Showing 177001 words to 180000 words out of 241571 words
Chapter 60 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊
55
Yadda Mama take kokarin kula da ni yasa na rage damuwa sosai, domin kuwa ta tsaya min yadda ba zan bukaci kome ba, hatta asibiti sai da ta nima min kusa da gida, Taima tana shigowa muyi hira, har take kawon min yadda suka yi da mijinta, har ga Allah mijinta yana sonta sosai kawai Uwarshi ce matsala, shiru nayi ina kallonta. "Kina son Mijinki ne?" Gyada min kai tayi tana faɗin. "Ina sonshi Ummu shima sona yake. Kuma ya gaya min yanzu zamu bar Nijeriya ne saboda ya samu damar karo karatu a Italiya, kin ga kenan zamu samu sauƙin fitinar Mamansa." "Hmm! Haka ne tunda yana da bukatar ina ga ki bi mijinki Allah ya daidai ku, ya kuma baku hakurin zama da juna, sannan ki rike azkar, kina yawan sadaka ko ba yawa. Ki koma Yaranku hudu idan kika barsu zasu tashi cikin maraici, kina raye amma Yaranki zasu zama marayun dole. Kina ji kina gani wata zata lalata miki rayuwarsu." Na fada ina kauda kai ina kallon Mufidah da ta fara ƙoƙarin takawa kwana biyu nan, haka kawai zasu ta kiran sunan Babansu da *Da* daurewa nake bana kuka amma tabbas abin yana sosa min rai. "Ashe Mufidah ta fara takawa?" Inji Mama ta shigo dakin. "Eh wannan shine karo na biyu da ta gwada!" "A sayo sweet a raba sadaka Alhamdulillahi." Ta kunce habbar zaninta, ta fita tana bada aikan, tashi Taima tayi tana faɗin. "Na gode Ummu bari na koma!" "Tow ba kome Allah ta rufa asiri ya sa mu dace!" "Amin Ya Allah!" Ta fita na zauna shiru ina bukatar abin da zai rage min nauyin da nake ji, ina son na rage damuwa, koda Mama ta sake shigowa ta samu na b'ata shiru bata min magana ba, ta fita.
**
"Ina zamu haka?" "Gida!" Deen ya fada mishi, yana tuki. "Me yasa?" Murmushi yayi ya cigaba da tuki." Saboda ka tara dabbobi suna aikin su na dabbobi a gidan kuma kasan Hajiya bata da lafiya, dole tana buƙatar hutu!" "Tow ni daya ta haifa?" "Ba kai ɗaya ta haifa ba amma kai take buƙatar zama a wurinka!" "Ka daina min shishigi!" "Nayi Dan iska da ban daina kula ka ba!" "Mutuwa xan yi?" "Ko baka mutu ba zaka wahala!" "Me ya dace nayiwa Mahmoud?" "Lokacin da na gaya maka hatsarin barin Mahmoud a gida me kace min? Dan iska yanzu da ya lalata maka kome ai ka ji dadi, kai kada ka kara min maganar Mahmoud don wallahi xan ci zarafinku." "Idan kuma na ki fa? Idan naki fa Deen ka fita idanuna, mahaukaci!" "Duk haukata ban kai ba domin da xan gaya maka wani abu haukacewa zaka yi sai an daureka a turu." Shiru yayi yana kallon gefen hanya. "Yanzu ne ya dace ka fuskanci rayuwarka a bangaren Al'umma kana ta kokarin sauke nauyin da yake kanka, sai dai a fuskanci gidanka! Matanka da ka ajiye basu bukatar kome sai lokacinka." "Ni fa duk bukatata akan Ummu suke bayan nan bana jin zan iya mu'amala da wata mace, na rantse da Allah Sarkin da babu wani sarkin sai shi ba zan iya samun nutsuwa a tare da su ba, Saadiya ce ko Asiyah yarinyar da kai kanka kasan bata da nutsuwa idan suka kawo min reni zan kora su wallahi!" "Wannan kuma shine karya zama daram me jego ta hau gado!" "Mtseew!" Ya ja tsaki. Suna dab da shiga cikin gidan suka ga wasu cikin security na gidan sun shiga cikin gidan da gudu. Bude musu kofar aka yi Deen ya tambayi daya daga cikin masu tsaron kofar gidan. "lafiya!" "Fada ake tsakanin su uku ." Lumshe idanunshi yayi yana me sake murmushin baƙin cikin. Amma kuma sai ya ga babu amfanin tashin hankalin, suna shiga suka samu ana jan Saadiya akan Asiyah, Maryma na gefe kanta a fashe jini na zuba ana ƙoƙarin daure mata shi, amma yaki tsayawa. "Kai sake ta!" Da sauri suka kyale Sa'adiyya. "Tashi akanta?" Ya daka mata tsawa, tashi tayi cikin sauri tana haki. "Wallahi kika kara zagina sai na miki wanda ya fi haka!" "An fada uwarki tayi zaman kasar gadan lagos an fada din!" "Ke kuma Yar kwaya, Uwarki bata gaya miki gaskiya ba ke ba yar Alhaji Sanda bace a yawon bin malamai ta samu cikinki, idan karya ne kirata har ubanki na sani." "Wayyo Allah na, idan na yarda Allah ya tsine min!" Ta dauki muciya ta nufi Saadiya da shi. Fitowa yayi daga motar, tana ganin shi ta sake muciyar ta fashe da kuka. Sa'adiyya kuwa tasan waye shi don haka bata samu ba, ta wuce tana faɗin. "Kema uwar Munafukai baki ga kome ba, har ni zaki ciwa Amana ki shiga wurin asiyah wallahi sai kin bar min gidan nan tunda ba gidan Mijinki ba ne! Ni ba Ummu Hadiyya ba ce, da zaki zo gidana kina niman shiga jikin kishiyata!" Ta wuce tana yarfe hannu. "Ku kaita asibiti!" Har lokacin Tafida bai ce musu kome ba, ya wuce bangaren Ummu, key din da yake wurinsa ya bude kofar da shi ya shiga ya zauna ko ina yayi datti. Dakinta ya wuce ya bude sai yake ganin kamar zai ganta a gaban Mirror dinta tana kwalliya. Shiga dakin yayi ya zauna a bakin gadon, yayi shiru, kanshi a kasa.
Asibiti drive ya wuce da Maryam, sannan Deen ya wuce bangaren Hajiya ya same ta a parlour kwance, tana kuka don ta gaji da fitinar safe daban na dare daban yau kan ma har da Maryam a fadar nasu. "Tafida ya zo ko?" "Eh yana can bangaren Ummu!" "Allah sarki, Ubangiji ya bashi hakuri da juriya!" Ta fada tana jin kuka na zuwa mata, da sallama Ya shigo parlourn, ya nime wuri ya zauna kamar babu abin yake damunshi. "Aliyu ya kake?" "Lafiya lau Hajiya!" Ya fada yana kallon inda Fanna take ya ce mata. "sannu da kokari na gode!" "Nice da godiya, Allah ya shiga lamarinka!" "Amin Ya Allah!" "Aliyu ba zaka iya yin wani abu ka dawo da Ummu ba?" Inji Hajiya, dariya yayi yana faÉ—in. "Hajiya Ummu kuma? Hajiya kenan! Ummu sai dai wani me sunan Aliyu ba ni ba, domin duk yadda zan yi na fahimtar da ku girmanta da darajarta ai kun kasa fahimta, yanzu da ta bar ni ai kowa zai fahimci tana da amfani a rayuwata ko bata da amfani, a bar maganar Ummun nan kawai Allah ya baki lafiya." Daga haka ya bar zancen duk yadda taso ayi maganar amma fir yaki ya nuna mata ma shi ya hakura da Ummu har abada. Bakin nan ya mata ciwo tayi bakin ciki kamar me amma haka ta hakura, banda Allah ya bashi Deen a gefenshi waye zai tsaya mishi haka shi yasa yake ganin kamar ya rasa kome nashi da ya rasa Ummu.
Haka kwanaki suke cigaba da tafiya, kome yana ta tafiya kamar babu abinda ya faru, satin Deen daya ya koma wurin aikinsa, Hana barin kasar Tafida yayi bala'in sauyawa, wancan masifaffen yakusashe mara mutunci nan dai shi ne, sannan ya zama kamar dodo, idan yana gidan babu damar fada yana barin gidan zasu ta hauka da rashin mutunci kamar ba mata ba, ana cikin wannan yanayin suka samu gayyatar zuwa bikin dan shugaban kasa, don haka ana bukatar duk wanda zai je da Matarshi. Bai da niyyar tafiya da su amma saboda baya son magana yasa shi kiransu parlournshi, yana zaune ya zuba musu wasu takardu ya ce . "Gida ko Abuja, duk wacce ta dauka abin da yayi daidai shi kenan!" Da sauri Asiyah ta dauki takardan gaban Saadiya. "Mahaukaciya, ba saba zuwa Abuja ba shine da daukar na gabana!" Gyaran murya yayi Saadiya tayi shiru ta É—auka. Ai kuwa ta samu Abuja, ta wani kwashe da dariya. "Abuja!" Ya fada tana mika mishi takardan. "Bura uba! Idan na yarda shegiya nake wallahi ba zan yarda ba munafunci aka hada min!" "Waye zai hada miki munafunci ?" Inji Saadiya tana dariya tare da zaro idanu. "Annamimiya ba dake nake ba munafika yar Mace!" "Kutuma ina wasa dake ne jaka? Yar kwaya!" Ai kuwa suka kaure da fadar da suka saba. Kai masifa, tashi yayi ya nufi kofar fita ya rufe ya ja wayar wuta ya shiga zane su, bakiÉ—aya ya koma musu asalin Tafidan shi sai da ya musu ligis ya kara da cewa.."Wacce zata tafi ta shiga abujan na kara jin tari sai na ci kaniyar mutum. " da sauri suka bar parlour, suna fita waje suka hau fadar kamar kajin. Dafe goshinsa yayi yana jin kamar ya fasa ihu.j
***
*Ummu*
Ina kwance wayata ta fara ringing, dauka nayi ina me faɗin. "Titilayo!" "Ummu ina son ki hada ni da Mama Please!" "Ok!" Na tashi ina me fita waje na cewa Mama. "Tina ce akan layi?" Na mika mata, wani murmushi Mama ta sake tana amsa gaisuwarta. Kafin ta shiga jin abinda take fada fuskarta a sake ta kalle ni, tana murmushi. "Alhamdulillahi shi kenan a turo kome zata zo da yardan Allah!" Sannan ya juya tana faɗin. "Mama lafiya?" "Wai za'ayi bikin yar shugaban kasa ne, shine aka gayyaci kwararrun masu girki baiwar Allah nan, ta tuna dake!" "Ni kuma? A wannan yanayin?" "Kashe kanki zaki yi? Kina tsammanin dangin Tafida zasu bar shi ya dawo gare ki ne idan an yi magana akan cigabanki sai ki ce zaki iya wannan wacce irin masifa ce asiri Tafida ya miki ne? Dalla bani wuri tafiya babu fashi!" Dama na lura da zarar aka ce min nayi wani abu nace a'a zata fara cewa ai ina jiran Tafida ne, wannan abin yana sosa min rai, haka yasa na hakura na rufawa kaina asiri. "Zan je Mama!" Na fada ina jin kamar xan yi kuka. Bayan na koma na kira Tinah muka yi qmagana sosai, na ware na goge kayana dama uwani ta wanke min wasu. A cikin satin na bar Maiduguri bayan na sha nasiha a wurin Baba Bulama da Mama, na iso Abuja ta jirgi tinah ta dauke ni har gidansu na kwana, washi gari muka wuce fadar shugaban kasa, inda aka bamu tsare-tsaren da za'ayi yi dayawa chefs din da aka gayyata sai suka fara ja da baya, saboda sun sanni, abu daya nayi shine hade kanmu muka raba girkin yadda kowani team zasu yi, duk da daurewa nake amma bana jin dadin jikina. Haka nayi ta nuna musu ni ban san kome ba, saboda yadda nake ji na, sai Allah ya taimaka ban yi ta amai ba ko zubda yawu ba, sai dai bana cin abincin sam sai tea, haka yasa bana wasa da shi. Mu talatin ne masu girki da Ya Gunsa yar shehun Borno, ita ta tambaye ni yadda zamu yi na bata amsa tare da raba mu, yadda ba zamu taru akan abu daya ba. Ganin yadda na tsara mana kome sai aka ware mu kabilu uku, ni daga Borno da wata yar Abia, sai wani Bayo dan Abeokuta. A kasan kowannen mu akwai mutane goma goma, yadda kowa zai ji da jama'arsa, sannan aka ware mana kome. Sannan a kasar mutane goma akwai akalla mutane talatin, saboda yadda aikin zai mana kuma ya tafi dai-dai. Haka muka kwashe kwanaki biyar muna aiki ba ji ba gani sannan babu wanda zai ci abincin yayi tsammanin zai bashi matsala musamman ni da Ya Gunsa ta tsaya tana gabatar da ni ga wasu manyan mutane da masu gidajen abinci manya da hotel. Sai gashi mutane suna ta yaba min, ai kuwa ban yi wasa da wannan damar ba, na kara zage damtse nayi aiki sosai, kasancewata yar arewa kuma nayi abin bajinta muna gama aikin Ya Gunsa ta kira ni a waya wai na shirya zan tafi dinner, haka na ci kwalliya duk da lafayya ce sai dan hill da na saka sai tsiya suke min. "Hadiyya da gaske kana da Yaro?" Inji wata me suna bose. "Twins ma kuwa suna gida!" Na ji muryan Tinah. "Malama ke ake jira maza zo mu tafi!" Ta sha kwalliya kamar ita ce Amaryan, bin ta muka yi har inda motar ta yake na shiga ta rufe min, muka wuce inda ake taron ta mika musu gate pass. "Tunda abin na ya faru mun hadu da Aliyu kuwa?" "Manta da wannan zancen bai da amfani!" "Ummu yana da kyau ki gane cewa rabuwarku ba yana nufin ba zaku yi zumunci bane, ki gane mana!" Murmushi nayi domin bana jin zan yi magana. Har muka isa ita ɗaya take maganarta amma ni dai naki magana. Koda muka shiga cikin wurin rike hannuna tayi har wurin Ya Gunsa, ita kuma ta mike ta kai ni wurin Uwar Amarya aka gabatar da ni, sai jinjina min take,sannan muka dawo inda take na zauna wurin, muna xaune naga Tinah tana juye juye. "Lafiya kuwa?" "Lafiya lau!" Ta fada tana juyawa tare da mikewa. Ta nufi can ɓangaren Gwamnoni da matansu. Ban juya ba amma jikina ya bani akwai wani da yake kallona, kamar an ce na juya muka yi ido hudu da Tafida. Cizon bakina nayi kafin na mike a hankali, na cewa Ya Gunsa. "Bari ka shiga bayi!" "Ok ki bi wancan hanya zai kai ki bandakin!" "Na gode!" Na fada tare da nufar hanyar, a hankali ya mike shima ya bi hanyar.
Tunda na shiga ni ban yi kome ba, ji nayi kamar zuciyata zata buga saboda yadda nake ji, kallon madubin ban dakin nayi kafin na wanke hannuna sannan na bude kofar na fito daga nesa na hango shi, abin mamaki ni na saka laffaya fari ne ke ratsin golden, shi kuma yana sanye da wata material cream color, kallo daya nayi mishi domin na wasu yan mata suna tawowa ina ga sun zo nasu uzirin, ganshi tsaye suka tsaya daga nesa, zan wuce ya ce min. "Ko babu kome akwai Yara a tsakaninmu sannan da izinin waye kika zo nan?" Banza nayi xan wuce ya riko laffayana sai da ya zame a kaina gashina da ya dauka har bayana ya bayyana. "Don Allah ka kyale ni kafin a fara zargina da na zo Abuja sheke aya ce!" Sake ni yayi yana kallona bakinshi a sake, har na fita daga ban dakin. Kafin ya wuce yan matan da suke mishi magana. Haka yayi ta kallona har na zauna, dole na saka kaina farin ciki, na cigaba da hirana da su Tinah, komawa yayi ya zauna wurinsa Saadiya ta ce mishi. "Ni dai Tinah nan ba karuwa ba ce kuwa? Sai kace karuwa don Allah dubi shigarta haushi take ba ni!" "Kin ga kuwa tun sanina da ita ban tab'a jin labarin ta bi saurayi gidansu ba,sai dai ya biyo ta gidan Ubanta!" Shiru tayi ta kalle shi a fusace. "Malam magana ka gaya min?" "Akan me zan gaya miki magana ai ke First Lady ce ba a gaya miki magana!"shiru tayi tana jin yadda yake zugata hmm Tafida bai da mutunci ko daya, ya zageta ya kuma gaya mata abin da take mafarkin zama, hmm lallai fa yana kallon yadda Ummu take dariya tana shan ruwa, ai kuwa ta kware bai san lokacin da ya mike yayi ta ratsa mutane ya isa wurin yana bubuga bayanta. "Are You okay? Sannu ajiye ruwan haka!" Ya fada yana buga bayana har lokacin. "Ka bari!" Na fada ina kokarin ture hannunshi. "Ki tsaya ya buga hannunki! Ranka ya dade ashe kazo?" Jinjina mata kai yayi yana kallon yadda nake goge jikina!"
"Kambu Uban waye ya gayyace ki bikin nan...…...https://chat.whatsapp.com/DMCa4TXOqV712jNc1UBBRH
*Gidan zafafan kayan Mata masu kyau da inganci na yar mutan sokoto maman Yusuf likitar Mata,*
*Bayan kayan Mata muna tura abubuwan da zasu amfanemu game da Zaman auren da wasu magungunan da zaku iya hadawa da kanku da sauransu*
56
"Wacece wannan mara tarbiyya?" Inji Ya Gunsa budar bakin Tinah ta ce mata. "Hala mahaukaciya ce ta shigo ba bisa ka'ida ba" zata kara magana Tafida yayi maza ya ce musu. "Muna tare da ita!" Ya fada yana kallona. "Kin ji daidai ko muje asibiti ne?" Yadda yayi magana muryanshi babu wasa."Malam don Allah ka barni haka!" Na mike zan bar gurin, kafa Saadiya ta saka min na tafi zan fadi yayi maza ya tare ni na zube a kirjinshi, bakiÉ—aya wurin sai da suka mike, kamar an ce a haska mana hasken fitilar wurin ni da shi, ina sauke ajiyar zuciya nayi ina faÉ—in. "Allah ya Nagode maka da ka tsare ni!" Na d'ago kaina muna kallon juna. Janye jikina nayi na bar shi tsaye a wurin, domin na gama zama a wurin kenan, wurin motar Tinah na tsaya ban koma cikin ba, ina tsaye a wurin, wani mota ce tayi parking, sau daya na d'ago kai na kalli motar na mai da shi na sunkuyar ina kallon hotonsu Mufidah da Mufid, na shagala sosai a kallonsu naji ance min. "Assalamualaikum kema kina cikin yan bikin ne?" Kasancewar Muryan mace ce, yasa na d'ago kai na bude baki a hankali na ce mata. "Eh ku shiga!" "Tow Yayana ne ya ce ko zan miki magana ki shiga cikin wai nan babu tsaro!" Kallonshi nayi naga ya wani haÉ—e rai. "Kada ki damu ina jiran wata ne yanzu zata fito!" Ban gama rufe baki ba sai ga Tinah da Tafida. "Gata nan!" Na nuna mata, murmushi tayi ta koma ta gaya mishi, har zasu bar wurin sai ya kalli Tinah. "Kada ku sake kurkuren barinta zama alone!" Kallonshi tayi tana mamakin yadda ya mata magana yana me rike da hannun matar. "Ummu wani abu ya hada ki da shi ne?" "A'a kawai sun ce ka shige ciki na ce musu ina jiranki ne shi kenan!" Ashe ganin yadda yayiwa Tinah magana yasa Tafida tsare hanyar da zai shiga cikin hall din. "Bamu hanya!" Inji matar. "Ban gane me ya hada ka da wancan me lafayyar ba?" Domin yasan maganar da yayiwa Tinah yana