Showing 21001 words to 24000 words out of 242549 words
daina sonsa? Ba haka yake so ta dinga yi masa ba. Kishin da ya tsammaci gani wanda zai tabbatar masa da sauran matsayinsa a zuciyarta duk babu. Baya mantawa kafin wata dayan nan da ta kara musu ya cika gabadaya Nasima sai da ta gundure shi. Don ma yana jin sonta a zuciyarsa ne da bai san me zai faru ba. Yana ta tuhumar kansa me yasa ya yi saurin aurenta. Da ya sani kuruciyarta kawai ya mora ya bata abin da zai bata a waje. Yarinyar sam bata da aji.
"Wai Diya...sai kace wani dabba. Mtseww"
Tunawa ya yi Khadija ma tana fada idan ta so cusa masa haushi ya yi dan murmushi. Tunda dai bata tafi ba zai cigaba da lallaba abarsa. Da tsohuwar zuma ake magani. Mata nawa ya nema bayan aurensu amma duk inda ya gama yawonsa wurinta yake dawowa.
Da yake ita keda girki ranar da ya koma dakinta ta cigaba da yi masa komai yadda ta saba. Kallonsa tayi yana ta biyewa yaransa suna wasa tayi kwafa. Ba za ta taba bari ya gane kudurinta ba. Da kudinsa za tayi karatu. Burinta ta sami jari ko aiki a gaba wanda za ta iya rike kanta da 'ya'yanta. Komai dadewar lokaci, komai tsufa, za ta bar gidan Tahir.
Nasima kuwa ta dade a tsaye inda Tahir ya barta. Tsoro ya gama mamaye zuciyarta domin ta kula ba tun yau Tahir yake hantararta ba.
"Na rantse kayi karya Tahir. Ni da kai yanzu muka fara zaman aure."
A ranar ta tambaye shi zuwa gida ya amince. Washegari yana fita ta tafi wurin Laraba. 'Yan kudaden da yake bata ta fiddo duka aka bawa wani malamin tsibbu. Ya hado mata magunguna da bayanin cewa da basu zo ba a ranar zai saketa. Wai bokan Khadija ne yake musu farraku.
"Laraba kin ji ko? Na fada miki yanzu kamar bana burge shi ga yawan fada." Ta ce cike da gamsuwar karyar bokan.
Kulle-kullen da ya basu ta dauka ta tafi dasu gida tayi amfani dasu yadda ya ce.
To gidan dai rayuwa ake yau fari gobe tsumma. Khadija tana Zaria da yaranta sai dai Tahir ya ziyarce su. Ko suna hutu sai ta fake da karatun yaran. Sai lokutan hutu gama-gari take zuwa gidan. Karatunta take yi hankali kwance sannan tana sayar da zobo da ginger. Tun tana kullasu a leda har ta koma yin na roba. Kasuwa ta karbu har freezer ta kara saya da ribar cinikin.
***
"Ina cewa matarka bata da hankali ashe kaine babban mara hankalin. Inuwa! Inuwa ka bani kunya." Mal. Sa'adu ya furta rai a bace.
Sunkuyar da kai Inuwa ya yi kunya ta mamaye shi. Yayan nasa bai tashi yi masa tijara ba sai da yaga sauran matan kannensa sun zo wucewa. Ai kuwa tsayuwa suka yi a fakaice aka gama jin fadan.
"Amma saboda Allah Yaya kana ganin irin mutuwar da Sani ya yi. Idan bamu yi wani abu ba shi ma Abbatin haka zamu rasa shi"
Murya har dakuna mafiya kusa ake jin fadan Mal. Sa'adu yana cewa "Wanda ya rasu a wurin neman ilimi yana cikin jerin shahidai idan baka sani ba. Kuma tunda mutuwar ta kuruciya ce idan an je lashirar ba kai da Marin za'a fara cewa ya ceto ba. Kila ni da na assasa tafiyar ma sai ya gama daku zai ambaceni."
Inuwa dagewa ya yi shi ma"Ni dai gaskiya zan dauko shi na saka shi a ta allo da boko a nan."
"Ahap...tushen magana ya hito da za ka zauna kana yi min kwana-kwana. Daga makarantar 'yan aljanna za ka kaishi ta 'yan wuta. Wai ma shin 'ya'yanka aka fara kaiwa ne? Gidan nan kowa yana kaiwa. Don naka ya rasu sai ka kasa karbar kaddara?"
Fadan Mal. Sa'adu yaki karewa. Inuwa tun yana mayarwa har ya kasa katabus. Sauran 'yan uwansa ne suka hade masa kai aka fara yi masa nuni da cewa Mari tafi karfinsa kuma ita take juya shi. Bahaushen mutum da jiji da kai da gudun raini sai yaji tsoron kada su raina shi. Har kasan zuciyarsa ba ya so amma kuma rashin son ayi masa kallon mijin-tace ya danne komai. Sun kunno shi sosai sannan ya shiga ciki ya hau Mari da fada.
"Abbati ba zai dawo gida ba kuma ban yarda ki je Kano ganinsa ba. Tunda dai zasu zo hutun Takutaha nima ba zuwa zanyi ba."
Wani abu ta hadiye da ya tokare mata wuya da kyar sannan ta daga kai ta kalle shi. An kusa wata biyu da rasuwar Sani amma har yau ta kasa komawa daidai. Da ciwo mai raunana zuciya da ruhi a tare da ita. Dashi take kwana dashi take tashi. Duniyar sam ta daina yi mata dadi. Gani take ta gaza a matsayinta na uwa. Kwanakin farkon rasuwar saboda ta sa abin a rai har mafarkinsa take yi yana tuhumarta da wulakanta amanar Allah.
Shekararsa bakwai kacal a duniya. Sa'anninsa da suke cikin gata wasu ko kyakkyawan tsarki basu iya ba. Wasu su dawo daga makaranta suna bore suna ihun sun girma uwa ta kamasu tayi musu wanka da kanta. Wasu a basu abinci a baki. Wasu uwa ta shagwabasu da soyayya ba don su lalace a tarbiyya ba. Almajiri kuwa sai yadda Allah Ya yi. Ga kuruciya, ga rashin gata kuma a haka cuta za ta kama shi. Babu magani babu kuzarin yin bara sannan ba lallai a sami mai damuwa da halin da yake ciki ba balle a taimaka masa. Idan da tsananin ciwo zai saka shi amai a makwancinsu babu abin mamaki wurin samun masu yi masa tsawa da hantara kuma ace ya goge wurin. Idan ya yi zawo a jikinsa sauran dalibai su toshe hanci su guje shi.
(Ke da yake da yake yiwa shara, wanke-wanke ko zuwa aike idan ya yi fashi ki hau shi da fada. Cikin dan albashin da kike bashi ki cire na kwanakin da bai zo ba. Ya wuni a rana yana wanki ki bashi ragowar abincin jiya kila ko dumamawa baki yi ba. Hakika tallafawa almajirai kafin gwamnati da masu ruwa da tsaki su dakatar da wannan al'adar jihadi ne. Idan wani mahaifiyarsa tana da rai kuma ta yarda yazo wani tasa uwar irin su Mari ce ko maraya ne. Idan wasu duniya ta lalatasu kamar Abbati wani kuma is innocent kamar Sani.)
"Allah Ya kaimu Takutahan" ta iya cewa kadai.
Watannin sun wuce a yayin da bawa yake ta fadi tashin neman na kai. Wannan mummunar alfasha ta gama shiga jikin Abbati da Munzali. Ranaku daidai ne basa haduwa. Shazali da abokansa suka koma amfani dasu biyun. Saboda haka yanzu abincin Abbatin ma ko bai hadu da Munzali ba zai samu a wurinsu. Ya murmure fiye da yadda ya zo daga kauye. Ya kuma zama fitsararre mara kunya da kawaici. Babu mai saka shi ko ya hana shi a makarantar saboda Shazali ya tsaya masa.
Malaminsu ya dade da sallama su Shazali. Sun zame masa karfen kafa. Babu karatu kuma sun ki komawa gidajensu.
Ana gobe hutun Abbati ne tare da Munzali dasu Shazali a kangon suna cin abinci. Tsire ne da biredi sai kwalbar lemo a hannun kowannensu.
Shazali ya kusa sati yana juyayin gabatar musu da wata bukata amma yana gudun kada cikin surutu su fadawa wani. Amininsa ne ya ankarar dashi cewa ďa zasu fada fa da tuni wancan abu ya dade da yaduwa. Sai da ya kula duka suna jindadin abincin ya kawo zancen.
"Da ace kullum ni nake baku kudin abinci ko na baku ba gara ku dinga bina inda nake samowa ba ku ma ku dinga shanawa da kyau."
"Al'Qur'an ko ma ina ne ni dai zan bika." Cewar Abbati da zumudi.
"Kai fa Munzali?"
"Abbati ma zai yaje bare ni."
"A wurin irin abin nan da muke yi zasu dinga yi daku sai a baku kudi. Idan ku ka fadawa wani a take zaku mutu."
Wannan ba abin damuwa bane tunda sun riga sun saba. Abbati bai ji dadi ba saboda dole sai bayan ya dawo daga gida za'a kai shi.
Ranar da zasu tafi 'yan uwansa na wasu makarantun a Kano ne suka hadu da 'ya'yan makota duk 'yan gari daya suka tafi tare. Yana shiga mota ya shafe shafin su Munzali. Hankalinsa ya yi gida Baaba Marinsa yake son gani da kannensa. A nasa haukan yake son ganin Sani ya fada masa abin da yake yi yana samun kudi da abinci.
Zancen zuci yake wanda don dadin da abin ya yi masa har dan tsalle ya yi akan kujerar mota. 'Shi ma idan ya yi mu tara kudi mu kai Baaba Makka da Madina'. Bai san abin da yake ya munana ba. Ya dai san kila Mari tayi masa fada. Munzali ya ce manya ne kadai suke yi.
***
Mari tana yayyafawa itacen da ta gama yiwa Abbati miyar zabi taji muryarsa.
"Baaba. Baaba na dawo. Baaba Sani ma ya zo?"
Murnar da ta tashi da ita sai ta nemi komawa ciwon rashin Sani. Murmushi tayi saurin yi domin kada ya zata bata murnar ganinsa har ya iso gareta. Da murnarsa ya taho zai rungumeta sai taji kunya. Tsakar gidan da mutane duk an zuba musu idanu. Yana isowa sai zai riketa sai ta dafa kansa.
"Kun dawo lafiya?"
Bai biye mata ba ya rungumeta yana dariya.
"Lafiya kalau Baaba. Ina Sani? Ya zo gida?"
Kwalla ta sake tarar mata a karo na biyu ta kawar da kai gefe "Sani kadai ka sani ba ka cigiyar sauran?"
Uwargidan Mal. Sa'adu tana jinsu ta murmusa da gayya ta ce "Wai wane Sanin ake zance ne? Ko marigayi?"
Mari ta dubeta cikin bacin rai ganin Abbati ya juya da sauri.
"Haba Yaya Deluwa kya dai bari ko abin ci ne yaci mana."
"Au, wai dama bai ji labarin mutuwar kanin nasa ba?" Deluwa ta furta kamar bata ji me Mari ta ce ba.
Abbati sai ya matsa kusa da ita hankalinsa a tashe.
"Iya Deluwa wane Sanin ne ya rasu?"
Sauran matan gidan duk sai suka fito aka dinga cewa "Allah Sarki" da karyewar murya mai cike da alhini. Yanayin tashin muryarsu kadai sai yasa mutum yaji babu dadi.
"Sani ai ya kusa arba'in biyu a kabari. Yaro yunwa da rashin gata suka yi ajalinsa." Inji wata faccalar ta ta.
Deluwa ta cafe da saurin kwabarta "ko kiyaye bakinki dai. Ah to. Malam ya ce mutuwar jahadi ya yi tunda a bakin neman ilimi ne."
Wani irin kuka Abbati ya saka yana zubewa a wurin. Mari da ta sami damar motsawa ba ita ta tsaya ba sai a tsakar dakinta. Ita ma nata kukan take yi har Abbati ya shigo ta share idonta da sauri.
"Zauna in zubo maka abinci. 'Yan uwanka ma babu wanda yaci suna jiran dawowarka."
"Baaba da gaske saboda yunwa Sani ya rasu?"
Tambayar ta daki zuciyarta. Ta laluba ta rasa amsar da ta dace ta bashi.
"Bana son yawan tambaya. Almajiranci ne anyi an gama. Ka dawo kenan ba za ka koma Kano ba."
Nan fa Abbati ya yi wuf ya mike yana mai tuno Munzali da abin da suke yi sannan da irin abincin da suke ci wanda bai taba samu a kauyen.
"Ni dai zan koma."
Bata kawo komai ba a ranta illa gargadin da tayi tsammanin anyi masa akan kada ya zata ya gama karatun kenan. Kannensa mata ta kira suka hadu su hudu ta zuba musu abinci a babban farantin da ya kasance murfin fanteka. Shinkafa ta dafa musu wadda ta kwana hudu tana tsinta. Sai miyar dage-dagenta da tasha naman zabi taji gishiri da kafi zabo (vedan).
Farincikin ragowar yaran a bayyane yake. Cikinsu babu wanda bai hadiyi yawu ba tun kafin ta ajiye musu abincin. Naman ta saka musu yanka dai-dai shi kuma Abbati guda uku.
Abin dariya da ban tausayi ya hade duka lokaci guda. Ci suke kamar mayunwata yau an sami shinkafa. Abbati kuwa loma daya ya yi da kyar ya kasa ci. Ko kadan girkin da mahaifiyarsa ta sha wahalar hada kayan yinsa da wahalar girkawa bai burgeshi ba. Salam haka yake jin dandadon girkin. Miyar ma a idonsa bata yi kyau irin na wadda ya saba ci ba. Ga kannensa suna ta wawa shi kuwa shinkafa ma har ta soma gundurarsa.
Mari ta lura baya ci sosai duk sai ta damu. Me yiwuwa ko zancen rasuwar Sani ke damunsa. Sai da suka gama tayi masa magana. Naman ma tana kallo ya bar musu suka cinye.
"Abbati ka cire damuwa daga ranka ka dinga saka Sani a addu'a kaji. Yanzu me ka ke marmarin ci? Naga kamar ka kasa cin shinkafar."
"Da kin sani tuwo ki ka yi min Baaba."
Yana gama magana ta tashi. Iccen da ta zubawa ruwa ta tura gefe ta duba bata da isasshe. Yaran nata sun fice wasa dole ta saka mayafi ta fita. Da kanta ta karbo itace a wurin kanin Inuwa a waje tazo ta hura ta dora ruwan tuwo da miya.
Kan kace meye wannan ta gama tuwon dawa da miyar busasshiyar kubewa. Dakunan faccalolinta dake kusa da ita sai leken tsakar gidan suke ana hadiyar yawu. Inuwa kansa da ya shigo bai iya daurewa ba ya bukaci ta zuba masa.
"Malam ga fa naka abincin. Tuwon na Abbati ne."
Zai sake magana ta bude tasar yaga shinkafa da miyar nan. Tuni ya manta da batun tuwo ya tsoma hannu ko wankewa bai yi ba. Loma manya manya ya dinga shirgawa kafin ta farga sai kwano babu kwayar shinkafa ko daya. Ya daga kwanon sha ya kurbi ruwa sannan ya yi mata godiya. Akuyarta ta sayar ta auno shinkafa, kayan miya, zabi da kayan abincin da ya san bai ajiye ba kuma bashi da kudinsu.
Tana lura da yadda 'ya'yan gidan ke mata kai kawo a bangarenta saboda girkin da tayi. Da can ma tare suke cin abinci da nata yaran. Amma tun tafiyar su Abbati karatu aka dinga gulmarta ana cewa bata san darajar addini ba. Da kansu iyayen suka raba musu kwano. Gwaggo Mairo kadai ta kaiwa abincin ta sharesu.
Da Abbati ya dawo daga gaishe da 'yan uwa da ganin abokansa ta ajiye masa tuwon fuskarta dauke da murmushi. Wani guntun kakide da aka bata a gidan Sarkin Noma da take ta janjani yau duka ta zuba masa. A zatonta yadda Sani ya zauna cikin wahala da rashin abinci shi ma hakan ne.
"Ashe kakiden nan rabonka ne nake ta boyonsa sai ranakun daidai muke ci. Na san ka fimu bukata."
Kallon tuwon nan ya yi yaji gabadaya zuciyarsa tana tashi. Miyar a idonsa tsululu tayi sai mai a sama. Ya kile fiye da zato da tsammani. Abincin sayarwa ma ba na kowacce 'yar talla suke ci ba.
"Ci mana Abbati. Ko a baki ka ke jira na baka" ta ce tana 'yar dariya.
Kwanon ya ja gabansa ya saka hannu. Kadan kadan yake gutsira sai Mari ta tashi ta bashi wuri. Karshenta dadewar da suka yi basu hadu ba ce take saka shi kunyarta.
Tana tashi ya bi bayanta ya tabbatar ta bar harabar bangarensu sai ya dauko kwanon ya nufi garken awakinta. Dama tuwon ya yi da hannunsa tana kallo. Lokacin Inuwa ya aiko ta a bashi buta zai yi alwala a waje. Mamaki ne ya kamata yadda Abbati ya hade rai ya jagwalgwala tuwon ya juyewa awakin.
Ita bata ci ba. Bata bawa mahaifinsa da kannensa ba amma ya wulakanta shi haka. A jikin kyaure ta labe tana kallonsa har awakin suka cinye sannan ya ajiye kwanon a wurin wanke-wanke. Kwalla ta mayar da ta cika idanun ta taho kamar shigowarta kenan.
"Ba dai har ka gama ci daga fita ta ba?"
"Na cinye shi tas Baaba."
Da yake da akwai kuruciya a tare dashi bai yi lissafin tazarar lokacin da ta fita bai isa ace ya cinye ba.
Kada kai kawai tayi bata nuna masa ta ganshi ba amma daga ranar ta sanyawa duk motsinsa ido. Abinci kullum ci yake kamar magani. Da ya dan sami wanda zai ji kuzari sai ya tashi. Hankalinta fa ya tashi ta tafi wurin Mai maganin shawara ta karbo masa. Mutumin ba kudi yake karba ba sai dan abin sadaka. Haka tazo gida ta dinga tafasa masa yana sha tana yi masa sirace. Babu wani chanji a tare dashi amma haka ta daure kullum ba fashi sai anyi. Ana haka Jummai kanwarsu Inuwa dake aure a Karkarna wani kauyen Jigawan ne shi ma tazo ganin gida. Ta taho da 'yan yaranta guda uku su ga kakarsu Inna Mairo. Babban namiji da bai fi sa'an Sani ba sai kannensa mata biyu.
Ranar da ta kara wargaza farincikin Mari ta kama alhamis. Ita da Jummai ke gurfane gaban Mal. Sa'adu suna magiyar kar a mayar da Abbati Kano.
"Yaya tunda Mari bata so kuma ga abin da ya faru da Sani don Allah a hakura mana" cewar Jummai kamar za tayi kuka. Ita da Mari sun kasance aminai tun kuruciya.
Mari da take suruka ba zai iya zaginta ba amma Jummai sai da ta zubar da hawaye saboda kaifin maganganunsa gareta.
Suna can suna roka masa ingantacciyar rayuwa ashe shi kuma jarabar tsiyar da ya koyo ta kwana biyu tana addabarsa. Ya rasa da wa zai yi a gidan ba tare da an tona masa asiri ba.
Shigowarsa gida kenan daga wajen wasan gare-gare da suke yi da abokansa ya hango Hanne. Ita ce 'yar Jummai ta biyu. Ita kadai ce take kwaba kasa tana wasanta. Munzali ya bashi labarin ranar da ya yi da 'yar makotansu.
"Ba don munafukar Innayo dinnan ba da kullum sai na daukota munyi. Amma kawai ta shigo mana daki don gulma."
Bai manta yadda suka zauna suka zagi Innayo ba bayan Munzali ya ce masa matar uba ba uwa ba. Wannan karatun Asabe ne ya yi amfani dashi wurin sake batawa Abbati tarbiya. Bai taba raina amaryar babansa ba sai yanzu da yake jin da za ta shiga hurumin Mari zai rama mata.
"Hanne zo ki karbi adua" ya kirata yana fito da aduar da suka tsinto a hanyar gida.
"Bana sha."
"To zo muyi wasan doki. Sai na goyaki mu shiga dakin baya."
Dakin bayan kamar rumbu yake. Kayan abinci ne idan mazan gidan sun girbe amfanin gonarsu kowa nan yake ajiyewa.
Da sauri ta taso ta dane bayansa. Yana ta gudu da ita da wayo da wayo ya tafi dakin bayan.
('Ya 'yar uwa, ban ce ki dora zargi akan 'ya'yanki ba. Amma yana kyau idan suna wasa a kebantaccen wuri lokaci zuwa lokaci ki dinga lekensu a boye. Zamani ne muke ciki