Showing 24001 words to 27000 words out of 241571 words

Chapter 9 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14753

Mahaifiyarta tace min ta amince sai dai ko a tsakaninsu, Alhaji Muhammad Jadda bani na haifi Ummu ba amma wallahi a gaban Allah zan yi shaidar ta tun tana yarinyar bata musu da babba matukar kace mata yi nan zata bi nan, duk cikin Yaran gidan nan babu me hakurinta. Amma idan kuna ganin haka akwai matsala Allah ya zab'awa kowa abin da yafi alkhairi, domin kada muzo ana kace nace, sannan da Yarana da na haifa ne suka fada mishi haka na rantse da azumin bakina zan ce maka zasu aikata amma Ummu nayi mata shaidar da ko a bakin mutuwa nake xan bada labarinta." Baba wani irin mutum ne haka? Baba ya yarda dani sama da yarda da yayiwa Yaranshi. "A'a Alhaji Bulama ni naga fitila a gidanka, kuma ba zan tab'a barin shi ba sai ya haska min gidan Tafida, Yarinyar tashi ku tafi ku gaisa!" Ya fada yana kallona cikin kauna da soyayya. Haka na fita na nufi zaure. Ya fito cikin isa da kasaita. Kallona yayi ya ga na had'a kaina da bango. Yana tsaye kafin ya ce min. "Kika sake kika aure ne hmmm, da kafarki zaki gudu!" Kaina yana kasa nace mishi. "Ni Y'ace mai tarbiyya!" "Yar Mace ba? Yar tuwo-tuwo ba jahila irinki ake kira da fitila. Ita Babarki.." a lokacin na d'ago kai na kalle shi kamar xan yi kuka nace mishi. "Ina ganin darajar iyaye ko ba nawa ba, sannan kada ka sake ka zagar min mahaifiya, domin nasan darajarta tunda har uban riko na yayi min shaidar da ko a gaban Allah zai iya vada shaida Kaina haka ma yabwadata, kada haukarka ya ja ka zagar min mahaifiya domin na san darajarsu. Daga kalamanka na fahimci rufa maka asiri aka yi domin shigowarka gidan nan baka isa ba, baka da ikon shigowa wannan gidan gidan dattawan arziki ne da suka san tarbiyyar kansu da na yaransu. Bance ka zauna da ni dole ba amma kada ka zagar min iyaye domin suna da daraja sosai." "Me kike nufi?" "Ban nufin kome sai dai na gaya maka ko wuta suka ce na shiga xan amsa musu da harshen tarbiyya nace musu na amince kuma xan bi yadda suka ce. Domin na kara musu godiyar abin da suka yi min na zuwata duniya, ba kowa yake fahimtar haka ba sai daliban islamiyya wadanda suka samu tarbiyya suka koshi." "Ke!" Ya buga min tsawa, da sai da cikina ya kad'a. "Ni ne bansan darajar iyaye ba?" Ya fada tare da dukan bangon inda nake tsaye? Baya na ja tare da rintsa idanuna. "Na amince da aurenki, amma ina baki shawara ki sayo likkafaninki ki zo min gidan dashi yadda ko kin mutu ba sai an sha wuyar saya a wani wurin ba." Ni dai ban ce mishi kome ba, domin na lura kalamai na sun yi zafi muna tsaye muka jiyo muryan iyaye mazan, sake fuska yayi yana faɗin. "Gobe za a kawo miki kayan azumi da kayan sallah. Na gode sosai da amincewarki!" Ni dai ban ce kome ba domin na lura mugun dan wasan kwaikwayo ne. Haka suka tafi gida suka bar ni da ciwon kai. Har aka sha ruwa ban dawo nutsuwata ba, washi gari kuwa sai ga sako da kaya niki-niki kamar hauka,aka ce min yana waje sanye yake da blue jeans sai rigarshi red shirt, me guntun hannu, sai yanxu na ga dalilin da yasa yake hauka ashe Allah yayi halitta, sai na rena kaina na fita har inda yake na tsaya tare da sallama. Bai amsa ba ya ce min. "Nasan baki saba shan abin da na kawo ba kada a sayar domin ayi wani uzuri da shi, don Yasan getto area sun iya rayuwar reni. Akwai manyan atamfofi da lace maybe tunda kike baki tab'a sakawa ba,na so na saya gwal amma akace ku Yaran talakawa ai baku wani san darajar gwal ba!" Murmushi nayi na zaro yatsun hannuna, ina gyara zaman zoban hannuna guda biyu na gwal ne. "Wannan ka gayawa wanda ya gaya maka, ni Ummu zanin da nake shiga aikin tuwo-tuwo da shi super wax ce. Tun kafin a haifi uwar me sabulu balbela take da farinta, kayanka ka tsaya a baka su kai ne ma xan tausayawa da alamu arzikin da kake da shi na hucin gadi ne, jikan dan karuna!" Kasa magana yayi musamman yadda na rama cin mutuncin da yayi min, a fusace ya shiga motar shi ya bar unguwarmu. Kayan da ya kawo ko daya ban tab'a ba, kuma ban bari an tab'a ba, bai kuma zuwa ba.


*Aliyu Tafida Jadda*
Ya taso cikin wani irin rayuwa ne, mara dadi ko nace mara sukuni. Sakamakon irin gidansu. Shine ya na biyar a cikin gidansu. Hajiya Aisha itace mahaifiyarsu wacce suke kira Hajiya, yan uwa ne da Alhaji Muhammad Jadda, aka yi auren zumunta. Duk da suna son juna sosai haka bai hana Alhaji Muhammad karo mata kishiya ba, A haka suke zauna lafiya da Hajiya Baraka wacce ta boye halinta saboda Alhaji Muhammad Jadda bai dauki renin hankalin ba gidanshi akwai zaman lafiya. Alhaji yana da kanne biyu, Alhaji Nura sai Alhaji Saleh. Suna zaune a gida ɗaya bakiɗaya. Tun basu yi aure ba suke tare wa da Hajiya take daukar nauyinsu. Ma'ana cin da wasu abubuwan gidan, Alhaji Nura yayi aure inda ya auri wata Shuwa. Shi kuma Alhaji Saleh ya auri bafulata daga Yobe mai suna Zainab, sai dai haduwar gidan ya janyo wani gagarumin tashin hankali, domin bakidaya suka hadewa Hajiya kai, fadar yau daban na gobe daban ba kowa ya hadassa haka ba, sai zuwan Shuwa. Tana bin malamai sosai amma tafi ƙarfi wurin munafunci da makirci, da ita shi take hada Hajiya rigima da matan gidan. Wani tashin hankali da ya faru kuwa ba wani abu ba ne ya haifar da haka sai lokacin da Barakatu ta haife danta Khamil, wanda hajiya ce tsaye akan kome, Yaron bai amsa suna ba ya koma anan aka ce Hajiya ta kashe Yaron, duk da a lokacin Yaranta biyar, Abubakar, Umar, Rukayya, Maryam sai goyon Aliyu da bai wuce wata tara ba. Jin wannan lamarin iyayen Barakatu suka ce basu yarda ba, haka suka yi ta rigima har za a kai kotu, Alhaji kamar wanda ake ingiza shi ya sake Hajiya, ita kuma jin haushin haka ta ajiye mishi Aliyu, anyi juyin duniya nan ta amshi Yaron tace ba zata amsa ba, kada yaron ya mutu ace shima kashe shi tayi, haka Hajiya ta tsallaka Yaron da bai da laifi ta bar shi, a lokacin Abubakar ya bar makaranta yana kula da Aliyu, wanda Barakatu ta sako Yaron a gaba, saboda tsnar da tayi mishi. Wata rana Shuwa tayi bakuwa ta ga Aliyu ya mata kyau amma kuma cikin wahala gashi karami sosai. Kallon Shuwa tayi tana faɗin. "Ke Shuwa wannan yaron fa zaki more shi dauke shi ko gyara shi babu wanda zai fi ki moranshi!" "Ke ban haifa ba, ba zanyi wahalar dan wata ba!" Dariya matar tayi tana faɗin. "Kin manta sunana ne Rabi me idanun mikiya! Wallahi Yaron nan akwai kashin arziki a jikinshi na rantse kuma ki saka a bincika miki." Da wannan Shuwa ta fara kula Aliyu wanda Alhaji Nura yake gayawa Yayanshi abin da Shuwa take yi, Alhaji yaji dadi kamar me. Haka yayi ta mata hidima a lokacin kuma kishin Barakatu ya dawo kan Shuwa. Duk da tana rike da Tafida amma babu zancen tarbiyya domin dai tarbiyya yayi gabar Aliyu yayi yamma, sannan ta cusa mishi kiyayar iyayenshi daga Alhaji har Hajiya wacce ta auri wani dan kasuwa a Chadi. Haka Aliyu ya taso da tsanar Hajiya domin yana ma jin maganar Alhaji wani lokacin. A hankali ya fara bin Yaran unguwa yana yan sace-sace, nan ma sai da Alhaji yayi da gaske, sannan ya bar wannan halin. Bayan an gama haka ne ya fara bin yan bangan siyasa ko secondry school bai gama ba, tan Alhaji ya b'aci a lokacin ya dauke shi zuwa sudan wurin wani abokinsa. Anan ya samu nutsuwa sai dai Aliyu Tafida ya taso bai da kunya bai san girman kowa ba, abin da ya sani ka tab'a shi zai tab'a ka. A duniya bai da abokai sama da Deen da Mahmoud, domin kuwa sune suka taso tun Yarantarsu, Deen iyayenshi talakawa ne, sab'anin Mahmoud da iyayenshi suke da kudi sosai, sai dai a duniya babu abokin sirrin Tafida kamar Deen domin me zasu yi babu me jin abin da ya faru a bakin Deen sab'anin Mahmoud da bakinshi kamar reza. Dukkansu Deen ya fisu tarbiyya sosai domin yana bala'in tsoron iyayenshi, shi yasa da suka ga zai lalace irin na Yaran masu kuɗi Babban ya tura shi bodin school, kamar yadda aka tura tafida Sudan, sai Mahmoud ne yake gararanba a unguwarsu, haka yasa ya lalace amma idan baka sani ba sai ka zata bai aikata kome tun yana secondry school yake bin mata, da suka gama Tafida yazo hutu Deen ya zo shima anan suka kara haduwa, yayi kokarin bayyana musu sabbin abokan da yayi, kai tsaye Aliyu Tafida ya ce mishi. "Waɗannan yan iskan zan tsaya ina abota dasu, kaga ina da ra'ayi ni ba zan iya mu'amala da su ba, ka fahimta." Shima Deen yana tare da Tafida, amma Mahmoud gani yake Deen yake zuga Tafida. A lokacin gwamnatin jahar Borno ta bawa Yara masu kokari scholarship a cikinsu har da Deen. Kuma ikon Allah an tura su Sudan. Ba karamin dad'i Tafida ya ji ba, a rayuwar Tafida Deen yayi yaki sama da yadda ba a zato, domin kuwa ya saka shi akan hanya, daga wasa da ibada rashin mutunci duk sai da Deen ya raba shi da su, Deen bai kara wasa da damarshi ba sai da ya ga Aliyu yana kiran mahaifinsa sau uku, duk da Alhaji Muhammad Jadda yayi wasa da damarshi na tsayawa a matsayin Uba, Amma Deen ya nunawa Aliyu illar rashin tarbiyyar da yake nunawa mahaifinsa. Wani bin har fada suke yi. Wani abin da yake karawa Deen kaunar Aliyu bai taɓa mishi gori ba, a'a gani yake kome na Allah . Sai dai inda Deen ya kasa nasara akan Aliyu shine mahaifiyarshi, a duk lokacin da ya fara mishi zancenta tow sai sun yi kwana uku basa magana sannan Aliyu yayi ta zazzaɓi kenan. Haka yasa Deen ya daina mishi zancenta domin baya kaunarta. Asalin kinta yake kamar zai mutu. Haka suka gama karatunsu na degree inda Deen ya karanci kimiyyar kera-kere. Yayinda Aliyu Tafida ya karanci kimiyyar siyasa, domin kuwa haka kawai Allah ya daura mishi burin siyasa yana da shekaru ashirin da daya ya hada degree shi da Deen dinsa,suka dawo a lokacin Mahmoud yake kawo musu zancen Yan mata. Dariya Aliyu yayi ya ce mishi.."kai mace take damu ni nan mace bata gama!" Deen ya ce mishi. "In sha Allah ba xan yi aure ba sai na hada degree na biyu zan duba macen da ta dace da ni!" "Kai Malam sai ka tsufa baka yi aure ba kenan!" Inji Mahmoud kyale shi suka.yi, samari biyun nan komawa jami'ar Maiduguri suka yi inda suka sake fitowa da wasu kwalayen degree na biyu, a lokacin Idanun Aliyu ya fada kan siyasa, saboda yayi wani aiki a majalisar wakilai na Nijeriya, a nan suka hadu da Alhaji Mansur Goza, mutumin nan shaidani ne.


Hajiya Aisha.
Tasan tayi laifi na barin Aliyu, amma matar nan bata tab'a kwanciya ba tare da ta mikawa Allah sunayen Yaranta ba, bata tare dasu amma saboda tashin hankalin ta barsu a baya bata barci sosai, sai ta mike tsaye ita ce sadaka ita ce ta saka ayi musu sauka, a lokacin da taji labarin Tafida yana hannun Shuwa, saura kiris ta kauce Hanya Allah ya taimaka ta dawo kan hanya, matar nan mijinta yana da rufin asiri,domin sai da ya kara biya mata aikin hajji. Ta je tai ta addu'a Allah ta kare mata Yaranta. Hajiya bata tare da su amma tana jin Allah yana kare mata Yaranta. Haka suka shekara ashirin bata saka su a idanun ba. Sai wani rasuwa da aka yi a family tazo ta'aziya. Taga yaranta wanda ta zame musu baki. Tayi kokarin danne zuciyarta, domin bata ga wani abu me muni a tare dasu ba, sai dai Yaran sam bata gabansu. Haka ta dawo tayi ta kuka tana gayawa Allah lamarinta, bayan shekara daya ne sai ga Yaran su hudu suka zo mata, tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa hatta makota sai da suka zo tayata murna. Kishiyarta ma kamar tai yaya don murna domin ta kwashe yaran kishiyar duk ta riƙe, kwanan su biyu anan suke gaya mata an saka bikinsu Maryam da Rukayya zasu koma. Tayi murna sosai bayan tafiyarsu mijinta ya bata kuɗi suka yi sayayyar kayan aure, mota guda aka kai gidan Inna aka ajiye da bikin taso haka tayi gayyar mutane aka sha biki, Alhaji Muhammad Jadda ya kuma tsaya sosai akan Uwar Yaranshi, domin sun so cin mutuncinta.ya ce bai yarda ba ko babu yara kanwarshi ne, bayan gama biki yaje har chadi, yayiwa Mijinta godiya da irin dawainiyya da yayi dasu.


Aliyu ya fada harkan siyasa, duk da Alhaji bai so ba, haka Shuwa tai ta zuga shi ai Alhaji baya son cigaban shi ne da yan dakinsune, da Yawan Baraka ne da tuni ya tsaya musu, haka ya ƙara rura wutar kiyayar iyayenshi a ranshi, daga ƙarshe sai Alhaji ya zuba musu idanun domin yasan ana zuga Aliyu a gefe. Ya fara da wakilin matasa na unguwarsu ya samu damar rike muƙamin kansila da goyan bayan Mansur Goza, ana gama wannan shekarun ya samu Chairman na karamar hukumar borno, a lokacin ya rike kudi kamar hauka. Kwatsam Alhaji Mansur Goza ya kara janyo shi harkan ya saka har ya samu takarar dan majalisar jahar,babu yadda ba ayi yayi aure ba amma fir yaki. Addu'ar Hajiya yana bibiyarshi ta ko ina haka yasa bayan shekara hudu ya samu damar zama ɗan majalisar wakilai, a lokacin yana da shekaru talatin da biyu. Anan lissafin ya fara kwacewa Tafida domin kuwa bai da kunya bai da kalamai abin da ya fito bakinshi yake yabawa kowa. Ga dan iskar renin hankalin. Rigimarsu ta fara ne lokacin da Alhaji Mansur Goza ya fara takura mishi da ya bashi kudi da yayi mishi kaza shi kuwa ya fara gajiya yace ba zai yi ba, ai kuwa dake ya fishi sanin siyasa yasa aka dawo da shi, aka yi ta rigima wanda ta ja har aka kore shi a aiki. Haka bai isa ba sai da Mansur Goza ya fara farautar rayuwar Aliyu Tafida. Domin sau biyu ana rutsa shi har da wani sara aka mishi a gadon bayanshi. Anan ne Alhaji Muhammad Jadda ya kai karar Mansur Goza har Fadar shehun Borno. Lokacin sakataren shugaban kasa yazo gaida Mai martaba, aka case nan Alhaji Muhammad Jadda ya juya turanci aka yi ta bugawa kada ku manta Alhaji Mansur Goza irin jahilan yan siyasan nan ne da basu da wani ilmi kawai ana amfani ne da sunan siyasar. Aikuwa abinka da renon Ingila mai martaba da suka yi gwagwarmaya tare da Alhaji suka tsaya aka yi magana Mansur Goza ya ce ya cire hannun shi akan Aliyu ko ciwo yayi a kama shi, haka yasa Sakataren shugaban kasa ya cewa Alhaji Muhammad Jadda ya ce mishi. "Aliyu yana da matasa iya su kadai zasu iya tsaya mishi amma yanxu domin kara karfaffa mishi gwiwa zan shigar da batun shi ga shugaban kasa!" "Dr Mandara ni bana son harkan ne!" "Shi yasa aka yi ta binka, amma ka ki tunda ka haife siyasa sai hakuri amma yanxu ma zan kira shugaban kasa na gaya mishi dama tun kwanan baya yace yana niman matashin da zai kira musu jama'a."
Duk da Alhaji bai so ba haka yayi musu fatan Alkhairi. Haka Aliyu ya kara tafiya siyasa kuma Allah ya mishi nasibi.


Hajiya shuwa tana da yarta wacce ta boye ta, mai suna Sa'adiyya, yarinyar ana zargin ma bata da Uba, amma haka Hajiya shuwa ta boye ta, domin tasan zata zame mata makami mai linzamin. A lokacin da Aliyu ya fara samun kyakkyawan rayuwa dama a gabanta yake a lokacin ta dawo da yarinyar kuma kowa ya amshi yarinyar saboda yadda Hajiya shuwa ta saka aka tarbiyyar da ita. Tana da hankali a idanun da mu'amala amma shaidaniya ce kamar Uwarta, sannan kashewa yarinyar kudi take kamar bala'i, a lokacin da ta gama tsara Aliyu Tafida ya kai inda ya dace gashi a matsayin da ya dace su more shi sai ga Alhaji Muhammad Jadda ya sako batun ya sama mishi mata, wanda bai mata dad'i ba, da Aliyu ya gaya mata yaga yarinyar bata mishi ba hakuri tai ta bashi tana cewa. "Naso yadda na sha wahalarka, ga kanwarka Sa'adiyya nasan zaku yi farin ciki da had'a ku!" Dama can Sa'adiyya tayi mishi ta ko ina amma ganin abin da Alhaji ya Kunno yasa aka yi ta artabu da yan uwanshi musamman da ya gaya musu irin Ummu....
***
*Ummu Hadiyya*
Ban san meye shirinsu Mama ba, amma kuwa naga har Kano suka yi ta tafi sannan ga Karami da yake ta aiko da kaya wanda ashe Mama tayiwa Ummu Kulsum magana anata sayan kaya a Turkiyya. Aka sallah yazo aka yi bikin sallah aka wuce a lokacin aka fara hidimar bikina wanda ashe an saka tun cikin azumi, ko yan gidan babu wnada ya sani daga Mama sai Hajiya Amina aka yi ta hidima wanda aka saka goshin sallah layya. A lokacin na firgita sosai domin rashin mutuncin Aliyu bai bari ba, biki saura sati biyu aka kawo kayan aure da aka yi min shi a wulakance saboda ganin ai ni yar talakawa ce, sai dai ganin irin kayan karban da aka basu tare da tukwaici yasa Aunty Yaana ta koma ta gayawa Alhaji Muhammad Jadda abin da ya faru, an kawo kayan da kwana hudu aka.sake kawo wanda yafi na farko Baba yayi ta fada ya ce shi ba sayar da ni zai yi ba. Domin an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login