Showing 159001 words to 162000 words out of 242549 words
bahaushe da ake cewa idan kana neman rakuminka ka duba har cikin allura.
Dakin da suke meeting ya shiga ya zauna yana jin zuciyarsa tana wani irin bugu. Ya rasa me yake damunsa tun wayewar garin yau. Ransa a jagule yake ga fargabar da bai san dalilinta ba. Ya san dai yana matukar tsoron wayar nan ta fada hannun wani a cikin gidansa. Mutumcinsa ne zai zube wanwar. Matansa sun san komai amma ba zai so su gani kamar yadda suka ga sakon Yumna ba. Amma 'ya'yansa fa? Wanda Farha ta gani ya ishe shi jin kunya har ya mutu. Tunanin Yumna da ya yi sai ya sake kad'a shi wata duniyar. Rabonsa da ita tun ranar da wayarsa ta bata. Kamar sauran 'yan matansa ita ba bata da numbar kowane layi sai na wannan wayar. Yadda take babu hankalin nan yana tsoron kar ta zo gidan ta ce tana nemansa.
Wuni ya yi yana ta tufka da warwara har aka gama ayyukan da ya saka ba a ga wayar ba. Bai iya tabuka komai ba ya tafi gida.
*
Kurar da bata taka kara ta karya ba a dakinsa ya fara karkadewa kafin ya shiga wanka. Idan bai yi da kansa ba ya san Mami ba za ta bar Sauda ko Mardiyya suyi masa ba. Musamman da yake daga tafiya suka dawo za ta ce suma sun gaji.
Yana gama shiryawa ya dare gado zai yi ramuwar bacci sai ya bige da chatting. Hirar kwallon kafa ce suka kusa yin awa guda suna fafata musu shi da abokansa a group dinsu. Daga kwance sai da ya koma ya zauna. Can aka turo hoton jerin wasannin da suke magana a kai da sakamakon. Lilu bai san lokacin da ya yi ihun murna ba. Club dinsu ne suka yi nasara kamar yadda suka fada. Sun cinye musun. Yana cikin murnarsa Suhaib ya shigo sanye da wandon bacci da singileti. Da gani shi ma wanka ya sake yi zai kwanta.
"Ka fa hanani bacci da ihu."
Lilu ya daga hannuwa irin na masu saranda yana murmushi.
"Takawarka lafiya dan rigimar Mami yanzu nima zan kwanta."
Suhaib bashi da zabin da ya wuce yin murmushi.
"Kai kuma Dan-ta-kife din Mami ko?"
"Kada ka dora min sunan da ba halina ba."
Suhaib ya gyara tsayuwa gami da yin kwafa "ni rigimar halina ce kenan?"
"Banda rigima tun dazu me ya hanaka bacci sai yanzu daga yin ihuna za ka fito?"
Tsuke baki Suhaib ya yi ya juya yana murmushi. Me kuwa ya hana shi bacci sama da tunanin yarinyar da ya gani tare da makaniken nan? Haushinta ya kamata yaji a ganinsa. Sai aka yi rashin sa a ta cike tunaninsa da wasu abubuwa da bai saba kai kansa garesu ba. Wai yau shi ne yake tunanin wace makarantar gaba da sakandire ce za ta fi kusa da gidansa (Alh. Tahir ya mallaka musu filaye shi da Lilu wadanda ake kan aikin ginawa) idan matarsa iyakarta sakandire kafin auren.
Dariya ya kama yiwa kansa na yadda aka yi daga haduwar rana daya ya san cewa iyakarta sakandire. Koda ya koma daki maimakon ya kwanta kamar yadda ya yi niyya sai ya zura jallabiya ya nufi bangaren Jiddo.
A dakin Lilu bayan fitar Suhaib da karewar musun nasu sai ya soma hamma. Gajiyar biki da ta tafiya tayi masa rubdugu lokaci guda. Mikewa ya yi ya nufi gaban socket din da yake saka chaji. A nan yaga chajarsa da bakuwar waya. Tsorata ya yi don bai ga ta inda za a ce wayar ta shigo dakinsa ta jona kanta ba. Yan uwansa kuma duka ya san babu mai irinta. Kamar ya tafi kiran Suhaib sai ya fasa. Yanzu kowa zai kara raina shi ace bai iya komai ba duk bakinsa. Ya daure zuciyarsa ya daga hannuwansa ya karanta musu Ayatul Kursiyyu ya tottofe.
"Kun dai san nan dakina ne amma duk da haka ban ji haushi don kun jona chaji da chajata ba" ya rage murya da salon rokon arziki "ina neman izini in cire in saka tawa ko rabin awa ne?"
'dillll'
Yana rufe bakinsa text ya shigo wayar. Hanjinsa gabadaya ya kanannade saboda tsoro ya koma kan gadonsa ya haye har kafafunsa.
"Daga magana sai ku turo min text? Indai chaji ne na hakura har abada." Ya zuro kafarsa yana kallon kofa gabansa na faduwa "don Allah zan fita inje dakin yayana. In je?"
'dillll'
Wani text din ya kuma shigowa. Dole ya fasa fita yana fadawa kansa cewa gargadi ne ake yi masa. Ya koma yana mika hannu yana janyewa duk a tsorace
"Bari in duba don kada ace nayi rashin kunya. Ni din banza in ja daku? Ku da ake cewa sai kun shekara dari kuke fara samartaka...."
'dillll'
"Naji. Naji!
Ya dauki wayar sai dai a kulle take. Abinka da fitinannen matashin zamani. Ya manta da tsoron da yake ji ya koma kokarin gano pattern din budeta. Bai sha wata wahala ba ya samu bayan yan dabaru. Abin da ya daure masa kai bai wuce ganin pattern din sak irin na Abbansu ba. Kai tsaye wurin messages ya shiga. Ya tarar da sakonni sun tasarma dari. Kuma wani abin al'ajabi na layin basu fi a kirga ba. Sauran kuwa harrufa ne wasu D, V, J, gasu nan dai. Na sama saman da suka yi alamar sune aka yi yanzu ya bude. Harafin dake jiki Y ne.
(Naji labarin tafiya kayi da tsofaffin matanka. Shi ne ka kasa daukar wayata saboda kana jin tsoronsu? Anyways an tabbatar min yau ka dawo. Na baka zuwa azahar idan baka kirani ba zan zo har gidan ai ba bakona bane. Aure ne dai ko ana so ko ba a so sai na amsa sunan matar Alh. Tahir)
"Abba?" Ya ambata a raunane, hawaye na zubo masa. Duk wani kuzarinsa ya kau sai zafin kirji.
Tarin tambayoyi ne a kansa na son sanin yadda aka kwana a ragaya. Neman amsa ya shiga yi ta hanyar bin text din yana maimaitawa. Bai samo amsar komai ba sama da haddace mummunan sakon. A kasan ransa kuma sai tunanin me zai fi dacewa ya yiwa wannan mai tsautsayin da ta iya shafawa idonta toka ta turo wannan sakon. Cikin sauri ya koma baya ya soma bin sauran harrufan da aka adana sunan mutane dasu ya bude nasu sakonnin. Sannan ne kuma jikinsa ya yi mugun sanyi. Hira ce tsakanin Abbansu da 'HARUFFA' daban daban ta rashin da'a. A haka ma ya kula amsoshin Abban basu da tsayi sosai. Wannan kuma dama ya yi ne domin tsira daga forwarding chat ko screenshot da ake yi a whatsapp. Dena binsu ya yi ya koma saman wanda suka yi musaya da Y. Nata da yawa korafi ne akan rashin zuwansa da maganganun aure. Har tana cewa mahaifinta ya ce idan bai zo ba a satin zasu fasa bashi ita.
Ko kadan Lilu bai damu ba idan Abban aure zai yi. Salon hirar ce tafi daga masa hankali domin alamu sun nuna cewa ba a hira aka tsaya ba. Yaci karo da inda aka yi zancen hotel da guest house. Da kuma godiyar 'yan matan akan tarin kudaden da ya basu. Whatsapp yaso dubawa sai dai babu shi akan wayar.
Yana nan kansa ya rarrabu wurin fassara abubuwan da ya gani yaji shigowar wani sakon. Y din ce dai. Kamar dama jiranta yake yana shigowa ya bude.
(Kaga fa ina tunanin ciki ne ma dani. Zan yi test a gida idan positive ne zan turawa Farha hoton ta whatsapp. Sai a yiwa tsofaffin gwangwanye albishir sun kusa samun karuwa.)
Kuka Lilu yake tamkar yaron goye. Karshen sakon ma da kyar ya iya karantawa saboda cikar hawaye. Nambar ya kwashe ya zuba a wayarsa. Tunda ya kai nambobi shidan farko sunaye masu shigen nambar suka dinga raguwa. Yana saka ta bakwai sai ya rage suna daya.
YA YUMNA kamar yadda suke kiranta shi dasu Sauda a matsayinta na aminyar yayarsu.
Kin tsayawa ya yi sai da ya rubuce ta duka ya tabbatar da sunan da ya gani. Yana jin lokacin da zazzabi ya rufe shi hade da wani irin sanyin jiki. Bashi da hujjar karyatawa saboda harafin da ya gani a wayar Alh. Tahir ya kara bashi tabbaci.
"La haula wala quwwata illa billa. Abba? Ya Yumna?"
A gigice ya mike da ya tuna ma'anar sakon karshe. Indai Yumna ciki ne da ita kenan komai ma ya faru tsakaninsu. Zuciyarsa a take ta tashi saboda kyamar hakan da yaji. Ya fada bandaki ya amayar da duk abin da ke cikinsa. Baki kawai ya kuskure bayan ya gama ya fita daga dakin.
*
Duk gidan Alh. Tahir babu wanda Jiddo ta tsana a tsukin kwanakin nan kamar Suhaib. Da can da baya shiga shirginta mantawa ma take dashi. Iyakarsu da juna idan zasu wuce kuma suna kusa taji sautin tsakinsa. Tsakin da tun aurenta da ubansa take ji kuma bai taba damunta ba. Ba kuma wani abu ne ya janyo yake yi mata shi ba sai kamasu da aka yi a daki wanda shi ma yaje wurin.
Abubuwan da suka biyo baya da auren nasu sun taimaka kwarai wurin dasa masa tsanarta. Sai gashi bayan shekaru sun shude ta sake bude kofar sabunta zarginta a zuciyarsa. Alal hakika bai yi wani mamaki ba lokacin da yaga tana shirin barin wurin dinner da makaniken nan. Sanannen abu ne cewa indai bawa ya kulla aminci da zina to ba makawa sai ta kawo masa ziyara watarana. Mahaifinsu yace yaji ya gani wurin sabon Allah. Dolensa kuwa ya girbi shukar da yayi ko ba dade ko ba jima. Shi dai adduarsa kullum bata wuce Allah Ya tsare masa mahaifiyarsa da kannensa.
Sallama hade da kwankwasa kofa ya yi da ya isa bangarenta. Mai'aikinta ce ta amsa ta bude masa. A hakimce kan two-seater yaganta tana waya. Ganinsa a tsakar falonta ya mugun firgitata. Lafiya ko rashinta basu taba kawo shi inda take ba. Yau da yazo ta san lallai akwai matsala. Wayar faduwa tayi daga hannunta ta kuma gyara zama ba shiri.
"Nambar makaniken nan zaki bani." Cewar Suhaib, fuska babu annuri.
Jiddo sai ta daburce duk saboda gudun tonon asiri. A haka ta cije ta harare shi.
"Rashin kunyarka ta isheni Suhaib. Idan ban ci darajar shekaruna ba ai ya kamata in ci na matsayina a gidan nan."
Surutunta bashi da gurbi a kwakwalwarsa balle yaci darajar neman ta maimaita domin ya fahimta.
"Zan samu ko in tafi?"
Rainin wayonsa ya sake bata haushi. Wato ma bai ji abin da tace ba bare ta san ran zai yi aiki dashi. Yatsina fuska tayi ita a dole bata san me yake nufi ba ta ce,
"Wane makaniken?"
Wannan karon Suhaib ne ya hango rainin wayonta. Sai da ya dage girarsa daya sama ya murmusa. Harsashi zai hada mata a wurin Alh. Tahir don ranar tada bom din bata zo ba. Wannan ba aikinsa bane. Lokaci da talalar Ubangiji ga bawan da ya dage akan aikin sabo zai cimmata wataran.
Wata irin murya ya yi amfani da ita sai a rantse sangartaccen da ne a gaban mahaifiyarsa yana zuba shagwaba.
"Don Allah ki bani Anti Jiddo."
Ita kanta da taji muryar sai da ta kara tsorata fiye da farkon zuwansa. Ta san dole akwai abin da yake nufi da haka. Ba dai ta zata maigidan ne da kansa ya shigo falon ba tare da ta kula ba sai yanzu.
Ran Alh. Tahir fari kal kamar takarda yau ga Suhaib a bangaren Jiddo. Yadda yake magana ya nuna masa sun jima da daidaitawa. Ya dinga zuba murmushi kamar sakarai har yana mantawa da halin da yake ciki.
"Wato kin saka danki a daki yana ta shagwaba aka rasa wanda zai amsa min sallama ko? Wai ma mene ne yake faruwa zan yi alkalanci."
Suhaib ya yi saurin bashi amsa kafin ta sami damar juya zancen.
"Nambar makanikenta na Kano nake so Abba shi ne taki bani wai sai na yarda gobe zan rakata shopping"
Wohohooo. Alh. Tahir da shi ma ba wani samun hira daga Suhaib din yake ba duk irin son da yake masa sai yaji kansa ya yi gingirin. Murmushi yaki yankewa a fuskarsa.
"To ai sai ka amince dan Jiddo"
'I reject it! Tuff, tuff' cewar Suhaib a zuci yana jin tsigar jikinsa na tashi saboda an kira shi dan Jiddo.
"Na amince. Don Allah ki bani"
Tsabar mamaki sai ta kasa cewa komai banda kai da take gyadawa kamar kadangaruwa taga manja. Sunan Danliti ta lalubo tunda Alh. Tahir ya musu karan tsaye yaki tafiya. Dama al'adarsa ce shiga bangaren kowa idan zai fita ko ya dawo.
Bayan Suhaib ya kwafe nambar ne Alh. Tahir yake tambayarsa me zai hada shi da makanike a Kano.
"Wani case ne babba ya taso tsakaninmu dashi."
Alh. Tahir ya dan bata fuska
"Ban gane ba? Wani abu ya yi maka?"
Suhaib ya yi hanyar kofa yana cewa "a'a, motar Anti Jiddo yaso lalatawa ba don Allah Ya kaini wurin da suke ba da wuri."
Sautin cikin Jiddo har kunnuwansu saboda tsoro. Suhaib kuwa ya fice yana jin Alh. Tahir na tambayarta me ya sami motar har aka nemo makanike shi bai sani ba. Rantse rantsenta kadai ya jiyo ya kara gaba don bashi da lokacin jin karairayin da zata yi.
*
Lilu kuma da ya fito bai zame ko ina ba sai bangarenta Mami Khadija. Ya yi zaton samunta ta kwanta ko shirin kwanciyar kamar kowa sai yaga sabanin haka. Laptop ce a gabanta ga tulin takardu ta soma barbazawa tana aiki. Gaban table din da aka yi mata musamman saboda aikinta yaje ya mika mata wayar.
"Ga wayar mijinki idan ya dawo ki bashi."
Tun shigowarsa take kallonsa amma furucinsa yasa ta koma yi masa firgitaccen kallo.
"Mijina? Mijina fa ka ce Lilu. Ko dai nice ban ji ba da kyau?" Ta furta a sanyaye.
Lilu ya cije lebe cikin bacin ran tuna abubuwan da ya gani.
"Mijinki maigidan nan nake nufi."
Laptop din ta tura gefe ta tashi tsaye tana dubansa.
"Ko agolanci nazo da kai gidan nan bana tunanin za ka iya budar baki ka kira wanda nake aure Mijina."
Duk shashancin Lilu bai taba zina ba. Mami Khadija ta dasa musu tsananin kyamar wannan laifin tun basu san kawunansu ba. Yafi kowa fitina a gidan amma akwai iyakokin da ko a mafarki bai hango kansa da ketaresu ba.
Kalaman Mamin murmushi suka saka shi.
"Mamina kinfi karfin haka a wajena. Wallahi indai mai mutumci wanda ya san darajar kansa data iyalinsa kika aura ni mai tayaki yi masa biyayya ne."
Da ya gama maganar ya dora wayar a kusa da tata ya fice da sauri. Zama a gabanta karyar masa da zuciya zai sake yi ya kaishi ga kuka. Tausayinta yake ji sai dai kuma jikinsa ya bashi ta jima da sani. A hanyar zuwa dakin ya dinga tuno irin nasihunta da fada da suna yara har kawo ga yanzu. Kusan komai yafi ta'allaka akan zina.
'Ba halinsa bane!' shi ne abin da Mami Khadija ta fara fadawa kanta a lokacin da taji kamar ta kwashe shi da mari. Kwalla ce ta taho mata saboda jikinta yana bata da wuya idan ba sirrin boye ne ya fito fili a wurinsa ba. Yadda Farha ta sani bayan Suhaib gashi yau shi ma ya sani. A ranta ta dinga tsarkake Mulkin Ubangijin da ya haramta zina. Hakika wannan kaba'ira tana zubar da mutumcin mai mutumci. Yau Lilu da bakinsa yake kiran mahaifinsa da wani suna ba Abba ba.
Kallon wayar tayi sau daya ta kawar da kanta. Alh. Tahir na shigowa bangarenta daga wurin Jiddo ta damka masa wayar daga bakin kofar da ta tare don kada ya shigo ciki.
"Lilu ne ya kawo"
Gumi a take ya tsatstsafo akan goshinsa.
"Ya ce wani abu ne?"
Mami Khadija ta kalle shi ido cikin ido ta ce "ya ce ga wayar mijina na bashi idan ya dawo"
Alh. Tahir ya karkata gefen fuskarshi gareta yana son tabbatar da abin da ta ce.
"Mijinki? Dani yake?"
Cikin ko in kula ta ce "a iya sani na ba."
Daga haka ta rufe kofarta ta barshi a wurin yana jinjina girman abin da yake samunsa a tsukin nan.
I just published "35" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1095418785?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=WH2D39oPR5sYCfkLu1mXT4fL9GeLPbHp2QiULVor2y52dl9oH29pjmjeOiXFaGwOC1HqE1U%2BRuVJYskywLegMBvivLLBGM9JeCauF9Iqcg5jKRTG62XjxazG0mL2u3NB
UWA UWACE...35
Batul Mamman💖
Yaa Rabbi!
Naji korafe korafe kai tsaye da ma na aike kala kala game da dorawa Lilu laifin da ba nasa ba. Na so kamewa daga bayar da amsa sai dai ku gani a rubuce. To amma wasu har ikirarin barin karatun suke. Jama'a idan kun barwa Batul labaranta ina ta kama? Sakon da nake fatan Allah Ya bani ikon isarwa bai je ko ina ba kenan. Ya zama dole na magantu.
Kafin na fara wanke kaina, ina so inyi amfani da wannan damar wurin yi muku godiya. Akwai gajiya matuka idan marubuci yana daukan dogon zango kafin ya yi post. Sai dai kamar kullum hakuri dai zan cigaba da baku. Ba da gangan bane. Yau da gobe ce wadda take nukurkusar daukacin al'ummar kasar duniya ba ma kasar nan ba. Allah Mabuwayi Ya kawo mana saukin lamura. Amin
To mu koma ga labarinmu. Kwanakin baya korafin akan yawan wahalhalun Innayo da rashin cin moriyar guminta ne suka yi yawa. Wasu har suna ganin kamar zan sagar musu da gwiwa wajen kulawa da amanar da Allah Ya bamu ta zuri'a. Ko daya ba nufina ba kenan. Labarin nan kacokan ban yi shi domin tsantsar nishadi ba. Wasu lamura nayi ta nazari a rayuwarmu shi yasa nake son yinsa ta yadda zaiyi kamanceceniya da zahirin rayuwa. Akwai Innayo bila'adadin a cikin al'ummarmu. Mace ta wahaltawa miji ta kuma wahaltawa 'ya'ya. Amma a karshe haka zata koma ga Allah da bakincikin dukkansu. Ta rayu a talauce ta mutu cikin talauci. To amma fa shafin rayuwarta ba zai kare a wurin Maqaginta ba muddin ta koma gareshi tana mai gaskata kadaitar mulkinSa. Daga lokacin ne ma zata fara shan romon ladan ayyuka da hakurinta har zuwa tashin qiyama. Sai dai taji ance ta wuce Aljanna gidan dauwamamen farincki.
Game da Lilu kada mu manta su waye iyayensa. Uba mazinaci wanda har yanzu babu wata kwakkwarar nadama a tattare dashi. Shin idan zina bata dawo masa a inda zai yi masa ciwo ba kuna ganin zai san Annabi ya faku? Zai ji ciwon da iyayen 'ya'yan da ya mu'amalanta suka ji? Zai yi nadamar ayyukansa har ma ya tuba? Sanin tsohuwar sana'ar maneman 'ya'yansa ba ta da babban tasiri indai ba an riga an daura aure ba. A yanzu kam ba zai