Showing 1 words to 3000 words out of 241571 words
Chapter 1 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
'YAR MACE....🌺
*Mai_Dambu*
#Wannan labarin zai iya daukar wani salo na musamman duk abin da za aji ayi nazarin ba sabo bane....
Paid book
01
Yau rana ce na musamman ga Aliyu Muhammad Jadda, wato Tafida yau ranar al'ummar jahar Borno zasu tabbatar da shi a matsayin halattaccen Gwamnar jahar Borno, wanda yayi daidai da haihuwar da nayi. Kallon Nurse din nayi da take nad'e yaran na ce mata. "Macen ce babba ko namijin?" Cikin girmamawa ta ce min. "Ranki shi daɗe, Macen ce babba." Ajiyar zuciya na sauke tare da faɗin. "Ya Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka Ubangiji ka bani ikon tunkarar yakin da nake shirin gudanar da ita, Ya Allah na rokeka a sarari da boye ka bani ikon yakar Aliyu Tafida har sai na kai shi kasa " Turo kofar dakin aka yi na zuba mishi idanu, ko kiftawa bana yi, "Inuwar!" Shiru yayi bai karasa ba, na kauda kaina ina kallon inda ake gyara Yaran, domin ina haihuwa sai da suka gama gyara min jikina sannan suka koma kan Yaran. Takowa yayi har inda nake zaune fuskarshi dauke da murmushi ya shafa kwantaccen sumar kanshi yana reading fuskana. Dauke kai nayi tare da cewa. "Harkalla ya faɗa!" Da wani irin sauri ya d'ago kai yana kallona. "Hala baka ji ba ne? Harkalla ya faɗa!" "A'a Hadiyyah kada muyi haka dake!" Zabura nayi wanda ban san ina da karfin na ce mishi. "Kace me? Kace me? Harkalla ya faɗa nace Tafida! Gasu can ba daya ba biyu na baka na gama!" Cikin masifar da yake dauke da ita wanda nayi imani da Allah ba zai daina ba koda kuwa kasa zata rufe masa idanu ne ya ce min. "Ke kin isa ne ki ce zaki ja dani? Saura awa uku na saka doka da oda baki isa ba wallahi, kuma ki ji da kyau babu wanda ya isa rabaki da Yarana ki ajiye wani harkalla ai kin fara kenan First Lady!" Ya faɗa yana sakar min muguwar murmushi, nima haka ce a kan fuskana. A hankali na zuro da kafata kasa, naji na tsaya daidai akan kafata. Ban ce mishi cikanka ba, na nufi inda kayana suke na cire doguwar abaya na shiga ban daki na watsa ruwa na gyara jikina,sannan na fito zuwa dakin an gama shirya Yaran. Yana tsaye akansu ba zan iya bayyana yadda yake jin Yaran a ranshi ba, amma nasani kamar yadda maza da yawa suke amfani da Yaran mace domin juya akalarta ni yanzu Aliyu Tafida yana hannuna ne da Yaranshi. Sai da na gama shiri tsaf sannan na nufi wurin akwatin kayanmu na ciro tsohuwar ajiya na nufi inda Yaran suke na ajiye mishi. "Wannan shine karshen Yarjejeniyar da muka yi, na sauke nauyin da Allah ya bani, kai ma sai ka yi adalci ka sauke nauyin da yake kanka!" Bude takardar yayi ya kalle ni dakyau. Ganin na shafi kumatun Yarinyar da take barci cikin kaya pink! Ya rike hannuna. "Diyyah me kike so na gayawa Duniya? Yau za a rantsar da ni! Yau kin haifa min Yara har biyu Diyyah ko don albarkacin Yaran nan ki hakura mu daidaita kanku waye zai rike mana su? Diyyah na taso babu uwa na sha faman rayuwa don Allah ki!" "Na rantse da Allah! Wanda babu wani sarki bayan shi ba zan zauna da kai ba, ai mun gama maganar nan tun wata bakwai baya me zai saka a dawo da shi. Tafida ka bukaci haka ni kuma na maka laifi ne? Ni da kai auren an yi bamu son juna, ni va irin matar da kake ba ne, Tafida zuwa yanzu ya dace mu fuskanci rayuwarmu Yara ne gasu nan na baka su don Allah kada mu samu matsala akan haka! Ana jirana a waje Allah ya tayaka rikon al'ummar Borno da kewayensa, Ubangiji yasa daga nan har matakin shugaban kasa. Na gode sosai!" Na juya a hankali ina jin hawaye na shirin zuba min. "Ummu me kike so na gayawa Abbana da Inna?" Cak na tsaya tare saka bayan hannu na goge hawaye da yake zuba min. "Abba adalin Uba ne, Inna dattijuwa ce me hangen nesa. Sun bani tabbacin wata rana zan tsaya na kwaci yancina amma babu wanda ya bani tabbacin zan cigaba da zama cikin kaskantacciyar rayuwa! Ni Yar mace ce, Kwantai ce sannan ni yar tuwo-tuwo ne, baka gajeruwa me sufar kwado, mummuna yar kabilar Babur...." Ji nayi ya toshe min bakina ta baya. "Ya isa haka! Ya isa haka!" Ya faɗa yana haki Idanunshi ya kad'a jajjur fuskarshi ita kanta tayi jar ne sosai. "Ki min uzuri bayan gama bikin rantsuwa zan zauna dake!" Kallonshi nayi shekeke! Dariya ya kwace min nace mishi. "Ni ce zaka zauna da ni? Ka manta ne na tuna maka? Ka manta kace baka ga ranar da zaka zauna da ni domin Sulhu ba? Ko ka manta ne ka ce min tunda Abba ya auro maka ni zaka dauke ni kamar takalmin ka ce idanu lokacin da kaji bukatar kayi ado zaka shure ni yadda kake so? Ko ka manta da cewa ni din nan dai gajeruwa jahila yar kananun mutane ce! Ni da Allah ya halicce ni ne domin kawai ka biya bukatarka baka fatan ka haɗa iri da ni! Ga mata." "Ya isa haka!" Ya faɗa da mugun karfi da yasa ni ja da baya! "Me yasa tuntuni baki fito da wannan nufin ba sai yanzu? Me yasa? Ke kiyi duk abon da kike so wallahi babu shegen da ya isa ya sani sake ki kada ki ga ina bin ki, ki tsammaci don ina tsoron ki ne!" "Ai kuwa har abada ba zan sake zama a inuwar mutum irinka ba, wallahi billahi azim na gama zama da kai kana da damar cin mutuncina daga har ranar da zaka fara aiki ni kuma zan tabbatar na baka mamaki!" Na juya zan fita ya riko hannuna. "Ba kida hankali ne?" Ya faɗa da karfi. "Daga turu nake karewar rashin mutunci!" Na fisge hannuna,na barshi sake da baki. Kuma ina fatan na bar Tafida kenan har abada, haɗiye kukan da taso min nayi sannan na gyara tafiyata a hankali har harabar asibitin motar da aka kawo ni asibiti na nufa. "Na san ni mai laifi ne a gare ki, amma ba zaki tausayawa waɗannan bayin Allah ba? Basu da laifi ko ɗaya na san kin fahimci haka, don Allah kada ki sani kara jin tsanar wata mace." Dariya abin ya bani. Na juya tare da murmushi. "Sai me? Ai ba yau ka fara tsanar mace ba, ko so kake na gayawa duniya cewa Mutumin da zai zama wani abu a gare su yana jin tsanar Uwar da ta haife shi?" Rintsa idanunshi yayi ya bude a kaina yana kallon yadda na juya abina, zan bar Tafida na har abada amma dole ya fahimci girma da soyayyar Uwa ya gane cewa ita uwa ba abin yarwa ba ce. Kamar wani gigitacce ya riko hannuna yana faɗin. "Gaya min me kike so nayi?" Shiru nayi kafin na tura baki don da dama ya zama dabi'ata na watsa hannuna na ce mishi. "Ohon ka, duk abin da ka gadama kayi Tafida. Kai yanzu ai gwamnatin ne idan kaso zaka iya sakawa a kashe ko a kyale rayuwarka ce ba tawa ba!" Na fada zan juya ya riko hannuna kamar zai zube a ƙasa. "Gaya min me zanyi na sha azabar rashin Uwa kada Yarana Tarihi ya maimaita kanshi!" Dafe kirjina nayi da naji suna zuui-zuui wafce hannuna da ya rike nayi tare da nufar motar da sauri n shiga ya maza ya rike ni. "Tafida wallahi idan baka kyale ni sai na falla maka mari!" Na fada da kausassiyar murya da tasa shi tilas ya kyale ni,na rufe kofar motar. "Muje mudansir!" Babu uwar da zata haifi d'a ta bar shi a ranar farkon da ta haife shi, babu uwar da zata so ta juya tabar danta a halin yana bukatar ta. Sai dai na san haka da nayi shine mafita. Jinjina kaina nayi da jikin motar har muka isa unguwarmu bolari market can karshen layin anan gidanmu yake, a hankali Mudansir ya sulala hancin motar har kofar gidanmu, sai da ya ce min. "Hajiya mun iso!" Na juya da kaina ina kallon kofar gidan, kamar yadda nasan gidan yana nan a yadda yake babu sauyi, Kawu gwani na hango ya fito yana waya. A hankali na janye idanuna daga kanshi, "Hajiya mun iso!" "Tow!" Nace a sanyayye ina jin kamar na rabu da bukar ne na haifi abu, Kawu gwani a wannan lokacin kamar fama min sabon b'acin rai ne, kamar nace mu juya sai na fasa. "Hajiya ko na maida ki asibitin ne?" "A'a Mudan na gode sosai!" Na bude motar zan fita ya kuma jefo min wata maganar fa ta sani jin numfashina kamar zai fita. "Hajiya Ummu, ina ga barin yaran nan a hannun Oga Tafida ba mafita ba ne, duk abin da zao faru a tsaya akan juna. Su bayin Allah ne da basu ba basu gani ba." Shiru nayi kafin na kakaro murmushin karfin hali da kwarin gwiwa nace mishi. "Na gode da shawara!" Sannan na bude motar na barshi da dinbin mamakina. Eh kowa ma mamakina zai ji amma ni ba wani abu ne kawai na zaɓi haka ne don rama abin da nake ganin shi ne daidai, a lokacin da Tafida yake azabtar dani hakuri ake bani ana nuna min cewa idan na kashe auren kowa zai tabbatar da bani da mafadi. "Ke ina cikin?" D'ago kai nayi na kalle shi kafin ma kauda kaina ina faɗin. "Suna asibiti!" Na furta tare da nufar hanyar cikin gidan, shanye da mamaki ya rufa min baya, "Ummu kina da hankali kuwa? Ina Yaron da kika haifa!" A matuƙar gajiye na nufi ɓangarenmu, na fada cikin gidan da sallama. "Aunty Ummu?" Yan matan da suke taya Mama aiki suka faɗa. Mama da take dama gasarar kunu ta leko tana kallon yadda nake tafiya a hankali. "Ina cikin yake?" "Suna asibiti?" "Kamar ya suna asibiti?" Ta kuma wurga min tambayar. A gajiye na ce mata. "Mama na haihu dazun da asuba!" Sake kwaryan hannunta tayi cikin mamaki ta ce. "Kin fara hadiyar kwaya ne?" "Mama nima abin da na gani kenan!" Ya faɗa daga bayana! Takaici yasa na wuce zuwa dakin Mama. "Ke Badi'a kawo min bokiti a kwashe mata ruwan zafin nan, a sake daura wani!" Ta fadi haka tana fitowa daga zauren girkin. "Mama" "Kawu gwani je ka, kada Hajiya Balkisu ta ganka." "Amma " "jeka kawai!" Ta fada tana me shigowa dakin ganin yadda na kwanta tare da lumshe idanuna yasa ta shafa kaina tana faɗin. "Me yasa kika bar Yaronki?" D'ago kai nayi idanuna cike da kwalla nace mata. "Kin ce min ba zaki bani mafita na yaki da Aliyu ba? Kin kara da cewa zaki tsaya min a gabana da bayana, don Allah Mama kada ki ce kome." Kura min idanu tayi kafin ta ce min. "Ina nufin zan baki duk wani goyan bayana amma ba ina nufi ki ajiye Yaronki a hannun shi ba, idan shine ya bukaci haka shi kenan." Girgiza mata kai nayi tare da cewa. "Ni ce na zaɓi haka!" Kura min idanu tayi ina iya hango kwantaccen b'acin rai a cikin idanunta, murmusa min tayi sannan ta juya zuwa waje, can ta dawo da kunu a hannunta ta ce min. "Tashi ki sha." Babu musu Na amsa tare da kafa kai sai da na sha rabi sannan ta ce min. "Tashi ki sauya kaya an kwashe miki ruwan zafin ganyen Dalbejiua ne da ba a samu ba yasa kika jima!" Ta shige can kuryan dakinta na bita da kallo tarkace ta fara fitowa da shi, tana me cire su a leda, tana kallona na cire kayana, sannan na daura zanin da ta ajiye min sabo ne fil. Na dauka na daura ta ce min. "Ki duba sif akwai hijabi sabo ki dauka daga yau sun zama kayan wankinki da jego, sannan ki gaya mishi za a zo dauka miki kayanki na sawa!" "Tow amma kin san yau za a rantsar da shi?" Na fada mata ina kokarin fita daga dakin. Ta ce min. "Na sani mana Ummu! Aliyu Muhammad Jadda Tafida zaɓaɓɓen gwamnar jahar Borno ba!" Fita nayi domin na fahimci Mama tana fusace, kuma idan na sake nayi magana zanci Ubana! Ina fitowa waje ana kawo ganyen Dalbejiya. Ban daki na wuce, itama ta fito tana faɗin. "Sannu Sa'adu." Ya amsa ta shiga gyara ganyen sannan ta biyo ni ban daki, tunda kannena suke haihuwa ba ita take musu biki ba, domin Mama yar kasuwa ce kuma bata da lokacin da zata zauna musu daga Biu take dauko me zama a gidansu, har su yi arba'in amma ni dake yar gata ce na samu wannan damar. Shigowa ban dakin tayi tare da saka ganyen a cikin ruwan da yake tiriri. Ta yayyafa min a kafana sannan ta kuma diba ta zuba a karo na biyu. Karo na uku ta shiga yafa min ruwan sosai tana yi tana dauke kanta yadda ta ga ina jin dadin saukar ruwan a jikina. "An miki dinki ne?" "Eh!" Bata kuma cewa kome ba,ta cigaba da min wankar sai da ta kwashe rabin bawon sannan ta fito daga ban dakin ta hada min sauran kayan wanka ta kai min, ta tab'a ruwan bawon ta saka min gishiri a ciki ta ce min. " Shiga ki zauna!" Ba musu na zauna a cikin ruwan, ina cizon bakina. Sannan ta fita can ta kuma kawo min ruwan zafi da na kara wanka da shi sosai,lokacin da na fito ji nayi kamar an zare min duk wani gajiyar da yake jikina. "Ummu ashe an sauka lafiya?" Inji Jamila, murmusa mata nayi na wuce dakin. "Mama ina Yaron yake?" "Yana asibiti bai da lafiya." Idanuna ne ya cika da kwalla wato ita uwa wata tsani ce da ba kowa yake hawa ba, take ta gyara abin da na aikata da wani abu na daban, "Sa'adu ka kira min Yusuf yazo maza ya yanka min talotalona dama ya ishe ni!" Ta fada tana wucewa kitchen, dake gidan Mama baya rabuwa da masu sayan abinci yanxu haka kunu aka yi da kosai da alale na safiya. "Zakiya kina kwab'a dan waken ne?" "Eh Mama." Ta fada daga cikin ɗakinsu, "Tow ai waken da yake kan wuta ya nuna, ga Kwai ma na sauke miki!" "Mama Ina Uwani ne?" "Ta kai marden kayan miya ba!" Ina daki aka shigo min da alale da manja da yaji cikin kula har yana tiriri, ga kwai guda shida akai, ga kunun tsamiya da ta kuma dama min, "ki duba sif din akwai kayan Ummu Kulsum ki dauka mana!" Na juya na dauko kayan Ummu Kulsum na shiga kokarin sakawa. "Mama nonon yana zuba!" Banza tayi da ni. Juyawa nayi naga tana janyo wani bokiti no secret, ta ajiye min dambun kaza ce ta ajiye sai wani kwano samira shake da yajin kalwa, kafin kace me dakin ya dauki alamar jego. "Zauna ci, ki kwanta."
Baya da kura.
Kasa tsayuwa yayi ya nufi cikin asibitin, ya kalli Nurse dinda suke dakin kamar gulma suke,suna ganinshi kowacce ta kama gabanta. Wayarshi ya ciro ya kira Yayarshi."Maryam ki zo maza asibiti Ummu ta haihu." Kafin wani lokaci labarin haihuwar ya karade familyn Aliyu Tafida, kafin karfe takwas asibitin ya cika da yan Barka, sai dai duk wanda yazo ya ga Yaran turus yake yi idan yaji uwar Yara ta barsu. Shi dai a saninshi ba a tab'a yin haka ba, amma kamar kaddaranshi ce yake bibiyarshi yasa haka ya kuma faruwa da Yaranshi. Idanunshi ya lumshe yana jin yadda Inna take salati. "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Tafida lallai kin tunawa kanki asiri! Yanzu ke Tafida abin da kika yiwa yaron nan Ummu Hadiyyah kin kyauta kenan? Yaron nan Ummu Hadiyyah ta gama shan wahala dake shine zaki saka mata da wulakanci? Tafida ki ji tsoron Allah wallahi halinki bai da kyau!" A fusace Tafida ya kalli Inna da ya fahimci har duniya ta nad'e ba zata daina mai da shi mace ba, ta kuma daina mai da mace namiji ba ya haɗiye takaici ya kalli Hajja Gana ya ce mata. "Hajja gaanah ki gayawa yar uwarki don Allah yta shiga gaba Ummu Hadiyyah ta amshi Yaran nan wallahi kukansu hana ni sakat yaƙe!"
Domin ya fahimci zuwa yanzu babu wanda zai tsaya mishi mahaifinsa da yaji labarin yaki zuwa asibitin ma, kuma yaki magana ma, Yayunshi maza da mata kowa sai cewa yake Allah ya kyauta yanzu ya fahimci suna shirin juya mishi baya, Kallon Maryam yayi da ta dauki Macen da bata da yawan kuka ta ce mishi. "Tafida kasan lokaci yana tafiya, kuma!" Zuba mata idanu yayi kafin ya ce mata. "I wishing da mafarki nake da na farka! Zafi biyu nake ciki." Ƙarar da wayar shi tayi ne ya saka shi. Kallon wayarshi yayi wanda an kira yafi sau saba'in ya kuma juya ya kalli Jariran da suke kyankyara kuka ji yayi kamar duk duniya babu wanda aka tab'a tubewa mutuncinsa aka watsa a titi kamarshi tsinkayo muryan Hajja Gaanah yayi tana faɗin. "ABIN DA KIKA SHUKA, SHINE ZAKI GIRBA MARA KUNYAR KARYA ANAN KIKA CEWA annah Yaron nan Ummu Hadiyyah tana haifa miki Yara xaki kawo masu kula da su daga can ƙasar arna su musu irin tarbiyyar da kike so kai Yaron nan Ummu Hadiyyah dan halak."
Kasa yayi da kai daidai kira na saba'in da daya yana shigo mishi. "Ki dauka kada ki saka a fasa rantsar dake a matsayin gwamna." Safiyudeen ya gani a hankali ya dauki wayar. "Saura awa uku, ga kayanka ya iso kana ina ne?" "Ina cikin tashin hankali, Ummu Hadiyyah ta haihu ta bar min Yaran!" "Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Me yayi zafi Tafida!" "I don't know!" "Ka sani Aliyu Tafida ka sani Aliyu kasan me yasa ta barka!" "Ya zanyi tow yaran suna kuka sun ki amsar