi kararsa.

"Muje na raka ka Lilun Mami." Farha ta ce hannunta a jikin hannun kofa.

Mardiyya ta janyo hannun Sauda bayan ta fito daga motar.
"Zo ki rakani muma mu taba."

Kamar ba su Suhaib yake kira ba duka kannen nasa suka fice suna dariyar yadda jikin Lilu ke rawa yana zaro wayarsa. Jingina ya yi a jikin motar ya gyara kwalar rigarsa. Farha ya mikawa wayar ta karba tana murmushi.

"Allah Sarki 'yan matan KASU zasu shiga uku da hotunan karya."

Yana zura hannayensa a aljihu idanun Abbati dake zaune a mazaunin direba yana ta dariyar hirarrakinsu suka sauka akan Farha.

"Ya Ladif" ya sami kansa da furtawa a hankali yana shafar sumar kansa da take shan gyara.

'So ne? Wannan ce soyayya?'

Karon farko a rayuwarsa mace ta burge shi. Mace ta dauki hankalinsa. Ganin Farha ya yi tamkar tauraruwar da wata ba ya cika sai da kasantuwarta kusa dashi.

It was love at firI just published "10" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/ZvVtc6Nojab




UWA UWACE...10

Batul Mammanđź’–




Allah don isar da tafi kowacce isa
Allah don mulkin da bashi da wa'adi
Allah don rahamar da bata yankewa
Allah don girman zatinKa
Allah don kadaitar mulkinKa
Allah don buwayarKa
Ka karawa Annabi SAW daraja
Ya Rabbi mamallakin sammai da kassai Ka kare mana zuri'a daga dukkan sharri.
Ya Allah Ka karesu daga sharrin masharranta da sharrin kawunansu domin hakika kowane dan Adam akwai dabi'ar da aka halicce shi da ita mai kyau ko akasinta. Ya Allah kar Ka buga misalin Allah wadai damu ko 'ya'yanmu.
Ya Allah Ka azurta iyayenmu da mafi girman daraja da daukaka daga cikin AljannarKa. Allah Ka yafe musu, Ka jikansu, Ka kara musu lafiya, Ka kyautata halayensu, Ka inganta mu'amalarmu dasu da kuma sauran mutane. Amin


RABBIR HAMHUMA KAMA RABBAYANI SAGHIRA




***

Babu sautin da kunnuwan Abbati suke ji sama da bugun zuciyarsa. Sassanyan murmushi ya kufce masa a lokacin da ya dora hannun damansa akan kirji saitin zuciyarsa.

"Ya Farha kawo kema na dauke ki" muryar Lilu ta katse tunaninsa.

"Farha" ya gwada kiran sunan akan harshensa.

Daga wajen murmushi tayi wanda ya kara narkar da zuciyarsa ta ce
"Haka kawai ina tsaya masu motar su fito a tsareni in sha kunya."

Mardiyya da Sauda ya dauka har lokacin Munzali bai fito daga wajen tela ba. Farha ta gaji da surutunsa na rokon ta dauka ta jingina da motar bangaren direba.
"Irin abin nan zanyi kamar nice mai motar na zo shopping."

Hannun ta kama kamar za ta bude, Lilu ya saita ta zai dauka Abbati kuma ya cire lock. Tana dan daga handle din kofar ta bude. Daga ciki ya turota ai sai ta gigice su duka hudun suka kwasa a guje suka nufi shagon Mama Nasima. Suhaib na ganin haka ya fito daga mota da sauri. Wurin Abbati dake tsaye yana dariya ya karasa ya mika masa hannu.

"Don Allah kayi hakuri"

Abbati ya saki fuska sosai "ni zan baka hakuri saboda na tsorata maka kanne. Muje na tayaka kiransu" ya nuna hanyar matattakalar da suka hau.

"Kar ka damu na san inda suka je" Suhaib ya bashi amsa yana hawa benen. A ransa yake ayyana mutumin yana da saukin kai duk kuwa da cewa kana ganinsa tun daga sutura har fatar jiki ka san akwai kudi.

Shagon Nasima da take sayar da kayan kitchen suka shiga. Allah Yaso babu kwastoma ko daya a ciki sai 'yar budurwar dake tayata aiki. Mardiyya ce ta fara shiga ta hau ta da fadan da ta fara a waya.

"Tsinannen yawo da rashin kishin uwarki yasa ki ka bijerewa maganata ko? Wace uwar za a baki a wurin da yasa ki fita da sassafe kafin na tashi?"

Tuni idanun Mardiyya suka kada suka yi ja tana shirin yin kuka. Farha, Lilu da Sauda sai suka yi turus. Mama Nasiman kanta ta dan ji kunyar ganinsu amma sai ta fuske.

Fuska ba wani annuri ta ce "yau kune a nan? Ince dai lafiya."

"Lafiyar kenan. Kanwarmu wadda babu mai iko da ita sama da Alh. Tahir mahaifinta muka kawo" Lilu ya bata amsa shi ma fuska a hade.

"Rashin kunya zaka yi min? Khadija ma..."

"Wallahi kar ki soma. Da fa bamu san asalin balbela bane." Farha da bata da hayaniya ta ce a tsiwace. Ita da 'yan uwanta basa gani su kyale in dai abu ya shafi mahaifiyarsu.

Mardiyya kuka ta saka. Ita ma ta san labarin auren cin amanar da mahaifiyarta tayi da babansu. Ba dai su san da maganar suna neman juna ba amma sun san mai'aikin gidan ce. Haka zalika sun san Anti Jiddo 'yar uwarta ce. Sauda ma kukan take tayata. Ana haka Suhaib ya shigo. Mama Nasima ta nuna masa kannensa cikin bacin rai.

"Ka fita dasu kafin na kira Alhaji. Ba zan yarda ku zo har nan ku min rashin kunya ba."

Da ido kawai ya kallesu suka fice daya bayan daya.
"Kiyi hakuri"

Ya ce da ita bayan sauran sun fita. Maminsu ta gargade shi sosai akan yiwa matan babansa rashin kunya. Mota suka nufa ya karbe mukullin daga hannun Lilu. Bai ce dasu komai ba yaja suka tafi. Suna fita Abbati da Munzali suna shiga shagon Mama Nasima.

Yawun bakinta taji ya kafe ta nemi na hadiya ta rasa saboda ganin matasan masu kudi a gabanta. Komai da komai na suturar jikinsu da ido ke gani iri daya ne. A cikin 'yan dakiku ta gama lissafin tsadar kayansu ta gane sun tsallake raini nesa ba kusa ba. Harara ta gallawa Mardiyya wadda take jin zafin zuwanta a mace gashi bata sake haihuwa bayanta ba. Jikinta na rawa saboda rashin sanin daraja da kimar kai ta matsa gabansu.

"Alhaji me ku ke so? Ke Debora miko musu katalog (catalogue) dinnan su duba kaya."

Kamar wani zai rigata da sassarfa ta ce su biyota office dinta. Wani dan daki ne da aka sakaye daga gefe da kofar gilas. A nan take zama idan ta shigo shagon. Waige waige Abbati ya dinga yi yane neman su Farha. Munzali yana 'yar dariya ya tura shi gaba zuwa ofishin Mama Nasima tana fesa airfreshner.

"Tunda ka kawomu ko kofi ne sai ka saya." Ya rada masa a kunne.

Da suka shiga sun sameta tana goge kujerun zaman baki da dankwalin kanta. Murmushi take ta dokawa ta nuna musu su zauna.

"Mardiyya. Ke Mardiyya kawo musu abin sha. Alhaji me zaku sha? Idan babu sai Debora ta sauka ta siyo."

Sai da Mardiyya ta goge hawayenta ta taho zuciyarta tana zafi. Haka ta tashi ta fahimci mahaifiyarta tana bare-bare da zubar da mutumci gaban masu kudi. Idan ta sansano kudi a jikin mutum to babu ya shi a wurinta. Yaro sa'an Mardiyya ma sai ta duka masa. Neman kudi take kamar tayi sata. Tunda bata da magajin da zai tatso mata da yawa a jikin Alh. Tahir sai ta fake da kasuwanci tana kwasar kudi son rai. Duk da haka tana son kasuwancin domin yana hadata da manyan mutane.

Shigowar Mardiyya keda wuya idanun Abbati suka sauka a kanta. Murmushi ya yi sosai.
" 'Yan mata ashe nan ku ka gudu. Dama ku muka biyo. Ina 'yan uwan maki?"

A darare ta kalli Mama Nasima sai taga ta kyafta mata ido da sauri. Da dariya ta ce dasu "Ba dai Mardiyya ku ka biyo ba? Ikon Allah. Ai 'yata ce ta cikina. Waye surukin nawa a cikinku?"

Mardiyya ji tayi ina ma kasa za ta tsage a lokacin ta shige ciki. Daga ganin mutane ta kasa zaune ta kasa tsaye.

Ita kuwa Mama Nasima ko amsa bata jira sun bayar ba ta dora da cewa "zo ki zauna bari na kawo lemon da kaina."

Da taga Mardiyyan ta kasa daga kafa ma saboda takaici ta soma fada "meye haka ne zaki barsu jira kamar sa'anninki?" Ta dube su da dan murmushi "kuyi hakuri fa. Yaran yanzu da ka ce kana son su sai su dinga ganin kamar kun zama sa'anni."

Tana fita Mardiyya tayi saurin zagayawa yadda zata fuskancesu da kyau.
"Don Allah kuyi hakuri da maganar Mama. Sannan kayi hakuri da muka tsaya a jikin motarka."

Murmushi Abbati ya yi yana jin tausayinta. Yanayin abin da mahaifiyarta tayi ba kowa ya kawo masa rai ba sai Munzali. Haka Asabe take gigicewa idan suka je gidan. Yanzu kamar ta goya shi bayan da almajiri take kiransa. Munzalin ya kalla yaga ya yi shiru. Ya tabbata shi ma ta bashi tausayi ne.

"Ga mai motar nan ni dan rakiya ne."

Caraf a kunnen Mama Nasima. Da saurinta ta karaso ta zuzzuba musu maltina mai sanyi a kofunan tangaran da yanzu ta bude daga kwali cikin kayan shagon. Da zata basu har wani dan durkuso tayi wanda ya tsayawa Mardiyya a zuci don takaici.

"Ma sha Allahu. Ai nima mota ta tana nan a waje. Zaku ganta wata koriya koriya nan. 3.8 miliyan maigidanmu ya saya mana ni da kishiyoyina. Mu uku ne nice ta biyu." Ta dan yi shiru na abin da bai kai sakan biyar ba sannan ta cigaba da magana tana tura musu tray din da ta dora kofunan "ku sha mana ai an zama daya. Ya sunanku ne?" Ta kare da tambaya tana doka murmushinta mai ban haushi.

Munzali zai yi magana Abbati ya take masa kafa ya nuna kansa
"Ni suna na Abbati shi kuma Munzali."

Kacokan ta mayar da hankali gare shi "Allah Sarki Alhaji Munzali. Ya su Mummy? Ya fama da jama'a?"

Kasa jurewa Mardiyya tayi ta fice. Wannan zub da kimar ya yi yawa. Abbati da Munzali kuwa da kyar suka danne dariyarsu. Munzali ne ma ya yi karfin halin cewa zasu tafi.

"Kun dai karbi nambar wayarta ko?"

"Yanzu zamu karba" Munzali ya bada amsa yana yin gaba.

Tana ganin Abbati ma zai fita ta dakatar dashi "Alh. Abbati ai da ka jira shi a nan. Sai da irin haka zasu fuskanci juna."

"Haka ne" ya ce yana tsayuwar dole.

Suna fita Munzali ya karbi nambarta. Hakuri ne dai take ta bayarwa ya ce kada ta damu. Nambar ma ya karba ne saboda kiran gaggawa da Abbatin yayi masa. Bai sani ba ko zai bukaci hakan.

A ciki tambayoyi ta tsare Abbati dasu ya dinga bata amsoshin da ya ga dama. Ba jimawa Munzali ya kira shi ya ce mata zasu tafi. Haka ta taso Mardiyya a gaba har bakin mota suka rakosu.

"Ka gaishe da Mummy da Daddy don Allah. Ka turowa Mardiyya nambarsu sai na kira mu gaisa a fara sabawa da juna."

Munzali da Abbati na ganin sun bar wurin suka hada ido suka kwashe da dariya.

"Mutumina ka gaishe da Mummy da Daddy" cewar Abbati yana kyakyatawa.

"Ya kaga Asabe tana amsa sunan Mummy" shi kuma Munzali ya ce yana tasa dariyar.

Sai da maganar ta fito ya yi saurin kallon Abbati ya doki bakinsa da kansa "sorry Abban Qibdiyya Allah subul da baka ne."

Abbati ya girgiza kai "ni dai na fada maka UWA UWACE. Tunda ta kawoka duniya tayi maka komai."

Duk da Munzali yaso daurewa amma sai da muryarsa ta dan yi rawa ya ce "Komai fa ka ce Abbati. Asaben ce tayi min komai?" Wani zazzafan hawaye ne ya sauko masa gashi shi yake tukin lokacin ya share ido da karfi "na rantse maka idan yau za a bani zabi kai zan zaba akan uwar da ta haifeni. Bata damu da komai nawa ba sai aljihu." Yana maganar yana hawaye sosai. Haka Allah Ya yi shi mai matukar son kulawa. Kuma duk yadda ya kai da basarwa ba karamin kwadayin ranar da Asabe za ta nuna masa mahimmancinsa yafi karfin kudi yake ba.

Hawayensa ya tayarwa da Abbati hankali ba shiri ya sake karbar tukin. Shiru suka yi a motar har suka wuce Zariya sannan Abbati ya katse shirun motar.

"Munzali"

"Na'am" ya amsa yana ciccijewa irin na wanda ransa ya baci yana jiran rarrashi.

"Dadina da kai ka ki girma. Ko kunya babu kake faman kuka kamar karamin yaro."

"Allah abin ne da haushi." Kawai ya sake fashewa da kuka.

Abbati yana tuki ya daga hannu ya make shi a kafada "ka min shiru don ubanka. Haka kawai za ka dinga min kuka kamar na dauko rikakken rago."

A take Munzali ya soma dariya ya karkace baki ya ce "ɓaaaaa, ɓaaaaa, ɓaaaaa"

Abbatin ma dariyar ya kama yi. Sai da suka yi mai isarsu sannan ya yi gyaran murya wanda yasa Munzali mayar da hankali gareshi.

"Misali a kawo maka mace da namiji duka kyawawa ace ka zabi daya wanne za ka zaba?"

"Me yasa ka tambaya?"

"Maganar sai mun zauna ka bari muje gida"

"Nifa ka san bana son jan rai kawai ka fada."

Bakinsa ya ji ya dan yi nauyi amma yana ganin dole ya yi magana.
"Munzali yaushe zamu daina wannan sana'ar?" idanunsa akan titi ya cigaba da magana tunda ya samu hankalin Munzalin na gareshi "ina tsoron kada mu dore a haka har asirinmu ya tono mu gogawa Qibdiyya abin da ba zai kankaru ba."

A hankali Munzali ya ce "ka sami macen da ka ke so ne? Ko yarinyar dazu ce da kaimu shagonsu?"

"Ko daya" ya sami kansa da cewa saboda yadda zuciyarsa ta raya masa cewa bashi da tsaftar jiki da ruhin da suka isa bashi dama ya furtawa Farha kalmar so.

"Idan kana so mu daina ka sani ba zan tsallake maganarka ba. Nima fa na san haramun ne amma hanyar da na sani kenan ta samun kudi."

"Munzali bamu da maraba da karuwai fa. Biyawa mutane bukata muke yi su biyamu. Bana so mu tabbata akan wannan abu" ya ce yana dan tsare shi da ido.

Jikin Munzali ya dan yi sanyi. Yana son bari shi ma amma yana tsoron kada haka ya zama dalilin rabuwarsa da Abbati.

"Idan mun daina me zamu yi?"

Abbati ya ce "yanzu zamu ga amfanin adult education (yaki da jahilcin) din da muka yi. Kudaden da muke samu muyi amfani dasu mu bunkasa shagunanmu na kasuwa. Ko mu bude irin super store dinnan ko mall."

"Kai kana sha'awar mata ne?" Munzali ya kasa hakuri sai da ya tambaye shi.

"Na zata bana yi Munzali amma daga baya na gane nafi son mace akan namiji. Nifa sana'a na dauki abin da muke yi sai kuma sabo. Amma ina ji a jikina zamu iya dainawa idan mun sa kanmu. Mu dai yi tunani a kai mu nemi mafita."

Kai tsaye Munzali ya amsa masa sai dai yana ji a jikinsa zasu wahala. Sun girma cikin wannan dabi'a har ta kai da kyar yake iya zuwa ga matarsa. Cikin Qibdiyya ma rabo ne kawai ya sani. Shi kuwa Abbati rashin so da mugun halin Hanne na dauke dauke yasa duk zuwansa gareta baya wuce rabo. Sai gashi 'ya'yan ma basa zama. Dadin dadawa sun saba da rike manyan kudi. Suna cikin matasan dake tashen kudi da 'connection' na sannin manya a yanzu

(Ina so 'yan uwa su sani cewa mutane masu neman jinsinsu kala biyu ne. Akwai homosexuals masu neman jinsinsu kadai. Basa taba sha'awar wani daban. Akwai kuma bisexuals. Sune masu sha'awar jinsinsu walau mace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login