Showing 216001 words to 219000 words out of 241571 words
Chapter 73 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
na shi na san yana yi ne na dole,, domin ya kwantar mana da hankali, amma nashi hankalin ba a kwance yake ba, wannan abin ya ƙara saka ni cikin zulumi, wanda ya kai da ko motsin kirki bana iyawa ba tare da na kalle shi ba, tun da muka bar jidda, naji hankalina ya dawo jikina ya zamu kwashe da Mama kut, bata san nazo nan ba, wannan shi ne asalin satar fita. Hankalina yayi bala'in tashi, jirginmu sai da ya sauka a abuja, sannan muka yi bankwana da Tinah, kayan da muka saya tun zuwan mu can ta ce min zata aiko min idan sun iso, kafin mu wuce Maiduguri nayi sallah da ake bina, sannan muka jira jirgin can muka wuce, wato nice ban fahimci waye Aliyu ba domin tun anan Abuja yan majalisun wakilai na jahar Borno da na dattawa suka zo mishi gaisuwa, a lokacin yake gabatar musu da ni. "Ga Madam nan!" Sai na tsaya kallonshi, shi akewa Ta'aziya tare da ni, yana fada musu. "Ai akan cinyar Madam ta rasu, she love Madam sama da yadda take sona, ni da ta haifa." Sai suce ayya, sannu. Haka ta fita ya gama gabatar da ni a ga mutanenshi koda yake ya nuna musu Abba. Sannan muka bar Abuja, kallona Asiyah tayi tana faɗin. "Don Allah me yasa Ya Aliyu yake sonki? Bayan kin ki dawowa gare shi." Murmushi nayi domin na lura Asiyah wawuya ce sosai. "Ban tab'a cutar da kowa saboda da shi ba, na aure shi ne tun yana Tafidan shi ba yanzu da ya zama me kumbar sosa da wasu suke rubibinsa ba, ni na san waye shi kafin yau, don haka idan yayi min wani abu kyautatawa ce domin bayan ni babu wacece zata ce miki tasan waye Aliyu." Gyada kai tayi tana faɗin. "Hmm!" Ta cigaba da kallon waje, bata kara min magana ba, nima kuma ban bi ta kanta ba, domin kuwa yadda zan taradda Mama yafi kome d'aga min hankali. Koda muka iso garin ya hadu da hadari dama tun a jirgin ake fada yanayin zai iya sauyawa saboda yanayin damina da muke ciki. Muna sauka ruwa na tsinkewa, zama muka cigaba da yi a cikin jirgin har wurin karfe uku kafin ruwan ya tsaya muka fito, tawagar mai girma Gwamna suka iso karbanshi, ana ta mishi gaisuwa, koda muka bar airport abin da ya ce ya kara gigita min lissafi na. "Kiyi hakuri ki cewa Mama tayi hakuri, ban sani ba ko zan zamu kara haduwa" kallonshi nake yana tsaye har na shiga motar a jikin window ya tsaya ya ce min. "Thank you for everything!" Ni dai ban ce mishi kome ba, har muka bar airport din, shima gidanshi suka nufa. Sai da aka fara ajiye Abba a gidan yayi ta bashi hakuri da ban baki, ya gyada kai, koda suka isa kofar gidan ya samu tarin Jama'a da alamu anan zaman makoki kenan, har cikin gidan suka shiga Deen ya hango a barandar gidan yana zaune da Umar. Nufarsu yayi suka mike hannu Umar ya mika mishi suka gaisa kafin suka rungumi juna. Daga nan suka zauna yayi ya gaiswa da bakin wurin, har da Deen. Shi dai bai ce kome ba, wani almajiri yayi sallama ya shigo ya durkusa ya ce musu.."Ni muna tare da ita ne a wancan unguwar yau nake jin labarin rasuwarta to Allah ya mata rahama." Daga nan yayi ta addu'a, addu'a yake yana karawa har sai da yayi kamar ba zai daina ba, Deen ya ciro dubu goma ya bashi sadaka, a wurin a hankali suka hada mishi kudi sosai. Sannan ya tafi sai yanzu mutuwar ta shiga jikin Tafida, domin sai da ya kebe yayi wanka yayi Sallah azahar da La'asar. Domin su a masallaci zasu yi, haka ya sa shi yi a gida. Yana zaune, Asiya ta shigo da sallama abinci ta kawo mishi. "Har kin yi girki?" "A'a kawo min Fanna tayi daga cikin gidan!" "Je ki ci na koshi Deen zai kawo min abin da zan ci!" "Tow!" Ta fada tana barin parlourn, jallabiyar da yayi sallah ya sauya sannan ya fito ya nufi cikin gidan bangaren Hajiya, a parlourn kawayen Maryam da Rukayya ne ana ta cin abincin ana hira. Yadda yayi sallama yasa kowa ya shiga hankalinshi. Yadda yake musu wani irin kallo kafin ya juya zai fita, Fanna ta ce mishi. "Kowa za a kawo maka abinci ne?" "A'a!" Ya fada yana barin parlourn, mai zai yi da abincin? Barandar da Deen yake ya nufa ya zauna suka kara gaisawa. "Su Ammah sun zo, an jima zasu zo gaishe ka!" "Kace tayi min kunu." "Eh nasan zasu zo da abinci bari na ce ayi maka kunun!" Shiru yayi yana me kiran Matarshi ta gayawa Ammah tayiwa Tafida kunu, bayan ya gama wayar ya kalli Tafida. Shigowar Umar da Abubakar yasa shi zuba musu idanu. Domin ya lura da yanayin Umar da ya sanya. "Aliyu ko zaka zo zamu yi magana!" "Tow!" Ya ce yana mikewa, parlourn shi ya nufa da su, suna shiga parlourn Umar ya kalli Abubakar cikin fushi yana faɗin. "Ka maimaita abinda ka fada?" "Hmm!" Dariya yayi yana faɗin. "Ka zata tsoron Tafida nake ne da ba zan fadi abin da na fada ba? Karya nayi ne? Waye zai san shi da naci ba? Mutuwar Hajiya ba mutuwar Allah da Annabi ba ne shi ya kashe ta domin mulkinsa!" A firgice Tafida ya kalli Babban Yayansu da ya furta wannan kalaman da suka fi kome muni. Tsuma jikin Tafida yake jininshi yana wani irin tafasa, ranshi yana wani irin zafi, kallon Abubakar yayi ya ce mishi. "Ban san me kake nufi ba, ban kuma gane me kake faɗa ba ko zaka iya maimaita abin da ka faɗa!" Mamaki ya kara rufe Abubakar ɗin ya ce mishi. "Kana nufin baka fahimci abin da nake nufi ba? " "Eh ban fahimta ba!" "Jinin mahaifiyarmu ka bada domin mulkinka!" "Tow meye ribana?" "Waye ya sani!" "Ka je na barka da Allah!" Wannan shine abin da ya iya furta mishi, wato yan uwan Tafida mugaye ne, bayan Fitar su Deen ya kira ya gaya mishi kome, yana dafe kanshi. "A gayawa Abba mana!" "A'a kada ka gaya mishi kyale shi na barsu da Allah!" Ya furta yana murmushin baƙin ciki, da damuwa.
Ummu.
Tunda na dawo Mama ta rasa gane kaina, asalima bata tambaye ni abin da ya faru ba, amma tabbas naga yanayin sanyi da tausayi a idanunta, domin tunda na shigo gidan na samu wuri na zauna nayi kuka har sai da kaina ya fara sarawa, sannan na shiga nayi wanka da alola nazo nayi sallah. Ina zaune ta shigo tana kallon yadda nake ta addu'a, a hankali ta ce min. "Kiyi addu'a Allah ya zab'a miki abin da yafi alkhairi idan gidan Tafida ne Allah ya tabbatar idan ba gidanshi ba ne, Allah ya baki wani mijin da ya fi shi." Kasa cewa Amin nayi, taya zan gaya mata Tafida Mahaifiyarshi ta bar min amanarshi, taya xan gaya mata yanzu Tafida Amanarshi Hajiya ta bani.? Mama zata fahimci yadda ake ji kuwa? Ba ta gane yadda ake ji ba, abinci ma sama sama na ci, da Tunanin Tafida na kwana, washi gari ban tashi da wuri ba, tun bayan Sallah asuba na cigaba da barci, wurin karfe tara na farka ashe har ta bada abinci a kai gidan.
Wurin karfe daya wayata ta samu charger. "Key bangarenki yana nan a hannunki?" Girgiza kai nayi na ce mata. "Yana wurinsa!" "Ki rashi zan yi magana da shi ne!" Wayar na dauka na kira shi sannan na mika mata. "Waalaikumunsalam Malam Deen, ina Tafida yake ya hakuri kuma? Hajiya lokaci yayi!" "Alhamdulillahi, yana kwance ne baya jin dadi!" "Tow ko za a samu key din shashin Ummu gamu nan dawowa." "Tow Mama za a samu!" Ya fada cikin farin ciki. Mika min wayar tayi sai godiya yake. "Gobe za a kawo miki kayanki, tunda akwai wasu a can, Yaran kuma ki bar su anan, Tafida bai da Hajiya kece hajiyar yan uwansa kuwa ba zan kyale kowani dan iska ya kara tab'a min ke ba....71
Ba dai yanayin da na shiga yasa Mama zata mai da ni ba? Ba dai damuwar da nake ciki yasa take ganin kamar don Tafida na shiga ba, idan don haka ne tabbas Mama ta sake kulle ni kamar baya, Babana na kira na ce ya bawa Mama hakuri ko na mata laifi ne. Tambayata yayi na gaya mishi, ya ce min. "Baki mata laifi ba, ina ga halin da ya shiga ne take tausaya mishi. Ki bita duk abin da ta ce." Ya fada min sai naji bakiɗaya jikina yayi sanyi na kasa magana ma, haka muka yi sallama yana ta min addu'a. Tashi nayi na saka doguwar riga, sai yafi da na yafa ina son magana amma ina tsoron yadda zata dauki lamarin. Tare dasu Uwani muka nufi har da Yaran, lokacin da muka isa Deen yana bakin kofar gidan har parlourna ya bude mana, wanda aka share aka goge, tunda muka zo naga ana ta lekenmu, "Bari xan mishi magana!" Inji Deen, Yana fita sai ga Rukayya tare da Saadiyyah. "Burinku ya cika an kashe Hajiya!" Inji Rukayya, zata kara wani maganar, kamar wanda aka koro shi sai gashi nan ya fado parlourn. "Idan baku bar min gidana ba, sai na saka an rufe ku na har abada!" Ya fada da karfi, da sauri suka fita. Zuwa yayi ya durkusa gaban Mama kanshi a sunkuye, "Umnu zata iya ruwa a duniyar da nake kuwa? Ki tafi da ita kada wani abu ya same ta." "A matsayinka na gwamna ana bawa matanka security da duk wani abin da ya dace na tsaro,ina ga suma sun isa babu me iya cutar da ita. Idan kuma suka sake wani abu ya kara faruwa ni zan shigar su kara. Yanzu rashi aka muku me zai saka muyi fushi har mu harzuka? Ummu ce dai zan dauka mata lauya domin bana jin zan kara yarda wani ya cutar da ita." Tashi yayi ya suka fita da Deen, bangaren Hajiya ya nufa Deen ya rike shi. "Gobe za ayi addu'ar Uku, daga gobe zasu bar gidanka kayi hakuri." Da wannan ya dakatar da shi, amma zuciyarshi ba dad'i, bayan Magariba su Mama suka tafi, kulawa da Tafida ya dawo hannuna a daren, duk da a halin da yake ciki tambayata yake na duba Asiyah kuwa, gaskiya naji babu dadi ya ni da nazo akan jinyarshi zai hada ni da wata Matarshi. Sai dai kuma wani abu da na kasa fahimta shine tsakanin Tafida da Asiyah waye yake jinya? Domin a lokacin da na fito duba ta, na same ta a bakin kofar tana tsugune, "me kike yi a cikin sanyin nan!" Mikewa tayi ta ce min. "Aunty Baby, dama nazo duba Ya Aliyu ne!" "Ki shiga yana cikin!" Na juya ina bata hanya, kamar zata tashi sama ta bi inda na nuna mata, tana shiga yana jingine da allon gadon. "Ya Aliyu!" Ta kira sunanshi, bude mata hannu yayi, a hankali na juya na koma parlourn. Ina jin kamar na bar gidan, amma babu damar haka. Kukanta da dariyarta a lokaci guda take yin shi, kafin can na ga ya fito da ita a hannunshi. Sunkuyar da kai nayi ina jin hawaye na zuba min, idan Wannan shine kishi tabbas bai min adalci ba, me yasa ban yi kishin Sa'adiyya ba? Ɓangarenta ya wuce da ita, ya kwantar da ita sannan ya dawo ya same ni har lokacin ina parlourn hawaye na zuba min. "Ummu!" Ya kira sunana yana zama a gabana. D'ago kai nayi ina kallonshi, hawaye na zuba min. "Nasan da zafi kuma da ciwo, amma ina son ki aro hakuri da juriya, Asiyah yarinya ce da take buƙatar kulawarmu, duk abinda yake da wa'adi wata rana zai wuce. Na rasa Hajiya." Rufe bakinshi nayi da hannuna. "Kayi hakuri ba zan kara ba. Na fahimce ka sosai." Na fada ina danne kukana, hannunshi bakiɗaya yana cikin nawa, kafin ya daura kanshi a cinyata, nayi ƙoƙarin danne kukana amma ban iya ba haka nayi sosai.
Can na matsa mishi muka koma daki, a dakin ma yana kwance a cinyata. Haka muka kwana domin ina jingina da allon gadon, cikin dare naji yana nishi, bude idanuna nayi na zuba mishi, k'amkame ni yake yana faɗin. "Ban kashe Hajiya ba, bana son mulkin ma bana bukatar Ummu wai ni ne na kashe Hajiya!" Addu'a nake tofa mishi ina shafa kanshi har ya yi shiru, tashi yayi yana kallona yana d'aga hannunshi. "Ummu da gaske ni na kashe Hajiya?" Girgiza mishi kai nayi ina shafa bayanshi, ajiyar zuciya yake saukewa yana kara k'amkame ni. Lallabashi nayi muka shiga ban daki yayi alola. Kusan rabin daren mun shi ne a tare, washi gari kuwa naki barinshi ya fita da Deen muka yi magana na gaya mishi yadda ya kwana. "Tafida yana buƙatar addu'a sosai ina ga har sauka za ayi mishi!" Ya fada yana barin parlourn.
*Malam Zailani*
Shiru yayi yana kallon Deen, "Yanzu ka fahimci abin da na gaya maka wani lokaci da ya wuce? Tafida da kai da Ummu kuna tare da shi ne dad'i ko wuya, ba zaku iya fushi da shi ko ku rabu da shi ba, Allah ya gani ina son alakarku! Ka je ayi sadaka a rabawa kowa da kowa Allah ya kare mu da mugun ji da mugun gani, duk wanda yake da wani abu don ya cutar da shi Allah ya mai da mishi." "Amin Ya Allah!" Ya furta, sannan ya bar gidan. Tare da katon jarka zam-zam.
**
Karfe goma ya farka, ina parlourn da Asiyah. Motsin da naji yasa na tashi itama tashi tayi tana zare idanu. "Ko zaki je ki kula da shi ne?" Na tambaye ta, yake tayi tana faɗin. "A'a jeki kawai!" Ta zauna tana kallon kofar, sai da na shiga na samu yana zaune. Ban daki na shiga na hada mishi ruwan wanka, sannan na fito na ce mishi "bari na turo Asiyah ta taimaka maka!" "No need Ummu!" Ya fada yana janyo ni na zauna a gefenshi. Yadda yake sauke ajiyar zuciya zai kara tabbatar maka yana kukan zuci ne,haka nayi ta shafa hannunshi har ya yi shiru sannan na raka shi ya shiga ban dakin. Fitowa nayi na ga idanunta kuru akan kofar dakin. "Tashi ki je ki cire mishi kayan sawanshi." "Tow!" Ta fada da sauri tana nufar hanyar dakin, "kin karya kin sha magani!" "A'a ina jiran ya bani ne maganin yana wurinshi!" Sai wani abu ya fado min ko shine dalilin zuwanta jiya, kitchen na dawo na ga kayan tea ne kawai na hada mana sannan na wuce na kai dakin lokacin ya fito tana share mishi ruwan kanshi, sai murmushi yake mata wanda kana gani kaga na dole ne. "Aunty Baby!" "Na'am!" "Sannu da kokari!" Fita nayi na basu wuri na bi ta daya kofar na koma bangarena, a can na gyara gidan na shiga kitchen, number na duba a wayar Tafida na kira shi muka yi waya babu kayan abinci. "A'a akwai a wurinsu Maryam." "Ka kawo min nawa kawai don ba zan amsa a wurinsu ba!" Domin idan na kai kaina wurinsu nice na zo fitina. Haka na gaya mishi na kwanta jiranshi domin nayi wanka. Wurin karfe sha daya ya kawo abincin dake an saka addu'ar sai karfe hudu na yamma, a gidanmu kuwa abincin sadaka har da masa da panke Mama tayi, a gidansu ma Hajiya Salamatu sun yi abincin sadaka tunda a gidan Tafida za ayi addu'ar, haka na daura abincin nima don ya ce ayi abincin. Kafin karfe uku n gama na kai mishi na shi, na samu Deen yana parlourn har a shi, Asiyah tana kwance a saman kujera rike da kanta. "Daadi jikin ya motsa mata ne?" "Eh dazun tayi ta zubar da jini!" "Sannu Asie!" Murmushi tayi sai lokacin na ga hancinta yayi ja alamar jini ya bushe idanunta sun wani haske sosai, "sannu ya jikin naki?" Tashi zaune tayi tana tallafe fuskarta. "Da sauki kin ga na tashi ai." Mika mata wayarta yayi yana faɗin. "Mamanki?" Fuskarta ce ta sauya daga yadda take ta kalle shi. "Dauka!" Dauka tayi tana faɗin. "Hello Mamyn!" "Asiyah kuma sai ki daina daukar kirana ya kike Ashe Maman shi ta rasu gamu muma zamu zo gobe in sha Allah!" "Eh tow Allah ya kawo ku!" "Amin Ya Allah!" Sannan ta kashe wayar ta mika mishi. "Zata zo gobe!" "Hmm!" Ni sai ma shiga duhu daga Tafida har Asiyah kamar suna boye wani abu, bayan na ajiye abincin Tafida ya ce min. "Zamu tafi wurin addu'a a gidan Abba idan zaku tow maza ku shirya!" "Tow!" Nace mishi, na shiga na shirya su Uwani suka kwashi kayan abincin muka tafi da shi, tunda muka fita take jingine da kanta. "Bakya jin dadi ko?" "Eh Aunty Baby!" "Waye ya gaya miki sunan nan ne?" "Ya Aliyu yace shi kuma yana kiranki yar ka..." "Asie surutu ko?" Dariya tai tana faɗin. "Kana son kada na fada ne!" Haka muka isa gidan, gidan ya cika sosai kamar me, muna shiga aka shiga gaishe gaishe. Idanun Sa'adiyya yana kanmu. Ta lalace kamar ba ita ba, dauke kai nayi muka wuce dakin Abba. Bayan mun gaisa ya ce mana. "Ku tafi dakin Maman Sharif!" "Tow!" Muka ce sannan muka fita, dakin Hajiya Kaltuma na nufa tana ganina ta mike har jikinta yana . "Ummu!" "Na'am Hajiya!" Na gaishe ta da ta'aziya na mata, bayan mun zauna na wuce dakin Hajiya Salamatu, anan muka zauna har aka gama addu'a aka fara watsewa, sannan na wuce dakin Inna Hajja Ganaah tana ganina ta fara gaishe ni. Sai da suka sake samu kuka. Bamu bar gidan ba sai dare, a yadda na fahimci Asiyah bata da lafiya sosai, boyewa take lokacin da muka iso gidan, na bude motar zan fita ta ce min. "Yau Hajiya kwananta uku ko?" Juyawa nayi na kalleta zuciyata tana wani irin