Showing 27001 words to 30000 words out of 241571 words

Chapter 10 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14691

saka bikin da gaggawa.


Alhaji Muhammad Jadda yayi ta bashi hakuri, tare da niman alfarmar kada a kawo ni da kome, anan ne na ga amfanin Mama tace ai ba ta san da haka ba, kayan fa an riga da ayin min.....
N500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


10


Shi dai Alhaji Muhammad Jadda bai so haka, domin shi gani yake auren da aka basu baka karamin alfarma aka yi musu ba, bikin na kara matsowa abubuwa suna kara fito domin kuwa shi dai wanda ake kira da ango tunda ya koma Abuja ba kara jin motsinsa ba, wata juma'a ina lissafin kudin abinci aka, ban d'ago kai ba don naji muryan Yara ne. "Aunty Baby kina da bako a waje!" "Tow gani nan zuwa!" Don a tunanina shi ne ya zo. Shiri nayi domin yau ba zan yarda ya gaya min magana na kyale shi. Haka na mike na daura mayafi kan gown din jikina. Na fito daga cikin gidan, abin mamaki ba shi ne wani ne da ban gane shi ba. Na isa har inda yake cikin mutumtawa na gaida shi. "Barka dai!" "Yawwa Hajiya Ummu Hadiyya!" Shiru nayi kafin na ce mishi. "Ban gane ka ba." "Eh gaskiya ba zaki gane ni ba, da farko sunana Mahmoud abokin Tafida wanda zaki aure a yan kwanaki da suka rage. " "Ai na fahimta! Da Fatah lafiya ko!" "Eh tow lafiyar kenan shi yasa nazo na taimaka miki kada ki dauka nima azzalumi ne!" Sai yanzu abin ya fado min dashi ranar suka yi ta min dariya. Murmushi nayi kafin na ce mishi. "Ina jinka!" "Dama ina son na gaya miki ne, ki dakatar da iyayenki akan aurenki da Tafida domin ba mutumin kirki ba ne." Shiru nayi fuskata dauke da murmushin takaici na ce mishi. "Tow yanzu me kake so nayi?" "Yawwa Ummu ni ina son ki fasa aurenshi ne, sannan zan yiwa Iyayena magana su zo don na ga ke yar mutunci ce, kin san darajar iyayenki!" Cike da mamaki nake kallonshi abokinsa ne kut da kut yazo yake sararshi wani irin abota ce haka? "To na gode sosai da shawararka, amma ina son ka sani iyayena ba kananun mutane ba ne, idan suka ji labarin nan zasu iya min fada ni kuma duk abin da za ayi min fada bana fatan ya faru, na gode sosai maganar zaka turo manyanka bari na tuna maka haramun ne nima a cikin nima, hadisi ne ingantaccen daga Bukhari da Muslim, na Barka lafiya." Na juya zuwa cikin gida, "Aliyu ne?" "A'a" kallona Mama tayi tana son magana amma sai ta share tana me cigaba da aikinta.
Tun bikin saura kwanaki biyar nayiwa duk kwastamomina sallama tare da gaya musu aure zan yi ga Kanwata Uwani zata cigaba daga inda na tsaya, sun yi fatan alkhairi, wasu ma washi gari sai ga shi ana ta turo min gudummawarsu, ban san yan gidanmu sun fitar da anko ba. Sai daren da aka kawo min kayan da zan saka na zuwa dinner ne oho can suka sani. Abin mamaki wannan gayen da wanda yayi musu magana ranar zuwansu na farko suka zo ya kawo min kayan. Dake ni da Uwani muka fita, ita ta amshi kayan. "Hajiya Ummu ni sunana Deen shi kuma wannan.." "Mahmoud ko?" Na tambaye shi, a dan razane shi Mahmoud din ya kalle ni. "Ya aka yi kika san sunanshi." Murmushi nayi nace mishi. "farkon zuwanku!" Gyada kai yayi ya ce min. "haka ne kiyi hakuri wakili zai zo amma sai ana jibi biki!" "Ba kome na gode! Sai an jimarku!" Na juya na koma gida domin tunda aka saka bikin na rage saka manyan hijab wanda yake nuna kankantatta.
"Deen gayen nan ya samu mace, asalin yar dakar idan kana jin mace yar dakar yarinyar nan ce. Idan ya sake ya rabu da ita ni zan shiga na fita na aureta domin irinsu Ummu Hadiyya ba matan su Tafida ba ne." Sake baki Deen yai yana kallon Mahmoud. "Kana nufin zaka iya cin amanarshi kenan!" "Idan ya bani kofar haka zanci domin shima yaci Amanar iyayenshi wurin amsar zabinsu!" Naushi Deen ya kai mishi me karfin da sai da ya fasa mishi baki. Dariya yayi yana faɗin. "Ko zaka kashe ni wallahi ba zan barwa Aliyu Ummu ba domin matsiyaci ne da bai san darajar Iyaye ba, idan ka isa ka dakatar da ni." "In sha Allah, matukar ina Numfashi ba zan tab'a barin Aliyu ya rabu da Ummu ba matuƙar ina raye sai na kare martabar Aurensu ko haka zai zama karshen rayuwata." Dariya Mahmoud ya cigaba da yi yana faɗin. "Muje bingo! Amma ka sani matukar kudi na aiki sai na raba su dama daya tak nake nima na bawa kowa mamaki! Tafida Tafida kowa tafida kowa Tafida kowa tafida kowa, Nasara Tafida iyaye na gari Tafida wife material Tafida, Aboki irinka tafida , degree da Masters Tafida. Ni ne koma baya babu wanda yake fadar Mahmoud." "A'a Mahmoud muna sonka kada ka lalata mana abotarmu ta yaranta don Allah kada ka zama me son kai!" "Wani irin kuna sona? Kai ka raba Ni da yardan tafida baya shawara da ni bata gaya min kome akanshi, sai dai na ji kuna tattaunawa a sirri. Haka shine abota? Haka shine aminta? Dama an fada abota ta mutane uku tow akwai munafiki a cikinsu kuma ba kowa ba ne sai kai!" Ya share gefen bakinshi da ya fashe yana faɗin. "Na jima da sanin kome kuka saka a gaba sai kunyi nasara, kai kana aiki a state University Maiduguri, shi yana tare da shugaban kasa, ni kuma Uwar me kuka mai dani?" Ya fada da karfi Deen sai yaji kamar da gaske sun yiwa Mahmoud kuskure. "Mahmoud babu wanda yaki ka, Mahmoud ka san ba karfi iyayena suke da shi ba, wannan matakin da nake Allah da gwamnatin jahar Borno suka kawo ni wurin, wallahi ban tab'a maka kallon wanda ya gaza ba, Please na haɗaka da Allah kada ka shiga wannan zabin da Abba yayi mishi wallahi Tafida yana buƙatar mace ta gari, kai kanka kasan gidansu ba barin shi suka yi haka kawai ba don Allah mu taya Hajiya karkato da hankalinshi" yadda Deen yake magiya ya ce mishi. "Ya wuce na hakura! Na bar zancen." Ajiyar zuciya Deen ya sauke, sannan Mahmoud yasan ko mutuwa yayi Deen ba zai tab'a fitar da maganar nan ba domin mutum ne mai mugun sirri da zurfin ciki.
Duk wani abun da ake na al'adar kanuri babu wanda ba ayi mana ba, Baba ya tafi har wurin Mahaifina ya gaya mishi kome da kuma Maganar auren da cewa za a kawo daurin auren wurinshi. Cikin girmama lamarin juna, sannan ya dauko kudi kusan miliyan daya ya bawa Baba Bulama ya ce mishi. "tun daga ranar da aka haifeta nake ajiyar shi nasan mace ce kuma Yar hidima ce wannan ku kara da shi, sannan akwai kayan gara. Domin nasan kabilar da tayi aure cikinsu mutane ne masu matukar girmama lamarin Gara!" Duk da Baba Bulama so hana shi, amma yaki. "Ita ce daya tal min a duniya don ma Hadiza ta hanani ita, na gode sosai da irin dawainiyya da kayi min wallahi ka biya ni, amma don Allah ka turo min mijin na zaga da shi wurin yan uwnaa!" A take Baba ya kira Alhaji ya gaya mishi har ya haɗa su da Baban suka yi magana, Alhaji ya jaddada mishi gobe tafida zai zo kuwa. Sannan Baba Bulama ya ce mishi. "Zasu zo tare da Ummun In sha Allah!" Koda Baba ya dawo haka ya sami Mama da maganar, bata ki ba ta gaya min, na dauki kayana kala biyu domin Baba ya ce na kwana a can ranar daurin Aure za a wuce da ni gidana. Mama kan bata so haka ba amma yadda Baba Bulama ya fada bata kauce zancenshi, haka ni da Uwani muka shirya domin ban yi a raina Aliyu zai zo ba. Haka na kwana ina juya zancen, da safe wurin karfe takwas sai ga sallamarsu har cikin gida suka shiga suka gaida Baba dasu Ummi da Umma, yan matan da suka.fara zuwa hidimar bikin da yan uwan Mama sai aka fara surutu dama wannan Ummu zata aura. Lokacin da ya iso part dinmu ya samu Mama tana ta lissafin kayan abin da za a sayo a kasuwa. Cikin sakin fuska Deen yake gaida kowa yana me godiya da fatan Alkhairi. Shi kan ina hango shi ta window yadda yake yiwa Mama wani irin kallo irin na renin hankali. "Aliyu kake ko? " ta nuna Deen girgixa kai yayi yana murmushi yana nuna tafida da ya sunkuyar da kai kamar mutumin kirki, "Allah ya shiga lamarinku bakiɗaya ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba! Ku tafi kada rana tayi muku!" Ta fada tana me kallon Uwani da ta fito dauke da jakarmu. "Uwani maza ta fito ku tafi!" Ina jinsu, sai da Uwani ta kara kirana na fito ina me zama a kusa da ita. "Mama!" "Meye kuma Ummu? Bana sallame ki ba!" A hankali na gyada kai zan yi magana kuka ya kwace min. "Mama idan nayi miki wani laifi don Allah ki yafe min, ki saka min albarka kamar yadda Mahaifiyar Nana Mariam ta saka mata don Allah ki albarkaci rayuwata da yawun bakinki, Mama don Allah ki yafe ." Cikin dauriya ta ce min. "In sha Allah ko kare kika rike Ummu sai ya miki biyayya sai ya soki domin Allah yana son masu biyayya ni kuma me zance bayan wanda kika min, Ummu idan har yawun bakina zai zama albarka da alkhairi in sha Allah babu abin da zaki tab'a Allah bai albarka ce shi ba, Ummu Hadiyya in sha Allah ba zaki tab'a baya ba sai gaba, kiyiwa aurenki biyayya ki kuma rike shi Ibada Allah zai cike miki duk wani gurbin da zaki rasa Ummu Hadiyya in sha Allah ba zaki tab'a danasanin auren nan ba, ko zaki yi na lokaci ƙalilan ne. Aliyu ga amanar Ummu Hadiyya, sannan zan gaya maka gaskiya idan ka sake wani abu ya rabaka da ita ba zan mata dole ba zan tsaya mata gabanta da bayanta, kai kanka da danginka xaku yi alfahari da samunta a matsayin Mata da suruka. Sannan ban da duka" d'ago kai yayi da sauri yana kallon Mama. "Eh ban da duka na fada maka, ka dake ta wallahi sai na rama mata." Sai kuma ta sake yar dariya kafin ta shafa kaina tana faɗin. "Gudaliyya ba zata yi abin da za a dake ta ba sai dai a rashin sani. Ku je Allah ya muku albarka!" Ina kuka haka muka bar gidan cike da soyayyar mahaifiyata itama ina barin gidan sai share kwalla take, tunda muka dauki hanya Deen yake tsokanata. "Yau naga shagwab'e Hajiya Ummu ba naji kina da kanne ba, Yan mata ina kune kannenta?" Tab'e baki Uwani tayi tana faɗin. "Idan shagwab'e Aunty Baby ya motsa ina ga ko yaron da aka yaye ya salama mata, ina dalili ya sani jin kishinta!" Uwani bata da mutunci, amma tana da kirki.


Garin Biu.
Anan Babana yake kasancewar shi, dan kabilar Babura ne, lokacin da muka isa gidan wanda Uwani ta sani amma ni ban sani ba, domin ban tab'a zuwa ba. Babban gida ne me cike da ahali. Lokacin da muka iso kofar gidan da jama'a tun kafin motar ta tsaya sai ga Babana ya taso yana me murmushi, anan na fahimci yanayin jikina daga gare shine, don ma shekaru sun ja. Bakine amma dogo kasancewar ni kuma Yar guntuwa, siriri ne amma kana ganinshi ka ga wanda ya wadatu da rayuwa me kyau. "Ummu Hadiyya;" ya bude motar cike da farin ciki da zumudin ganina. "Yarinyar da ta aka tafi da ita tana tsumar goyo yau gata mijin da zata aura ya kawo min ita. " ya fada cikin farin ciki da raha. Fitowa Deen yayi shi da Aliyu suka gaida shi, sannan muka shiga cikin bayan mutane na ta mika mana gaisuwa, sannan wasu sun ji labarin ai wanda yar shi zata aura wakilin shugaban kasa ne, Babana shine Sarkin noman biyu. Domin tun daga zauren gidanmu zaka fahimci Babana attajiri ne, don alkama ce aka yi ta jerata ya kai buhu sama da arba'in har sai da ta tab'a silif din zauren, da muka shiga babban parlour shi, ridine a cikin buhu har sai da ta cinye rabin parlour. Cikin murmushi ya ce mana. "Parlour yayi kaɗan ko? Tow ya za ayi store ya cika da kayan abinci, shi yasa aka saka wasu nan." Sannan ya kalli Tafida da yake ta kallon hoton parlour, kafin ya saukar da idanunshi ƙasa. "Yarona sannunka da kokari." Kafin ya ce min. "Tashi muje cikin gidan ki gaida iyayenki!" Haka muka shiga cikin gidan, a hanya na ga ana ta wucewa da tire manya-manyan ana wucewa parlour Baba da shi, dakin Uwargidanshi muka nufa tana ganina ta mike. "Ikon Allah! Yau ga Ummuna Hadiyya a gidan nan!" Murmushi nayi nan aka yi ta shigowa ana min Barka da zuwa ashe ni yar gata ce, na tuna lokacin da na tab'a tambayar Mama Ubana ta mare ni. Haka suka cika min gabana da abinci, Uwani tana tab'awa ta gudu gidansu. Bayan nayi sallah aka ce naje parlour Baba na tafi, nan baba yayi min nasiha tare da su Aliyu, wai zasu tafi. Bawan Allah nan da kokari yake domin kajin gida guda biyar manyan zakaru sai zabbi guda biyar da katon toron agwagwa ya saka musu sai madaran saniya danye da galan din zuma. Ya saka aka hada musu. Har wurin mota muka rako su bayan sun gaida yan gidan tare da bin gidajen Yan uwan Baba ya gaishe su. Cikin gidan na koma. Baba ya ce na zo parlourn shi muka ta hira, yana bani labarin kanshi da hotonsa lokacin yana aikin gwamnati. Da kuma dalilin rabuwarsu da Mama. Na sha kuka domin Babana yana son Mama har gobe, sannan yadda yake nuna min haka daga kalamansa na fahimta, yayi aure aure amma Allah bai bashi haihuwa ba sai akan Mama ita kuma bata sonshi haka Allah ya ƙaddara aka haife ni. Sannan ya ce min. "Duk abinda nake nima dominki nake yi. Kaf wannan hatsain da kome naki ne. Ni ban da wata bukata na dai ajiye su ne ko wata rana zaki zo ko ce min kina son wani abu, sai na fahimci Hadiza ta toshe wannan hanyar da zaki nime abu a wurina. Alhamdulillahi da bata miki rikon uwar wani ba, ta rene ki a matsayin nata amma naji ba dad'i da kika ki karatun boko!" Sosa kaina nayi ina dariya. Sallah ya tashe ni na tafi cikin gidan, abin da na fahimta suma gidan hidimar bikina ake, da dare sai sha biyu ya rako ni dakin Mamawo, uwargidansa na kwanta. Tun asubar fari aka fara hidima, bayan nayi sallah asuba aka ce naje yana kirana, ina zuwa ya zuba min kaya ya ce min. "Sunce aurin aure karfe sha daya ne ina son mu tafi ne yanzu domin mahaifiyarki ta bukaci a kai ki wurinta!" Girgiza kai nayi nace mishi. "Na rayu a gabanta, yau daya ta bar ni ka raka ni ka ji!" Na fada ina kallonshi hawaye ya cika min idanuna. "Tow taya ni zabar kayan da zan saka to!" Wata farar gizne na nuna mishi wanda ya sha aikin hannu, ya ce min. "Shi kenan!" Haka na fito ina jin shi yana fadawa Mamawo. "Idan an daura auren zan gaya muku sai ku taso! Ina Ummu Hadiyya!" Na fito ina faɗin. "Na'am baba!" "Yawwa babu abun da kike bukata ko? Mamanku zata baki sako zamu tafi Allah ya miki albarka." Gyada kai nayi kaina a kasa. "Allah ya tsare!" "Amin Ya Allah " suka fita, ina komawa ciki wata yar Kanwar Baba suka zo da Mai lalle, ta zauna da min ja hannu da kafa, yarinyar me suna Raliya ta ce min. "Aunty Ummu an miki kitso kuwa?" Girgiza kai nayi. "Zan iya bude kan?" Ya tambaye ni, murmushi nayi na ce mata. "Aljanuna zasu tashi!" Dariya yayi tana faɗin. "Sai mu musu turaren barkono!" Zame hular kaina tayi tana faɗin. "Masha Allah!" Ba kome ya saka ta fadar haka ba, sai yawan gashin da Allah ya min wanda na fahimci zuriar Babana ne na gado, domin Babana gashi har wutar shi alamar genen dinsu yana da karfi. Itama Raliya tana da gashin. "Yanzu haka zamu kai ki babu gyaran gashi wannan amarya da kayan ban mamaki kike! Bari na kira Bintu me gyaran gashi ta gyara kan nan!" Ta fada tana zungure kaina!" Can sai ga matar tazo sai dai ba wuta. "Mamawo a saka mai a inji a gyara mata gashinta!" "Ki kira Sama'ila ya tashi injin akwai mai ai ko jiya da ita aka kwana!" Man wanke kai aka saka domin ta tambaye ni relax nace mata a'a don haka man gyaran gashi aka dauko na kayan auren Raliya sai mamaki nake ina son magana ta hanani. "Zan gayawa Baba Malam zai mai da min wasu balle ma idan auren yazo zai min wasu kayan, kema ai an bada kudin kayanki tun da aka fadi maganar aurenki idan zamu kai ki za a kawo kayan." Murmushi nayi domin na fahimci Babana yana son ganin farin cikin duk wnada yake tare da shi. Kafin karfe goma an wanke min an ja min gashin, sannan na gaban goshina aka gyara min su tass.
--- A Maiduguri tunda Aliyu suka dawo yake wani niman hanyar rigima, Deen ya kyale shi yayi yadda yake so, a parlour Hajiya shuwa suka hadu shi da su Maryam da Rukayya,sai zuga shi suke akan kada ya sararawa Yarinyar. "Yar matsiyata kin ga wani gidan da muka je ban da noma babu abinda ake yi!" "Ayya My Son bana son abin da kike yi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login