Showing 18001 words to 21000 words out of 242549 words
taji ciwon nakudar da ya zarce na Abbati. Lokutan da ta dinga sake-saken burikanta akan kyakkyawar rayuwar da take masa fata kamar yadda ta yiwa Abbati. Fuskar Saninta wanda yake ta kuka ba zai je almajiranci ba take gani. Yaron da jiya jiyan nan ta ganshi ana turmususa a cikin kasa akan lomar abinci.
A kwana na biyu da rasuwar ta dan dawo hayyacinta. Kuka take yi ta rungume ledar magungunan da ta bashi. Muryarsa ke yi mata amsa amo tana jin lokacin da yake rokonta ta kara masa magani. A yayin da wasu zafafan hawaye ke kwarara a idanun Mari sai ta bawa Inuwa tausayi. Shi ma din zuciyarsa ta dinga raya masa lallai su dawo da Abbati gida.
Wani abin ban tausayi ga wannan mata bai wuce har ita ma ta koma ga Allah SWT ba za ta taba sanin ainihin sanadin ajalin danta ba. Komai a rayuwa yana da sila. Hakkin ran Sani yana rataye a wuyan jama'a da dama. Babban cikinsu Mal Sa'adu mai ingiza kai yara almajiranci. Ga Inuwa da ya kasa jajircewa wurin kare amanar da Allah Ya bashi ta 'ya'ya daga dan uwansa. A gefe guda ga Malamin tsangayarsu da bai rike amanar da aka bashi ba ta yaran mutane. Matar da yayi bara a gidanta ta bashi lalataccen abinci saboda rashin sanin girman hakkin bil adama. Yaran da karancin tarbiya da kulawa ya janyo suka yi masa duka akan abincin da ya samo. Mai sayar da maganin da bashi da iliminsu ga mutane saboda neman kudi. Gwamnatin da ta yarje masa yawo a tituna da kwararo yana sayarwa bayan bashi da lasisin bada magani. Kaico! Hatta Mari da ta bawa Sani magungunan nan bisa rashin sani da tsantsar soyayya irin ta uwa da ďa bata tsira ba. A takaice dai the society killed Sani!
***
Kalmar hutu kanta tana da dadin fada a baki balle kuma idan jiki zai same shi a aikace. A wurin Innayo kuwa daga mai arziki sai wanda bai san ciwon kansa ba kamar Asabe ke hutawa. 'Yan mata biyar a gabanta babu mai basu sai abin da Allah Ya hore mata daga kasuwancinta. Biki ko suna da wuya yake hanata dora tukunya. Abin da ya kama dole taje to lallai wata cikin 'yan matan za ta zauna a gida. Yau kuwa dole ta saka ta zaman gida tana hutun dole.
Ranar ta kama litinin. Ta tashi da ciwon kirjin da ya kan damketa lokaci zuwa lokaci. Yaran nata kuma duka suna makaranta. Zara da bata kaunar karatu sai gayu ta so zaman jinya amma Innayo ta kora ta. Hudu suna zango na uku a makaranta. Jarabawa ake yi ta canjin aji ba za ta so a sanadiyarta wata ta maimaita ba. Babbar kuwa shekararta ta farko kenan a School of Nursing. Ayyukan da basu zama dole ba Innayo ta dauke mata a gidan saboda kawai ta sami isasshen lokacin karatu.
Tsakar gidan nasu tsit sai ita kadai a daki. Alh Rabi'u yana kasuwa. Asabe kuma makota ta shiga saboda an kusa sauke sanwar rana. A can za ta ciko cikinta su kuma yaran ta dafa musu gurjiya kowa ya ci ya sha ruwa babu ruwanta.
Zumbur Innayo ta tashi da ta tuna ta sa a jika mata gero tun dare amma ciwo ya hana ta wanke a kai nika. Idan ta barshi zai lalace gashi har kwano uku. Tashi tayi da kyar tana dafa bango ko ruwan ne ta samu ta canja. Bandaki ta fara zagawa domin rage mara taji taku da 'yan maganganu anayi. Gida na jama'a bata wani damu ba ta kammala ta fito. Babu kowa har yanzu a tsakar gidan ta zauna tana wankin geronta.
Kwana biyu da suka wuce Munzali ya yi wata magana da dan kanwar Asabe da yazo musu hutu. Shi satin da ya gabata suka gama tasu jarabawar. Yaron mai suna Halliru ya girme shi da kusan shekara biyu.
"Idan ka yarda muka yi aradu yau abincinka da nama" ya ce saboda ya fahimci amfani da kayan kwadayi yana taimakawa wurin samun biyan bukata.
Halliru ya kai masa duka a kafada yana dariya"ashe kai gara ne ban sani ba" karkada hannu ya yi tare da jijjiga kai yana yi masa kallon rainin wayo "to bari kaji in fada maka da mata ake yi ba maza ba. Na taba gani a lungun gidan Mai kalanzir din unguwarmu."
Dan jim Munzali ya yi yana nazari daidai kwakwalwarsa kafin ya ce "kai ka taba yi da macen ne?"
A kunne Halliru ya rada masa cewa suna yi da kanwarsa idan babu kowa a gida. Ya kara da yi masa bayanin yadda suke jindadi. Shi ma 'yar makota ce da ta girme shi ta koya masa shi kuma ya koyawa kanwar. Da 'yan shekarunsu ya kwadaitawa Munzali son gwadawa.
Shi ne fa ya bawa 'yar makotansu inda Asabe ta shiga kwadayi kafi-kaza ya taho da ita gida lokacin da Innayo ta zaga.
Tare suka je gidan da Asabe ta kore shi da mugun kallo "shegen yaro kwalamamme. Ka biyoni salon taga munyi mata yawa taki zuba min abincin. Banda abinka idan ta bani ba zan rago muku ba?"
Cike da tsiwa ya ce "za dai ki rago musu. Yaushe rabona da cin abincin makiyalla."
Baki ta sake maganar ta shigeta ta daga hannu za ta kai masa mari "kut! Nice ma nake makiyalla?"
Juyawa ya yi zai tafi idonsa caraf akan 'yar gidan da bata fi shekara shida ba. Da sauri ya dago ledar kafi-kazan yana kiranta. Kafin ta iso sai da Asabe ta karba ta barbada a tafin hannunta ta lashe.
"Munzali kenan. Kai dai ba dai mutane masu insani ba. Kwanakin nan har wani kumatu ka dire." Ta kai hannu ta yi masa dukan wasa "ni ko saura ne ka dinga rago min a leda mana. Sai bakin hali irin na ubansa."
Shigewa tayi shi kuma Munzali ya sami damar hillatar yarinyar suka tafi gida. Ya zata gidan ba kowa. Dakin Asabe ya shiga da ita inda babu kowa ya ce ta zo ya koya mata wani abu.
Da kananun shekarunsa shaidanci ya shige shi har ya sami amincewarta ta cire kaya yadda ya umarceta. Karatun Halliru ya soma aiwatarwa akan yarinyar da bata san me ake yi ba.
"Kar ki fadawa kowa kinji. Zan dinga baki tsamiyar biri da kafi-kaza."
"Harda tsamiya gaye?" Ta tambaye shi da murmushi.
"Duk abin da kike so zan dinga baki indai baki fada ba."
A can gidansu kuwa Asabe tana ta sharbar faten tsakin da babarta ta bata.
Innayo tana wankin gero taji kamar ana magana kasa-kasa. Gajiya tayi da sharewa ta tashi ta nufi dakin. Duk a zatonta abokan Munzali ne. Satin da ya wuce Asabe ta tafi yawonta aka zo aka dauke mata kudin dashi. Tayi ta rantsuwa wai cikin 'ya'yan Innayo ne. Shi ne ta tashi ta leka don kada a sake sakata biyan kudin da ta san karya ake musu.
Tana daga labule tayi mummunan gamo. Da sauri ta afka dakin ta cakumi wuyan Munzali ta kifa masa wani gigitaccen mari. Tana dukansa amma jikinta ke rawa kuma ita ke fitar da hawaye. Idanunsa kyamas abin sa ya ja wandonsa ya mayar. Yarinyar kuwa ko a jikinta. Kafi-kaza ne tayi dumu-dumu dashi tana ta lasa.
Ta baya Innayo taji an riko mata wuya tana juyowa Asabe ta dauketa da mari ita ma.
"Kashe min dan zaki yi?" Ta kwance dankwali taci dammara "muguwa, makira. Ba tun yau na san magadan Alhaji sun tsole miki ido ba. Wato niyarki ki karshi a daka babu kowa ki fice."
Yau daya Innayo ba ta kishi take ba. Tausayin Asabe ma take ji saboda wannan halayya idan Munzali ya tashi da ita ba karamar masifa bace.
"Ai dai kya tambayeni me ya yi kafin ki fara sababi. Ganinsa fa nayi akan wannan yarinyar daga shi har ita ba wando...."
Wani irin bugu Asabe ta yiwa kasa da hannu ta tafa hannuwan tana hargagi "ahayyeeeee....anyi walkiya na ganki Innayo. Yau dai rigar munafunci ta sauka an miki tsirara a idona. Wato kiyayyar taki da 'ya'yana har ta kai kiyi musu irin wannan sharri mai muni."
"Asabe. Asabe ki ajiye maganar kishi ki duba tarbiyar 'ya'yanki. Meye ribata idan nayi masa sharri."
Juyo dashi Asabe tayi duk da fargabar dake zuciyarta amma sam ba za ta yarda Innayo tayi mata dariya ba.
"Kai Munzali wai da gaske ne?"
Sai da ya kumburo baki ya ce "Biyoni tayi fa shi ne ta ce in kaita bayi tayi fitsari. Kawai ina cire mata wandon ta hau dukana."
Ajiyar zuciya Asabe ta sauke ta kalli Innayo "to kin dai ji. Haka kawai za ki kulla masa sharri. Yo Allah na tuba yaron nan nawa ma yake? Me ya sani? Ko an fada miki kowa ma irin wadancan shirgin ne da ki ka tara a daka suna yawon ta zubar?"
Lokacin ya yi! Tana kai karshen maganar Innayo ta rama marin dazu. Ba lafiya gareta ba amma tuni ta manta da ciwon. Zagi ba irin wanda Asabe bata yi mata ba ta ja gefe tana kallonta. Damben da take so ta biye mata suyi ne ba za tayi ba. Munzali salin alin ya ja hannun yarinyar ya kai ta kofar gidansu ya kara gaba.
Dare ya raba Asabe ta kasa baccin kirki. Tashi tayi ta koma rumfarta ta taba Munzali.
"Ka tabbata dazu Innayo karya tayi maka?"
Sai da ya murza ido saboda bacci sannan ya ce "Halliru ne ya ce wai da mata yafi dadi."
A baya ta daka masa duka a razane "bude ido don ubanka. Kayi da gaske?"
Lokacin ya wartsake ya girgiza kai "ni ban yi mata komai ba."
Jinjina kai tayi ta ce ya kwanta. Ta san karya yake. Har kasan zuciyarta ta yarda da Innayo da subutar bakinsa ta dazu. Sai dai kuma ko ana muzuru ana shaho ba za ta taba yarda ace laifinsa bane. Wannan magana anyi an gamata daga yau.https://my.w.tt/seH8zVi968
UWA UWACE...5
Batul Mamman💖
Assalam alaikum ma'abota bin wannan labari. Ina alfahari daku kuma ina godiya. Ayi min hakuri saboda dogon jinkirin da ake samu ba post. Yau da gobe sai godiyar Allah. In sha Allah duk lokacin da na samu dama zan dinga typing har komai ya daidaita na dinga yi a kai a kai.
Abu na gaba mutum biyu sun ankarar dani cewa akwai wani littafin mai suna Uwa Uwace a manhajar okada. Kasancewar sunansu daya coincidence ne. Nawa kyauta ne wancan kuma na kudi. Saboda haka zan dinga kara inkiya a gaban nawa sunan domin a daina samun rudani.
Ina godiya
Ina muku SonSo
Stay Safe
***
Kwana goma cif da tarewar Nasima a gidan Tahir. Amarci suke irin wanda iyayen gida ke tsoron ayi musu kishiya su ga irinsa. Kullum sabon nau'in fitsara da rashin kunya Nasima ke kirkira wanda zai batawa Khadija rai. Abin da bata sani ba kuwa shi ne fitar Tahir da aurensa kacokan daga zuciyar Khadijan. Zaman 'ya'ya take yi kamar yadda matan aure da yawa suke yi. Bata da dogon buri ko hangen komai sama da inganta musu rayuwa. Ba don su ba komai wuya da tuni ta koma gidan mahaifinta.
Sati guda ta sani addini ya bawa amarya budurwa tayi tare da ango kafin a raba kwana tsakaninta da ta gidan. A sati dayan sai take yi musu girki na kyautatawa ba don ta burgesu ba sai don ta sami ladan rama sharri da alkhairi. Anyi satin an wuce shiru Tahir bai yi mata maganar su raba kwana ba. Girki kuma bata ga alamun Nasima za ta shiga kitchen ba sai ta cigaba da yi saboda yaranta.
Tana cikin wanke salad Nasima ta shigo kitchen din dauke da kwalin sabon food flask. Tukunyar shinkafar da Khadija ta bari ta karasa turara ta nufa kai tsaye. Khadija bata nuna ta san da wanzuwarta a wurin ba sai da taji ta bude tukunyar. Don karfin hali ma harda cokalinta a hannu ta danna shi kasa domin ta tabbatar ruwan ya tsotse.
"Lafiya?"
Baki ta murguda mata gami da fari da idanu "lafiya kamar ya?"
Ran ta ya soma baci sai dai tayi alkawarin Nasima tayi kadan tayi fada da ita.
"Abincina naga kina shirin budewa."
"Abincinki ko abincin mijinmu? Naga dai shi ya saya don kin girka hakan ba ya nufin ba zamu ci ba."
'Kar ki biye mata' Zuciyarta ta kwabeta a lokacin da taji kamar ta mareta. Suturar jikinta da tun tarewarta irinsu take sakawa ta kalla ta kawar da kai. Gajeren wando ne da bai kai rabin cinyarta ba sai damammiyar vest. Anayi ne don ta tofa ace ta ce shi yasa take bawa iska ajiyarta.
"Ki jira na dibarwa yara tukunna."
Wani irin kallon raini Nasima tayi mata ta soma cewa "ke kin i..." sai taji an bude kofa kuma ta tabbatar Tahir ne. Langabe kai tayi ta kwantar da murya tana bubbuga kafa duk jikinta na rawa "ni dai don Allah Anti Khadija ki karba haka nan. Wayon hutawa kawai kike yi min kin barni inata fama ni kadai."
Kitchen din Tahir ya shigo Nasima ta kwabe fuska tana yi masa shagwaba "Diya (Dear) wai kaji ta kara mana satin amarci ba yanzu za'a fara rabawa ba."
Ko ita ta sarawa kissar Nasima. Jinjina kai tayi harda 'yar dariya.
"Sai fa ba Diya ba"
"Me ki ka ce?" Tahir ya tambayeta ta da murmushin jindadi a zatonsa sun fara hada kai ne.
"Ban ce komai ba" sai ta mayar da dubanta ga Nasima "na baku wata guda don Allah kada ki ce baki karba ba. Da so samu ne ma zan fi son karba idan ki ka fara tofe-tofe da tashin zuciya."
Ta karasa maganar ne tana dibar abinci. Da ta gama ta zo fita ta dakata a gaban Tahir.
"Af...Diya" ta furta kalmar yadda Nasima ke fada da tsantsar rashin wayewa "na ce kada ka manta yaba kyauta tukwuci. Zan zo amsar nawa idan mun gama cin abinci. Da yake ma mu ba mayunwata bane idan za ka saurareni yanzu na san zasu iya jira."
Lebensa ya cije. Magana Khadija ta yaba musu daga shi har Nasima. Haushi ya kama shi ya nemi yunwar ya rasa. Data kawo musu daki ko kallo kwanukan basu ishe shi ba. Tunanin maganganun Khadija ne ya addabe shi.
"Waye ya bata izinin karin kwanakin ma?"
Ya yi kwafa shi kadai. Kila fushi tayi don ya kara kwana uku akan bakwai din. Nasima ya kalla wadda har yau bata dena yiwa abinci cin yunwa ba ya tashi.
A daki ya sameta ta goya Sauda. Tana ganinsa ta dauko form din JAMB ta mika masa. Ta riga ta cike komai, izininsa kawai take nema.
Kallon rashin gamsuwa ya fara yi mata ta hade hannuwanta biyu a kirji. Fuskarta babu alamun za ta yarda da kalmar a'a.
"Da can me yasa baki taba cewa zaki koma makaranta ba da na hana sai yanzu. Don nayi aure kina tunanin bani da sauran hurumin sawa da hanawa a gidana?"
"Kana dashi matsawar ina amsa sunan matarka. Amma ina so kayi min adalci guda daya. Kar ka manta har na koma ga Mahaliccina hotonku kai da matarka ba zai taba..."
Baya so ta kai karshen maganar saboda kar ta ga alamun kunya a tare dashi. Karanta form din ya shiga yi da karfi har sai da tayi dan murmushi.
"Bari nayi sauri naje banki kafin su rufe na ciro miki kudin registration. Allah Ya bada sa'a."
Anyi an gama komai cikin nasara. Khadija ta sami gurbin karanta Business Administration a ABU Zaria. Shirinta take yi hankali kwance ta manta da duka wata damuwar gidansa.
Nasima tana ta fama da laulayi. A gabanta take wasu abubuwan kamar su tara yawu da yunkurin amai. Idan tana yi da tsantsar tausayi zaka ga Khadija tana yi mata sannu. Ko daga murya bata taba yi mata. Haushin da take son bata karshe ita take ji.
Gida Tahir ya kama mata a Zaria mai daki biyu da falo. Ana saura kwana uku ta tafi ya shiga dakinta yaga akwatunan da ya tabbatar ba nata bane ita kadai.
"Kada ki ce min da su Suhaib za ki tafi."
Murmushi ya gani a fuskarta da ta dago kai. Ya fara tsanar murmushin saboda yadda bakar magana cikin nutsuwa take biyo bayansa.
"Haba Diya. Kada ka ce min kayi zaton zan barsu a wajen amarya. Yanzu don Allah idan kai ne ita zaka so na bar maka 'ya'yana? Idan kaine ni za ka bar mata 'ya'yanka?"
Shiru ya yi ta fita daga dakin ya bi bayanta da sauri. Tsohon dakinsa wanda ya zama na Nasima ta shiga. Rabonta da dakin tun tana kwashe 'yan tarkacenta. Zuciyarta wani irin kunci tayi mata. Bakinta har yana daci saboda tunawa da yanayin da ta taba ganinsu amma ta daure.
Sallama tayi Nasima ta zo ta bude kofar tana yatsina. Ganin Tahir a bayanta sai ta saki fuska.
"Anti nemana kike? Ai da kin turo su Lilu sun kirani."
Sai da Khadija ta kallesu su biyun sannan ta ce "dama Diya ne ya ce na bar miki yara nace gara dai mu koma Zariyan tare. Kina fama da laulayi ba iya wahalarsu zaki yi ba. Duk da haka dai na ce bari naji ta bakinki."
Langabewa Nasima tayi don bata ga dalilin da zai sa ta karbi yaran ba. Daga haka ma tana fatan maganinsu ya ci tayi gaba kenan har abada.
"Zan so zama dasu Anti. Bari dai na sauke nauyin nan da kaina zan zo na dawo dasu."
"To kai kaji Diya. Za ta so zama dasu amma sai ta haife nata. Bari na barku zan karasa hada kayan."
Tafiyarta tayi ta barsu Nasima na rungumo shi yana kwacewa. Fada ya soma yi mata ba ji ba gani.
"Yanzu ke ko kunyar idona baki ji ba ki ke nuna ba za ki iya zama da 'ya'yana ba?"
Turo masa baki tayi da tsiwarta ita ma.
"Haka ka ji na ce? Kuma nima dai haihuwar nan zanyi. Idan ma takama ake yi da 'ya'ya nima zan haifa maka wasu."
Ransa yake ji a jagule. Dama gashi ta fara sire masa. Abin da yake doki ya riga ya samu har ya fara tunanin komawa titi abin sa. Ga Khadija duk ta canja. Da yatsa ya nunata kamar zai tsokane mata ido.
"Bar ganina haka wadannan yaran basu da na biyu. Ina son abuna kuma idan kina neman zaman lafiya a gidan nan dole ki so su."
Bai kara saurararta ba ya tafi dakinsa ya banko kofa cikin bacin rai. Zama ya yi yana tunanin me yasa yake ganin kamar Khadija ta