Showing 69001 words to 72000 words out of 241571 words
Chapter 24 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
ki saya mana kifi tarwada me rai a saka a abu a kawo min Allah ya bamu sa'a!" "Tirkashi taya haka zai faru? " dariya yayi ya ce mata. "Kin ce yarki ta zauna a gidan ko? Kuturu yana da kuturta kuma mutane suna kyamarshi, makaho mutane na tausayarshi. Saboda makantashi. Ita yarinyar zata tayi ta kyamar komawa gidan shi, shi kuma zai ta tausayin yarki. Sannan yarinya zata zama kurma bata jin maganar kowa, sannan zata yi shiru da bakinta kamar bebiya yadda kowaye ya mata maganar ta koma dakin mijinta ba zata tab'a sauraronshi ba koda Uwarta ce. Idan har aiki zaki yi fa dole ki nimo kayan nan idan ba haka ba labarin da nake baki yarki tana gab da rasa Mijinta, sannan ki gaya mata ta kiyaye kanta domin ita ce zata lalata mana aiki kuma aikin mu idan muka yi miki kin san abin da yake karya shi? " "A'a ban sani ba Malam!" Murmushi yayi ya fada mata. "Ki gaya mata ta tsaya a inda take matuƙar bata nutsu ba, yarinyar zata dawo ba zato ba tsammani!" A fusace shuwa ta juya ga Yarta tana mata wani irin kallo. "Sannan Malam wacce hanya ke karya aikin?" "Sai kin zo min da kayan aikin!" Ya kashe wayar, hannu ta daura a kai tana jin kamar ta fasa ihu. "Yanzu kika sake aikin nan ya kuma lalacewa kamar wancan na aurenki wallahi sai na miki baki, ba zai yiwu tun da kuruciyata ake gaya min akwai wanda gidan da zan yi mulki da dan gidan yazo nazo ki raba Ni da wannan damar baki isa ba wallahi kika sake wannan aikin ya lalace sai na miki baki." Gyada kai tayi tana jin kamar tayi kuka, wancan aikin da suke maganar ya lalace kuwa an ce tana shiga dakin Ummu tsirara tana zagaye gadonta tow ba makawa Ummu ko ta bar gidan ko tayi hauka. Shine lokacin Ummu ta fara jin kamar idan tana gidan kamar zata yi hauka har tafida ya amso mata rubutu.
Zuwa yanzu shirinsu akan Ummu ba karamin aiki bane domin su a ganinsu, kin dawowar da tayi yana daga cikin aikinsu da suka yi.
**
*UMMU*
Ban farka ba sai dare na farka wanka nayi nayi sallah, sannan na ci abinci naji bakiɗaya kamar an cire min ciwon kan da yake damuna. "Mama sannu!" Na fada mata tana shan kunu. "Yawwa Ummu, ya jikin naki?" Murmushi nayi ina faɗin ."da sauki sosai Mama, babu ciwon kan sai gajiya da rashin kuzari. " "Allah ya ƙara afwa!" Shigowa Doctor Sagir yayi yana faɗin. "Gawa taki rami!" "Sai na gayawa Babagaji!" "Mama ya me jiki?" "Da sauki!" "Da sauki!" "Baki tambayi kishiyar da angon ba!" "Na huta da yen-yen, da wasu muryansu a shake!" Murmushi yayi yana faɗin. "Kai Mama kina jin murya me dad'i!" Dariya tayi, "Sister ya jikin naki?" Ya dauki abin gwanji ya gwada kirjina, sannan ya gwada jinina. "Gobe zaki koma gida, sannan ban da cin gishiri banda amfani da ruwan zafi fa, ki raba kanki da tunani. Addu'a shi ne babban mafita ayi yawaita azkar ban da yawan tunani kin ga Baba yana cikin damuwa yanxu haka ya rasa yadda zai don Allah ki daina saka damuwa a ranki ko don mahaifin ki!" Sunkuyar da kai nayi ban ce kome ba, a sanyayye na d'ago kai ina son tambayarshi. "Shima bai da lafiya ne?" Saka hannu yayi a aljuhun rigarshi. "No zai iya kamuwa da ciwon ne matuƙar kina kwance kin san ke daya ya mallaka idan aka ce mishi ga halin da kike ci shima girma ya hau kanshi kwanciya zai yi ki tuna ko don shi You need to survive.....
*Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CShgPK2Dsi8GIrvd5njOML*
*Ina mata yan yayi shin ko kun san kayan da Ummu take amfani da shi, yana fitowa ne daga shahararren Shagon nan na R&U Exclusive Kitchen and More! Kayan kitchen ne na gani na fada ina iyayen Yan mata ina iyayen Kwailayen ga dama ta same ku, Uwargida da Amarya, Budurwa da bazawara maza ku fito ga kaya nan sayan na gari mai da kudi gida. Kayan mu daban da na shago!*
#Mai_Dambudhttps://chat.whatsapp.com/HYpizDjKAkJB4QClSeLTvw
*R&U BAG's GALLERY! Wai da gaske kun manta ne na gaya muku? Tow R&U ta kara dawo muku da kayan ado da kawwa wanda Ummu First Lady take amfani da su, tow dai Ummu tace na gaya muku a sirrince! Kawo kunnunku 🙉 a wannan R&U BAG's GALLERY babu abinda babu domin kamar kanti kwari ne a gidanki! Muna da kaya irinsu Atamfa, lace, shadda! Karewa dai har da lefe, kayan fadar kishiya, kayan Fitar suna na mai jego, kayan toshi na wanda saurayi zai kaiwa budurwa! Waya miyar sai a mota, muna bada dai-dai har da sari ku shiga domin tabbatarwa idanunku*
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
*Hajiya Aisha!*
Kallonta kawarta tayi ta kuma kalli kishiyar Hajiya Aishan wato Balaraba. "Wallahi Shatu ba zan yi kafarta ba Y'ayanki shiga tsakaninku aka yi, yanzu ya dace ki mori ribar Haihuwa amma ce kin barwa duniya su! Balaraba wannan abin ya dace kuwa?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Gaskiya abu bai yi dadi ba, kuma bata da lafiya sosai amma suka manta da ita!" Murmushi tayi me sanyi ta ce musu. "Basu manta da ni ba, tafiyar da nayi na barsu lokacin da suke buƙatar kulawata yasa suke jin babu dad'i amma nasan suna sane da ni!" Shigowar wasu Yara ne yan mata, Umma Marka ta mika Baban Yaron me suna Hafiz wayar Hajiya kai. "Hafizu kira min Ummu Hadiyya!" Hajiya bata so ba, amma babu yadda ta iya domin bata son su ce tana da taurin kai don sun damu da ita. Ai kuwa kira daya zuwa biyu ya shiga. "Hallo! Ummu Hadiyya ce?" Can cikin sanyin murya ta ce . "Eh Ni ce!" "Fisabiilillahi Ummu Hadiyya, ke da muke saka ran zaki gyara kome shine kika bari aka dawo da Hajiya Shatu? Bata da lafiya sosai tana kwance kome bata yiwa kanta, kada ki manta kema Uwace ban gaya miki haka don na muzanta miki amma ta saka rai akanki zaki gyara tsakaninta da Yaranta, Hadiyya ki yi wani abu domin kin san danta da Yaranta suna da halin taimaka mata don Allah ki yi wani abu kada ta mutu a wannan yanayin don Allah na zuba gwiwata a kasa ina rokon arziki."
"Umma Marka ko?" "Eh Ni ce!" Ta fada da sauri, "ki ce tayi hakuri ta ba ni lokaci zuwa nan da gobe Allah ya taimaka mana y bamu sa'a!" "Amin Ya Allah! Ubangiji ya shiga lamarinki ya sakawa Yaranki tausayinki da jin kanki!" "Amin Ya Allah! Umma Marka ki bata hakuri in sha Allah zata samu lafiya!" "Tow Allah ya miki albarka ya bawa Yaranku ikon miki biyayya!" "Amin!" Kashe wayar Umma Marka tayi tana kallon Hajiya Shatu. "Yanzu ba gashi ba!" "Ai Aliyu ne yana jin na koma zai ta faɗa!" "Tsoron shi kike ji? Gwamna kika haifa fa? Daya maaikacin banki daya dan kasuwa me kike bukata kuma ko a jikinshi ai kin huta!" Gyada kai tayi tana hango rigimar Tafida. "Allah yasa mu dace!" Duk suka ce mata "Amin!"
**
*Ummu Hadiyya*
Kallona Mama tayi tana faɗin, "Kin san dai gobe za a sallame ki, kike bukata saka kanki cikin wani damuwar?" Kallonta nayi kafin na kurbi kunun da yake kofin da dan zafinsa. "Na sani!" "Tow Allah ya kyauta!" "Amin!" Na furta ina kallon Mufid da yake ta wasa shi daya Mufidah tana bayan Mama. "Mama me yasa Yara suke kin iyayensu bayan sun sha wuyarsu?" Girgiza kai tayi tana faɗin. "Daga Iyaye har Yaran akwai soyayya mai zafi da sanyi a tsakaninsu, matukar uwar ta shayar da dan na tsawon wata daya zuwa goma lokacin da ya fara gane dadin nono har abada soyayyar nan ba zata tab'a karewa ba. Sai dai idan shiga tsakani aka yi!" Ajiyar zuciya na sauke ina tuna irin laulayin da nayi sannan nazo nayi ta fama da matsanancin ciwo har na haihu amma ace Tafida da Yan uwanshi sun manta da hakkin Uwarsu. "Wani abu ne?" "A'a!" Na fada ina shan kunu. So nake Mama ta bar dakin amma kamar ta sani taki fita, muna haka sai ga Ummi tazo ita da Mahirah ta dauki Mufid tana faɗin. "My love gaya min gaskiya mintsini nawa Mamanmu tayi maka don na lura tafi son Mufidah akanka!" "Me xanyi da me kukan banja!" "Mamanmu cefenen yau babu nama haka zaki yi miyar kuka lami!" "Yau naga tijara a wurin iyayenta zamani Hajiya Balkisu idan zaku tafi ki tafi da shi na baki shi!" "Alhaji Bulama sai ya rushe kanshi don kada ya ga shi fari ne ya zata zan koma bayanshi nafi son Dan bakin mijina!" "Mahirah kin ji dai danki ban da masauki!" "Wannan hade kai kuka mishi don kunya dan beauty!" Haka suka yi ta hira da tsokanar Mufid una dariya, bayan sun gama suka mana sallama domin Kawu Gwani ya kawo su kuma ya dawo yana jiransu. Na rasa gane kan Gayen nan bakiɗaya yaki ko shigowa gaida ni. tare suka fita da Mama ta raka su na dauki wayata ina kallon waye xan kira! Deen wata zuciya ta gaya min sai naga kuma bai dace ba sai na kira Baban Ilham wato Umar. Bayan mun gaisa sama-sama nace mishi. Kawai sai na rasa me xan gaya mishi sai nace mishi. "Ina son magana da Maman Ilham ne!" "Ok tana zuwa zata kiraki!" Kashe wayar nayi ina cewa na gode. *Abba* abin da wani bangare na zuciyata ya sanar min kenan, kiranshi nayi a hankali na fara magana da shi cikin nutsuwa, ina kuma tuna mishi girman hakkin Uwa da aka tauyewa Hajiya idan ta musu a wannan yanayin yana da hali bai taimaka mata ba, Allah sai ya musu hisabi. Na gyara zamana da kyau. "Abba idan wannan shine horon da zaka yiwa Hajiya tabbas a tsawon shekaru sama da talatin ta horu, kai ko a kotu ce iya hukuncin da Alkali zai mata tsawon shekaru goma ne zuwa sha biyar amma Abba ita tsawon shekaru sama da talatin tana amsar hukuncin laifin da bata aikata ba, sannan Abba taya uwa me kaunar yaranta zata manta da su, Hajiya bata taɓa mantawa da Yaranta ba, ba iyawarka yasa yaran suke cikin amincin Allah ba, tana can gefe tana tayaka rikonsu nasan na wucd makadi da rawa amma a duba lamarin a tura a daukota kai dan uwanta ne ko babu aure gidanka gidanta ne, ko bata zauna a gidanka ba a nima mata inda zata zauna kayi hakuri da abin da na fada, amma nayi mata gobe zata ji yadda muka yi." Sannan nayi mishi sallama ina jin kamar na sauke nauyin da yaƙe kaina. Tunda na fara wayar kaina yake sunkuye ban san Mama ta shigo ba sai da na d'ago kai na kalleta. "Me yasa ba zaki koma dakinki ba, idan kin san kina gefe guda kuma zaki saka ayi?" Murmushi nayi ina faɗin. "Ba zaki gane ba, komawana dakina bai da nasaba da haka Mama ki min fatan Alkhairi Ubangiji yasa haka shine mafi alkhairi!" Bata ce kome ba, ta wuce ya kwantar da Mufidah. Muna jira jefi jefi, nasan a ranta bata jin dadin yadda na kafe, amma saboda laluran da nake fama da shi yasa ta kyale ni.
---
*Abba*
Tunda suka gama waya da Ummu ya ji kamar kanshi zai fashe, shima yana da kaso me girma na raba A'isha da Yaranta. Zazzafar huci ya fesar, ya dauki wayarshi ya kira Umar cikin abin da bai wuce minti talatin ba ya hada kan Yaranshi. "Abba lafiya ka tara mu?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce musu. "Mahaifiyarku ba lafiya!" "Abba ba Tafida ya Kaita asibiti ba?" Inji Rukayya. "Ke uwa ce kina da Yara maza da mata, idan suka miki abin da kuka yiwa Mahaifiyarku zaki ji dadi?" Hadiye yawu tayi. "Amma Abba ita ta tafi ta bar mu fa!" Inji Maryam. "Karuwa ce ita?" Da sauri suka d'ago kai suna kallonshi. A tare suka girgiza kai, "tow ita wacce? Bayan ta bar ku?" "Matar wani ce! Kuma ba zai yiwu ta tafi da mu ba." Inji Abubakar, "me yasa kika watsa da ita? Baku tunanin wata rana Yaranku zasu watsarku? Kusan nauyin da yake kanku na ta? Tafida ka ji tsoron Allah, kana son mulkinka ya tafi maka yadda kake bukata? Ka juya ga mahaifiyarka, idan kana son kayi yadda kake so ka koma gare ta. Manyan masu laifi na duniya Allah ya amshi addu'ar iyayensu bai hukuta su ba, sai bayan ran iyayensu kada ka rasa wannan damar dukkanku kuna da damar kyautatta mata idan ta rasu a wannan lokacin ko bana muku fatan amma kuma wallahi Allah sai ya girgiza duniyarku!" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da cewa. "Umarni na baku!" "In sha Allah!" Suka fada bakiɗaya suna masu kallon juna, "Umar gidan da yake kusa da naka a gyara shi, Tafida ka tura motar asibiti a daukota gobe nan, Abubakar Yaya Babba kai nake son ka tsaya kome a kawo min na asibitin na gani." "In sha Allah!" "Maryam ki amshi kudi a hannun Tafida ki sayi kayan abinci ki kawo min na gani a kai mata. Rukayya zan baki kudi a saka mata kome a cikin gidanta!" "In sha Allah!" Ya sake kallon Rukayya. "Na sanki da son rai, na sanki da son kai, zan baki kudin iya abin da zaki sayo idan aka samu matsala xan bala'in baki mamaki, ina sane da satar da kika yi abuja, ina sane da sharrin da kika kullawa Ummu, ina sane da kome. Wallahi kika sake wani abu ya faru da abin da na baki ki saya sai na saka an rufe min ke tunda kin zama bera!" Tsoro ne ya kamata domin Abba baya fadar magana bai cika ba, "in sha Allah zan kula!" Ta fada muryanta yana rawa. "Ku je!" Duk suka mike banda Tafida da yake zaune yayi kicin-kicin da fuska. "Uban masu gida muje!" "Babu inda zanje Abba ka shiga maganata da Ummu!" Murmushi irin na manya Abba yayi ya ce mishi. "Ina ruwa na? Kaga Tafida ka tafi wurin hidimarka!" "Abba kayi wani abu wallahi na gaji da abin da ake min ka saka baki a dawo min da mata." "Idan naki fa Mr Governor!" Ranshi ya kara b'aci, "wallahi ba zan tab'a sake ta ba sai dai ta zauna da aurena." "Akwai kotun Muslunci ai!" Mikewa yayi fuuuu ya bar parlour. Yana fita Abba ya saka dariya kamar ba yau da safe yake cewa idan ya dawo Umara zai sake ta ba yanzu ya dawo ya ce ya fasa sakin. "Ja'iri!" Kiran Deen Abba yayi ya ce bayan Isha yana nimanshi. Haka kuwa ya faru bayan Isha sai ga Deen ya zo.
Bayan sun gaisa Abba ya mika mishi fura da nono, amsa yayi yana sha yana zuba santi. "Deen na kiraka ne akan Abokinka!" Gyara zama Deen yayi yana ajiye furan. "Sha kada ka damu" cigaba da sha yayi. A hankali Abba ya warware mishi yadda suka yi da Ummu akan Hajiya. Abba bai kai karshe ba Deen ya ce mishi. "Yarinyar nan yar aljanna ce kuma a aljannan First Class take!" Murmushi Abba yayi yana faɗin. "Na yarda da abin da ka fada, Ummu yar Aljanna ce. Yanzu abin da nake son naji daga gare ka shin kana ganin na shiga maganar Ummu da Tafida?" Gyara zama Deen yayi sannan ya ce mishi. "Abba zan yi farin ciki idan Ummu ta dawo gidan Tafida, amma kafin yau ka fara bincikan me yasa Ummu ta dage bazata koma gare shi ba, idan kayi haka ka mata adalci. Tafida yana buƙatar space sosai ya gane su waye a tare da shi lokacin da bai da kome ya kuma fahimci me ake kira zafi da dadin dandano rasa abin da kake da shi. Tafida ya ga lallai yana ji yana gani zai rasa abinda yake ganin na shi ne, Abba idan da Ummu Kanwata ce da muke uwa daya Uba daya. Wallahi Billahi azim, sai na saka Tafida ya rasa yadda zai yi domin sai na toshe duk wani hanyar da zai ganta ko ya mata magana, na fadi haka ne a matsayina na abokin shi amininsa, sannan ban yi haka da wata manufa ba, na san kai Uba ne kuma zaka.ji babu dadi a kalmai na amma adalci kake magana akai. Ka bar Tafida ya nime Ummu a karo na biyu. Idan ya fadi kuskuren shi ne, ya kada shi idan yayi nasara halayyarshi ce ya sauya. Yanzu nauyi uku ne akan shi na farko Al'ummar Borno na biyu Mahaifiyarsa, na uku Ummu Hadiyya ka barshi yayi ta fama kamar yadda ya iya fita yakin niman zaben gwamna haka zai fito yakin niman dawowar Ummu ni da kai mu koma gefe mu taya shi da addu'a, Tafida ba yaro ba ne da kullum sai an rike hannunshi a da can Yaro ne da bawa Ummu a yanzu kuwa tunda ya iya ajiye wata macen tow ba makawa yasan abin da yake mishi ciwo, don haka ka kyale shi ka zuba mishi idanu kamar yadda kace kana jin kunyar Yarinyar ka kyale shi kada ya zubar maka da sauran kunyar a duniya idan akwai yarinyar da ta cancanci kira da mace ta gari Ummu ce domin ta shanye duk wani abin Tafida. Kuma bata tab'a kai karar shi gida da wurinka ba, Abba ana barin halas don kunya, ka barta indai har tana gidan iyayenta ta iya tuna maka hakkin Hajiya tow Wallahi bata bukatar a takurata, sannan ciwonta yana kokarin tab'a mata zuciya ne, bata tab'a gayawa wani matsalarta ba, kada a takurata ta ga kamar don ta hada zuri'a da Tafida yasa ake mata haka, don Allah." Murmushi Abba yayi yana kallon Deen ya ce mishi. "Ina niman alfarma daya Deen!" Murmushi Deen