Showing 174001 words to 177000 words out of 242549 words
bashi tana cewa taji kamar ya kirata ne. Sai da ya gama fadan ya koma dakin yana cilli da kaya.
"Me kake nema ne in tayaka?"
"Mukullin dakin Rabilu nake nema wanda na bari a cikin wando"
Kai ta jinjina tana tunanin wato can zai je da yarinyar. Dauko mukullin da ta gani da tana ninke wandon tayi ta mika masa. Haka ya warce shi a hannunta ya fita da gargadin ta jira sai ya tafi.
*
Sakon da Ayaah ta turawa Suhaib ya riske shi ne suna kurkusa da unguwarsu Danliti. Tun fitowarsu har yanzu bai fasa ambaton Allah cikin addu'a da fatan nasara ba. Da ya gama tura mata amsa ya sanar da abokan tafiyar tasa abin da ta ce. Guda a cikinsu sai ya ce su karasa gidan nasa. Kila suyi sa'ar samunsa ko su tambayi matarsa ina yake.
"Muna ma iya cewa ta kira shi ta ce anzo nemansa akan motar da ya dauka da 'yan sanda. Na san da wuya idan bai tsorata ba"
Shawararsa ta sami karbuwa suka karasa. Da yake Allah Maji roko ne sai gashi sun sami fiye da abin da suka saka rai.
Wanda ya bada shawarar ne ya yi sallama a kofar gidan. Ta fito da yaranta da 'yar ghana must-go wadda ta zubawa kaya. Ta ganinsa ta dan saki fuska suka gaisa. Ba tare da bata lokaci ba ya ce,
"Idan kin san inda Danliti yake ki fada min don Allah. Daga gyaran mota ya dauko motar wani mutum. Yanzu haka yace 'yan sanda zai kawo mana."
Sauke jakarta tayi daga dakalin kofar gidan tana cewa "ba zan fada ba don laifin nasa ya kara yawa a dukkan dakikar da 'yan sandan suka wahala nemansa. Sannan idan kun hadu ka fada masa ya aiko min da takardata."
A rikice ya ce "kiyi hakuri ki taimaka mana"
Su Suhaib suka firfito ta dubesu ta kau da kai.
Suhaib din ne ya tako gabanta ya dubeta a mutumce ya ce "don Allah ki taimakeni kada ya keta haddin 'yar mutane. Har makaranta ya bita ya daukota yana shirin bata mata rayuwa."
Da sauri ta dago kai tana mai tono yarinyar da ta gani.
"Bari na shiga adaidaita sahu ku biyoni in kaiku inda nake tunanin zai kaita"
Suhaib ya ce na gaban ya koma baya ita da yaranta su zauna. Su da suke makanikai basu fitar da warin jiki irin nata da na yaran ba. A haka kuma ba karamin kokari take ba. Duk albashin Danliti a cin banza da hofi sai yan mata yake karewa. Sabulun wanka da wanki sai tayi kamar ta ari baki. Ruwa ma iya na girki kadai yake saya mata. A haka take cancanawa suyi wanka bayan kwana bibbiyu ko uku. Ga zafin gari da ake fama.
Kai kawai Suhaib ya dinga kadawa cikin takaicin wai wannan matar aurece. Mace da ake son a mutunta amma ita ce nata mijin har yake da guts din zuwa kofar gidansa da yarinyar da zai nema ta gani. Kodayake ba kansa farau ba da ya tuna nasa uban. Neman tsari ya dinga yi akan fadawa wannan kaba'ira ta zina har suka kai kofar dakin Rabilu. Ya kuwa laluba aljihunsa ya bawa yaran dubu goma ya ce ga kudin mota. Bata cuci kanta ba ta karba tana ta godiya.
***
Da kuka Ummita ta shiga gida duk da irin gargadin da Abdulkarim ya yi mata akan tayarwa iyayenta hankali. Kasa daurewa tayi tana shiga ta fada kan Innayo tana kuka. Hasiya ta saki cokalin dambun da take ci ta tashi da sauri tana tambayarta me ya faru.
Maimuna da Innayo basu dade da shigowa gidan ba. Kuma hirar dadewar Ummita da rashin samunta a waya ake yi sai gata ta fado.
"Ki yi min magana Ummita me ya same ki?" Hasiya ta sake tambayarta tana hawaye tun kafin taji me ya faru.
"Anti an sace Ayaah. Har makaranta wani yazo ya bawa maigadinsu kudi ya tafi da ita"
Hankalinsu ashe bai tashi da kukan Ummita ba sai yanzu da tayi magana. Kan kace meye wannan gidan ya rude da kukan mata. Murja, Hasiya, Ummita da Maimuna babu mai rarrashin wani. Innayo ce tayi ta maza ta daure tana basu hakuri. Suna kukan suka ji sallamar Honourable da yaron da ya taya shi rike Abbas suka je aka yi test. Kukansu ya saka shi shigowa tun kafin su amsa. A nan yaji labari mara dadi. Gidan ya sake cika da Larai (mahaifiyar A'i) dasu Hasina kannenta. Sun zo duba Abbas ne saboda Honourable ya fada musu za ayi masa aiki. Wannan ya sake dagula lamarin domin fada ne kuma yaso kacamewa.
Larai tana kuka ta ce "Hasiya naji labarin kina da ciki ai. Wato kafin ki haifa zaki fara daidaita 'ya'yan marigayiya saboda kina tunanin samun gado tunda maigidan ya soma farfadowa."
Hasiya bata iya cewa komai ba da yayyenta suka hada baki ana ta fada mata maganganu. Innayo ta hana Maimuna da ma Murja da Ummita din mayar da martani. Batan Ayaah ne a gabansu ba zantuka marasa amfani a gaban suruki ba. Maigidan kansa kasa tsawatarwa ya yi saboda yawunsu da kuma damuwar da yake ciki. Tunda ya ce suyi shiru suka ki sai kawai ya fita zai tafi makarantar. 'Yar nutsuwar da ya samu ma ta biyo bayan kiransa da Abdulkarim ya yi suka shigo gidan tare. Shi ya fada masa case na hannun 'yan sanda ana bincike. Ko sau daya babu wanda ya yi tunanin kiran wayarta saboda gargadi da jan kunnen da Hasiya take mata akan zuwa da ita makaranta. Duk sun zata wayar tana gida saboda haka babu amfanin kiran.
***
"Shigo mana Baby" Danliti ya ce da Ayaah bayan ya zura mukulli ya bude dakin shagon Rabilu.
Rainin wayon nasa ne ya bata mamaki ta ce "ban gane in shiga ba? Ya zaka ce min zan je gaishe da mahaifiyarka ka kawoni nan?"
Hagu da dama ya dan waiga bai ga idon kowa a kansu ba kawai ya fizgota cikin dakin ya rufe kofa. Budar bakinta zata yi ihu ta rufe sakamakon tozali da hoton tsohon saurayinta Rabeel (Rabilun Danliti).
Cikin kidima ta ce "Dani dama ka san Rabeel?"
Danliti ya kwashe da wata irin dariya harda tafa hannuwa kamar biri a hannun mai wasa dashi.
"Idan ya shigo anjima zai yi miki bayanin da zaki gamsu. Ni nan cire hijabi zaki yi mu farantawa juna rai."
Kallonsa tayi taji dukkan wata tsana ta duniya ta tattara a kansa. Ga haushin rashin hankalinta da ta bari ya yi wasa da tunaninta.
"Ashe abin da aka fada min gaskiya ne duk da dama bana tunanin mai fadar zai yi min karya."
Danliti bai wani damu da maganarta ba ya kama kayan aron jikinsa ya soma cirewa. Ayaah ta juya ta fara dukan kofa da ihu taji ya daka mata tsawa.
"Juyo nan ki gani"
Ta juya a fusace ai kuwa tayi tozali da kakkaifar wukar da yake nuna mata. Shi ma cikin fada ya ce,
"Ki kama bakinki ko idan na gama wallahi in kashe ki in kashe banza."
Durkusawa tayi a wurin ta fashe da kuka "me nayi maka da ka zabi cutar dani?"
Kishingida ya yi akan katifar daga shi sai singileti da gajeren wando masu dan banzan datti yana wasa da tsinin wukar ya zuba mata idanu. Sau daya ta kalle shi taji amai ya taso mata. Wani uban gashi ne a hammatarsa wanda da gani har kitso zai yi.
"Bana son munafunci bayan na san kema kina so. Banda gulma me zai sa ki biyoni wai zaki gaishe da Mummy? Ni Innata tana kauyenmu."
"Naji na cuci kaina don Allah kayi hakuri ka barni na tafi"
Danliti ya sake yin dariya "dama ai ba kwana na dauko ki kiyi mana ba. Za dai mu gwangwaje a jikinki ne kawai mu kaiki gidan tsohonki." Kula ya yi kamar tana danne amai ya dinga dariya "wai nan kyamata kike ji? Tabdi. Yarinya wannan jikin yau zai kafa miki tambarin da har ki mutu ba zai goge ba"
"Allah Ya fika" ta ce cikin kuka tana tofar da yawu."
"Ke dai anyi azzaluma. Kina ta kada jiki a gabana amma kin kasa karasowa ki bani kasona? Ki taso kafin na farde kayanki da wukar nan"
Duk wata magiyarta bata yi tasiri ba. Gashi babu halin buga waya. Karshe kayanta ya umarceta da ta cire ta zo ta same shi akan katifar. Da taki ya taso ya kamata ya tsarge hijabin ya wurgar dashi. Ayaah ta fashe da wani irin marayan kuka mai ban tausayi. Duk wata hudubar Anti Hasiya ta dinga dawo mata. Matsatsiyar rigarta ya gani yana karewa surar jikinta kallo harda lasar labba. Ta sake dukawa tana bashi hakuri ya dagota ta mike ya dalla mata mari saboda ransa ya kai makura sannan hakurinsa ya kare.
"Ni ban daukoki domin na gwada miki karfi ba. Soyayya mai zafi nake son mu shayar da juna amma kin tsaya kina neman yi min taurin kai. Wallahi idan kika bari na saka miki karfi yau ko uwar da ta haifeki ba za ta ganeki."
Hankadeta gefe ya yi ya koma ya kwanta rigingine da wukarsa a gefe ya dauko tecno dinsa ya kunna wata mahaukaciyar waka ya kure sautin.
"To maza ki cire kayan ki zo muyi rawa."
Ayaah taga cin mutumcin da tozarcin nasa sun wuce tunaninta. Yadda zata samu ta karbi wukar hannunsa ma dabara ta kare mata. Bata daddara ba kawai ta juya tayi masa ba zata wurin dukan kofar dakin da hannuwa biyu, iyakar karfinta. Danliti ya taso a guje bayan ya jefar da wukar zai kamota. Iskancin nasa na matsorata ne domin kuwa yana tsoron 'yan layin su farga a dauki mataki. Sun saba kawo yan matan da suka amince ne ba jjc irinta ba.
*
Ayaah na wannan bugun Suhaib na gama mikawa matar Danliti kudi. Kusan a tare shi da tawagar makanikai da ita suka kalli kofar. Baiwar Allah sai ta kada danta tabar wurin. Duk lalacewa bata son yaron yaga ubansa a yanayin da ta tabbatar zai shiga na muzanci nan da dan lokaci.
Jikin Suhaib na tsuma ya karasa jikin kofar suna biye dashi ya soma bugawa iyakar karfinsa.
Danliti da Ayaah suka kalli kofar a tare. Dankwalinta da gashinta ya hada ya yiwa mugun riko dama yana shirin fizga yadda zata ji zafi aka yi bugun.
"Waye?" Ya tambaya muryarsa ta fito kamar ta kyanwa don ya tsorata.
Ogansa ya yiwa Suhaib alamar ya yi shiru sannan shi ya yi magana da kaushin murya.
"Mutumin banza bude ka bani mukullin mutane don tare muke da 'yan sanda"
Yawu ya hadiya ba shiri " 'yan sanda kuma?"
Sake buga kofar Suhaib ya yi da karfi Danliti yaji kamar ya saki fitsari a wurin. Yana can hankalinsa a rabe da tunani bai farga ba Ayaah ta dauki wukar da ya yar sai kawai gani ya yi ta nuna shi da ita.
"Ko ka bude kofar nan wallahi ko na burma maka wukar nan a cikinka"
Shi ya jiyota, na waje ma kowa yaji abin da ta ce.
Jikin kofar Suhaib ya raba da sauri ya ce "Ayaah?" da taushin murya.
Kuka ta fashe dashi tsabar farinciki "na'am?"
"Kada kiyi abin da zamu yi regretting kinji ko?"
Kai ta gyada tana wani kukan ta dubi Danliti "ka bude ni"
Gaba kura baya sayaki. Wukar hannunta bata dame shi kamar jin muryar shegen yaron nan ba. Idan bai bude ba ma zasu balle kofar ne ayi masa abin da aka ga dama. Saboda haka babu yadda ya iya haka ya zura mukullin ya murda kofar.
Mukullin yana yin karar ta bude kafin ma ya zare sakatar da ya saka ta sama yaji sun yi baya tare da kofar. Wawan bugu Suhaib yayi mata da kafa sai da ya jijjigeta gabadaya ta balle. Ayaah na ganin hasken waje bata yi wata wata ba ta danna kai a guje sai ji tayi sun yi karo da mutum har suna shirin faduwa. Dole ya saka hannuwa ya tarota. Tsigar jikinta da nasa suka tashi lokaci guda da suka hada ido cikin ido karo na farko tun haduwarsu.
Da sauri Suhaib ya sanya hannu ya rabata da jikinsa. Kallo guda ya sake yi mata ya runtse idanu. Rigarta ko kadan bata dace da ganin idanunsa ba balle na wasu. Bai yi tunanin komai ba ya shiga balle maballan shirt din jikinsa. Rigar dogon hannu ne da ita. Cireta ya yi ya rage farar T-shirt din jikinsa. Ayaah bata ankara ba taji ya dora mata rigar ta gaban kirjinta.
"Rufe jikinki ki jirani a waje" ya ce ba tare da ya kalleta ba. Da sauri ta fice kuwa ta koma gefe tana share hawaye.
Kansa tsaye ya fada cikin kazamin dakin mai warin kazantar kaya da ta fasikancin da aka jima ana yi a cikinsa. Da kafa ya doke kofar daga kan Danliti yasa kafarsa dake cikin hadadden cover shoe ya danne tsakiyar kafafun Danlitin.
Razanannen ihun da Danliti ya yi sai da yaje kunnuwan makotan shagon. Mutane suka firfito ana kallon ikon Allah. Ayaah kanta durkushewa tayi ta cusa yatsunta a cikin kunne. Tsinuwa da zagi kala kala daga bakin jama'a ana fadin yadda suka mayar da dakin dandalin yan mata.
Suhaib kuwa bai ragawa Danliti ba don ko kadan bai yi niyar cire kafarsa nan kusa ba. Ogan makanikan ne ma ya ji tsoro yaje ya riko shi.
"Yallabai ka yi hakuri ka bari a hadashi da hukuma kada ka dauki mataki a hannunka."
Kamar ba zai dauke kafar ba sai ya cire. Sauran mazan kamar su ya yiwa suka dinga sauke ajiyar zuciya. Suhaib ya shammacesu ya sake daga kafar kawai kuma buga masa. Ihun Danliti har yafi na dazu don suma ne kawai bai yi ba saboda azaba.
Biyu cikin makanikan suka leka waje wurin Ayaah.
"Ki zo ki yi masa magana kada yayi kisa"
A hanzarce ta tashi ta koma kofar dakin. Ta san sunan shi tunda kannensa sun fada taji. Amma bata san ita me ya dace ta kira shi ba. Wasu hawayen ta goge ta sami kanta da cewa,
"Yaya"
Suhaib ya juyo ransa a matukar bace
"Ban ce ki fita ba?"
"Ka zo ka kaini gidanmu don Allah"
Yadda tayi maganar da sanyin murya ya taba shi sosai. Cije lebensa ya yi don bai so barin Danliti haka ba ya biyo bayanta. Haka ya tasata a gaba har bakin motarsa don baya son kowa yaga bayanta. Da kansa ya bude motar har ta shiga sannan ya rufe ya zagaya barin direba ya zauna. Yana tuki yana kula da hawayen da take gogewa lokaci-lokaci da rigarsa mai kamshi. Sai da suka bullo titi ya yi mata magana.
"Ina zamu bi?"
"Dama"
Shiru ya sake mamaye motar na 'yan dakiku sannan ya ce,
"Ba kya jin magana ko? Abin da ya faru shekaranjiya bai isheki ba sai da ki ka biyo shi"?
Da jajayen idanunta da suka rine saboda kuka Ayaah ta dube shi.
"Kayi hakuri don Allah."
"Ya tabaki?" Ya tambayeta idanunsa na kallon titi.
Ta girgiza kai tana wani kukan. Ba don sun zo ba da yanzu tana can ya gama da ita.
"Dago kanki ki dinga yi min kwatance"
Umarninsa tabi ta dinga kwatanta masa har suka shiga layinsu. Nan ta tarar da motar 'yan sanda har biyu a kan layin.
"Kinga abin da kika janyo a gidan ko?"
"Ai ba zan kara ba"
Suhaib ya taka burki ba shiri ya kalleta "tunanin karawa dama kike yi?"
"A'a" ta amsa masa da sauri.
Da ya tsaya tare suka fito daga motar. Shi da ita duka kunyar suturar jikinsu ta kamasu.
"Kinga abin da kika ja mana ko?"
Kunkuni yake don bai san da yaya ma zai shiga gidansu ba. Tsayuwa ya yi a hanya yace ta karasa. Tayi narai narai da idanu za ta yi kuka.
"Don Allah kazo kayi musu bayani. Yau ina jin Baba sai ya yi min duka."
"Banda abinki Ayaah, ance miki bana so a dake ki ne?"
Baki ta bude amma bata iya cewa komai ba ta rufe. Ta zata ba zai karasa din ba sai gashi ya cigaba da bin bayanta har kofar gidan. A tsorace ta saka kafa sai ta dawo da baya. Gabanta ke faduwa bata san abin da iyayenta zasu yi mata ba.
"It will be okay. Ki shiga"
"Wallahi zuciyata kamar za ta fito ta baki."
Tausayi ta bawa Suhaib sosai. Bai san tun yaushe take ta kuka ba yau ga wani ta fara na tsoro. Rab'awa ya yi ta gefenta ya shiga kofar farkon sosai.
"Assalam alaikum wa rahmatullah."
Murya tafi biyar da ta amsa. Amma a ciki Ayaah ta bambance ta babanta da Anti Hasiya.
I just published "37" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1133888814?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=8bORFMwuNDQyr%2BfdoI7yxGIK4CEE8lbtGac2Zw5bWunyGWNSmVrSo5i2xfNSEwWAqh9k101JzBETDaJ4m%2FU5XfSegbkS4kRSc%2Bon%2FQk3gZry7YcyktZ%2BmwMkk%2FSCjmwv
UWA UWACE...37
Batul Mamman💖
{Fatan alkhairi ga masu bibiya tare da hakurin jiran post. Ba zan gaji da bayar da hakuri ba. Ciwon hannu ya sakoni a gaba. Wadanda muke group tare da masu turo sako private duk sun daina ji na sai jifa-jifa. Sakonninku birjik a whatsapp da wattpad harma da instagram amma dubawa ta gagareni. Masu kira Allah Ya saka muku da alkhairi. Babu dama na daga waya sai nayi jinyar hannu. Ina kan magani yanzu kuma Alhamdulillah sauki yana samuwa. Shi yasa nake ta lallaba hannun. Na so kwarai sai na kammala tas kafin na kara post. To amma na sami kiran wasu da sako wadanda suka ce na turo abin da ya samu ko babu yawa. Bana son zama mai karya alkawari tunda na kan ce na kusa a yayinda nake jin saukin hannun. Da zarar ciwo ya dawo sai na bar rubutun. Ku kara hakuri mu lallaba har mu kai karshen Uwa Uwace.}
For THE QUEENS, because they deserve it. Na gode
***
Abbati ya zagaye gidansa yafi a kirga. Babu wani lungu da sako da bai leka ba bayan fitowarsa daga wurin Baaba Mari. Akwai wuraren da rabonsa da taka kafarsa tun ana ginin. Wasu irin tunane tunane suka dinga zarya a cikin kansa. Son muhallin nasa ya darsu a zuciyarsa irin wanda bai taba ji ba. Sai idanu sun zaga sosai a cikin garin nasu ma za a sami gida makamancin nasa. Lallai shi yasa ake cewa idan an ga matashi da kudi bayan bashi da kwakkwarar sana'a ya kamata a bincike shi. To wai ma ya aka yi bai taba jin korafi ko da wasa game da tarin arzikinsa da wadak'ar da yake da kudi ba a garin? Ko ana tsegungumi a bayan idonsa ne bai sani ba? Yau daya da ya yiwa gidan kallon tsanaki sai ya fahimci yawan titsiyen da Baaba Mari take