Showing 78001 words to 81000 words out of 242549 words

Chapter 27 - UWA UWACE COMPLETE BOOK by Fatty Noor.txt

09 Oct 2025

3411

bai yarda ba sai ya rantse masa tare da fadin karyar da ya shirya tunda Shazali ya kira shi kwanaki biyu da suka wuce.

"Chief Harrison ke nemanmu. Shazali ya yi masa bayanin mun daina yaki yarda. Shi ne yace gara daya daga cikinmu yaje muyi masa bayani baki da baki. Wai a haka yana iya zargin ko hadin baki ne muka yi da abokin nan nasa da suka yi fada."

Saboda yadda yake fitar da maganar daki daki da sanin cewa karya ce ya sharo har wani irin bugu yake jin zuciyarsa tana yi. Da wahala idan akwai watarana da suka taba yiwa juna karya shi da Munzali.

Munzali ya saurari dogon bayanin amma abu daya ne yafi daukar hankalinsa. Hade girar sama da kasa ya yi kamar Abbati na kallonsa ya ce
"Wait! Ba mun ce ko waya ba za ta sake hadamu da Shazali ba? Menene nasa na kiranka yanzu?"

"Na fada maka..." Abbati ya soma fada yana jan motarsa gaban bututun zuba man.

"Yes ka fada naji amma ban yarda ba. Haba Abbati! Shazali dan is** ne kuma gogaggen makaryaci. Ka sani ko wata manakisar ya shirya maka tunda ya san Chief yana mutuwar sonka."

"Nima nayi tunanin haka sai na ce gara naje dai muyita ta kare dasu kawai." Shi ma da yake maganar ba shigarsa take ba saboda raunin hujjar da ya bayar. Da wane baki zai fada masa cewa kwanaki biyu kenan da ya sami alert mai tsoka kuma ana jiran yaje ya yu aikin kudin?

"To amma me yasa baka fada min ba? Me yasa kuma baka jira mun tafi tare ba?"

Abbati sai ya amsa masa da cewa baya so ya kawo masa matsalar da zata sa ya bar 'yan uwansa a yanayin da gidansu yake. Ya dora da nuna masa illar rashin ganin ko mutum daya cikinsu saboda matsayin irin mutanen da suke bi a da.

Munzali tun yana ta kokarin kure shi da tambaya saboda rashin gamsuwa har ya hakura ya amince.

"Don Allah ka kiyaye kar suyi maka wayo don na sanka sarai."

Abbati ya saki rai jin Munzalin ya dauko wasa.
"Ai baka da kunya dama kuma yau tun safe bamu hadu kayi min ba. Zan kira ka idan na kuma tsayawa yanzu zan hau titi."

Sun gama sallama Munzali zai katse kiran ya fasa. Haka nan yake jin wani irin nauyi a ransa.

"Abbati wallahi idan ka bari suka yi wani abu da kai ALLAH YA ISA."

Wani irin radadi ya rike duka jijiyoyin idanun Abbati saboda kukan da yake jin zai iya yi. Tafiyarsa daidai take da cin amanar Munzali, Baaba Mari da tuban da ya kuduri niyar yi.
"Me ka ce?"

"Allah Ya isa na ce. Mutumina kayi duk yadda zaka yi ka fito lafiya. Kaga ka jirani in zo mu tafi tare mana" ya kare a raunane yana mai jin tsoron kada ayi amfani da saukin kan Abbatin.

Sai da ya dake ya iya cewa "kaima ka san zan kiyaye. Idan na sami damar ganinsa a daren yau ma to gobe zan dawo in sha Allahu."

"No..a'a fa. Wane irin da daddare? Ka jira gobe ku hadu koda a restaurant ne da rana tsaka kuma a wuri mai mutane. Ka fada masa komai ka. Kuma ka tsaya akan bakanka ka ce musu mun daina duk aure zamu yi." Ya dan sako wasa yana dariya kasa-kasa "Idan kana dawowa ka jirani a Kaduna inje wurin Diamond girl."

"Wai da gaske ka ke akan yarinyar nan?" Kyakkyawar fuskar Farha na dawo masa tar a idanunsa.

"Tausayinta naji ranar nan. Sai nake ganin kamar irina ce ta tashi uwa bata damu da ita ba. Tunda kai ka fasa da yayarta ni dai ina ciki da kanwar. Allah Ya kiyaye hanya."

Daga haka ya ajiye wayar zuciyarsa babu dadi. Abbati kuwa kwalar idonsa ya hana zuba sai zafin dake yawo a ilahirin jikinsa. Dama can sun san haram suke aikatawa amma shaidan yafi karfin zukatansu. Yanzu kuma da suke jin sun shirya komawa ga Allah sai shaidanu suke neman hanasu. Wani irin abu ne ya soki kokon ransa da ya ayyana a ransa ko bashi da rabon tuba ne? Ko dai baya cikin masu dacewa da rahamar Allah? Zuciyarsa sai ta sare. Karfin gwiwarsa ya ragu. Tsoro da fargaba suka mamaye dukkan tunaninsa. Me yasa suka biyewa son zuciya a wancan lokacin? Ya akayi ya zama daga cikin masu raya zunubin mutanen Annabi Luďu AS? Tabbas ya san basu da alhakin dulmiyar da kowa amma idan ya tuna sun rayu kwatankwacin rayuwar karuwa sai yaji ya tsani kansa. Sun bi musulmi sun bi kirista. Manyan masu fada aji a kasar nan duk suna tafin hannunsu domin sun san sirrinsu. Kafin ya isa Kaduna zazzabi ya rufe shi. Tukin gagararsa yake neman yi don sau biyu yana auna arziki bai karawa wani ba. Da tambaya ya samu aka kwatanta masa asibiti mafi kusa da titin da yake bi na fita gari.

DOCTORS HAVEN
Shi ne sunan da ya gani an rubuta kato a jikin bangon dake kallonsa na asibitin.

(Yana daga cikin kokarin Shaidan la'ananne akan bayin Allah ya sarar musu da gwiwa yayin tuba. Ya kan sanyawa mutane hopelessness har kaji kamar tuban ba zai amfaneka ba. A bangare guda kuma Allah SWT zai iya jarabtar bawa da kalubale domin Ya kara masa ladan hakuri da jajircewa wurin tuba. Muhallishshahid shi ne kada mu karaya. Mu dage iyakar dagewa mu tsaya akan bakanmu. Idan Allah Yaso sai mu rayu cikin zunubi kuma Ya saukaka mana tuba da komawa gareShi. Sannan rahamarSa ce idan Ya so ya kawo mana nau'ikan jarabawa akan hanyar tubanmu domin mu kara imani. ALLAH SHI KADAI NE BASHI DA ABOKIN TARAYYA. Ya bamu ISTIGFARI domin Ya daukaka darajarmu rana gobe kiyama. Idan mun tsaya da ikilasi to lallai Allah zai bamu mafita da izininSa.)

***

Mami Khadija na daki tana aikin tsara slides (power point) na lecture din da take dashi da 'yan masters sati mai zuwa taji kamar ana kiranta a waje. Gilashin idonta ta tura ciki sosai ta tashi daga gaban teburin aikinta da sauri.

"Sauda? Farha? Mardiyya? Kai waye yake min wannan kiran ne kamar ana kuka?"

Hanyar fita zuwa bangarensu tabi inda take jin muryoyin. Sai da tayo kusa ta fahimci Sauda da Mardiyya ne suke kukan. A bakin kofa taci karo da Sauda wadda ta taho domin kiranta. Nan kuma idanunta suka sauka akan Mardiyya tana girgiza Farha tare da kiran sunanta cikin kuka. Da gudu gudu ta karasa gabansu ta durkusa a wurin.

"Me ya sameta?"

"Bamu sani ba Mami. Daga duba status din Yumna ta fadi." Cewar Mardiyya hannunta na rawa wurin shafawa Farha ruwa a fuska.

Ran Mami Khadija ya baci sosai ta ce "Yumna? Gaya min yadda abin ya faru. Sauda dubo min mazan nan mu kaita asibiti."

Bayan fitar Sauda ne Mardiyya ta fadawa Mami abin da suka sani.

"Na duba banga hoton ba amma na tabbata ganinsa ne ya sumar da ita."

Fuskar Mami tamkar bata taba murmushi ba baŕe dariya ta tashi tsaye. Lilu ne ya shigo lokacin Farha ta bude ido da kyar.

"Ku bani wayata" ta ce a tsorace tana gudun kada su ma su gani.

Yadda tayi ya tabbatarwa Mami Khadija cewa lallai hoton ya shafi mahaifinsu. Wayar ta mika mata don ta sami saukin rai har tana nuna mata kamar ranta ya baci ganin bata da lafiya amma tana neman waya. Farha bata ce komai ba sai kai da ta sunkuyar. Kunyar mahaifiyar tasu take ji sosai da tausayi. Ga wata irin tsana mara takunkumi da take hauhawa a zuciyarta ta mahaifinsu.

Mota ta ce su wuce ta tafi dauko mayafinta a daki. Ta dauko jakarta ta saka wayarta a ciki. Ji take kamar ana caccakarta da allura saboda bakin cikin halin da Alh. Tahir ya sakasu a ciki. Albarkacin 'ya'yan nan yaci kuma yake kan ci da tuni ta bar gidansa. Ba za ta yarda ya lalata mata tasu rayuwar da rashin kamun kansa ba.

Doctors Haven asibitin da suke zuwa duka gidan Lilu ya kaisu. Farha da kafarta ta shiga kuma tana ta rokon Mami akan su koma gida.

"Zan saba miki idan ki ka sake magana Farha."

Bata sake cewa uffan ba har aka kira sunan file dinsu suka shiga wajen likita. Abu na farko da likitan ya fara gani shi ne jininta dake barazanar haure mizanin zaman lafiyar dan Adam.

"Hawan jini nema yake ya tashi daga ciwon manya zuwa na kowa da kowa."ya ce a kokarinsa na yiwa Mami Khadija bayani "ki saka mata ido ta cire damuwa daga ranta kada a gaba ya zame mata ciwo."

"In sha Allahu zan kula doctor. Nagode."

'Yan rubuce rubuce ya yi a takardar gabansu ya mikawa Farha takardar. Magungunan da zasu saya ne ya rubuta.

Shiru suka fito babu mai magana sai hannunta da Mamin ta rike. Gani take kamar idan ta saketa damuwar dawowa za ta yi har ta kuma sumar da ita.

"Jeki mota ki huta na karbo magungunan."

Muryarta can kasa duk tayi laushi ta ce "zan iya Mami ki je ki zauna."

Lilu yana bangaren da aka jere kujeru ya hangosu ya taso. Mami ta ce ya tafi da Farha mota su jirata. So take kawai su bar inda take ta samu ta fito da zahirin halin da zuciyarta take ciki babu rufa rufa. Tana kallo suka sauka daga matattakalar kofar fita waje sannan ta sami wuri ta zauna maimakon sayen maganin. Hawayenta ta bari suka sauko a lokacin da ta sanya fuskarta a kan tafukan hannayenta. Yana daga cikin abin da take gudu ace duka 'ya'yanta sun san halin mahaifinsu. Sai gashi bayan Suhaib ga dukkan alamu Farha ma ta sani yau. Rayuwarta da ta sadaukar saboda karesu tana shirin zama shirme da bacin lokaci muddin aka tafi a haka. Yaranta zasu daina ganin girman mahaifinsu. Tarbiyarsu za ta tawaya domin yana da hakkin matsayin uba a wuyansu. Wace irin rayuwa zasu yi a gaba? Wane irin mutum Allah Ya jarabceta da aure? Yana da damar karin aure. Ga kudi. Kai idan ya so ma ya sake su duka ya sake sabon zubi a gidansa da dai wannan kazamar rayuwa mara fasali.

A cikin motar Lilu ne yake ta damun Farha akan ta fada masa wane irin hoto Yumna ta turo mata. Tausayin yayar tasa yake ji har yana hasashen ko dai mutumin wani ne da Farhan take so a gefe.

Maganar hankali irin wadda bai saba ba yake yi mata tare da ban baki
"Kin san dai babu wanda zai auri matar da ba tasa ba. Ki bar mata shi kawai. Naki mijin fa idan ya tashi zuwa sai Kaduna ta girgiza."

Murmushi tayi wanda ya hade da zubowar hawaye. Za ta barshi ya cigaba da wannan tunanin har zuwa lokacin da kowa zai sani. Iyaka dai bata fata ko kadan wani ya fahimci akwai mummunar alaka tsakaninsu tun a waje.

A lokacin da suke 'yar hirarsu ne kuma idanun Lilu suka kai bakin gate din asibitin. Motar Suhaib ce take shigowa yana waya dasu Sauda masu damunsa yaya jikin Farha. Motar bayansa wanda ya zata mai ita yana jiran ya wuce ne shi ma ya yi nasa parking din ta soma karar horn da karfi.

Tsaki ya ja da karfi saboda anki daina danna horn din "Zan kiraku Sauda" ya jefa wayar gefensa ya kauce.

Har ya gama parking babu sassauci a karar horn din. Mutane suka fara kallon motar ana 'yan surutai. Kimanin minti biyu a tsakani da suka fahimci ko motsi motar bata yi sai hankula suka fara tashi. Suhaib yana so ya shiga ya ga halin da kanwarsa ke ciki ya dakata. Shi ya fara zuwa gefen direban ya kama hannun zai bude yaji a rufe. Gashi gilas din da duhu baya ganin komai. Farha da Lilu da 'yan tsirarun mutanen wurin sun firfito an tsaya a wurin. Ta gilas din gaban motar suke iya ganin kan matukinta akan sitiyarin kuma baya motsi.

"Ki koma mota Farha bari mu gani ko zamu iya balle kofar a fito dashi" cewar Suhaib ganin tana tangadi kamar za ta fadi.

Bata san me ya fito da ita ba kamar yadda Abbati bai san ya akayi ya iya daga kansa dake tsananin ciwo a lokacin ba. Sannu a hankali yake dagawa saboda kwankwasa gilas din da ake yi ta kowane gefe ana cewa ya bude domin a taimaka masa.

Sakan daya, biyu, uku...goma, talatin...idanun Abbati suka sarke cikin na Farha suna kallon juna. Bata tabbatar shi ne na diamond plaza ba amma fuskar ba bakuwarta bace. Abbati kuwa mamaki ne ya kashe shi a zaune. Da ace bai ga Lilu yaron da ya fara tsayuwa yin hoto a motarsu ba, da Suhaib wanda ya bashi hakuri da sai ya ce lallai gizo take yi masa. Kai ya girgiza a hankali ya runtse idanunsa sannan ya sake budewa yana kallon inda take. Fuskar da ta zame masa hoton zuciya ya sake gani ta dan yamutsata tare da dafa gaban motar don kada ta fadi. Rana ce ta take sosai mai zafi.

'Uncle Abbati?' Ta yiwa kanta tambayar da sunan da ta lakaba masa lokacin da ya dinga kiranta Ya Farha.

'Bata da lafiya' shi kuma wani sashe na zuciyarsa ya sanar dashi yana mai jin karfi na zuwar masa. Cire lock din kofar ya yi Suhaib ya bude da sauri. Ya zuro kafarsa waje hasken rana na saka shi kare fuskarsa da hannu saboda yadda yaji kamar ta kara masa ciwon kai.

"Lilu kula da Farha kafin mu shigar da mutumin nan ciki"

Sune kalaman da Abbayi yaji matashin da ya bude kofar yana kokarin rike shi ya fada. Dubansa ya kai gareta yaga yadda take takawa a hankali duk da daya saurayin wanda yake tsammanin shi ne Lilu din ya riketa. Takunta da duk wani motsinta ya dinga zama a zuciyarsa tamkar ana zana shi da kakkaifan alkalami. Yana da tarin matsaloli a kansa amma sake ganinta sai ya kankantar da komai. Tubalin dan guntun ginin da ya soma yiwa zuciyarsa katanga daga barin soyayyarta ya ruguje baki daya. Irin wannan coincidence din yafi karfin rainawa. Bai iya dauke ido daga kallonsu ba har ta shiga mota ta kwanta a baya.

Bin Suhaib da wani Security din asibitin ya yi ciki. A hanya suka hadu da Mami Khadija, wata mace da ya gani mai cike da haiba da nutsuwa tamkar mahaifiyarsa Baaba Mari. Wannan kam da gani babu tambaya uwa ce ga wadannan bayin Allah. Fuskarta kamar ba ita tasha kuka ba. Bandaki ta shiga ta wanketa sannan ta goge kwarmin idonta da kwalli ya bata ta daidaita shi. Kallon Abbati tayi wanda ko ba a fada ba ta san bashi da lafiya sannan ta tambayi Suhaib ko waye shi. A takaice ya labarta mata yadda suka hadu ta kalle shi da tausayawa.

"Bari na kaiwa Farha maganin sai naja motar shi kuma Lilu ya jiraka. Ka zauna dashi har ya dan sami kuzari sai ku kira 'yan uwansa." Ta sake kallon Abbati "Allah Ya sauwake kaji."

Tafiya tayi suka karasa reception. A nan Suhaib ya fahimci Abbati bashi da file a asibitin da ya amsawa matar wurin cewa babu amma zai iya budewa yanzu.

"Kiyi masa amfani da namu" cewar Suhaib yana tura mata file din da ta dauko lokacin "idan yana bukatar budewa ayi daga baya. He needs a doctor now (yanzu likita yake bukata)"

Abbati ya yi masa godiya sosai. Da zai shiga wurin likita sai Suhaib ya tambaye shi wanda ya kamata a sanarwa yana asibitin.

"Daga Kano nake kuma Abuja zan wuce. Idan na fito zan kira kanina" ita ce amsar da ya bashi.

Suhaib sai yaji ba zai iya tafiya ya barshi ba. Jira ya yi har likitan ya leko ya ce waye ya kawo Auwal. Tunda bai san sunansa ba sai ya dan yi daburce kafin ta tuna cewa wanda ya rako shi kadai ne ya shiga ciki.

"Gani" ya fada yana mikewa.

"Yauwa Suhaib ashe dan uwanka ne. Koda yake naga file din gidanku. Me yake faruwa ne ake ta zuwa da hawan jini. Nasa is very bad damuwa tayi masa yawa dole zan kwantar dashi don nayi monitoring dinsa."

Bin bayansa Suhaib ya yi. Nan ya tarar da Abbati a zaune amma ya kifa kansa a teburin likitan. Da fitar likitan wayar Shazali ya amsa wanda ya fada masa maganganu masu tada hankali. Yayi haka ne saboda gudun kada Chief Harrison ya nemi Shazalin ya maido da nasa kamashon kudin.

"Ran Chief ya baci fiye da zatonka. Yanzu haka ya tura gidanka na Kano a taho da kai. Mutanen sun tabbatar masa baka gida ya ce a dauko Munzali tunda tare kuke."

Abbati yana da saukin kai. Saukin kan da yawansa ya sanya Baaba Mari gudun tafiyarsa almajiranci. Gashi yau dashi Shazali yake amfani.

A raunane ya yi magana "Na fada maka ina hanya. Gani a Kaduna da kyar na karaso asibiti. Bani da lafiya Shazali." Kausasa murya ya yi duk da bata fita da karfi ya ce "Idan ka shigo da Munzali cikin abin kuma wallahi sai na nuna maka nawa kalar haukan".

Ya san Abbati sarai. Ba zai taba yi masa karya ba saboda shi mutum ne kaifi daya kuma mai yawan kyautata zato. Ba dabi'arsa bace bincike da bin kwaf balle ya gano karyar da ya yi masa. Hasali ma Chief Harrison ya bashi damar kawo masa kowane irin namiji. Da ya ce zai kawo Abbati ne ya kara nasa dubu dari akan abin da ya bashi.

"Tsakaninmu bata baci Abbati. Ka maida wukar. Zan yi masa bayani sai na hada shi da wani."

Suhaib ne ya taimaka masa zuwa dakin da aka bashi ya kwanta. Yana wurin aka zo aka dibi jininsa domin gwaje gwajen cututtuka irinsu maleriya. Bayan an gama an soma yi masa karin ruwa aka hada da allurar bacci. Baccin na fizgarsa Suhaib yana son sake tambayarsa wanda zasu nema ya kula baya cikin hayyacinsa saboda karfin allurar. Likitan ya ce yana bukatar hutu sosai.

Waje ya koma inda Lilu yake zaune akan mota yana jiransa. Mukullin ya cilla masa yana yi masa bayani.

"Ya yi bacci kafin ya bani nambar wani nasa na kira. Zan zauna kaje gida ka karbo bedsheet da bargo don na kula akwai hadari."

Lilu ya tafi shi kuma ya koma ciki. Har Lilu ya dawo da kaya niki niki wanda Mami Khadija ta hado

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login