Showing 72001 words to 75000 words out of 242549 words
Fatakwal ta ce kuea da wa Allah Ya hadata. Banda Zara bata gabanta da kila sai ta hada mata da hannu.
"Babu inda za ka je. Ka tura direba a kaita gaban iyayenta. Shi kuma wanda ya kaita asibitin ka kore shi. Ni da Zara ne a gidan nan. Na rantse sai ta zauna a gidan iyayenta. In ta san wata bata san wata ba."
Dan wani tunani tayi ta tashi da sauri ta ce su tafi gidan Innayo kafin ya tura direban. Alh. Unais bai fahimci hikimar haka ba sai da suka isa gidan. Mahaifiyarsa tayi dabarar sabule kanta da shi daga zargi a gaban iyayen Zara.
Innayo ce kadai a daki tana sauraron rediyo taji sallama gami da kamshin turaren da ya gauraye kofar dakinta. Muryar ba ta Munzali ba ce. Shi ne mai shigowa kwana biyun nan ya cika su da kamshin turare mai dadi. Amsa sallamar tayi ta janyo mayafi za ta lullube jikinta ta leka sai kawai aka shigo. Girgiza kai tayi ganin ko waye bai dauki bata lokaci tayi izinin a shigo da mahimmanci ba. Alh. Unais da ta gani daga bayan matar da ta luluka tunanin inda ta san fuskarta ya bata mamaki matuka. Mikewa tayi jikinta na rawa da tunanin ko wani abu ne ya sami Zara. Rabonsa da takowa dakinta tana jin tun gaisheta da suka zo bayan auren.
"Ina masu jegon naji dakin naki shiru?" Cewar Hajiyan Fatakwal tana murmushin dole.
Ita dai hankalinta a tashe ta ce "wane masu jegon kuma? Waye ya haihu?"
Hajiyan Fatakwal sai ta fiddo idanu kamar gaske "bangane ba Maman Zara. Ya ina maganar Zara da 'yarta da suka taho nan wankan jego yau kwana biyar kina cewa waye ya haihu?"
Allah Sarki Innayo. A gigice ta mike tsaye, zaninta na sabulewa tana kamo shi da kyar.
"Kuyi min bayani yadda zan gane. Zara bata zo gidan nan ba kuma babu wanda yake da labarin haihuwarta."
A gabanta Alh. Unais ya kira direban da aka umarta kawota gida ya ce ai asibiti ta ce ya kaita tun ranar. Innayo sai taji kamar an dora mata dutse a kanta. Me yake faruwa? Mayafin da ta dauko lokacin da taji sallama tayi saurin yafawa tana tambayarsu sunan asibitin. Yana fada ta kira Hasiya ta fada mata. Ita kuma lokacin Maimuna tana gidanta.
"Ke da Maimunan ku sameni a can."
'Yar pos dinta ta dauko akwai kudi a ciki saboda Munzali ya bata dubu ashirin shekaranjiya da ya zo. Ashe kudin zai mata rana. Ko mukulli bata saka ta rufe dakinta ba tabi bayansu Hajiyan Fatakwal.
Duk tsiya hankalin Alh. Unais yana kan matarsa ita kuwa Hajiyan Fatakwal dama burinta ta sada bak'ar k'aya sunan da ta lakabawa Zara da gidansu. Ko danta zai dawo da ita ba yanzu ba. Tunda ko kusa bata da niyar shiga asibitin Innayo na isowa jikin motar da sassarfa za ta bude baya ta dakatar da ita. Ita ba za ta iya zaman mota tare da wannan matar da ta kode da wahalar rayuwa ba. Karshenta ta cika motar da wari.
"Maman Zara ina ga gara fa ki shiga adaidaita sahu saboda daga asibitin gida zamu wuce."
Innayo sai tayi turus. Matsananciyar kunya ta kama ta sakamakon wannan cin fuska. Ta fahimci motar ce ba a so ta shiga. Banda haka ko ma ina zasu wuce tunda wuri daya zasu yanzu me zai hana a tafi da ita. Wani abu mai kaifi ya soki zuciyarta saboda tunawa da cewa wadannan mutanen Zara ta fifita akanta.
'Yar dariya ta kirkiro "laa babu komai ku wuce ai na gane sunan asibitin."
Hajiyan Fatakwal ta tabe baki "to sai kin iso"
Innayo na kallo suka ja mota. Hanyar titi ta nufa da zafin nama idanunta cike suke taf da hawaye. Bata zaci Zara ta kaskantar da ita ta yadda surukanta zasu kyamaci hada abin hawa da ita ba. Duk da haka kuma bata fasa adduar samunta lafiya ba.
Za ta shiga adaidaita sahu kenan taji kira daga bayanta.
"Innayo ina zuwa?"
Munzali ne don ta gane muryar tun kafin ta juya. Da hannu ya sallami mai adaidaitan ya fito a ladabce ya bude mata bayan motarsa. Tana shiga ta soma kwararo masa addu'a har ya zagayo ya zauna.
"Allah Ya tsare jinka da ganinka Munzali Ya rabaka da duniya lafiya. Nagode. Nagode. Nagode." Ta ce tana danne kwallarta. In wani ya ki ka wani zai so ka. Wadda ta haifa ta ja mata wulakanci. Ga kuma dan mijin da bai damu da komai nasu ba ya martaba ta.
Yaji dadi har ya kasa boyewa. Asabe bata yi masa addu'a irin haka. Kudi ne dai idan ya bata mai yawa ta ce 'nagode'. Idan ta raina ta ce 'an gode'.
"Ina za ki da ranar nan?"
Yadda suka yi da mijin Zara ta fada masa. Ransa kuwa ya baci da salon wulakancinsu ya hau fada.
"Bar bata bakinka. Zara ce ta nuna musu bamu da wata kima a idonta. Rabonta da zuwa gida wata goma kenan."
Haka suka yi ta tattaunawa akan tabarbarewar gidansu har suka isa. Da bata ga motarsu a waje inda ake ajiye motoci ba sai ta fara tunanin ko ba daidai taji sunan ba. Suna shawarar zuwa gidan Zaran tambayar sunan asibitin tunda babu nambar da zasu iya kira sai ga su Hasiya. Munzali ya fita ya tarosu yana fada musu babu tabbas nan ne.
"Ina jin fa nan ne" cewar Hasiya "bari mu shiga mu tambaya."
Munzali na fadin sunan Zara a reception idanuwa suka yi kansu. Sai surutai ana nuna su da baki da hannu da masu yi da wutsiyar ido. Ashe Zara tana da dangi a kusa take zaman asibiti a yashe.
Har dakin da take aka kaisu. Zuciyoyinsu duka sai da suka karye da ganin Zara. Tayi wani irin duhun da kana gani za ka gane wahala da dauda ya kawo shi. Lebe ya bushe fatar ta daddago kamar wadda ta shekara a kwance. Idanunta kuwa sun yi zuru duk ta zabure. Duk wannan bai kama kafar halin da 'yar talikar jaririyarta take ciki ba. Wani tsami take bugawa sosai. Maimuna tayi saurin dorata a cinyarta ta bude diaper (pampas) da nufin canja mata. Gabanta ya yanke ya fadi da abin da ta gani. Cikin rawar murya ta soma salati.
"La'ila ha ilallahu...Zara?"
Innayo da ta bada hankalinta tana sauraron bayanin likita game da Zara sai ta juyo. Munzali da Hasiya ma suka kallota.
"Menene kuma?" Innayo ta tambaya da alamun rashin hakuri.
Hannu na rawa Maimuma ta bude pampas din yarinyar ta tsanyara wata irin kara kamar ba jaririya ba. A tunaninsu ma ko fatar gabanta ta biyo pampas din sabods tsabar jikewa da cika da tayi. Alamu sun bayyana karara ba ta yau bace. Duk abin da tayi a ciki ya canja launi zuwa wani abu daban. Ya ci fatar jikinta da danshi ya d'ad'e jikinta. Likitan ta fita ba jimawa ta turo mai shara da filas din ruwan zafin office dinta saboda kafin a dafa ma zai bata lokaci.
Maimuna ta shiga da yarinyar bandaki tana yi mata tsarki Hasiya na zuba ruwan. Su biyun aka rasa mai hana 'yar uwarta zubar hawaye. Innayo kuwa kirjinta ke zafi amma taki kuka. Wace irin masifa ce wannan da Alh. Rabi'u ya sanya gidansa a ciki? Su kadai ya bari su tarbiyantar da 'ya'yansu.
"Allah Ya gani nayi bakin kokarina Zara. Ban rageku da komai cikin abin da Allah Ya hore min ba. Amma yau gudun zama dani kar ace babarki talaka ce mara ilimin zamani ya kawoki nan."
Baki Zara ta zumburo "me kuma nayi?"
Janyo hannunta Innayo tayi daga kan gadon tana cijewa saboda ciwo.
"Babu abin da kika yi Zara. Zo mu tafi gida. Ba zan bata bakina akan ki ba tunda na san sarai ba kya cikin hayyacinki."
Bayan an gama tsarkin ko pant basu nema sun sakawa yarinyar ba saboda yanayin jikinta sai zani aka dan rufa. Munzali yana kasa ya nemi bill din Zara aka ce masa ai family file ne.
"Ku bani daga ranar da dawo ita kadai"
Aka lissafa masa ya basu kati suka cire. Zai so ganin mijinta da wallahi sai ya naushe shi. Ace matarsa tana asibiti amma don wulakanci suka yiwa Innayo alkawarin karya suka ki zuwa.
Kayanta gabadaya suka saka a mota suka tafi gida. A hanya Innayo ta ce Hasiya ta duba mata Sahad na cikin gari ta siyo madara mai kyau ta yara. Pos dinta ta bawa Hasiyan amma Munzali ya hana. A gurguje ya shiga ya siyo kala uku saboda rashin sannin wadda zasu fi so. Zai yi rantsuwa bai taba jinsa ya cika mutum ba irin yau. Gashi yana ta kai kawo wurin kyautatawa jininsa. A duniya ba zai taba mantawa da Abbati ba.
Suna isa gida Innayo da kanta ta hada itace murhu biyu ta dora ruwa a manyan tukwane. Asabe tayi mamakin ganin shigowarsu tare da Munzali sai dai ganin Zara da son jin kwaf ya hanata yi masa fada. Tana jinsa ya kira Ummakati ya ce tazo gida yau ko gobe Zara ta haihu.
Tsaki tayi da karfi "meye sabo a haihuwarta da ka ke kira min 'ya daga gidan miji?"
Bai ce komai ba saboda ya san sai ta janyo rigima idan ta fara maimaita zancen tana rashin arziki.
Kafin ruwan ya tafasa Innayo ta rufe kofar dakinta ta duba jikin Zara. Ajiyar zuciya kawai tayi ta kira Uwani a waya.
"Kun tashi daga wajen aiki?"
Uwani ta dan yi jim tana tsoron amsar da za ta bayar saboda bata san dalilin tambayar ba. Can dai ta ce
"Eh mun tashi ina gida." Jin kamar Innayo za ta yi magana ta kara da cewa "wallahi kin ga wata ya yi nisa dan abin hannuna duk ya kare."
"Ajiye karyarki wata rana kila in tayi fure tayi miki amfani. Yanzu dai ki fadawa mijinki ina nemanki da gaggawa. Ki taho da kayan aikinki. Dinki za ki gyarawa ...."
Uwani taji kamar ta dora hannu a ka. Ta dade tana gudun ranar da Innayo za ta dinga kiranta taimakawa wani saboda aikinta. Kamar su allura ko karin ruwa da ta kan saka ta kafin tayi aure. Idan an yi lokacin ba kasafai take bari a biya ba. Sai dai ta dinga addu'a tana cewa arziki ne wasu na amfana da iliminta. Tana aure ta nuna bata son cigaba da wannan sadakar dolen. Idan ba za a biya ba kowa yaje asibiti. Bata jira jin karshen maganar ba ta ce
"Gaskiya Innayo ki ce su tanadi kudi. Dinkin ma idan ba haihuwar farko bace ni har dubu goma ina karba."
"Allah ba zai hana ni abin da zan biyaki ba. Ki yi sauri." Kawai ta iya cewa ta kashe wayar.
Uwani sai jiki ya dan yi sanyi. Amma tunda za a biya bata ja lokaci ba ta shiga motarta ta taho gidan. Sanda ta iso Maimuna ta gama yiwa jaririyar nan wanka. 'Yar na kuka ita ma tana yi saboda tausayin jikinta.
Zara kamar mutum mutumi tana zaune a daki har aka gama. Hasiya ta bude akwatin ta daga kaya duk na maza. Cikin unisex ta samu guda daya ta kaiwa Maimuna ta saka mata. Pampas kuwa bayan an shafe wurin da man kade sai aka barta a bude domin ta sha iska. Ana shiryata Hasiya ta hada mata madara tunda da feeder a kayanta. Maimuna ta bata ta sha sosai sai bacci. Duk sai ta basu tausayi. Innayo sai lokacin tayi kwalla. Tashi tayi ta bar wurin saboda bata son zuciyarta ta karye. Zara ta bata mata rai fiye da duka wani abu da ta taba yi a baya.
Da Uwani ta iso Innayo ta gama hada ruwan wankanta a bandaki.
"Maimuna dauki 'yarki ku koma bangaren Asabe don na sanki da raguwar zuciya. Kar ki kuskura ki zo min kofar daki sai an gama."
Da sauri-sauri kuwa Maimuna ta mike. Tunda taji ana zancen gyara dinki hankalinta ya tashi. Dakin Asaben ta je ta gaisheta ta sami wuri ta zauna.
"Lafiya dai ko? Naga mun gaisa har 'yar na gani amma kin gaza tashi."
"Aiki za ayi a dakin Innayo zan tafi idan an gama"
Kasa cewa komai tayi ta barta don bata ga alamun za ta fita ba. Munzali ya fita tunda ya kawosu amma ya ce zai dawo.
Innayo ce tsaye da Zara a bandaki ta soma gasa mata jiki da tawul. Zafin ruwan bai sa tayi niyar gudu ko korafi ba sai da hannun Innayo ya kai cikinta. Nan fa ta kwala kara wadda tasa Asabe zabura a gigice.
"Ke Maimuna gayan gaskiya. Me ake yi a dakin Innayo? Wannan dai duk ragwantar mace ba tayi shi a matsayin kukan wankan jego ba."
Ita ma dai a tsoracen ta ce "naji ta ce Uwani tazo da kayan aiki"
"To ni dai ina nan. Babu inda zan leka wallahi. Banda daukan hakki ai da ta fada min na tafi unguwa yau...uhmmm bari na shiga makota" ta tashi ta figi mayafi. Ihun Zara duk ya tayar mata da hankali.
Cikin Zara Innayo ta dinga dannawa iyakar karfinta da tawul. Hasiya ta rike hannuwanta saboda taki tsayuwa da kyau. Cikin sa a kuwa sai ga audugar da aka bar mata a ciki tun ranar da ta haihu ta fado ta cika wurin da wari. Tuni ta koma bakikkirin babu kyan gani. An barta ne tun lokacin da ta kasa zama ana cikin kwashe mata jini da taji sakon Hajiyan Fatakwal game da haihuwar mace.
Fadowar audugar yayi daidai da wata ajiyar zuciya da ta sauke da karfi. Innayo ta cigaba da yi mata wanka ta gasa jikin sosai. Sannan babu batun kyama ta zauna ta wanketa da ruwa mai zafin da bai yi yawa ba. A nan taji yadda wurin dinkin yake yauki saboda rashin kula. Da ta gama suka fito ta umarci Uwani ta duba idan ana bukatar sake dinkin ne ayi mata.
Hasiya ficewa tayi ta koma falo. Uwani tana dubawa Innayo na kallonta.
"Kin yi shiru. Tana bukatar sabo ne ko kuwa?"
"Wannan din ya dauko hanyar warkewa. Idan aka ci gaba da tsaftace shi ba za ta bukaci sabo ba."
"Da kudina Uwani kar ki cutar min da 'ya. Idan kin san wannan zai iya bata matsala ki ware shi ki sake mata wani."
"Haba Innayo nima fa kanwata ce. Ta yaya zan cuceta? Tun zuwana kun ki fada min abin da ya faru da ita."
"Idan ta dawo daidai ta fada miki da bakinta. Naga kuna dasawa labarin ba zai miki wuyar samuwa ba. Nawa kike chaji in an kiraki amma baki yi aiki ba?" Innayo ta fada fuskarta babu wasa.
Magana ce ta fahimta kuma ita ma sai yanzu taga wautar abin da tayi dazun a waya.
"Ko ina karba ai banda wannan. Don ban san Zara bace da ba zan yi zancen kudin ba Innayo. Naga kamar baki jidadi ba."
"To Allah Ya bada lada."
Daga haka Innayo bata sake bi ta kanta ba. Tuwon da tayi da rana wanda tasa Hasiya ta dumama ta zuba ta dinga bawa Zara a baki. Tana karba hawaye wani na bin wani a kumatunta. Tunda audugar nan ta fito taji kamar an tasheta daga bacci. Duk abin da ya biyo bayan nan ta sani ta kuma tuna me ya faru dalla dalla.
"Wani wurin na yi miki ciwo ne?" Cewar Innayo lokaci guda tana kai hannu wuyan Zara taji ko akwai zazzabi.
"A'a" ta amsa a raunane
"To madalla. Ci abincin ko kya samu ki ji kwarin jikinki."
Daga haka bata sake cewa komai ba. Zara ta dinga kallonta tamkar wata sabuwar halitta da bata taba gani ba. Kukanta bai tsagaita ba amma da za a saka mata wuka a wuya ba za ta iya cewa ga takamaimai abin da yake yawo a ranta ba. Abubuwan da yawa. Malmala daya da rabi ta cinye ta sha kunu fiye da rabin kofi sannan tayi gyatsa.
Innayo ta dauke kofin daga bakinta sannan ta mika mata wayarta da suka dauko daga asibitin.
"Kira mijinki yazo ya daukeki."
Ba Zara ba hatta Maimuna, Hasiya da Uwanin da bata gama sanin me ya faru ba maganar ta basu mamaki.
Idanu cike da hawaye Zara ta ce "Innayo a hakan zan tafi?"
"Ba a hakan ki ka zabi asibiti akan wannan dakin ba? Kije gidanki ki karasa jinya Zara. Allah Ya raya miki 'yarki."
"Don Allah Innayo..." Maimuna ta fara roko ta juyo kuwa tayi mata wani irin kallon da yasa bakinta rufewa gum.
Da zasu fice ma baki dayansu daga dakin da taji dadi. Kuka take son yi. Kukan tausayin Fatima Zahranta. Kukan rashin sanin laifinta a wurin tarbiya da rainon 'yarta. Kukan matakin da take son dauka domin nunawa Zaran cewa dama can talala take yi mata. A daidai lokacin kuma Alh. Rabi'u ya daga labulen kofar ya leko dakin...
***
Shiru Yumna tayi har Alh. Tahir ya gama magana sannan ta tashi daga jikinsa tana yi masa wani banzan kallo.
"Aure fa kace? Ni za ka aura? Gaskiya nafi son auren yaro daidai dani."
Mamaki sosai ya kama shi da karfin halinta na yi masa rashin kunya. Yarinyar da take sa'ar 'yarsa. Wato don ya sakar mata jiki da fuska take ganin kamar yanzu kansu daya. Ba don Yakumbo ta sake jaddada masa batun auren nan ba da tuni ya saka ta a bolar da yake jefa wadanda ya gama cin moriyarsu.
"Kinga samu wuri ki zauna ba maganar wasa bace. Hotonan da ki ka turo duka matana sun gani."
Rawa jikinta ya dauka ta saki wayarta a kasa ta kuma bi bayanta ta zube a gabansa.
"Me? Ka ce min basa taba wayar. Na shiga ukuna. Idan suka fadawa Mummy wallahi kasheni zata yi kawai." Ta fashe da kukan firgici.
Shi ma ba zai so tonawa kansa asiri ya fada mata gaskiya ba sai ya ce "da suka tuhume ni a kai na nuna musu cewa aurenki nake son yi. Yanzu duk sun zuba ido suna jiran jin batun aure ko hoto ya tafi gaban mahaifanki."
"Na shiga uku" ta sake fadi cike da jimani "yanzu me zan ce da Farha?"
Gabansa ya fadi shi ma amma sai ya dake.
"Bana son munafurci. Baki san da Farhan ba ki ke bina duk inda na nema?"
Murguda masa baki tayi "ai dai ba ni na kawo kaina ba kai ka nemeni."
Tashi ya yi ya kimtsa jikinsa sannan suka karkare magana.
"Matashin da ki ke son aure babu wanda zai yarda ya zauna da irinki. Ko an fada miki mazan yanzu jahilai ne? Gane masu yawo ba wahala yake musu ba.