Showing 36001 words to 39000 words out of 242549 words

Chapter 13 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3393

babu damuwa. Qka bar Munzali ana ta sa mishi ruwa lokaci zuwa lokaci, yana samun kulawa mai kyau jikin sa yana kara kwari.

Bayan sati daya kuwa ya koma gidan Shazali, da kansa ya dauke shi a babur dinsa ya kai shi rijiyar zaki wurin gidan da ya sama musu din dan ya gani, a lokacin babu gidaje sosai a wurin. Gida ne ba laifi dan har da dan gate dinsa.

Gidan dubu dari aka kama haya, ya biya dillalai da sauransu de komai ya kama dubu dari dari da arbain sai canjin sa dubu dari biyu da sittin ya mika masa duka.

Ya ce "ga canjin ka ni bazan dauki komai a ciki ba. Ku rike wataran zai muku amfani. Aiki kuma duk randa kuke son ku cigaba da samun kudi to kun san inda zaku sameni."

Ya damka masa mukulli da takardun da akayi cike cike (tenancy agreement) yace gobe kazo ka sameni zamuje kaima ka sa hannu a gaban maigidan a karkare komai da komai.

Farinciki a gurin Abbati a wannan lokacin ma bazai misaltu ba. Ya koma asibitin, ya sanar da Munzali halin da aka ciki. Shi kanshi mamaki ya ishe shi. Yanzu gida ma Abbati ya kama musu kawai don saboda yana jiye masa komawa gaban iyayen shi tunda da idon sa ya gani cewa ba kaunarsa sukeyi ba.

A cikin sati guda suka tarkata suka koma can. Shi dai Munzali ya koma gida Asabe, har ta fara murna tana fadin ashe har an fito da kai, tana neman ta fara mai zancen ko za a samu kudi a wurinsa ko wani abu, yace mata ya samu aiki ne, an basu gida a Rijiyar Zaki da shi da abokin aikin sa, kasuwanci sukeyi zasu dinga tafiya Abuja da Lagos.

Farinciki ya isheta tana ta murna hadi da yadawa Innayo habaici ita uwar mai shi. Danta ya samu aiki zai dinga shiga cikin manyan mutane.

Munzali bai wani jima ba ya tattara yan komatsan sa ya fice ko tunanin ta tasa kaninsa ya bi ya gano inda ya koma bata yi ba. Sannan bata damu da mahaifinsa ya san halin da ake ciki ba.

Shi ko Abbati daman ba abin da ya cewa Malamin makarantar su, kawai shafawa akayi aka neme shi aka rasa. Ya san yanda zaiyi da iyayensa duk ranar da ya koma gida.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Shekaru hudu da soma rayuwarsu su kadai haramtaccen arzikinsu ya bunkasa. Da fari Abbati ya so su bar mu'amala da Shazali amma abu yaci tura. Sun riga sun saba da wannan masifa sannan rashin kudi a hannunsu ba abu bane da zasu jure. Musamman ma shi Abbati da su Mal Sa'adu suka taso a gaba da bani-bani. Lokacin Inna Mairo ta rasu. Deluwa ta zige Jummai mahaifiyar Hanne cewa kudi ne dashi amma Mari kadai yake bawa. Jummai da kullum abin da ya yiwa 'yarta a shekarun baya yake dasa mata jin haushinsa sai ta hau dokin shaidan. Ba dama yaje ganin gida sai sun tatike shi. Bayan Hanne ta tare ya fahimci ashe kukan dadi yake da farko. Da yake a cikin gidansu aka basu daki Deluwa ce ta zama uwardakinta. Hanne har laluben aljihu tana yi masa. Sannan basu da sirri komai sai ta fada mata. Saboda haka duk abin da yazo dashi gidan kowa sai ya sani. Bai isa kuma ya ce babu ba sai zagi ya koma kan mahaifiyarsa. Ita ake dorawa laifin hana shi yi musu alkhairi da karbe komai nasa.
Wannan abu yana ci masa tuwo a kwarya. Dalilinsa kenan na cigaba da wannan mummunar alfasha. A ganinsa da kudin da suke mutuntawa zai samawa Baaba Mari lafiya daga sharrinsu. Yau da wata sana'ar ya koya a wurin Munzali sabanin wannan da kila wani karatun za a biya ba wannan ba.

A bangaren Baaba Mari kuwa da ta fuskanci irin kudaden da Abbati yake facaka dasu musamman lokacin auren kannensa sai da tsoro ya darsu a zuciyarta. Rufo kai tayi bayan an gama bikin tazo har gidan neman Baba Inuwa. Ranar ta sha habaici a wurinsu musamman matarsa da suka dan yi zaman kishi. Toshe kunnuwa tayi a gidan wata makociyarsu da tayi masauki ta jira ya dawo.

"Ni kuwa Malam ka taba zuwa ganin ubangidan yaron nan a Kano? Wace irin riba suke samu har yake iya daukar nauyin abubuwan da suka fi karfinsa?" Ta furta cikin girmama lamarin.

Jinjina kai ya yi yana tunani, lokaci guda shi ma yaji zuciyarsa ta dora masa alhakin rashin binciken dan nasa. Bai kai ga bata amsa ba suka ga Mal. Sa'adu ya nufosu a kofar gidan fakam-fakam yana baza babbar riga.

"Salamma alekun. Kai Inuwa tashi ka wuce gida." Ya ce fuska a murtuke sannan ya kalli Baaba Mari "kin dai ji kunya. Ni tunda nake ban taba ganin rashin kunya irin wannan ba. Ki taso kafa da kafa tun daga Maigatari ki biyo bazawari. Don kin haifa masa yara shi kenan kuma bashi da sauran rayuwa?"

Baba Inuwa har yanzu shi da 'yan uwansa basu da katabus sai abin da yayansu ya ce ya tashi da sauri.
"Ba abin da ka ke zato bane. Magana tazo akan irin kudaden da Abbati yake juyawa da bamu san... "

Hannu ya daga kamar yana magana da dan karamin yaro "kai arrr. Kinibibin matan ne ban sani ba ko me? Ta taho dai bikonka tana so ayi kome tunda ta rasa manemi shi ne za ta fake da sakawa yaro ido." Ido cikin ido ya kalli Baaba Mari tayi saurin dukar da kai "ko kin ki ko kin so Abbati jininmu ne kuma mun fiki iko dashi. Dan abin da yake kashe mana ki ke bakinciki shi ne zaki soma tada zaune tsaye da tsugudidinku na mata. To ahir dinki. Idan baki da kalamin san barka a gare shi ki kama bakinki akan aibata shi."

Ranta in ya yi dubu ya baci. Ta gaji da wannan fin karfi mara fasali akan 'ya'yanta. Auren ma da akayi duka matan a nan cikin gidan ake rabawa'ya'yan 'yan uwa.

"Allah Ya san zuciyata. Yaran nan amana ce Ta bamu nake kokarin saukewa kun hana. Idan har Abbati yana mugun abu ina masa fatan shiriya. Ina addu'a Allah Ya bude idanunku ku gane gaskiya komai tsawaitar lokaci."

"Rashin kunya za ki min?" Cewar Mal Sa'adu cike da mamakinta.

Baba Inuwa don kada ya bata mishi rai shi ma ya hauta da fada "rashin kunya za ki yi masa Mari?"

Bata ce komai ba ta koma cikin gidan da ta fito. Su Baba Inuwa ma suka koma nasu gidan yana jin yayansa yana mayar da zance akanta. Karya da gaskiya haka ya hada ya kara mata bakin jini.

Daga ranar Abbati ya ci alwashin yin kudi sosai domin ya saya mata mutumci a idon duniya. Ya kuma yi sa a. Tunda ragamar gidan ta dawo wuyansa ya koma mai sawa da hanawa. Hatta Mal Sa'adu komai sai ya ce a jira Abbati ya zo.

Da karfin ikonsa yasa aka mayar da auren Baaba Mari da Baba Inuwa. Ita dai bata so ba amma ta dawo ne saboda saka ido akansa.

Zancen da ake yanzu nadin sarautar Sarkin Samari za ayi masa a garin Kirikasamma. Haihuwar Hanne uku duka yaran kafin suna suke komawa. Duk da baya sonta yana son haihuwa. Kudi ne sun tara sun tada kai. An kai iyaye Hajji an rushe gida an sabunta shi. Karafaren gida mai bangare biyu suka saya a Sharada cikin Kano suka tayar da ginin zamani guda biyu iri daya sak.

Kamar Abbati shi ma Munzali da kudi ya sayawa kansa soyayyar iyayensa. Asabe jiki kullum yana rawa akan bukatunsa. Shekara biyar baya ya auri 'yar kanwarta mai suna Zakiyya. Dangi duk sun dawo jikinsa sai yadda ya ce. Daga haihuwar farko suka rabu saboda tana da wayo. Ta matsu kwarai ta gano ainihin sana'arsa. Ganin ta fara zarginsa ya saketa daga zuwa gida wanka. Yarinyar kuwa ya saka mata Mariya saboda soyayyarsa ga Abbati. Komai na sunanta Abbati ne ya yi. Ya bata yarinyar da shagwaba da gata. Qibdiyya suke kiranta. Bata rasa komai ba. Idan suka yi tafiya har gasar yi mata siyayya suke yi. Duk wanda tafi son kayansa ya dinga tsokanar dayan kenan. Tuni suka daina neman juna. Sun mayar da alfashar sana'arsu kadai suna cewq kawunansu idan sun tara da yawa zasu tuba.

Qibdiyya ce farincikin Munzali da Abbati.
Qibdiyya sanyin zuciya da idanuwansu.
Qibdiyya ta kara kusancinsu.
Qibdiyya ce JARABAWARSU!

***
A cikin kunnuwan Innayo aka yi kiran sallar asuba na farko da na biyu amma har aka idar bata iya mikewa daga gado ba. Ilahirin jikinta ke ciwo kamar ana soka mata allurai. Wannan yana da nasaba da ciwon hakorin da take fama dashi tun shekaranjiya. Mukamukinta na dama, bangaren hakorin mai ciwo ya kumbura suntum. Uwa uba kwanakin nan saboda zafin da ake fama dashi kusan kullum da ciwon kai take kwana ta wuni. Taje asibitin sha-ka-tafi na unguwar satin da ya wuce an ce jininta ya kuma hawa. Ba dole ya hau ba?!

Ita kadai take kwana ta wuni kamar mayya. Rayuwarta a matsayin matar aure suna kawai ta amsa amma babu alamunta idan ka cire rabon 'ya'ya. Asaben ma bata gaban Alh. Rabi'u. Shi dai ya ci banza da hofi a titi ya zauna gulma a majalisa. Idan ya dawo maigirki ta mika masa abinci idan ya ga dama ya tsakura. Dan na cefanen ma ya daina basu, a cewarsa 'ya'yansu sun kawo karfi.

Lamarin Uwani har yanzu da take matsayin Metiron (matron) a asibitin Nasarawa bai chanja zani ba. Sai an kai ruwa rana ihsani ke giftawa tsakaninta da Innayo. 'Ya'yanta kuwa basu saba da kakarsu ba. Da wahala ta saka su a ido. Idan ta leka gidan saboda dadewar da Uwanin take bata zo ba sai ace suna makaranta.

Maimuna da Salima ba cas ba as! Saboda tabarbarewar rayuwarsu da ta 'ya'yansu Innayo ta kasa daina sana'a. Ranakun da jikinta ya motsa ne kadai bata 'yar tsala. Cinikin a jikinsu yake karewa. Nasu 'ya'yan suna yawan zuwa domin a wurinta sun fi samun abin ci. Idan sun zo ba komai take karuwa dashi ba sai dadin wahala. Amma haka take jurewa da wasa da dariya su tayata aikin abincin ta basu su ci su kaiwa uwayensu.

Zara? Hmmm, babu abin da ya canja a tattare da ita sai kudi da mijinta ya sake yi. A yanzu haka har gidan mai gareshi. Ga shaguna da motocin haya. Yana sakar mata sosai amma kunyar a dinga rabata da Innayo yasa sai ta dade bata waiwayeta ba. Ya kara aure kuma matar 'yar masu kumbar susa ce. Idan ana taro 'yan uwan surukan gidan suyi ta shiga da fita cikin kayan alfarma ana kece raini. Ita da bata da na nunawa sai ta zabi kawai ta rayu babu su da dai su matso jikinta taji kunya.

Su duka hudun nan Innayo tana zubar da hawaye akan rayuwarsu ta yanzu sabanin mafarkinta. Sai dai duk kukanta a kansu bai kai wanda take yiwa Hasiya ba.

Tarihin da take gudu ne yake maimaita kansa akan 'yarta mai jin kanta. Hon. Habu ya shiga gagarin 'yan siyasar da aka daina damawa dasu kafin shekara da aurensa da Hasiya. Kan kace kwabo ya sayar da duk wata kadararsa sun dawo rungumar hannu. Ga Abbas a kwance har yau jiki yaki lafiya. Hasiya sai ta koyi kunshi take yi a unguwa. Sannu a hankali tayi suna mutane suke zuwa sosai. A rana sai ta sami dubu biyu ko uku. Idan satin biki ne kuwa har takwas tana hadawa. Lallen nata dari biyu dari uku take karba. Da wannan kudin suke cin abinci har ta bawa Honorable na sokewa a aljihu. A nasa bangaren shi ma yana fafutuka sai dai babu canji. 'Ya'yansa sun dauki Hasiya uwa banda Ayaah. Ita ce karama amma tafi kowa daukar zugar kakarsu Laraba da sauran kannen mahaifiyarta. An nuna mata Hasiya bata kaunarsu da zuciya daya, nema take ta rabasu da mahaifinsu.

Wannan bauta da Hasiya take yi a ganin Innayo babu abin da zai biyo bayanta sai kwatankwacin wanda ya sameta. Yau an wayi gari wadanda ta karar da karfinta akansu duka sun gujeta. Shi yass ta ari halin da ba nata ba tana kuntatawa Honorable da 'ya'yansa kawai don ya gaji ya sako mata 'yarta.

Gwiwoyinta sun dade da sarewa akan ganin hasken rayuwa. Ta jima da karbar kaddararta amma bata yarda Hasiyanta ta zama Innayo ta biyu ba. Za ta yi iya yinta taga wannan aure mai tsahon rai ya turgude kowa ya huta.

('Yar uwa ko kin san cewa yanayin gidan miji yana taimakawa wurin shaping din wace irin uwa mace za ta zama? Mata da yawa na aure da kyakkyawar zuciya amma abin da suke tararwa a gidan aure sai ya sauya musu zukata. Kuna tunanin da Alh. Rabi'u ya cika namiji Asabe ta isa ta zama ballagar uwa? Ba don bakin halinsa ba me zai sa Innayo mai kyakkyawar zuciya ta dage zai auren Hasiya ya mutu duk da su Ayaah 'ya'yanta ne?)

Ummi da Murja sun gama sakandire da gumin Anti Hasiya. Magungunan Abbas ita take saya. Kudin makarantar Ayaah yana wuyanta har yanzu. Honorable yana bakin kokarinsa amma samunta a kunshin nan yafi nasa nesa ba kusa ba. Jarabawa ta Allah dai har yanzu ita ko batan wata bata yi ba.

Jarabawar Innayo da Anti Hasiya ta shallake dukkan danginsu ta fada akan Hajaratu Ayar Allah.




****

Sautin muryar shugaban tsangayar kimiya da fasaha a jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) ce ta karade dakin taron inda yake cewa
"And lastly, the award for best research goes to none other than the reknowned Pharmacologist in person of Dr. Khadija Khalid." Yana dariya ya kara da cewa "Please keep clapping until she comes to the stage."

Zuciyarta sai da ta doka dan tsallen murna gami da faduwar gaban dake tattare da sanin cewa yanzu idanu zasu yi mata caa. Cike da farincikin ganin wannan rana da ta kammala PhD dinta har gashi ana yi musu convocation ta mike tsaye. Mazaunin maigidanta Alh.Tahir a teburin manyan baki ta kalla da tunanin ganin zai dan karfafa mata gwiwa koda da gyada kai ne kafin ta hau. Bata yi mamakin ganin ba ita yake kallo ba. Za ta iya rantsewa ma bai ji lokacin da aka kira sunanta ba. Cikin dandazon mutanen da suka zo domin iyalansu ta nemo babban danta da ido. Dan halak din ita yake kallo yana dago mata hannuwansa bibbiyu fuskarsa dauke da madaukakin murmushi. Wannan kadai ya isheta. Ta tashi cikin takun girma ta hau stage din.

Sanye take da doguwar riga da zani na swiss voile navy blue mai adon yellow din fulawa. Ta daura dankwali irin na Maryam Babangida sannan ta yane kanta mayafin kashka mai kauri yellow. Komai na jikinta ido zai nuna maka na kudi ne. Fuskarta babu kwalliya mai hayaniya. Sauda autarta taso fente mata fuska taki yarda. Suna waje saboda mutum biyu aka yarda a shiga dasu dakin karbar takardar shaidar gama karatun.

Suhaib na ganin ta hau ya mayar da idanunsa ga mahaifinsa. A take duk wata fara'arsa ta dauke. Alh. Tahir ne yake yiwa wata inyamura dake zaune a bangaren ragowar baki magana. Kujerar da yake a teburin manyan baki tayi kusa da bangaren inda su Suhaib din suke kuma ita ma yarinyar nan take. Kayan jikinta sun dameta ga uban attachment a ka.

Vice Chancellor (VC) din University of Nigeria (Nsukka) ne zai bata award din. Sai da ya gama kwarzanta kwazonta sannan ya damka mata. Ta karba da murmushi ta juya koda wasa bata yi gangancin sake kai idanunta inda Alh. Tahir yake ba. Yau ranar farinciki ce wadda ta kara kusanta ta da cikar burinta.

Bayan an gama kowa ya watse ita kadai ta fita daga hall din. Ta zata Suhaib na bayanta sai da tayi masa magana taji bai amsa ba.

A ciki Alh. Tahir bai san Suhaib din na kusa dashi ba. Complimentary card dinsa ya mikawa inyamurar bayan ya rubuta nambar da tabbas za ta same shi idan ta kira.

"Kar ki manta ki kirani." Ya kanne mata ido "sai kin fini farincikin amsa wannan gayyata."

"My Alaji..dole zan kira" ta ce da gurguwar hausarta tana mika hannu.

Basu ankara ba daga ita har Alh. Tahir din sai ganin hannu suka yi a tsakiyarsu. Ya warce katin ya dukunkune shi a hannunsa sannan ya sakarwa yarinyar murmushi.

"Kin fadi jarabawar da Babana ya yi miki. Da baki karba ba kyautar kudi zai yi baki."

Yarinya ta zaro idanu waje na rashin fahimta. Alh. Tahir kuwa sai uban murmushin dole yake kamar sauna yaga wawan zama.

Da turanci yadda za ta fahimta da kyau Suhaib ya ce "Abba ya ce 'yan matan yanzu duk basu da tarbiyya indai sun ga kudi basa jin komai wurin bin dattijai marasa tsoron Allah."

Hankali a tashe jin ta kusa yiwa kanta sawarwara ta shiga jijjiga kai "nooo, ahhh. Abeg na the name I wan see. Alaji shebi I say I no go follow you."

Suhaib ya kalleta ya kalli mahaifinsa ya yi gajeren tsaki ya sa kai ya fita. Duk tsiya da jaraba dai ya tabbata dole Abban nasu ya hakura da ita.

A waje kuwa zuciya cike da farinciki Mami Khadija ta fito daga hall din, tana ta waige waigen neman 'ya'yanta cikin daruruwan jama'ar da suka cika harabar wurin, kowa yazo convocation din 'yan uwan sa.

Tana tsaye tana kallon su dai dai ta ji an taba kafadarta. Ta waiga nan ta ga Suhaib tsaye yana sakar mata murmushin nan da ya saba yi mata mai cike da tausayin ta hadi da nuna sanin halin da take ciki. Har kullum Suhaib ya kasance mai shiga damuwa akan yanayin da ta tsinci kanta a hannun maihaifinsu.

Murmushi ta maida masa tana kara jin tausayin dan ta a cikin zuciyarta. Iya tsahon rayuwarsa tana ganin bai taba damuwa da wani abu ba sama da ita da kuma halin da take ciki, komai nasa ita ce. Bangaren mu'amalarsa da mahaifinsa kuwa, a lokuta da dama tana ganin kamar laifinta ne da ya raina shi. Sai dai kuma babu yadda zatayi, duk iya kokarinta na ganin ta dauke damuwa daga fuskarta yayinda take tare da Suhaib, tabbas sai ya gane halin da take ciki.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login