Showing 210001 words to 213000 words out of 242549 words
ta janye filon. Ba arziki kuwa Alh. Rabi'u ya tashi cikin dimuwar kasa tantance inda yake. Ido da suka hada ne ya sanya shi yin kwafa da wani bahagon tsaki.
"Ki adana rashin mutumcinki zuwa in gama baccin nan don wallahi idan ki ka kunno ni yanzu sai na saba miki. Bar ganin jiya kin min yadda kike so ban tanka ba. Tara ki nake." Yana gama magana ya sake mayar da kai kan shimfida.
Tsaki tayi cike da bakinciki ta ce "Malam ka tashi mu tafi gidan Munzali. Yanzu su Innayo suka dawo an sallame shi yana gida."
A fusace ya tashi zaune ya kai wa katifa naushi "Wohoho Asabe!...Allah dai Ya jikan Innayo ba don ta mutu ba. Ko kusa tarbiyarku ba daya bace. Bata san musu da miji ba balle tsaki. Banda shirmenki ma a ina kika taba ganin namiji yana rawar jiki akan ciwon 'ya'yansa kamar wani dan daudu?"
Asabe bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba. Ta daga murya kuwa ta kwalawa Innayo kira. Ba jimawa kuwa ta iso. A tunaninta wani fadan suke yi wanda karshenta ya janyo Alh. Rabi'u ya taba lafiyar jikinta. Da ta gansu kalau sai ta juya za ta koma. Asabe ta yi azamar dakatar da ita ta bata labarin abin da yake faruwa.
"Da satin da ya wuce ne naji yabonki daga bakin Alhaji da nace kila malami ki ka canja."
Murmushi ne ya subucewa Innayo. Asabe kuwa ta hararai Alh. Rabi'u sannan ta ce "wannan magana har zuciyata nake fada miki"
Kafadarta Innayo ta dan tura tana mai cewa "Mu bashi wuri ya shirya sai ku tafi"
Haushi kuwa ya turnuke shi har wuya ganin da gaske 'yar maganar nan ta Innayo tasa ta daina yi masa tijarar da ta fara har tana shirin fita. A da tasu ta zo daya har ta kai suna kulla yadda zasu bakantawa Innayo rai a cikin hirarsu. Amma cikin kankanin lokaci komai yana neman sauyawa. Idan ya bar Innayo ta cigaba da shigewa Asabe ya san za a wayi gari ta karta masa rashin albarka fiye da yanzu. Karshen matsalar ba zai wuce ta hana Munzali bashi kudi ba wamda ko kusa ba zai jura ba. Zai zama cikakken lusari kuwa idan ya bari haka ta kasance.
Dakin Innayo dake cike da 'ya'yanta da wasu cikin jikoki duk sun ji lokacin da Asabe ta kirata. Uwani ma a hanyar fitarta daga dakin suka yi kicibus da ta shigo gidan. Hasiya kuma daga asibiti wurin Abbas suka wutu nan domin jajen batan Qibdiyya. Maimuna ma abin da ya kawota kenan. To dukkaninsu ko gaisuwar kirki basu samu yi da mahaifiyar tasu ba ta fita. Shi yasa da suka ji shiru bata dawo ba sai suka fito duka su biyar din da tunanin tabbas akwai matsala. Da isarsu kofar dakin ne kuma wanda ya yi daidai da sanyo kan Asabe da Innayo zasu fito sai furucin Alh. Rabi'u wanda ke duban Asabe yasa su cin burki.
"Dama na dade da sanin cewa kina da karancin hangen nesa. Banda haka har me ya faru da zai sa ki fara jin maganar Innayo akan tawa? Amma ance jiki magayi, ga ki ga ta nan. Ranar da munafuncinta ya bayyana kansa gareki za ki hankalta."
"Ke kuma" ya juya ga Innayo wadda jikinta ya yi sanyi akan maganganunsa "Kin bi kin cika min gida da zawarawan 'ya'yanki da basa tsinanawa kowa abin azo a gani. Masu takamar kudin cikinsu me suka taba yi miki na bajinta banda wulakanci da raini. Talakawan ne kawai a nanike dake saboda har yanzu suna morarki" ya daga yatsa kurkusa da fuskarta cikin fushi "baki isa ki shiga tsakanina da matata ba saboda haka ki fita idona in rufe."
Yatsan ya sake matsowa dashi kamar zai shigar cikin idonta tayi saurin runtsesu. Alh Rabi'u ya bita da kallon raini sannan ya dubi su Uwani da suka gama shigowa daya bayan daya. Da yake suma din a wuyansa suke tuntuni sai yaga dama ce ta amayar musu da cikinsa.
"Tunda muke dake ko naira dari cikin 'ya'yan nan babu wadda ta taba bani ta neman albarka. Abin ya jima yana ci min tuwo a kwarya sai kace ba jinina ba"
"RABI'U!!!"
Innayo ta kira sunansa da karfi, da kaushin murya da kuma sigar gargadin kada ya dora wata magana daga nan. Su Hasiya ma kowacce 'Baba' take ambata cikin tashin hankali banda Uwani. Ita kadai ta taka har gabansa ta dube shi duba irin wanda ko kusa bai kamata ya gilma tsakanin uba da 'ya ba.
"Mu ne kake zargin ba jininka ba ko kuwa duka 'ya'yanka da ka sakarwa uwayensu ragamar kula dasu tamkar marayun da basu da galihu?,"
"Mahaifin naki kike fadawa haka Uwani? To indai don nice bana son ki shigar min na yafe. Ki ja kannenki ku fita."
Kalaman Salihi ne suka dawowa Uwani ta dubi Innayo da kishiyar kallon da ta yiwa mahaifinta dakiku kalilan da suka wuce. Kwalla ce taf ta cike idanun dattijuwar da ta kawota duniya har ta fara saukowa. A take taji ta kara tsanar kanta da dukkan halayyar da ta gwada mata a shekarun baya.
"Nayi miki alkawari daga yau ba zan kara sabawa umarninki ba. Don Allah ki yafe wa rashin biyayyata ta yau domin idan ban yi ta ba bana jin zan taba yafewa kaina balle in roki gafararki akan abin da ya gabata. Tuni kawai nake son yi masa akan abin da na tabbatar ya sani."
Maimuna, Salima, Zara da Hasiya basu iya boye mamakinsu akan furucin Uwani ba. Asabe kanta sai da ta jinjinawa lokaci da dan Adam yake cewa bai bar komai ba. Yau Uwani ce tayi laushi irin haka a gaban uwar da kowa ya san bata gani da kima.
Innayo kuwa dan murmushi tayi wanda babu wanda ya fahimci ma'anarsa. Ta dai gyada kai alamun lamuncewa Uwani tayi abin da tayi niya ga mamakin dukansu sannan ta sami wuri akan tilon kujerar mai dakin ta zauna.
Kallon baki da hankali Alh. Rabi'u ya yi mata ya ce "kina nufin kin amince ta yi min rashin albarka?"
"Baba"
Sunan a tausashe ya fito daga bakin Uwani. Shi Alh. Rabi'u ma hantar cikinsa sai da ta kada saboda tana bude baki ya tsorata. A iya sanin da ya yi mata ba bata da tsoro balle kunya. Tunda ta iya yiwa Innayo shi waye da ba za ta yi masa ba?
"Naaaa...na'amm?"
"Allah Ya azurtaka da 'ya'ya goma sha uku. Cikinmu wa za ka bugi kirji ka ce ka taba siyawa magani ko da na ciwon kai ne ?"
Shiru ba amsa.
"Rai tara a cikin 'ya'yanka kuma duka mata Innayo ce ta dauki ragamar komai da komai namu har aure. Idan akwai wadda ka sayawa cokalin tafiya gidan miji ka kama sunanta a gaban matanka."
Idanusa kamar 'ya'yan bararriyar gurjiya ya yi tsilli-tsilli dasu ya kasa hada ido da kowa a dakin.
"Banda fitowa daga tsatsonka babu wani abu komai kankantarsa da za ka yi tutiyar cewa ka taba yi mana a matsayinka na mahaifinmu."
"Ya isa haka Uwani" cewar Maimuna saboda tsoron kada tayi rashin kunyar da zata koma ta taba mutumcin mahaifiyarsu.
"Ki barni Maimuna. Ni ba Innayo bace da zan zauna ina hadiyar bakinciki da bacin ran da zai iya haifar min da ciwon zuciya ba. Ba kuma Asabe bace da zan biyewa rashin kulawar miji in sakarwa duniya 'ya'ya ba. Banda shiriya ta Ubangiji ce da tuni munyi qaurin suna cikin gantalallun mata."
A salube Asabe ta ce "nima harda ni Uwani? Na zata tunda mun shirya da Innayo ba sai kin fadi aibuna ba."
Kaza huce kan dami. Maganar Asabe kofa ta budewa Alh. Rabi'u ya hauta da fadan borin kunya.
"Wato ni ta cigaba da fadan nawa kenan?" Ya kalli Uwani a fakaice ya ce "To duk tsiyar mutum sai na daga kafa uwarsa za ta shiga aljanna. "
"Haba dai Baba" cewar Uwani tana murmushi "Fir'auna ma duk kudi da mulkinsa wallahi yana ji yana gani Asiya RA za ta wuce aljanna kuma babu yadda ya iya."
Duk inda bacin rai yake yau ya sarkafi zuciyar Alh. Rabi'u. Abin takaicin ma dariyar da Asabe ta kece da ita wadda tayi sanadiyar murmushin su Zara. Baki yana fitar da kumfa kuwa ya ce "ni kike hadawa da Fir'auna? Innayo kina jin abinda 'yarki take cewa ko? Kina kuma kallon ragowar 'ya'yan naki suna yi min dariya."
Kallonsu tayi tana mamakin har a wannan lokacin ita kadai yake jingina wa su tamkar dasu ta zo gidan.
"Ku shige mu tafi"
Uwani sai cewa tayi "Allah dai Yasa ba wani laifin na kara yi ba. Ni gaskiya ce kawai nake son fada masa a matsayinsa na wanda ya yi sanadiyar kawomu duniya."
Zara tayi saurin karbe zancen da fadin,
"Baba ba komai Uwani take son fada maka ba illa ka sani cewa Allah baya zalunci. Babu ta yadda mutum zai cutar da abokiyar zamansa sannan ya yi zaton idan anje lahira sai an shawarce shi za ta ji dadi. Tsaf za ta wuce aljanna ta bar miji akan layi"
"Dani kike Zara?" Alh. Rabi'u ya ce cike da mamaki. Wato baki dayansu suna ankare dashi kawai sun yi shiru ne duk tsayin shekarun nan. Anya idan ya yi sake ba za su karasa kwance masa zani ba?
Salima ma tunanin gidansu da gashin k'umar da Ale Gambo ya yi mata yasa ta ce "ba kowacce mace bace take da zuciyar yafiya. Idan an fadawa mutum kuskurensa ya kamata ya yi ya karba. Sai ya bayar da hakuri tare da rayawa a zuciyarsa cewa ya daina. Domin duk wani bacin rai ko hawaye komai kankantarsa da miji zai dasawa matarsa ba bisa hakki ba sai an fitar mata da hakkinta."
"Sanin hakki da kyautatawa ke rike aure ba kudi ko talauci ba Baba. Idan neman na kai ne babu wanda ya kai Innayo. Kyawun hali da hakurinta kuwa hatta 'ya'yanmu suna jinjinawa. Amma mun tashi da ganin babu wata mu'amala a tsakaninku sama da kyara da hantara" inji Maimuna tayi maganar idanunta suna ciccikowa da kwalla.
Hasiya ce ta rufe zancen gabadaya da cewa "Baba iyaye su suke koyawa 'ya'yansu tausayi da jinkansu. Innayo tayi iya yinta sai dai ance zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Kamar yadda Maimuna ta ce ne, mun tashi mun san cewa mahaifiyarmu tafi borar mata kaskanci a wurinka. Wannan ya yi sanadiyar kyamarta daga 'yan uwana na haihuwa da ma wadanda ta tayaka sauke hakkinsu ('ya'yan Larai)"
"Ina miki kallon mai hankali ashe duk uwar darin ce ke da Uwani?"
"Ko kusa Baba. Ita fa da a namiji ta zo na tabbata halayenku sai sun yi tagwaitaka"
A kufule Uwani ta ce "Innayo kina jinta fa"
Hasiya ta ce "nima gaskiya zan fada muku kamar yadda ki ka faro. Baba kaga duk wanda ya zama sanadiyar aikin alkhairin wani yana da lada gwargwadon aikin. Haka ma zunubi. Mun riga mun girma kowa yana da littafin ayyukansa. Amma hakan ba zai hana wadanda suka bada gudunmawar aikin ladan ko akasinsa samun rabonsu ba. To ka duba adadin matanka da 'ya'ya...baki dayanmu sai Allah Ya tambayeka game da amanarmu da Ya baka. Baka san rayuwar kowa a cikinmu ba balle ka san ko za ka iya fidda kanka a ranar. Ina jiye maka tsoron komawa ga Allah a wannan yanayin. Kada ka manta duk hawayen Innayo a lokutan da Zara da Uwani suka cusguna mata saboda sun koyi kinta daga wurinka sai Allah Ya saka mata. Kuma..."
Hannu ya daga ya dakatar da ita "ya isa haka! Ba dai Munzali bane ake maganar zuwa duba shi? Zani. A bani wuri na shirya."
A tsakar gida Asabe ta tari Innayo ta ce mata ta zo su tafi gidan Munzali tare. Tayin ya zo mata a bazata. Tabbas ta matsu ta san halin da Qibdiyya take ciki. Satar dan mutum harda baraza akan rayuwa da lafiyarsa abu ne mai ban tsoro. Sai dai sabanin amsa gayyatar da Asabe tayi mata sai ta girgiza kai.
"Ke da Alhaji kadai ya kamata ku je"
Asabe tayi turus tana kallonta kafin ta ce "ni wallahi na dauka mun fara shiri ashe ba haka yake a gun ki ba?"
Dariya ta so bawa Innayo sai ta buge da murmushi.
"Mun shirya mana Asabe. Bana son zuwana yasa Alhaji sake botsare mana a hanya ko a can. Gara ku tafi ku biyun ko a samu ya je yaga halin da dansa yake ciki.
Asabe bata wani gamsu ba. Hasali ma dai tunani ta shiga yi akan ko yadda take hango matsala haka Innayo din ita ma. Sai tayi saurin cewa,
"Kema kina hasashen akwai matsala a gidan ko? Nayi zaton sanin hakan ne ma zai sa ki biyomu domin jin mene ne yake faruwa."
"Ba ayi ciki domin abinci ba kadai. Ku biyun dai ya cancanta ku fara zuwa ku san damuwarsa. Wani sirrin tsakanin uwa da yaranta ko uba ba'a so ya ji. Zuwana zai iya zame muku karan tsaye. Fatana ki jiyo alkhairi irin wanda da kanki ma zaki zo ki bani labari".
I just published "44" of my story "UWA UWACE...". https://www.wattpad.com/1221355520?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=BatulMamman17&wp_originator=mpYDskUeiEG9CDOyYcH9FvuBE0%2BCoe14jmvbGzpiBRqafRYhxsXC16Ye3NBepzEEktaVzMIHCAjQYFg6eqHR9XLj0QFKsEQwC5UNTmz7wRiPUkR9mR7KjaZ7sSHP9RXu
UWA UWACE...44
Batul Mamman💖
***
Baba Mari bata yi mamakin jin halin da Qibdiyya take ciki ba tunda Munzali ya riga ya fada mata. Yadda Zakiyya ta shiga damuwa ga Hanne duk ta tsorata yasa bata nuna musu ta sani ba, saboda gudun tambayar da bata san amsarta ba. Jikin Qibdiyya da Zakiyya ta so bude musu su gani ta hana. Yawan bude jikin babu alkhairi indai ba gyara zai kawo ba. Hakuri ta dinga basu a yayinda suke ta hasashen abin da ya faru har suka ji karuwar muryoyi a falon. Zakiyya kuwa da zafin nama ta fita da ta tantance ta Munzali a cikin wadanda suka shigo. Ganin ya shigo da wani matashi sai ta hadiye abin da ta so fada.
Fuskarta kawai ya kalla ya gane cewa ta san halin da Qibdiyya take ciki. Ba tare da yi mata magana ba ya gaishe da su Mal. Inuwa. Ya kuma sanar dasu cewa Abbati yana hanya. Tun shigowarsa gidan da yaga motar Buba ya fara tunanin akwai baki daga Kirikasamma. Sai kuwa maigadi ya tabbatar masa da hakan da ma su waye bakin. Kafin ya shiga ciki ya kira shi. Kin dauka ya yi kamar yadda ya yi hasashe, sai kawai ya tura masa sako. Shi kuma bai tashi dubawa ba ma sai da ya tsaya a danja. Kansa ya sake daukar chaji. Wannan rana ta ki karewa tamkar ita ce ranar wankan da ake cewa ba a boyon cibi. Mika wuya kawai ya yi ga sarautar Allah tare da fatan nutsuwar zuciya ya ziyarce shi a duk sa'ilin da ya tuna wannan ranar a gaba.
Yana shiga harabar gidan ya hango Asabe da Alh. Rabi'u a tsaye suna magana. Ba shiri ya kashe motar ya fito a lokaci guda yana cewa su Mami su biyo shi. Ba don hankula a tashe suke ba da dukkaninsu sai sun yaba da tsarin gidan duk da kasancewarsu masu arziki.
Asabe na ganinsa ta tare shi da tambayar ko Qibdiyya ta dawo.
"Tana ciki na daukota"
Ajiyar zuciya ta saki sannan ta hau sababi da yiwa Shazali mugun fata.
"Abota da wannan la'anannen bata yi muku rana ba Abbati. Amma in sha Allahu yadda ya hanamu sukuni da ya sace Mariya sai ya riski bakincikin da ya ninka namu sau dari"
"Sata? Me yake faruwa ne Abbati?"
Mami Khadija ce tayi magana tana mai yi masa kallon tuhuma. Indai sace Qibdiyya aka yi ai babu mamaki a can aka bata mata rayuwa. A matsayinta na uwa, duk da satar mutum ba abin so bane amma a gareta kofa ce da danta zai iya tsira daga zargin da ake yi masa.
Kallon rashin sani Asabe tayi mata ya hada amsoshin ga baki daya ya basu a jumla guda.
"Mu shiga ciki sai a warware komai da yardar Allah"
Alh. Rabi'u wanda ya kosa da tsayuwar tasu amma tasirin kalaman 'ya'yan Innayo ya hana shi ya magantu ya ce "wanne ne bangaren naka? Maigadinku ya ce duka suna can."
Da hannu ya nuna musu tare da basu hanya su fara yin gaba. Jikin motar ya koma domin taimakawa Suhaib tunda da akwai matattakala kafin a shiga kowane sashe sai yaga Farha ta dawo za ta zauna.
"Muje mana" ya ce bayan Suhaib ya dafa kafadarsa.
"Zan jira ku a nan" ita ce amsar da ta bayar tana dan daure fuska.
Bata son bashi damar ya ce dole sai ta shiga. Ai sam bata ga tsari a shigar masa gida ba alhalin akwai abu a tsakaninsu sannan matarsa da iyayensa kamar yadda taji maigadi na fada masa suna ciki. Gabanta har wani faduwa ya dinga yi saboda tsoron kada Mami ta ce sai ta shiga dole.
Ji ya yi baya son barinta a wurin ya sake bude baki zai yi magana sai Suhaib ya yi belinta don ya gano inda ta dosa.
"Zai dai fi ta jira a wajen"
Kai Abbati ya gyada na fahimta. Ya so ya kalleta su hada ido sai yaji nauyinta ya sake rufar masa. Lallai wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa.
Da taimakonsa Suhaib ya shiga falon. Sun sami kowa a zazzaune ana gaisawa. Ganin Baaba Mari a falon ya taimaka wurin ragewa Mami Khadija zulumi. Don ma dukkaninsu babu mai kwanciyar hankalin tsawaita hira sabanin haduwarsu ta farko. Bayan gaisuwar ta tsahirta ne Abbati ya gabatarwa da Mami Khadija da duka wadanda suke wurin.
Zuciyarta kuwa ta tsinke cikin fargabar abin da zai iya samun Lilu. Da ya kula da sanyin da tayi sai ya ce "Mami wallahi ba na tsoron komai don ban aikata ba" iya jinta ita kadai.
Jinjina kai tayi a hankali cikin zuciyarta tana rokon Allah da neman tsarinSa akan wannan musiba da ta tunkaro su. Kwarin gwiwar da yawan jama'ar da suka gani a gidan yasa ta kusa rasawa ne ya dawo mata.
***
Maigadi na shiga bandaki Daddy da Umman Zakiyya suka turo karamar kofar gate din suka shigo. Umman tasu afujajan take tafe da zaninta a hannu ga hawaye ya jike mata fuska. Gidan Munzali suka nufa sai Farha dake cikin mota taga rashin dacewar barinsu su tafi bayan Maigadin ya fadi inda jama'ar gidan suke. Kafin su karasa ta bude motar ta fita ta dan daga murya yadda zasu ji.
"Suna wancan gidan" ta fada tare da nuna inda su Mami suka shiga da Abbati.
Umma ta dawo da sauri