Showing 30001 words to 33000 words out of 241571 words

Chapter 11 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14752

tunda Alhaji ne ya zab'a maka ita haka zamu riketa hannu bibbiyu."
"Haba Mama waye zai yi farin ciki wannan auren ga Sa'adiyya Yar dangi waye zai ji dadin auren Aliyu da yarinyar kabilu ne fa!"
"Allah yasawa auren albarka!"
"Ya kike son kawar da zancen Sa'adiyya idan aka kwana biyu dole ya auri wacce muke so, wallahi ba zamu tsaya muna kallon ki gama wahalar shi wata can ta more shi, ko Hajiya albarka abin da kika yiwa Aliyu Allah ne kaÉ—ai zai biyaki!" Inji Rukayya. Haka suka gama zuga Aliyu ita Shuwa tana dai gefe amma ranta yayi dubu ya b'aci, tunda Deen ya shigo da kayan da aka basu Alhaji yake kara jadaddawa Deen ya taya shi rikon auren Aliyu ya saka idanun a kanshi.


Biki me sunan biki aka yi a gidansu Aliyu, a ranar asabar al'ummar musulmi suka shaida auren Aliyu da Ummu. Wanda ya samu halartar manya mutane, yan siyasa, mai martaba shehun Borno, a wurin aurin auren Baba Bulama ya gabatar da Baban Hadiyya ga Abban Aliyu abin mamaki, sai gashi ashe abokai ne da suka yi barewa College, sai kuma lamarin ya koma na zumunci, aka yi ta tattaunawa har shi kanshi Shehun Borno ya san Baban Hadiyya Alhaji Kabir Biu. An yi daurin aure an tashi taron lafiya.


-
Tun karfe daya na rana, aka gama shirya kome tare da zabar mata hudu da zasu rako ni. Sai Raliya Uwani haka muka taso har da Mamawo da karfe shida muka iso sannan aka sake shirya tafiyar aka kawo ni gidansu Aliyu da yake Polo.....
N500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


11


Zan iya cewa dukkaninmu a wannan duniyar muna da kalubalenmu, sannan kowani mutum da nashi ƙaddaran nawa shine ya hankad'oni duniyar Tafida, tun kafin mu iso an gyara inda zamu zauna da abincin da zamu ci babu abin da muka nime tunda muka iso domin wasu mata biyu daya me yawan fara'a ce, tana da matsakaicin jiki. Sai daya da babu yabo babu fallasa, suka yi ta hidima damu sannan a bangaren guda akwai wasu mata biyu da suke ta shiga da fita. Wanda suka juya harshe shuwa, don ma akwai masu ji musamman Kulsum da take auren shuwa, a take ta fara shan jinin jikinta tana kallona. "Aunty Baby wannan dangin Mijinki suna maraba dake kuwa?" Bance kome ba kaina a sunkuye. Haka suka fita babu abinda muka tab'a sai sallah da muka yi Rooman ce ta kira Kulsum tana tambayarta batun dinner da aka shirya ashe ita mijinta can ya wuce da ita. Mu kuma nan an bar mu a zube babu wanda ya kara mana maganar fita wani wurin.
Shi da yan uwansa suke shirya abinsu lokacin da muka shigo lokacin suka fita wurin shagalinsu, inda suka maida wata wai me suna Sa'adiyya a matsayin Amarya.
---
"Mahmoud ina Deen yake?" "Hmm ina zan sani na kira ya ki ɗauka!" Tsaki yayi yana zaune a cikin motar, gefenshi Sa'adiyya ce ta cab'a kwalliya. "Muje idan kace zakai ta jiran Deen ranka ne zai b'aci muje next wifydinmu!" Inji Mahmoud, haka suka fito a motar rike da hannun juna, har cikin hall din. Inda yake cike da jama'a. Anyi hidima sosai, duk da haka hankalinsa baya kwance ya kira Deen ya kai sau dari amma bai dauka ba, karshe kashe wayar yayi abinsa. Rooman tana ganin abin da yake faruwa ta ja mijinta suka bar wurin sai fada yake tayi, ita kan bata ce kome ba. "Fisabiilillahi a rasa wanda za a bawa Aunty Baby sai wannan dan iskan Yaron mara mutunci wanda kowa yasan.kaf garin nan bai da da'a kaf gidansu babu wanda yake da bakin mutane kamar Yaron nan, rashin auren Baby ba yana nufin rayuwarta zata kare a haka ba ne Allah ya gani naji zafin wannan auren yaron nan bai da kunya." Ita kan bata ce kome ba,.har suka iso gidansu Aliyu. "Bappa zan kwana Please!" "Idan aka samu matsala ki kira ni don Baby zan barki amma.da wani ne ba zan barki ba!" Ita kan godiya tayi mishi tare da shiga cikin gidan, da taimakon Uwani ta shiga cikin inda muke, tana faɗin."Ban tab'a ganin aure irin naki ba, wallahi taya ga Amarya anan wata ta zama ke a can? Idan baya sonki me yasa zai yarda a aura mishi ke wannan cin mutuncin da me yayi kama?" Turo kofar dakin aka yi daya matar me fara ce ta ce mata. "Ba ance babu dinner ba?" Zata yi magana nayi saurin dukar gefen cikinta. Ashe matar ta lura. Murmushi tayi ta ce mata. "Anyi dinner ne?" Kallona Rooman tayi tana me kallon matar ta girgiza kai tayi. "Ba zaki fada ba kenan?" "Tow me zance? Amarya anan ango a can da wata mace? Yayata ce fa?" Rufe bakinta nayi bayan na cire mayafin . "Ya isa haka!" Na rungumeta domin kuka zata yi. "Me yasa daga kawo ki sai tozarci?" Inji Kulsum. "Don Allah ki bar maganar nan, don Allah?" Nasan zan ga abin da yafi haka amma bana son tashin hankali. "Kuyi min alƙawarin Mama ba zata ji ba!" "Munyi!" Suka fada har da Raliya da Uwani. Don iya su suka tsaya min. "Don Allah Hajiya a bar maganar nan ba wani abu ba ne da zai zama babba a wannan lokacin. Don Allah!" Na fada ina kallonta. Murmushi tai sannan ta ce min. "Sunana Hajiya Kaltuma nice Amaryan Alhaji Muhammad Jadda, na ji dadi da Aliyu ya same ki a matsayin Matarshi, amma ban ji dadin abin da ya faru ba. Kiyi hakuri da abin da zai biyo baya amma nima uwa ce ina da Yaran da na rike ba xan so ayi.musu abin da aka miki ba, sai da safe." Haka ta fita tare da barin dakin, rufe kofar nayi na zauna a jikin kofar na hade kaina da gwiwata, "Aunty Baby!" D'ago musu hannu nayi nace musu. "Ku kwanta kawai!" Na cigaba da zama a wurin. Ban san me nake ji ba amma har karfe daya na dare lokacin da suka dawo ina zaune a banki kofar dakin. Can naji ana ta fada a cikin gidan bakiɗaya, tashi Kulsum tayi tana me kallona har lokacin ina zaune. "Baki kwanta ba ne?" "Bana jin barci ne!" "Meke faruwa?" "Ban sani ba!" Tsaki tayi ta kwanta domin muna jin hayaniyar amma da kusan shuwa ake yinsa. Kuma muryan na mace ce ba namiji ba. Ban daki na shiga nayi alola na fito na gabatar da sallah ina sallah naji ana buga kofar wurin karfe uku da wani abu. Haka na yi sallama na bude kofar. Gabana ne ya fadi nayi baya ina hadiye yawun bakina. "Fito munafika!" A hankali na ja kofar domin yayi maganar yadda iya ni zanji. Cafko hannuna yayi tare da fitar dani daga cikin gidan, wurin motar shi ya kai ni ya wurga ni cikin motar ya shiga. "Ke jakar ina ce? Ke wacce irin dakikiya ce dabba mara hankali? Matsuyaciya mara hankali har kin isa ki hada ni da mahaifina? Wallahi kika sake kuskuren shiga tsakanina da shi mutuncinki wawuya sakarya dabba kawai" tunda ya fara zagina kaina a sunkuye yake ban iya motsawa ba domin ji nake duniyar tana min yawo. "fita min a mota tinkiya kawai!" Wani irin zazzaɓi ne ya rufe ni, Dakyar na bude motar na fito jikina yana rawa, ga sanyin alfijir da ya fara ketowa wanda ya haɗa min wani irin zazzaɓi da tashin tsigar jikina. Dakyar na koma dakin, ban iya kuka ba domin na nime kukan na rasa. Har aka kira sallah asuba ina zaune a wurin Dakyar na tashi nayi na koma na kwanta bayan na tashi Kulsum. Tun da na kwanta ban farka ba, sai karfe biyu na rana. "Amma lafiya dai ko?" Hajiya Kaltuma ta tambaye ni bayan na farka. "Lafiya lau!" Na fada ina gyara zama. "An kai miki ruwa ki shiga kiyi wanka. " haka na tashi jikina babu kwari, na wuce nayi wanka da alolan azahar na fito nayi sallah aka kawo min kaya na sakanOllfaya. Ina zaune aka kawo min abinci,kaɗan naci domin bani da dandano a bakina. Haka na ci na bar sauran, yamma can aka fara hidimar biki sosai a gidan, yan gidan mu duk sun iso dama tun bayan daurin auren aka kawo gara da yasa èduxl k masu adawa da lamarin a jikinsu yayi sanyi, a da can shi yaso ya kama haya ne amma Abbanshi ya hana ya ce ya fara xama a gidan ya ga yanayin zamanmu, dangin Mama da yan uwa babana sun zo a kai ni cikin gidan wurin Abba, bawan Allah nan dattijon kwarai ne, domin ya amshe ni hannu bibiyu sannan ya hada ni da matanshi biyu hajiya Salamatu da Hajiya Kaltuma. Sannan aka fito dani aka yi budar kai. Anyi hidima sosai wnada yasa abin da Mama tayi ita da Mijinta da Mahaifina ya kashe karfin zukatar yan uwansa. Sannan aka dauke ni zuwa bangaren da zamu zauna wanda tunda aka yi jere babu wanda ya kara shiga sai yau da za a mai dani bangare na. Anyi hoto ko nace ni nayi nawa da yan uwana da abokan arziki, shi yayi na shi tare da yan uwanshi, da kuma yarinyar da Rooman take nuna min ita a matsayin amarya da aka yi dinner da ita. Ban yi mamaki ba ai kowa yasan cewa ni ba irin kalarshi ba ce, yadda take narkewa a jikinshi yasa na kara jin tausayin me yasa na kawo kaina lahira, a gefe guda wasu yan mata da bansan su ba, suka zo har inda nake daya ta koma bayana tana faɗin. "Na baki shawara? Tun wuri ki bi yan uwanki gida, domin nan gidan sai ki roki mutuwa ma!" Idanuna ne ya cika da kwalla, kaina a kasa har suka gama iskancinsu ban ce kome ba, kiran sallah yasa aka fara watsewa aka wuce da ni dakina wanda kayan da Mama ta zuba na san Allah kaɗai zai biya ta, haka na sake wanka na sauya kayana. Sannan a hankali yan uwana da kannena suka yi ta watsewa. Ya rage ni daya kamar rai, tun ina saka ran jin motsin wani har na daina na mike tare da rufe kofar dakin na kwanta, duk tsayin ranar yau bana jin nayi shi cikin farin ciki da walwala ba tare da abin da Tafida yayi min bai fado min ba. Haka na zauna a cikin dakin har dare yayi sosai. Kafin nayi alola na kwanta, sama-sama nayi ta jin dariya da karfi tare da yan hayaniya. Ciwon da kaina yake yasa na tashi a hankali na nufi kofar dakin, bude kofar nayi, a hankali na maida tare da rufewa, na juya na koma gadon na kwanta. Ina jin kamar nayi kuka ne ko nayi meye oho, Tafida ne da yarinyar sai Mahmoud da yake ta kallon tv, asalin abin da ake a tv wani american film ne mara kyan gani. "Ya Aliyu kaga gayen abin da zai yi gaskiya nayi missing wannan Film din!" "Kai tashi ka tafi gida, kema tashi na raka ki." Ya fada yana kashe tv din. "Kai fa dan iska ne, ya muna kallo zaka kashe ma ko zaka shiga wurin wancan abin ne?" Inji Mahmoud. "Ove my death body, ku tashi ku tafi kada mai gidan nan ya san kuna nan ku sake jangwalo min wani magana!"


Mikewa suka yi Sa'adiyya ta ce mishi. "Kayi min alƙawarin ni daya ce naka, kuma kace zaka aure ni kada ka ci amanata. Domin na rena wancan yarinyar." Tsaki yayi yana nuna mata hanya, duk suka fita, sai da suka fita sho Tafida ya raka Sa'adiyya Mahmoud ya bishi da sauri yana faɗin. "Man na manta wayata fa!" "Ok jeka nima zan lallaba Saadih kafin na shiga gidan!" Ganin yadda Tafida ya bashi damar shiga cikin gidansa babu wani abu ya bashi damar nufar gidan. Yana zuwa kofar Ummu ya nufa dama bai wani manta kome ba, buga kofar yayi.
Jin yadda ake buga kofar yasa na ce. "Waye?"
"Zo ki karba!" Yadda akayi maganar ban kawo ba Tafida ba ne, yasa na bude kofar. Turo kai zai yi na ja kofar da karfi. "Lafiya?" Murmushi yayi yana faÉ—in. "Har yanzu ba zaki hakura da zama da shi ba? Kin san ina yake? Yana tare da yarinyar da yake fatar ya aura suna can suna." Ya tsaya yana kare min kallo daya daga kasa har sama, rufe kofar nayi da karfi tare da rintsa idanuna. "Ummu Hadiyya ina me baki shawara idan ma ba zaki rabu da Aliyu ba, me zai hana mu ji dadinmu." Komawa tsakiyar gadona nayi na dunkule wuri guda na fashe da kuka, wacce irin masifa ce Wannan. Haka ya gaji ya tafi ban ma san tafiyarshi ba.
A hankali ya shigo zai wuce cikin gidan, turus yayi yana kallon Tafida da Sa'adiyya wacce take wani narkewa tana kuka. "Ke wuce kafin na karya kafarki!" Inji Umar da yazo gidan sakamakon Attack din Abba da ya tashi aka kira shi domin maganin asthmar shi ya ƙare, da sauri ta wuce cikin gidansu. "Wai yaushe xaka yi hankali ne? Aliyu me kake son zama ne? Fisabiilillahi a daren farko ma sai ka cutar da kanka? Tow wallahi bari na gaya maka idan Abba ya samu labarin abin da kake yi ko wallahi babu ruwa mutumin banza kawai." Ko cikanka bai ce mishi ba ya wuce abin sa. Yana shiga ya kalli kofar dakin Ummu ya kai wa kofar naushi, ya wuce.
Jin irin bugun da aka yiwa kofar yasa ni tsayar da kukan da nake yi, jin an wuce na sauke ajiyar zuciya. Kwana yayi yana shirin yadda zai yi Ummu domin kuwa ta shiga rayuwarshi.
Washi gari.
Tunda nayi sallah asuba na kwanta ban kuma farkawa ba, sai karfe daya na tashi nayi alola da wanka na fito na shirya cikin wata material, ina daura dan kwali naji muryansu Kulsum, da sauri na gama na yaga mayafi na fito. "Aunty Baby irin wannan barci ko!" Ware idanu nayi Taima da tazo tare dasu, ta saka dariya tana faÉ—in. "Bari muga ko tafiyarta ya sauya ko tana dingishi!" "Bana son iskanci! Wannan ai rashin kunya ce" na fada ina dauke kaina. Kayan hidimar girki ne da aka zuba su a cikin cantaine daban daban, suka shiga kitchen suna jera min. Kullar abinci muka gani, Kulsum ta buÉ—e doya da kwai ce tayi sanyi sai kunun alkama da farfesun kaji. "Mun zo miki da abinci fa! Ga wani kuma!" Ya nuna kullar da na bude. "Ina kewar abincin Mamana!" Na fita parlour na ja na fara ci a hankali, ina lumshe idanuna. Su kuma suka ci wanda suka samu, muna cikin gyara gidan aka sake shigo da abinci, muka karba da fara'a tare da godiya, mun wani likis, sannan suka tafi, can wurin La'asar daga cikin gidansu aka fara shigowa ana gaisawa, duk da nasan an kawo musu nasu kayan garan haka na shiga cikin na dibo musu tsatsafa, nakiya, dubulan tawaita da cin-cin da gereba, da duk wani kayan da aka kawo min na shake musu tire da shi, na koma na dauko ruwa da lemon gora na ajiye musu. "Wai Sannu da kokari!" Suka yi ta fada, can da suka gama zamansu suka mike tare da tambayata. "Babu leda ne mu juye" "akwai "kitchen na koma na dauko musu ledan na kawo musu, sannan na juye musu.


Tun ranar da aka yi wuni ban kuma saka shi a idanun ba, haka na cika kwanaki uku babu labarinsa amma cikin gidan ana kawo min abinci da kome, na gaji da zaman haka yasa da safe Nabila yar rikon Hajiya Kaltuma da ta kawo min abin karyawa. "Don Allah ko zan bi ki na gaida mutanen gidan da Abba?" Murmushi tayi tana faÉ—in. "Dama Hajiya ta fada tace zaki shigo gaida Abba." Ta fada min tana faÉ—in. "Muje!" "Tow bari na saka hijab ba!" Na shiga cikin dakin na saka hijab dina sabo ne dal, a cikin kayan da Babana ya turo min. Tana gaba ina baya tun daga tsakar gidan nake gaida masu aikin gidan, suna amsawa da Mamaki, wanda ni dai ban san dalilin haka ba, har muka isa parlour Hajiya Kaltuma muka gaisa."Nayi tsammanin zamu shigo tare da Aliyu ne?" Sai aka bar ni da zare idanu, ina yake don ban san me zance ba. "Tashi muje parlour Abbanku!" "Tow!" Na amsa mata, sannan na mike na bi bayanta har zuwa parlourn shi. Yara mazan na zaune sun zage shi har da Aliyun, "Barka da hutawa Abba!" "Yawwa Ummu Hadiyya! Barka dai da fatan kin tashi lafiya!" "Alhamdulillahi!" "Ki mishi ya jiki bai ji dadi ba!" Inji Hajiya Kaltuma Ta fada min. "Ayya sannu ya jikin, Ubangiji ya baka lafiya yasa zakkar jiki ne."
"Amin Ya Allah, ya bakunta?" Ya tambaye ni yana kallon Aliyu da ya hade rai. "Alhamdulillah!" "An jima za a kawo miki cefane ba sai kin jira an girki daga nan ba, ki fada idan an kawo miki ki ci! Domin yar Sarkin noman ba zata zauna jiran matan gidan ba, Mahaifinki mutumin kirki ne, shi yasa kika san hukunci da idanu. Babanki ya rike house captain makaranta, ya kula da mu yan jahar Borno, duk wani dalibi idan akace daga Maiduguri yake tow ya dauke mu kamar danginsa. Idan kika dauki halin Alhaji Kabir Biu tow nayi imani da Allah babu wanda ya isa cimmaki amma sai kin koyo jarumta irin nashi." Gyada kai nake kawai, babu abin dadi kamar ka ji ana gaya maka waye mahaifinka.


Mikewa Aliyu yayi ya fita, "kana karawa Borno masu, tashi na kai ki wurin Inna da Salamatu!" Haka na mike na bita har parlour sayar mata ba yabo ba fallasa muka gaisa, sannan na fito

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login