Showing 234001 words to 237000 words out of 242549 words
na rashin kiranta da ya ce zai yi domin ta duba Qibdiyya. Hakuri zai bata sai ta kula da ramar da ya yi. Mantawa tayi da fadan ta koma tambayarsa damuwarsa.
"Na manta gidanmu ba irin da bane, da na sani ban zauna abubuwa suna ta damuna ba a cikin kwanakin nan" yace ba tare da wasa a fuskarsa ba.
"Komai mai wucewa ne Munzali. Tunda muka dinke da Innayo kaima kawai ka jira lokaci. Kafin ka farga zaka ga ya koma tarihi. Ko ka bayar dashi ko rike abinka a zuci"
Karfin gwiwa ya samu daga gareta wadda da ita ya yi amfani wajen jajircewa iyayensa suka bi shi.
***
Sheikh Dr. Abdallah Saraki ya saurari jawabin Munzali da Abbati da dukkan nutsuwar da ake bukata daga malami. Labarinsu gabadaya izina ce kuma babban darasi ga iyaye da su kansu 'ya'yan.
(Ni din ba Malamar addini bace. Daliba ce mai koyo har yanzu. Bakin gwargwado ina nazari da bincike kafin na kawo wani batu mai girma cikin labaraina. A nan ma na duba matsayar malamai na kuma hada da tawa fahimtar. Saboda haka idan mai karatu yaci karo da abin da ya sabawa nasa ilimin, kada a manta cewa wannan labari ne. Abin da ya shafi fatawa a nemi sahihancinsa a wajen maluma. Rabbi Yasa mu dace da khairi duniya da lahira. Amin)
Da Alh. Rabi'u ya ga zai fara magana, hankalinsa kacokan ya mika masa. Yana so yaji malamin ya wanke shi daga abin da Munzali ya ce, wato yana da hannu a cikin lalacewar rayuwarsa.
Dr. Abdallah ya fara jawabinsa da sallama tare da addu'ar bude taro ko wani zama da za a tattauna abu mai mahimmanci. Sannan ya karkare da yiwa fiyayyen halitta salati SAW.
"Da farko zan fara da yaba muku tare da kara muku karfin gwiwa. Duk wanda ya nufi Allah SWT da kyakkyawar zuciya, to ya sani cewa Allah ba zai tab'ar dashi ba. Saboda haka ku cigaba akan niyyarku. Ko a duniya ko a lahira sai kun yi mamakin falala da girman Mahaliccinmu. Zai baku fiye da rokonku. Ya yafe fiye da tubanku domin Shi din gagara misali ne wajen jink'ai da tausayi."
Ya gyara zama saboda su san cewa zancena gaba yana da mahimmanci.
"Munzali ina so kai da iyayenka ku sani cewa tsaftatacciyar soyayya ce tsakaninka da Abbati. Irin soyayyar da Allah SWT Yayi alkawarin inuwar Al'arshi rana gobe kiyama ga ma'abotanta. Wato mutum biyu masu kaunar juna domin Allah Shi kadai."
Munzali ya hau murmushi yayinda Abbati ya dinga kiran sunan Allah a iya a lebbensa.
"Malam baka ji inda ya ce yana son Abbati fiye da kowa ba? Ma'ana fa harda mu. Babu jin nauyi ko kadan yake nuna min cewa yaron nan ya fini a wurinsa." Cewar Alh. Rabi'u yana huci.
Dr. Abdallah ya ayyana a ransa cewa lallai Alh. Rabi'u akwai gagarumin gyara a lamarinsa.
"Aikin sab'o sakamako ne na raunin dan Adam. Shi kuma rauni ana gane shi ne daga zuciya. Idan aka haneta ga barin abin da take so sai ta ce ta kasa. Idan aka umarceta da abin da bata so nan ma ta nuna gazawarta. To da zarar mamallakinta ya biyewa ra'ayinta ba tare da dora shi a mizanin hankali, dabi'a da addini ba, dole nadama ta saukar masa watarana. Alh Rabi'u, ka yi godiya muddin rai ga Allah da Ya bawa yaran nan damar fin karfin zukatansu a lokaci irin wannan. Gurbacewar zamanin nan ta kai ta kawo. An kawata zina ana tallatawa mutane. Tserewa tarkonta wallahi sai wanda Allah Ya azurta da jarumar zuciya. Wadda tana so din kuma tana tsoron mummunar makoma. Zuciya ta ma'abota tsoron Allah da kwadayin rahamarSa."
Asabe ta dinga gyada kai tana yiwa Munzali da Abbati kallon tausayi. Alh. Rabi'u kuwa cikin kosawa ya ce,
"Nifa so nake naji inda aka halattawa baligin namiji kaunar kato kamarsa har ma kake ganin cewa hakan ba laifi bane. Addinin nan bakin gwargwado nima fa na san shi. Maluman zamanin nan banda son zuciya da kwadayin abin hannun masu neman fatawa basu iya komai ba. Sai ayi ta halatta haram don kada ran mai kudi ya baci"
Kunya sosai ta rufe Abbati da Munzali. Asabe ta dinga bawa Dr. Abdallah hakuri. Shi kuwa ko a jikinsa. Mutane irin wannan da wadanda ma suka fi shi nawa ya gani?
"Soyayya tana samuwa ne daga kyautatawa. Babu ruwanta da jini ko alaka. A inda aka samar da ita a nan take samun wurin zama. Ku duba hikimar Ubangijinmu a wurin zamantakewar rayuwa. Da farko Ya sanya soyayyar da a zukatan iyayensa tun yana ciki. Wannan ita ce ainihin sunnar rayuwa game da iyaye da 'ya'ya. Duk wanda Allah Ya bamu mai kyau ko akasinsa. Nagari ko shakiyi sai kaga muna son kayanmu. Har muna jin ciwon hukuncin da mukan yi musu idan sun yi laifi. Su kuma 'ya'ya ana haifarsu ne ba tare da ilimin komai ba. Tunda anyi zuciya da kaunar mai kyautata mata, fuskar da mutum ya nufeta da ita, itama za ta je da kwatankwacinta. Yaro baya sanin wace uwa a gareshi a farkon rayuwa. Shi dai kawai wannan mai kawar masa da yunwa da kula da damuwarsa ita ce mutum a wurinsa. Wannan dalilin yasa wadanda maraici ke riskarsu tun a zanin goyo suke tashi da kaunar marikansu indai an yi musu rikon amana."
Daga nan Alh. Rabi' u ya soma shan jinin jikinsa. Asabe kuma ta soma hawaye.
"Yaran nan sun hadu a lokacin kuruciya. A shekarun da ko iyaye suna kokarinsu sai sun kara sun dage sannan an hada da addu'a. Dalili kuwa shine wannan shekara shabiyu zuwa sama mataki ne na farkon balaga. Lokaci ne da yara suke fara sanin kawunansu. Munzali yana da zuciyar tausayi da jinkai. Amma ya tashi da kishirwa da yunwar kulawa. Wannan shi ma a tsarin halitta zaka ga wani yafi wani cikin yara son kulawa. Wasu yaran tun kuruciya suna son a dinga basu damar yin komai su kadai. Wani kuwa burinsa na gaba ya sanya shi a hanya kullum. Yana son ayi ta ririta shi. In kun duba Munzali da ya san ya taimakawa wani tun kuruciya tabbas shi mutum ne mai raunin zuciya. Duk wanda zai ja shi a jiki shi ne mutum mafi girman kima a idonsa. Ya zo ya hadu da Abbati. Wanda shi kuma bai kasance daga cikin butulun mutane masu manta alkhairi ba. A zamanin nan duk wanda ya kawar maka da yunwa babu ya shi. Kyautatawa junansu a lokacin da ido da sawun iyaye baya garesu shi ya janyo musu shakuwa. Babu ce ta hadasu ba arziki ba balle ace wani yana kwadayin abin hannun dan uwansa. Kune ku ka kora danku zuwa ga mai kaunarsa da zuciya daya. Misalin haka kan faru tsakanin iyaye mata da masu raino. Idan mace ta sakarwa mai raino ragamar komai na danta, watarana sai ta mika hannu ya noke kafada. In ta dauke shi ta karfi ya yi mata ihun da jama'a zasu iya yi mata kallon mai satar yara."
"Tabbas malam kayi gaskiya" Asabe ta furta tana kuka "sakacinmu ya janyo Munzali ya hada Abbati da miyagun mutane. Dole yake kukan cewa ya yi sanadin bata rayuwar Abbati."
"Don Allah ku daina zancen wani ya bata wani cikinmu. Kaddara ce irin wadda bawa bai isa ya kauce mata ba"
Munzali ya kalli Abbati ya yi murmushi. Dama ya san haka zai ce.
"Ni dai duk da haka ka yafe min"
"Nima ka yafe min"
Asabe ta ce "Allah Ya yafe mana baki daya" ta dubi Alh. Rabi'u "Alhaji ka dai ji abin da Malam ya fada. Duka abin da ya ce babu wanda bamu aikata ba. Mu karbi laifinmu kawai mu tuba shi ne maslaha. Wani borin kunya ba namu bane"
"Ke, bana son rashin kunya. Kin sa danki da bare sun kawo ni nan domin a ci min mutumci ne dama?" Ya tashi tsaye yana karkade riga yadda ya saba idan ransa ya baci "tunda bani da amfani a gareku da 'ya'yanku yau dinnan ba gobe ba zan sauwake muku. Kuma ku zuba ido ku gani idan ban auro yara sa'annin jikokina ba. Wadanda zasu karbi irin kulawar da nake baku hannu bibbiyu suna son barka"
Maza irin Alh. Rabi'u masu kafiya, taurin kai, yiwa addini raguwar fahimta da karan tsaye suna daga cikin babbar matsalar arewacin kasarmu. Suna yin ba daidai ba. Sun sani sarai, kuma in an gyara musu sun san kurakuransu. Amma saboda bahagon tunani basa yarda su karbi gyaran. Kuma a haka wani mai zuciya irin tasu zai basu 'ya su aura. Ukubar da za ta fuskanta da sunan aure ba matsalar mijin da uba bace.
"Ba ayi haka ba Alhaji. In zaman nan bai kawo gyara ba ina ganin bai kamata ya kara lalata lamura ba." Dr. Abdallah ya ce dashi. A ransa yana mai cigaba da nazarin hanyoyin karkato tunanin dattijon.
"Na gama zama. Ki sameni a gida idan kun gama"
Abbati ne ya hana shi fita "Alhaji ka zauna ka yi mana shaida akan kudirinmu na gaba. Malam mece ce makomar dukiyarmu a yanzu da muka tuba?"
"A shari'ance dukiya kala biyu ce. Halattacciya da haramtacciya. Tunda kokontonku yana ga son sanin ko dukiyarku ta haram ce to akan ta biyun zamu yi magana. Ita dukiyar haram an kasata biyu. Akwai ta haramci a dalilin abin mallakar mai cutarwa ne kamar giya, naman alade ko mushe. Da kuma wadda ta haramta a dalilin hanyar samuwarta da izini ko babu izinin mai ita. Misali dukiyar da aka sata ko ta bokanci, kwangilar kisan kai, caca, sayar da kayan maye, karuwanci da ribaa. Kun ga irin taku dukiyar ta fado cikin aji daya da karuwanci. To game da wannan nau'in dukiyar wadda ake samu da izinin mai ita amma sanadin samuwarta haram ne, dukkanin malaman mazhabobinmu wato Imam Hannafi, Imam Hanbali, Imam Malik da Imam Shafi'i sun tafi akan cewa wajibi ne a rabu da ita. Ko dai a mayar da ita ga mai ita ko ayi sadakarta ga mabukata idan babu halin mayarwa. Ibnul Qayyim Aljauzi ma yana cewa a bayar din shi ya fi. Domin a lokacin samunta wanda ya bayar ya amfana da abin da ya biya kudinsa ne duk da cewa abin haram ne. A wani kaulin, Imam Al-Ghazali ma ya ce sadaka, zakka ko Hajji basu wajaba akan wanda duka dukiyarsa ta kasance haramtacciya ba.
Duka maluman nan sun yi duba ne ga ayoyin Alqur'ani da Hadisan Annabi SAW wurin fitar da fatawar. Misali, akwai wani hadisi wanda Imam Bukhari, Muslim, Ibn Majah, Nasa'i, Abu Dawud da Tirmizi duka suka rawaito [an karbo daga Abi Mas'ud Uqbah bin Amr RA cewa Manzon Allah SAW ya haramta kudin cinikin kare, kudin karuwanci da kudin bokanci.] (Ownership of Unlawful Wealth from Islamic Legal Perspective. Badruddin HjIbrahim da Azizah Mohd, 2017)
Hakika ba zan gushe ba wurin yaba muku matuka. Ina kuma yi muku albishir da cewa dukkan wanda ya bar wani abu da yake so domin Allah, to ladan wannan aikin yana ga Allah (Annawawi hadisi na daya). Zaku kwashi rabonku na alkhairi a duniya ko lahira. Ku sani dai cewa wallahi baku yi asara ba."
Kallon juna suka yi suka gyada kai a tare. In sha Allahu ba za su bari son duniya ya rufe musu ido daga barin mummunan alkaba'in da suka jima suna aikatawa ba.
"Akaramakallah akwai wani batu guda daya da ya rage. Ka san wannan abin yana tattare da matsaloli da dama da suka shafi lafiya. Musamman ga wanda ya tasarma barinta. A haka dai bamu da wani ciwo cikin ciwukan da ake dauka ta wannan hanyar. To amma mu dan yi bincike ana samun abin da ya shafi kwakwalwa. Hanyoyin da ya kamata mu bi a likitance domin kauracewa sha'awar da ta kan taso mana saboda sabo. Rashin kulawa zai iya janyo mana rubewa ko fitar tsutsa..." kasa karasawa ya yi saboda takaicin halin da suke ciki.
Abbati ne ya cigaba da bayanin "mun biya miliyoyin kudi ga wani asibiti a Italy wanda suka kware wurin dakilar da sha'awar sake fadawa zunubin. Sannan duk wata lalura da ta shafi lafiya wadda da wuya mu tsallakewa samunta a nan gaba kadan zasu magance ta. Tambayarmu a nan shi ne zamu iya zuwa? Idan bamu je ba Allah kadai Ya san halin da zamu iya tsintar kawunanmu. Sannan bamu da halin sake samun kudin da zamu biya. Duk abin da muka mallaka yanzu hatta waya zamu rabu da ita saboda duka da kudin muka samu"
Iska Dr. Abdallah ya fesar daga bakinsa. Wannan tambaya akwai rudani a cikinta. Ya dubi matasan ya auna duka maganganun da suka yi. Ya tambayi nawa suka biya yaji kudin ba na kusa bane. Bayan nazari ya fada musu abin da yake ganin shi ne mafita.
"Ku je ku nemi lafiyar ku. Domin sai da ita ne kadai zaku iya barin wannan abu har abada. Idan nace ku zauna ban yi muku adalci ba. Bani da halin sama muku irin wannan kudi. Iyakar shawarar da zan baku shi ne ku kiyaye. Kada ku dauki kari akan abin da ku kw san lallai zai isheku iya zamanku a can."
(Wannan ba fatawa bace. Fahimtata ce ba fadin malami ba)
Ragowar bayanin da aka yi shi ne ya dan taba zuciyar Alh. Rabi'u. Ya auna da kwakwalwarsa ba son zuciya ba ya tabbatar duk a kokarin samun lahira Munzali yake wannan abu. Shi kuwa wane irin shaidan ne a kansa da zai sa ya cigaba da riko da mummunar akidar da har mahaifiyarsa ta rasu bata taba goyon bayansa a kai ba?
***
Bayan Wata Hudu
Sannu sannu bata hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Abubuwa da yawa sun faru a cikin watannin nan ga jaruman labarinmu.
Mami Khadija ta koma hadadden gidan da Alh. Tahir ya mallaka mata ita da 'ya'yanta. Ta cigaba da aikinta cikin kwanciyar hankali. Iyayenta da Yakumbo sun yi fushi har sun sauko. Mardiyya bata yarda an barta ita kadai ba. Kamar yadda suma yaran basu kwashe duka kayansu daga wancan gidan ba. Musamman Sauda da Mardiyya da basa rabuwa. Kullum in basa wannan gidan suna wancan. Jiddo ta dade da tafiya. Gida ta kama mai kyau ta cigaba da shashancinta bisa zugar kawaye. Gidan ya zama dandalin fitinannun mata. Ba a dade ba kuwa suka cinye fiye da rabin kudin da Alh. Tahir ya bata. Tunda bata iya juyasu ba sai bushasha. A halin yanzu ta gamu da ciwon gonoriya. Kuraje manya manya masu dan karen kaikayi da kazamin ruwa sun firfito mata. Ga kudin asibiti ya soma gagararta.
Alh. Tahir ya auri Yumna domin biyayya ga umarnin Yakumbo. Da kuma rufin asirinsa akan abin da Mami Khadija ta fadawa 'ya'yanta. Ya daina bin mata kamar anyi ruwa an dauke. Rayuwarsa babu wani farinciki a ciki saboda rashin Mami da zubar girmansa a idon manyan 'ya'yansa. Mama Nasima ta rage rashin zaman gida saboda tsoron kada ita ma ayi waje da ita. Yumna kuwa babu wannan fadar da take tsammanin samu. Ga kudi ga komai amma mijin bashi da lokacin biye mwa shirmenta.
Lilu ya mayar da hankali akan karatu. Suhaib kafa ta warke ya koma bakin aikinsa. Ayaah tana nan a ransa. Suna yawan gaisawa a waya wadda bata wuce ya gida, jikin Abbas da jarabawarta (a tsarinsa sai ta gama jarabawa zai nemi soyayyarta wadda ya gama nutsewa a ciki). Farha ce ta koma abar tausayi a wurin Mami. A zahiri ta cigaba da gudanar da rayuwarta kamar da. A badini kuwa kewar Abbati tana neman wargaza tuninta. Kara son shi tayi bayan Mami ta fayyace musu komai kamar yadda Alh. Tahir ya fada mata. Ta dai sakaya yanayin haduwarsu da babansu. Sai ta ce wurin abokinsa yaje yaga Abbatin. Wayar duniya ta buga bata samunsa. Tunda tayi na sati ta hakura ta fawwalawa Allah.
A Kano gidan Innayo sai san barka. Kansu ya hadu 'ya'yan suna ta zumuncinsu. Asabe da Innayo ma kamar 'yan uwa. Maigidan ne dai sai a hankali. Yau fari gobe tsumma. Wata dabi'ar barinta yana da wuya. Tuni Zara ta koma gidanta bayan Hajiyan Fatakwal ta zo da kanta sun sasanta da Innayo. Aka yiwa Ummulkhairi taron sunan da ya shiga bakin 'yan unguwa. Da wuya a hadu ayi hira mai tsayi ba ayi zancensa ba. Uwani ma da kanta ta koma. Salihi dawowa ya yi gida kawai ya sameta a falo da Mubasshir suna hira. Yayi murna kwarai da irin canjin da aka samu a tattare da ita. Ya hadasu da Ummule ya musu nasihar zaman lafiyar da kowane magidanci yake yi. Har yanzu dai babu wani abu mara dadi da ya faru gashi har Ummule ta haihu. Uwani ce ta karbi haihuwar tayi komai babu ha'inci a gida. Saura wata daya suspension dinta ya kare. Sannan ba tare da sanin kowa ba sai mijinta ta dauki Zakiyya da Qibdiyya sun je asibiti. Duk wani abu da ya dace ayi Salihi ne ya dauki nauyin biyan kudin. Ita da 'yan uwanta duk sun karbi zancen da yabi bakin kowa na cewa karayar arziki ce ta sami su Munzali. Asabe ta gina zancen akan wanda Mami Khadija tace mata taji a wurin Alh. Tahir lokacin da ta kira tayi musu jaje.
Salima dai aure ya mutu murus. Ale Gambo ya yi rantsuwar idan bata koma ba cikin kayadadden lokacin da ya bata tana da damar sake aure domin babu shi babu ita. Innayo ta lamunce mata tayi abin da zuciyarta take so. Cikin farinciki don har ta murmure ta ce ta gama zama dashi. Kwanaki kadan da suka wuce ta gama iddarta.
Abbas ya warke ya koma gida. Sauki ya samu don ya fara magana kuma yana tafiya da kansa. Tsakanin su Honourable da Abdulkarim sai tarin godiya. Shi da Ummita soyayya suke yi mai ban sha'awa. Biki saura sati biyu. Ayaah ma ta gama NECO sauran WAEC wadda jarabawa biyu suka rage su kammala baki daya. Anti Hasiya ciki ya fito. Laulayi ya yi sauki sosai. Tana samun riritawa daga mijinta, mahaifiya, 'yan uwa da 'ya'ya. Haihuwa kawai ake jira. Karshen abin farinciki shine kulle Danliti da Shazali da Alh. Sadisu yasa aka yi. Duka malamai da masu gadin makarantar da sukw da hannu su ma an rufe su. Shi Shazali ma a kurkukun bai tsira ba domin kusan kullum sai