Showing 114001 words to 117000 words out of 241571 words

Chapter 39 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14726

miki aka yi da sauki ne da shi da zan rike mace sama da daya Hadiyya ki fito Ki gaya min bakya bukatar zama da ni mana!" Murmushi nayi na wuce shi don nasan ya cika haka suka fita, a waje ya amsa wayar yana me bude mata tsohon littafinsa na tijara, jin tana kuka yasa shi sasauatawa ya tambaye ta me ya faru, bai karasa ji ba ya kashe wayar ya nufi massalaci yana zargin Deen da hada mishi husuma me Deen zai yi ban da dariya.


Bayan fitarsu nayi alola na zo nayi sallah, sannan na kunna wayata na kira Uwani na gaya mata ba zan dawo ba, ta ce min ai Baba ya gaya mata. Murmushi nayi sannan na kashe wayar na ja Yarana muka shiga kitchen, mamakin yadda aka zuba kome na zamani nayi, ina cikin aiki wurin karfe biyu da arba'in da biyar, ya kira ni. "Ummu Hadiyya! Akwai matsala!" "Ina tare da kai babu wata matsala gaya min me nene?" Daga can na ji Deen yana faɗin. "wallahi billahi azim ba zata zauna a inda Ummu take ba, ka kaita gidan Abba ko ko gidan Hajiya ba zata zauna ba, Ummu tana buƙatar ka kana bukatar Ummu, meye amfanin kebewan da kayi ba don ku huta ba ne, Yaran nan wallahi ban da suna shn mama da na rabaku dasu, ko ka kaita gidan Maryam amma ban da Ummu."


"Wai me ke faruwa ne?" Kashe wayar yayi.
Mamaki ya kara kamani na kira Tafida, "zan kira ki!" Kashe wayar yayi..
**
A can kuwa Abin da ya faru, Asiyah ta sab'a lamba, domin ta tabo Saadiya a daidai lokacin da take cike da Tafida, abun da ya faru kuwa, tun da Tafida ya bar gidan bai gaya mata zai tafi bude sabon titi a wani kauye ba, take cika take batsewa domin a bakin yan gulmanta take jin labarin, har dare aka sha ruwa babu Tafida, ta kira Deen lokacin yana waya da ya gama ya kashe wayar domin shi dai bai da amsar da zai bata, wurin karfe hudu na asuba kamar ance ta fito ta hango Asiyah ta fito kamar daga ɓangaren Tafida, haka yasa ta kara kallon sosai ganin ta ga sun sake rungumar juna, kafin ta wuce inda take zama, tana ganin ya shiga Mota ya bar gidan. Jikinta yana tsuma kawai ta fito da gudu lokacin Asiya ta shiga bangaren da take ta rufe kofarta, komawa tayi ta shirya har karfe daya na rana Asiya bata fito ba, sai wurin karfe biyu ta fito. Ai kuwa Sa'adiyya tayi wuf da ita tayi ta bugata da kasa, tana bata kashi. Sannan ya yakushe mata fuska tana ihu karuwa kwartuwa me bin mijin wasu. Yadda kuka san mahaukaciya haka aka dauke Sa'adi baby akan Asiyah, duk abin ba dadin gani. Da ta samu ta shige dakinta ta kira Tafida tana kuka, shiri tayi amma bata zata wannan me kalar samudawan zata mata mugun duka haka ba, sai gashi ta yakushe mata fuska, sai da tayi kukan bakin ciki, bayan sallah juma'a Tafida yazo gidan ganin har lokacin Sa'adiyya tana ihun sai ta kashe Asiyah yasa Tafida kallon Deen. "Ku sake ta ku je!" Suna barin wurin ya nufeta. Aikuwa farar shaddan jikinshi ta damke wuyar rigarsa da ta yaga har kasa. "gaya min me nayi maka zaka ci amanata, ashe karuwa ka ajiye a gidanka, shine ka hanani hakkina, wallahi ba zan yarda ba muje ka bani hakkina nima na haihu kamar Ummu." "Kin ga nan ba kamar da can baya bane, ko ina akwai jami'an tsaro Please mu shiga daga cikin gidan!" Dake tana ganin girman Deen haka suka shiga rarrashinta da tambayar me ya faru bakincikin ya hanata fadar abin da ya faru sai kuka da rantsuwar matukar bai d'aga Asiyah a gidan ba zai samu gawarta, dakyar Deen ya kwantar da rigimarta, sannan yazo ya ga Asiyah sai da yaji babu dad'i. Yarinyar fuskarta ya kumbura. Shine yake tunanin ya kawo ta wurin Ummu ta yi jinya, Deen yace karya kenan. Ba zai yiwu lokacin da ya samu zai kula da kanshi da iyalinsa yace zai karawa kanshi yan sa'ido ba, don haka yasan yadda zai yi da ita......
#Tafida
#Deen
#Ummu
#Sa'adiya
#Asiyah
#Mahmoud🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


"Kada ki ce zaki dauki burgewa akan nawa rayuwar ni da Yarana muna bukatar Uwa a cikin gidan nan, don Allah ki mana alfarman ki zauna a gida, ina matukar kishinki!" Ya fada yana kamo hannuna, ji nayi kamar zan yi kuka wani ya fada min abin da yake ranshi wanin ma Tafida da kamar wuya gurguwa da auren nesa. Kasa magana nayi ya kai ni wani daki yana faɗin. "Wannan shine dakina, yayi kyau ko na sauya domin dakuna uku ne a nan bangaren, naki dakuna hudu saboda baki da wasu laluran. Bangaren dayan kuma akwai dakuna uku shima kamar nawa." "Duk yaushe ka yi gidan nan?" Hannunshi ya kai gefen fuskata. Yana murmushi ya ce talla aka kawo min lokacin muna abuja, shine na gayawa Deen ya shi kuma ya gayawa Abba. Kafin na turo kudin ma Abba ya biya sai na maidawa Abba kudinsa, amma kin san me? Ko da aka zo saka sunan mamallakin gidan Abba sunanki ya saka." Murmushi nayi sai na kasa magana, ya fito dani zuwa daya dakin yana cewa. "Duk wani abu na gidan Deen ya zuba min su." "Saboda baka da lokaci ne?" Gyada min kai yayi yana jan hancina. "Bani da lokacin da xan zauna nayi ta wannan aikin, shi da Matarshi da kanwarshi Jalilah suka min wannan aikin." Murmushi yayi yana faɗin. "Ina tsoron kada wata rana na juyawa Deen baya." "Idan haka ya faru zai maka uzuri! Domin shi ma'abocin uzuri ne!" Murmushi yayi wanda tunda muka fara zaga gidan shine akan fuskarshi, muna gama zaga cikin gidan ya ce min. "Muje ki ga bangarenki!" "Na gaji sallah isha zan yi na kwanta jikina duk ciwo yake!" "Wai ki ce zan yi tausa kenan?" Ya fada yana kashe min ido daya, parlourn muka dawo muka shimfida abin sallah, ya shiga bandakin parlour yayi alola nima anan nayi alola, shi ya jamu sallah isha da tarawee, muna idarwa na kasa hakuri nace mishi. "Kayi sauka ne kai ma?" Saboda yadda yake jan kira'a. Addu'a ya shafa yana faɗin. "Eh nayi na fara a Nijeriya zuwana Sudan Deen ya saka ni a gaba sai da na hada sittin hankalinsa ya kwanta. " "Gaskiya ya kyauta mana!" Jan kumatuna yayi yana faɗin. "kwarai kuwa ya kyauta min tunda Allah ya haɗa ni da Hafiza!" Janyo ni yayi muka kwanta a parlourn ina jikinshi kwance. D'ago kai nayi ina kallonshi. "Yan mata bar kallona, ni naki ne duk wacce zata zo tow sudinki zata samu;" rufe fuskana nayi a kirjinshi ina dariya. "Naji kamshin turaren Tina a jikinki dazun gaya min yadda kika gudu daga garina." A hankali na warware mishi kome, murmushi yayi yana faɗin. "Yarinyar nan baki da tausayi!" Ya tashi zaune, "Ni sau nawa ka tausaya min?" Na tambaye shi, "kishin yadda Abba yake sonki, yake kuma damuwa da ke yasa ni jin haushi, taya ni da ya dace ya bawa kulawa ya koma nawa Yar mage kulawa!" Ya fada ina kallonshi. "Ni ce ma mage?" Shafa kaina yayi yana faɗin. "Yes ke magena ce, idan ban yi kishin magena ba waye zan yi kishi. Ke magena ni muzurunki!" Ya fada yana rungume ni, dariya nayi ina kara k'amkame shi. "yaushe zaki min dambu ne?" Kallon bakinshi nayi na matsa a hankali na kai bakina, janyo ni nayi na zauna a jikinshi muna fuskarta juna. "Duk lokacin da kake bukata kazo ka ɗauka." Bakina ya kama da hakorinsa. A hankali ya sake yana faɗin. " Ba zata zaki min kuka ne kamar crybaby!" "Dake ka saba ganin kuka a idanuna ba!" Wayarshi ce tayi ƙara ya duba Mahmoud ya gani dauka yayi yana faɗin. "ya dai?" "Tafida dama na kira ne zamu zo da madam ku gaisa!" "Bana nan wallahi idan na dawo zan gaya maka sai ku zo mu sha ruwa tare" "ok na gode amma kana ina ne?" *Ka koyi boye mana kome hatta ni bana bukatar sanin privacy dinka!* inji Deen ya gaya mishi. "Eh tow bana kusa gaskiya!" "Tow ba damuwa, ko kana tare da yar baka ce?" "Me kace?" Ya tambaye shi a fusace. "yar baka nace ko kana tare da ita ne?" "Daga yau kada na kara jin ka ambaci Ummu da wanann sunan, Mata ta ce kuma Uwar Yarana, idan kuma ka sake raina zai b'aci zan yi hukunci." "Tow kayi hakuri na ga dai a bakinka naji!" "Eh a bakina ka ji na tab'a aibanta matarka? Ko na tab'a baka shawara ka cutar da ita?"
"Tafida kayi hakuri ban san ranka zai b'aci ba, amma yaushe ka fara sonta?" Wani ashar ya lailayo ya maka mishi take ya kashe wayar domin Allah ya gani yana bala'in shakkar Tafida. Jifa da wayar yayi, na bi wayar da sauri na dauko ina faɗin. "Ji kamar an ce min yar wuta." Na shiga duba wayar ina kallonshi. "ka godewa Allah da wayar bata fashe ba!" Na mika mishi wayar ina rike hannunshi, shafa bayan hannun nake. "Kada ka damu tun ina Yarinyar na taso da kushen mutane, wannan ba sabon abu ba ne." "Ummu idan baki yafe min ba Allah sai ya kona ni!" "Ba zai kona ni saboda na bawa kare da dokin damar cin zarafinki." Kwantar da kaina nayi a gefen kafadarshi, ina murmushi. Na fahimci Tafida ya sauya sosai, amma tijara yana nan babu abinda ya bari, wurin sha daya na dare ya haɗawa Yaran madara, muka basu, sannan nayi musu wanka da ruwan dumi. Kafin muka wuce dakin na kwantar da su, ban daki ya shiga ya jima kafin ya fito daure da Towel. "Taso muje!" "A'a jeka kawai!" Zuwa yayi ya dauke ni cak, sai ban dakin, ya sauke ni yana faɗin. "Kina tsammanin zaki kwanta min a haka ne!" Kayan ya shiga cire min, yana faɗin. "Malama babu bakin magana ne!" Ya cire rigar ya ajiye can gefe, sai pant da bra! Juyo ni yayi na rufe idanuna. "Cancadi, wannan bra din yayi min kyau, gaskiya ina son irinsu." Ya kai hannu yana ɓalle pin din. Ni dai bance mishi kome ba yana gamawa ya kai hannun kan abin da yake jan hankalinsa. (😡😒 Ni rashin mutuncin Tafida ya fara isata.) Ban iya lokacin da muka dauka a banɗakin ba, amma tabbas naji kamar yau na fara haduwa da d'a namiji, koda muka dawo daki sha biyu ta wuce, a bangaren Tafida kuwa tunda muka dawo dakin, ya makale min domin ba zance wani abu, ina jin labarin ayu amma yau naga makwafin ayu. Ban san yadda xan fada ba, amma tunda ya manne min bawan Allah nan daga ni har shi idanunmu biyu har aka kira sallah farko. Yana makale a jikina yana jin kamar zan kwace na gudu. A hankali yake bin kome tun kiran sallah farko, farko yake jan tafiyar a hankali cikin sanyi da kulawa, ban tab'a sanin halinshi na zahiri ba sai yau, yau ya fito min a mutum dinsa, na kuma fahimci waye shi. Kallon fuskarshi nayi cikin rawan murya na ce mishi. "Yallabai!" Bude idanunshi da suka ji ja ya zuba min. "asuba tayi kada mu rasa sahur!" Kamar dama jiran maganata yake kafin na rufe baki ya shiga aikin da ban san yana da karfin yinsa ba. Ni dai a hannunshi na ji a jikina, sai da na fashe da kuka saboda yadda ya fita hayacinsa haka yasa ni jin kamar Tafida baya mu'amalar aure da Sa'adiyya, domin da yanayi da kuzarinsa ba xai yi yawa kuma ya dauki lokaci haka ba, sai da muka kusan makara ya kyale ni, kasa tafiya nayi domin kafaffuna kamar ba zasu dauke ni ba, haka ya riko ni zuwa banɗaki nayi wanka asalima zama nayi cikin ruwan dumin, a gurguje na fito na samu ya hada min tea mika min yayi da zafi-zafi na sha sannan ya ce min! "Sannu kin ji!" Dake ina bakin gadon daure da towel, kasa kallonshi nayi ina gama sha ya mika min farfesun jiya, kafin ya wuce yayi wanka sannan ya fito shima yayi sahur. Ganin ina bawa Yaran nono ya dawo bayana ya zauna tare da saka hannunshi dukka biyu a kasan cikina. "Ina tumbin?" Murmushi nayi nace mishi. "Ya koma!" Shiru yayi kafin ya sumbaci dokin wuyata. Muna zaune a wurin aka sake kiran sallah, amsa Mufid yayi ya kwantar da shi sannan ya amshi Mufidah ma, kafin ya ciro min doguwar rigana, muka yi raka'atul fijr. Muna idarwa ana shiga sallah asuba, a tare muka yi sallah, bayan mun idar mun jima muna addu'a, da azkar sai da rana ya fara fitowa na rarrafa domin sai yanzu na ji kafar ya min tsami. Gadon na hau na kwanta don wallahi jikina ciwo yake, musamman yadda ya makale yaki kome don rashin kirki, na juya xan harare shi. Ware idanun yayi yana faɗin. "me nayi kuma ake hararana da alamu ana zagina a rai kenan, tow na yafe miki, yar aljannata!" Kwanciya nayi ya dawo bakin gadon ya zauna tare da rike hannuna yana murzawa, murmushi muke sakarwa juna, a hankali barci yayi gaba da ni, shima gadon ya hau ya kwanta a bayana, tare da janyo ni jikinshi. Ban da azumi babu abin da zai hana shi komawa ruwa shi ya san abin da ya ji ya kuma tab'a ya ji. A hankali shima barci yayi gaba da shi, wato ranar Tafida tun kafin yau ya mikawa Deputy koma ya ce mishi sai Monday.


***
A bangaren Mama tunda ta sauka ta kira uwani suka gaisa ta ce mata. "Ina Ummu!" "Yaronta bai da lafiya, sun kai shi asibiti ita da Deen wayarta kuma kin san tun tafiyarta ta saba barin shi a gida!" "Tow Masha Allah idan na samu lokaci zan na kiranku, yanzu lokaci ne na ibada a kwanakin karshe xan mika lamarin Ummu da naku ga Ubangiji, in sha Allah kafin na dawo zan yi addu'a sosai Ubangiji ya kawo miki miji na gari mijin marainiya kin ji Uwanina!" "Tow Uwata sai kin dawo Allah ya baki ikon mana addu'a!" Suka yi sallama. Mama tana son Uwani sosai irin so na gaskiya nan takewa Uwani yarinyar ma tana son Mama. Haka Mama da ta kira Baba Bulama shima ya gaya mata ai Ummu danta bai da lafiya ne, ganin duk bakinsu daya yasa Mama ta yarda, bata san cin amanarta suka yi ba.
***
Karfe daya da rabi na farka, na samu yaran an musu wanka sai wasa suke da junansu, idan ba mafarki ba ina ga har nono Tafida ya ciro ya basu amma dake barci ya ci karfina ban iya bude idanun ba. "sleep beauty!" Make hannunshi nayi ina faɗin. "Kai da Yaranka sai da kuka shanye min nono ko?" Na fada ina gyara zaman rigar jikina. "Ayya sun tashi na rasa yadda xan yi shi ne na gyara ki na basu kowanne ya kama, suna gama sha na dama masu madara suka sha, kin ga har wanka nayi musu!" "Yaushe ka dawo Nanny!" "Taso na hada miki ruwan wanka kin ji!" Tashi nayi na ga yaran aka wani abin wasan Yara. Yana tsaye yana kad'awa Mufidah da take bangala mishi baki, na zo na rungume shi ta baya, karatu Tinah. "Good afternoon My Yallabai!" Wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin. "Qurratul-Ayn! Kin tashi lafiya?" Juya mishi idanun nayi na wuce banɗaki, na leko yana tsaye inda na barshi. "Baby bani jakata akwai brush da toothpaste!" "Akwai sabi na bude mana!" Murmushi nayi na ce mishi. "Ban gani ba!" "Don Allah ki rike wannan muryan taki, wallahi ban shirya yin sittuna ba!" Ya shigo ban dakin ya dauka tare da matsa min. "fita kafin ka karya mana azumi!" Na fada a sanyaye. "Idan aka ga na suma kece wallahi!" Murmushi nayi na rufe ban dakin nayi wanka sosai, sannan na fito, shi da Yaranshi suna can parlour, na gyara jikina kafin na fito, muryanshi da naji da Deen yasa na koma dakin, sai kuma na saka Babban hijab na fito na gaishe da Deen, sai Hararata yake yana faɗin. "Ke bana ce kada ki fito ba!" "Ka ji guntun dan iska, ita Kanwata ce yayar Jalila ce, ka saka Ammah ce ta haife ta dan iska kawai! Ummu ina fatan bai miki kome ba ko?" Ya tambaye shi yana nad'e hannun rigarshi. Dariya suka bani na girgiza kai ina faɗin. "Bai min kome ba! Ya Sadika tana lafiya ta kusan sauka kan yanzu ko!" "Eh wallahi ina kyautata zaton karshen watan ko farkon sabon wata!"
"Allah ya raba lafiya! Yallabai kitchen nake son shiga na maka aikin kafin na tafi!" "Ba fa zaki tafi yau ba, sai wata sati!" Rufe bakina nayi da hannayena, wani irin tsoron Mama ya dirka min kamar an wurgo dutse daga sama. "Ka rufa min asiri!" Murmushi yayi ya ce min. "Allah da gaske wayar mana na saka an sace shi a can Saudiya amma fa za a dawo mata da shi, kiyi hakuri Alhaji Bulama da Babanki sun sani, hankalin Mama ya kasu gida biyu tana ibada kuma kafin faruwar haka tayi waya da Mijinta da kuma Uwani, ki fahimci wani abu ina son mu kasance tare shi yasa na zabi haka amma kiyi hakuri da abin da nayi, wallahi bani da zabi ne ina son na zauna da ke na wasu kwanaki kafin ta dawo Please!" Hawaye ne ya zubo min. "Yanzu kawai don ka zauna da ni sai ka sakata a zullumi bata yi magana da kowa ba." "Mama ba irin sauran iyaye ba ne, Mama tayi magana da kowa kafin na saka.aka dauke wayar amma bari Deen ja ce yarinyar ta maida mata wayarta." Juyawa nayi zan koma dakin ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login