Showing 75001 words to 78000 words out of 242549 words

Chapter 26 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3366

Gara ma ki yarda kina watanni zan sako ki. Kinga mun kashe bakin 'yan gulma. Wannan abu fa duk saboda ke nake yi saboda kada a gaba ki sami matsala da mijinki. Sannan zaki sami yadda kike so a wurina. Duk kasar da ki ke son zuwa zaki je. Infact na ma daina daukar matana rakiya sai ke." Da kudin ya sayeta duk da ba shi ya fara mu'amala da ita ba. Da su zai sake ninketa ya aureta saboda tsira daga bakin uwa.

Alkawuran sun mata dadi. Ba musu ta bada kai bori ya hau. Tunda ta amince bata ga dalilin auren ya zama na takaitaccen lokaci ba. Yadda ya yake da kudin nan gara taje ta kwashi rabonta da hujja. Iyayenta dai take ji sai dai kuma komai ya zo ba yadda ta zata ba. Alh. Tahir ya nuna mata da gaske yake.

A ranar da suka yi maganar da daddare yaje tsohuwar unguwarsu tare da Kawunsa daya da abokai biyu. Aka yi musu sallama da babanta wanda ya tarbesu da mutuntawa a falo. Yumna ce mai kawo ruwa da lemo ta shigo a nutse kamar ba ita ba. Tana fita abokin Alh. Tahir ya fadi abin da ya kawosu. Baban Yumna da mamaki ya ce,

"Alh. Tahir din da kansa ko dansa Suhaib?"

"Alh. Tahir din dai" cewar kawunsa.

Babanta sai yaji kansa ya yi nauyi.
"Abin ne ban fahimta ba. Soyayya ta aure kuke yi da ita Yumnan amma bani da labari?"

"Ko daya Alh Kabiru. Yanzu ne dai Allah Ya dora min son hakan shi ne na ce gara mu zo da manya ayi magana ta fahimta. Idan tana da miji ne babu wani abu. Na kawo Kawuna ne da abokai dama domin ka san da gaske nake."

"Ina zuwa" ya ce yana mikewa.

A falon ya barsu ya shiga wurin iyalinsa. Ya yi mamaki kwarai da Yumna ta ce ta amince kai tsaye. Mahaifiyarta kuwa tsalle tayi ta dire ta ce wannan cin amana babu hannunta a ciki. Komawa ya yi ya barsu a dakin tana ta yi mata fada. Zancen duniya baya buya. Yana da labarin kafin su dawo wannan unguwar Alh. Tahir ya auri mai'aikin gidansa da 'yar uwarta. Sun yi zama na 'yan shekaru a nan gashi sun sake tashi. Mutumcin dole ne ya shiga tsakaninsu dalilin 'ya'ya amma sam mutumin bai masa ba. A 'yan watannin da suka gabata ya fahimci wata irin rayuwa da 'yarsa ta fara. Zuciyarsa sam bata son yarda da abin da ya tabbatar halayyar 'ya'yan yayansa ita ma take bi. Zuwan Alh. Tahir bai kara masa komai ba sai tsoratar dashi. Aurar da ita zai yi kawai domin tsananta bincike zai iya haifar masa da ciwon zuciya. Ya kwallafa ransa akan tilon diyarsa. Ko kadan zuciyarsa ba za ta dauki tabbatuwar zarginsa ba.

Yana shiga falon ya ce musu ya amince kuma baya son a dauki lokaci. Su ma tunda a shirye suke sun sanar dashi zasu dawo nan da sati tare da kudin aure.

Ana kammala wannan Alh. Tahir ya shiga tashin hankalin yadda kwan nan zai fashe a wurin 'ya'yansa. Matan gidan sun riga sun sani. Bai san da idon da zai kallesu ba. A zahiri aurensu ba haramun bane amma ji yake kamar zasu san boyayyar alakarsa da ita.

***

Kwanaki sun zo sun wuce babu sako ko waya daga mutumin da ya kira kansa da Abbati a wurin Farha. Yafi sau hudu tana tankwara zuciyarta wurin son tambayar Mardiyya ko ta tura masa nambarta daidai. Da kanta take kwabar kanta cewa kar ta zubar da mutumcinta na 'ya mace. Daga cewa yana son su dauki hoto meye nata na kawo rai da buri ta dora a kansa? Karshenta ma yana da iyali. Yadda bata taba burge sauran maza ba bai ma kamata ta sakawa zuciyarta cewa kila ta burge shi ba. Mami ta ce ta cigaba da hakuri ta jira zuwan mijinta idan tana da rabon aure a duniya.

"Idan Allah bai kawo ba ki gode Masa akan sauran ni'imomin da Ya yi miki. Bana kin aure Farha amma akwai matan da zasu rantse miki da gidan mijinsu gara su tsofe a gaban iyayensu. Duk yadda nake son in ganki a dakinki da zuri'arki ba zan taba gurfana gaban malami domin nema miki miji ba. Allah ba Ya dorawa rai abin da ba zai iya dauka ba. Ki rike wannan."

Nasihar Mami Khadija kenan ta karshe a gareta ranar bikin 'yar kanwar Mamin da suka taso tare. Rashin aure daban da ace mace ta taso babu mashinshini inji bahaushe. Wannan yana tayarwa kowace irin dakakkiyar zuciya hankali ya sanya mata wasiwasi game da tsarin halitta da lafiyarta.

Sun tare a sabon gidansu wanda Alh. Tahir ya zuba musu kayan alatu kamar baya tunanin aurar dasu. Da kanwarsa ta tuhume shi akan hakan lokacin da suka zo ganin gidan cewa ya yi aure ba sayar da 'ya'ya bane. Duk wadda abu ya kawota gida koda ziyarar wuni ce tana da dakinta inda zata wataya tare da 'ya'yanta. Idan kuwa kwana ne babu mai cewa sun takura masa.

A bangaren 'yan matan wanda yake kusa da na Maminsu akwai falo madaidaici da kofofi uku na dakunansu. Kowacce da bandakinta a ciki kuma an kawata shi kamar na amaryar gata. Su kuwa mazan kowa da nasa. Duk da a manne suke da juna amma kowa kofarsa daban. Akwai falo da katon daki da bandaki a ciki. Matansa ma dakuna bibbiyu kowane da bandaki ga kitchen da store. Da yake kowacce kudi ya bata ta sayi abin da take so ita Mami Khadija sai ta adana nata a banki. Ta riga ta gama duk wata siyayya saboda gidan da ta gina. Yanzu ma 'yan haya take nema ta saka kafin ta ga me gaba za ta haifar.

Mardiyya da Sauda na kallo a falonsu Farha kuma na dakinta tana chatting. Sanye take da doguwar riga ta material wadda tabi jikinta ta fiddo da cikar tsarin halittarta. Gashinta wanda ya zarta kafada da kadan ta raba shi biyu ta tufke kowanne tana jiran shigowar maikitsonsu. Muhawara suke tafkawa a wani group game da wasu matsaloli ta whatsapp Yumna ta kirata ta dauka da dan murmushi. Kawar ta ta bata da matsayi kamar da a zuciyarta tunda ta fara harka da manyan maza. Sai dai tana kewarta sosai.

"Hajiya Farha meye duniya ne? Sai dai na ganki online ba hi ba hello."

"Kin yada ni ne Yumna daga fadar gaskiya" ta ce da dokin da yafi na lokacin da kiran ya shigo.

Yumna ta gatsina fuska sannan ta ce "to dai fada tsakaninmu ya kare. Duba status dina."

Kashe wayar tayi tana dariyar mugunta ta bar Farha da waya a kunne. A ganinta ko ma meye tunda har ta kirata ai da ta fada da baki. Kada kai tayi ta fara laluben sunan Yumnan a jerin sunaye dake bangaren status din.

(Alhamdulillah my lion has proposed. Wedding bells ringing)

Murmushin Farha sai ya koma dariya. Falo ta koma wurin kannenta tana tsallen murna ta nuna musu.

"Korafi ya kare Ya Farha ta shirya da aminiyarta." Cewar Sauda ita ma tana tayata murna.

Mardiyya kuwa rungume Farha tayi "congrats Sis. Ai na san sharrin fada da kawa. Ni da muka yi da Jamila har zazzabi na dinga yi"

Yadda ta fada ya sanyasu dariya. Farha ta zauna a nan inda suke ta kira Yumna.

"Wane lucky guy din (mai sa'ar) ne ya sace zuciyarki? Gaskiya sai nayi review na danna nawa stamp din."

Yumna taji dadin farincikin da ta tsammata daga Farha. Wannan zai taimakawa shirinta na farko wajen soma wargaza gidan. Ita yanzu hatta Mamin da take yiwa kallon uwa bata da sauran gashi a idonta. Mulkin da take zubawa a waje shi za ta dora a cikin gidan don ma kada a sami mishkila. Ba za ta ragawa kowa ba balantana ta bada kofar da wani zai takata a gaba. Wannan shawarar cousin dinta ce wadda suke yawonsu tare.

Numfasawa tayi zuciyarta tana dan dokawa da tsoro ta daure ta ce "sake duba status din na saka hotonsa. Zan dai zo har gida muyi shawara don ya ce nan da sati biyu yake son ayi komai."

"Sati biyu? Lallai ki ce zama bai ganmu ba. Amma kin san mun tashi. Ki bari zan zo kawai sai mu taho tare ki ga gidan."

So take ta ce mata ta riga saka kafa a gidan domin sun zo ita da Alh. Tahir yafi a kirga sai ta fasa.
"To shike nan. Sai na ganki."

Farha ta katse kiran ta koma kan status din Yumna ta sake budewa.

(My Lion and I {ni da zakina}) kadai aka rubuta slide din da ya biyo bayan wanda Farha ta fara gani.

Na gabansa ya sanya zuciyarta mummunar dokawar da bata taba yi ba tunda tazo duniya.

Mahaifinta ne Alh. Tahir sanye da singileti da dogon wandon shadda ya zauna akan wata doguwar kujera. Akan cinyarsa ba kowa bace illa Yumna daga ita sai wasu figaggun kananun kaya. Ga hannuwanta sakale da wuyansa yana dariya. Bidiyo ne na sakan biyar mafi tsaho da ciwo a zuciyar Farha. Mummunan gamo ne wanda ko Suhaib da Lilu bata fatan ganin dayansu da wata mace a haka.

Zazzabi, ciwon kai, tsananin bugun zuciya tare da sanyin jiki suka kamata. Jijiyoyinta suka neme daina kai sako yadda ya dace. Bata ji muryar kannenta ba lokacin da suke cewa ta nuna musu hoton mijin Yumna su gani. Bata ji bata ganin komai sai wannan bakin hoto da ya yi zaman dirshan a kwakwalwarta. Hawaye kuwa kamar ruwan famfo suka dinga ambaliya a saman kuncinta.

"Allahumma ajirni fi musibati....Allahumma. Innalillahi..." take furtawa ta kasa kai karshen ko daya.

A zabure Sauda da Mardiyya suka tashi suna tambayarta abin da ke faruwa bata kulasu ba. Mardiyya ta damke hannunta ta fizge wayar ta duba amma Yumna ta riga ta cire status din. Farha na gani ta danna musu delete.

Bata san tafiya take yi ba. Yaushe ta je bakin kofar bangarensu? Allah Masani. Ta dai tuna lokacin da ta mika hannu da nufin bude kofar domin ta fita. Daga nan komai ya dauke cak sai ihun Mardiyya da Sauda suna kiran sunanta.




*****
~Don Allah 'yan uwa lokacin saka facemask ya yi yanzu fiye da baya. Mu daina fita mu da yaranmu babu ita. Akwai hazo, akwai kura sannan akwai CORONA. Kafin sanyi ya kankama kurar nan za ta yi ta damun mutane musamman yaran dake zuwa makaranta.
Stay Safe~

#Comment
#Share
#VoteI just published "16" of my story "UWA UWACE...". https://my.w.tt/2soFKdUdtbb



UWA UWACE...16


Batul Mamman💖



Rahman Ya Rahman
Sa'idni Ya Rahman
Ishrah qalbi Qur'an
Imlah sadri Qur'an
Wasli hayati Qur'an
~~~~~Mishary Rashid Alafasay




"Ya naga kun yi carko carko kamar masu barin gari, lafiya?" Alh. Rabi'u ya ce idanunsa na binsu daidai da kallo. Baki ya saki da ya hango alamun jariri ne a hannun Maimuna ba kunshin kayan da ya zata da farko ba. Tambayar mai haihuwa cikinsu ya yi Uwani ta nuna Zara.

"Shi ne ki ka taho nan maimakon ki wuce gidan mijinki daga asibitin? Me za ayi miki a nan wanda ba za ki sami dubunsa a gidan Alh. Unaisu ba?"

Innayo tayi kwafa hade da murmushi mai ciwo.
"Dama me za ta samu a gidan uban da bai san ci da shanta ba tun zuwanta duniya bare a kai ga batun hidimar aure?"

Magana ce irin wadda bai taba ji daga gareta ba, shi yasa shigarta kunnuwansa ta gigita shi. Sake kallonta ya yi ko zai ga ta inda ta kuskure da wadda ya sani mai hakuri da kawar da kai tsayin shekaru. Ita kuwa Zara ta kalla.

"Ki kira mijinki ko direbanki ko ki tura a samo miki abin hawa ki tafi."

Zara ta sake fashewa da kuka ta koma rokon Alh. Rabi'u.
"Baba ka bata hakuri na zauna a nan kamar yadda su Hajiyan Fatakwal suka ce. Idan na tafi yanzu wallahi matsala zan samu. Sun ce lallai sai na zauna nayi wankan jego..."

"Laifi kika yi? Ko sakin ki ya yi?" Ya tambayeta cikin tashin hankalin kalamanta da na Innayo.

"Saboda na sake haihuwar mace.." ta fada a kunyace murya a kasa.

Maganar ta shigi Innayo sosai don ji tayi kamar da ita ake. Ita ce ake gorantawa haihuwar mata.

Alh. Rabi'u sai ya yi nufin burge Innayo yau daya dai tunda ya fahimci ranta a bace yake. Fada ya soma ba ji ba gani.

"Amma wannan yaro anyi dan iska. Ita macen ba 'ya bace?"

"Ta ina mace take 'ya? Ai ka barshi ya wulakanta matarsa yadda aka yiwa uwar da ta raina lokacin da take ta haifar mata. Ita kuma ka barta ta koma inda ya fi gidan mahaifinta dadi. Banda abinka ai duniya tafi bagaruwa iya jima."

Juyawa tayi ta shige dakin baccinta ta barsu a tsatstsaye su da mahaifinsu. Yana son cewa wani abu domin kallon neman agaji suke yi masa sai dai bai saba ba. Matsayinsa a gidan suna ne kawai. Ba ya bi ta kan yaran sai bukatarsa ta tashi kamar yadda ya yiwa Salima da Hasiya.

Basu bar wurin ba wani almajiri ya ce ana sallama da Zara. Alh. Rabi'u sai ya leka a zatonsa mijinta ne. Maimakon ya ganshi sai direba ya gani an aiko shi da kayan tea, ruwan roba da maltina masu yawa. Zuciya ta kwadayi sai ya basu hanya suka fara shigo dasu. Kafin su gama Munzali ya dawo. Tasa motar ma shake take da duk wani kayan bukatar maijego.

"Meye wannan?" Ya ce da yaci karo da ledar kayan tea din. Madara da milo manyan gwangwani bibbiyu. Sugar na kwali guda hudu sai su ruwan.

Alh. Rabi'u da sauri ya ce "Mijin Zara ne ya aiko mata. Ku shiga dashi falona saboda 'yan barka kada su gani ayi ta hada shayi ba kai ba ...."

Ai kuwa Munzali ya hasala. A iya saninsa yana bawa mahaifinsa kudin da bai ci ace gwangwanin madara zai daga masa hankali ba. Da karfinsa kuwa yasa kafa ya yi ball dasu. Direban da ya kawo da almajirin daya taya shi shigo dasu suka saki baki. Maimuna da Hasiya kuwa hakan ya musu daidai.

"Ka dauka ka mayar ka fada musu nan ba gidan matsiyata bane. Zara kuma ta dawo gida kenan. Ita dashi sai ya zo gaban mahaifiyarta ya bata hakuri. Ka ce masa wannan sakon UBAN Zara ne!"

"Ni?" Alh. Rabi'u ya ce yana dan ja da baya. Wannan ai sanadi zai masa ya toshe kofa daya ta arzikinsa. Ya kalli direban ya ce "kai wallahi ban fada ba. Alh. Unaisun nan ba wani ganin girmana yake ba za ka janyo min matsala dashi" ya kare yana hararar Munzali.

Kallon tsanar da bai yi niyya ba ya jefawa mahaifinsa sannan ya kalli Zara.
"Ke malama ki fa daina wannan kukan. Idan kin ga kin koma gidan wannan mara mutumcin to da yawun Innayo."

Ransa na kuna ya fita ya nemo masu taya shi kwashe kayan tasa motar aka shiga dasu ciki. Uwani na kallon wannan dirama yadda Innayo ta tsame hannu akan Zara da kuma irin rokon da Maimuna, Munzali da Hasiya suka yi ta fama har ta kyaleta. Hada kayanta tayi ta shiga motarta ta bar gidan kafin a gama daidaitawa. Ita kadai a motarta take magana kamar sabon kamu.

"Dole ma na karasa gini saboda bacin rana. Ji yadda Innayo take mata kamar ba 'yarta ba. Ita ma Zara banza. Da tana da hanyar samun kudi wallahi tafi karfin wannan wulakancin. Hummm. Ba gashi Munzali na shiga maganar Innayo ta sauko ba?"

Allah Sarki Innayo. Duk barazanarta bata fatan kora Zara inda bata da daraja. Tabbas ranta ya baci amma tauna tsakuwa kawai take yi. Ta jira asa baki a bata hakuri domin Zaran ta gane da gaske take yi ne. Magiyar su Munzali taje mata akan gaba ne ba wai don nauyin aljihun dayansu ba.

***
'Yar karamar jakarsa mai cin kayan da basu fi seti uku ba ya zuge sannan kamar wanda ya yi aikin karfi ya zauna akan gadon a gajiye. Rashin kuzarin zuciyarsa ne ya harbi duka gabobinsa har ya haddasa masa wannan yanayin kamar na mai ciwo. Babu sauran jirgi mai zuwa Abuja yau. Shi kuma halin da yake ciki ba zai barshi yaji dadin tuka mota zuwa Abujan ba. Kansa yaji ya sara kamar an buga guduma lokacin da Hanne ta shigo dakin ta buga kofar da karfinta. Damuwa ce fal a ransa ya rasa wanda zai iya fadawa domin ya sami mafita.

"Ashe daki ka shigo ina ta faman jiranka na zata kana wurin Munzali."

Kansa ya rike da hannu biyu saboda magana ma kara masa ciwo take ga wayar Shazali dake shigowa babu kakkautawa. Hanne bata kula da yanayin nasa ba ta soma fada masa tasa an kawo mata mai-aiki ya kawo kudin sallamar wadda ta kawota.

Da kyar Abbati ya iya bude bakinsa ya ce "yaushe muka yi dake zaki dauki mai-aiki da har zata zo ban sani ba?"

Tabe baki tayi kafin ta ce "tohhh, daukar mai aikin ma sai na fada maka? Naga ba sabon abu bane tunda dama akwai tafiya tayi."

Abin da ke ransa yafi karfin wata rashin kunya da Hanne za ta yi masa. Kada kai kawai ya yi ya bata kudin da ta tambaya sannan ya tashi.

"Abuja zan tafi yanzu. Ban san kwana nawa zan yi ba amma bana sa ran yin sati in sha Allahu."

"Adawo lafiya" Hanne ta ce hankalinta yana ga kudin da take kirgawa.

Shi ma bai kulata ba ya dauki jakarsa ya fice. Sai da ya zauna a mota ya saka wani hadadden bakin gilas sannan ya tayar ya fita daga gidan. Ya kusa Unguwa Uku wayar Munzali ta shigo masa. Gidan mai ya shiga ya bi gajeren layin dake ciki sannan ya gyara murya ya amsa wayar.

Munzali da shigarsa gida kenan "ina kaje ne? Na dawo babu motarka."

Abbati ya dan kaurara murya yana murmushi "kai fa ka fiye naci. Yanzu daga baka ganni ba sai kira. Wannan idan kayi aure matarka ta shiga goma bama uku ba."

"Naji. Ni dai ka fada min inda kaje. Wallahi ina ganin babu motarka gabana ya fadi shi yasa na kira ba wai don na damu da kai ba. Banda ni ma waye zai iya zama da masifaffe. Ka wani zama mafadacin karfi da yaji kwanakin nan. To dai ina kake in zo?" Munzali ya yi maganar yana shiga motarsa.

Dariyar da Abbati bai son yi ce ta kubuce masa har Munzali yaji sautinta.

"Ina hanyar Abuja."

"In kaje ka gaida Zuma rock."

Ya san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login