Showing 126001 words to 129000 words out of 241571 words

Chapter 43 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14707

basu bude ba, sai da Ummu ta bar min yaran na rasa wanda zai dauki Yaran ya rike min kowa gudu yake yana komowa gefe, daga nan na fahimci Ummu kaɗai zata zauna da Ni ba tare da ta guji wani abun da xan kara mata ba, a asibiti Hajiya nayi danasanin abin da na aikata. Yaran da aka haife su danyen jego wai Maryam take gaya min idan Uwarsu na zata rike su ba, sai dai na nimo wata mace ta shayar min dasu itama nata yaran sun ishe ta sannan danyen goyo ina zata kai su, Hajiya Maryam ta ce min na rabu da Ummu na kwace Yarana akan idanun Ummun aka yi gata nan da ranta, Hajiya na rasa wanda zan kira na ce ya rike min yaran kafin a gaban rantsarwa na rasa hatta Hindu cewa tayi ita ba zata iya ba, kowa gudun Yarana yayi Hajiya Allah ya sakawa da Deen alkhairi shi daya ne ya ce min, "Muje a kai mata idan bata amsa ba matarshi da Ammah zasu rike Yaran Hajiya ina jin yadda ake cewa Deen ya mallake ni, ba laifi matukar Deen da Haddiya zasu mallake ni tow ni zance don Allah su kara da bita zai zai, yadda ba zan tab'a bijire musu ba" ajiyar zuciya hajiya ta sauke tana kallon kofar dakin da Ummu take. "Hakurin da kayi da naka jarabawar, shine Allah ya baka mace ta gari wacce zata rungumi duk wani matsalarka, Tafida na gaya maka Ummu mutum ce ka riketa hannu bibiyu."


Bayan shan ruwa a daki nayi tarawe, na kwanta. Shigowa tai tana faɗin. "Ummu ya dawo!" Kamar xan yi kuka na ce mata. "Hajiya ni a nan xan kwana!" Kallona tayi kafin ta ce min. "Ummu Hadiyya!" Ta zauna a gefen gadon tana faɗin. "kada ki hukunta shi da laifin da bai san ya aikata ba,kiyi hakuri kada ki kaurace mishi, har yau Ali yaaro ne, ki dauki haka domin sakarai ne idan kika bi na zuciya zai ji ina ma da yana tare da wata macen tunda kin juya mishi baya." Yadda Hajiya take gaya min kuskuren da zan tafka idan nace ba zan koma gidan Tafida ba, sai na tsinci kaina da mikewa ma gyara zaman mayafina, ina ne rungumar Mufid. "tow Hajiya na shirya;" na fada kaina a sunkuye. "Yawwa yar albarka maza jeki Allah ya miki albarka." Haka na fito yana kallonmu, duk sai ya susucewa yana faɗin. "Hajiya idan tace anan zata kwana a kyale ni nima zan kwana anan." Hararanshi tayi cikin harshen kanuri ta ce. "hala baka da lafiya ne ko? Maza ka wuce da ita ka rarrashita an gaya maka haka zai sama muku zaman lafiya ne? Dole sai da rarrashi da ban baki zata manta da wani abu maza ɗauketa ku tafi! Allah ya baku zaman lafiya!" "Amin Ya Allah!" Ya fada, wani kula ta dauka ta raka mu da shi, ina murmushi. "Hajiya baki gajiya ne?" "Har yau gani nake kamar dan Babyn nan da na bari a wata goma sha daya ne a gabana shi yasa bana jin gajiya!" Murmushi yayi yana faɗin. "Hajiya kada ki saka Ummu ta rena na ni!" Duddu ta zuba mishi tana faɗin. "Tafi can ja'iri!" Haka muka fito security suka amshi kular hannunta suna gaishe ta sai albarka take saka musu, muma muka mata sai da safe.


Tunda muka bar gidan na kasa sake jiki da Tafida, ban sani ba ko haka shine irin nawa fushin amma na kasa sake jiki dashi , kuma shima da ya gane bai min dole ba, da muka isa gidan bangarena can na wuce ya zuba min idanun. Murmushi yayi yana faɗin. "Ran yan mata a b'ace yake." Haka ya kawo min Mufidah, ma gyara musu kwnanciya. "yau Ummu ban yi wanka ba, kin lalata ni kwana biyu ke kike min kome yau kuma kin ajiye subsidy din da kike min anya ba karshen rayuwata ba ne ya zo!" "Muje kayi wanka amma ni yau bana son hayaniya ne!" "Tow Yan matana!" Ban dakin na wuce ba hada mishi ruwan wanka zan fito ya tare ni. "Ki taimaka min muyi tare!" "Don Allah!" Na furta muryana yana rawa. "ok ba damuwa!" Na bashi hanya ya shige yayi wankar yana fitowa ya samu har na kashe wutar dakin ina kwance. Saka kaya ba ya hauro gadon ya kwanta a bayana, bai nime kome ba, amma kuma naji dadin haka domin zuciyata a cunkoshe yake da damuwa. Daga ni har shi babu wanda ya samu damar rintsawa saboda a kwanakin da muka yi ko ayu albarka, amma kuma hakan ya saka ni fahimtar wani abu shi mutum ne da baya iya takura maka a da can Tafida bai takura min ba ya bar ni sakaka kamar goyon gwauro . Haka muka kwana.


*Hajiya*
Da sassafe ta saka drive ya Kaita gidan Abba, tana shiga ta samu wanke wanke kowa na dakinsa. Kofar Inna ta nufa anan suka gaisa ta mata Barka da dawowa har suka tab'a hira kafin nan Hajiya ta fara gaya mata abinda ya kawo ta, shiru Inna tayi kafin ta ce mata. "Tow yanzu Yaron nan Sa'adiyya Mairamu ya ce Tafida da Ummu suka mishi duka cikin shi ma wata biyu ya zube, suna asibitin har yanzu Jadda bai ce kome ba. Kasan haka ya kama Yaron Asiya ya mishi duka aka ce fuskar Asiya kamar yayi karo da jirgin kasa, Ni lamarin Tafida bata bani mamaki amma Yaron nan Saadiya yasan Tafida yanzu hankalinta yana kan matanshi Ummu don haka ya dace ayi hakuri da juna amma Hindu ya ce ba a mishi adalci ba!"
Ran Hajiya ya b'aci ta fara faɗa faɗa, abin da ya tashi yan gidan har Abba haka yasa kafin wani lokaci lamarin ya rincabe, domin itama Shuwa ta dawo gida daukar wasu kayan, aka yi ta bata kashi da bala'i.. Hajiya Tayi rantsuwa ko Saadiya ta daina shiga harkan Ummu ko kuma Hindu ta bude mata dakin zawarci domin a tsaye take akan Ummu ba Ummu ta haifa ba amma babu wanda ya isa taka Ummu, kuma Maryam da Rukayya idan suka sake zuwa wurin Ummu Allah ya isa bata yafe ba, tunda ta roke su akan su fita harkan Ummu amma sun ki! Sannan ta bar gidan.
*Ummu*
A hankali labarin na saka Tafida ya daki Saadiya cikinta ya zube, maganar nan har IG da wasu blogspot aka dinga yayyata ni, har facebook ana ta kai zancen, a lokacin Ummu Kulsum da Ummu Rooman, suka fi kowa maida martani, saboda Saadiya tana da kawaye fitinanne irinta, haka yasa suka yi ta saka hotonta da hotunan mu da Tafida, ana ta mana zagin zogale, Ni dai ban san meke faruwa ba sai da Mahirah ta gaya min ita da Aunty Saadika!" Sannan na san meke faruwa, musamman da aka alakanta zubda cikin da cewa don kada su mori tafida ne tunda nayi mishi asiri shi da Iyayenshi. Na sake fita hayacina, domin al'amarin ya girgiza ni kuka kawai nake ina jin kamar zan mutu, ranar da aka ɗauki azumi na ashirin da biyar ranar bakona yazo, haka ya ƙara min yawan rikici da fushi sama da kullum. Shi kanshi Tafida bayi da nutsuwa domin matar Deen ta haihuwa, kwana biyu da suka wuce, kuma ina kai musu abinci, haka yasa nake bala'in jin haushinsa, ranar da muka kai na tsaya waya da Mama da ta kira ni, nake gaya mata matar deen ta haihu na zo kawo mata abinci ne. Muka gaisa komawa gefe nayi na zauna security suna tsaye a gefe can, naji wasu mata suna faɗin. "Eh ita ce wallahi, ita ce ta saka Gwamna a corner ai kin san ba banza ba." Sallama nayi da Mama na juya ina kallonsu, biyu nurse ne sauran kuma irin masu zuwa ganin likita ne ko me oho, takawa nayi har gabansu. Na tsaya tare da murmushi na ce musu. "tazo ta same ni da mijina ne, kun san azabar da na sha kafin ya zama gwamna? Kun san sau nawa na kwana ina kuka? Sau nawa na kwana ina gayawa Allah kuka na? Kun sani ne? Kawai don kun gani da shi muna dariya ba yana nufin jin dadi muka samu ba, ba zaku gane halin da kowacce mace da mijinta ya zama wani abu ta fuskanta ba sai Allah ya kai mazajenku matakin nasara, kafin yau har hotuna an saka akan na gudu waye ta tanbaya me yasa na gudu? Kawai daga labari yazo sai ku zauna kuna bata lokacinku mtseew!" Na wuce , Deen da Tafida da suka zo wurin suna kallonmu, sai bayan tafiyata suka karasa wurin take matan suka mike. "Kuna wasa da abincinku ne ko? Kanwata ce idan na kara jin wani gulma asibitin zan saka hannu a rufe! Munafukan banza." Inji Deen.


Tunda na shiga dakin muke hira da Jalilah da taxo itama. "Ni abincin Aunty Baby zanci!" "Allah baki isa ba, Ummu bani abincin nan kafin wannan mara kirkin su hadu da yayanta su cinye!" Mamanta kuwa sai dariya take mana. "Ina su yan biyu?" "Suna gidan Hajiya idan zan wuce zan amshi su!" Nan muka ta hira sama-sama har suka shigo sannan na tashi zan tafi ya ce min." Na sallame su Matori a motatta zamu tafi,!" "Tow!" Na fada ina jingina sai da ya gama muka fito gidan Hajiya ya wuce muka dauki Yaran muka nufi gidanmu, ganin yadda nake shan kamshi ya tattara ni ya ajiye a gefe, domin ya lura bana sallah tun da ya ga ban bishi sallah Magariba da Isha ba, da asuba ma haka sai ya share ya gane bana sallah ne, a haka ya kira wata Doctor Falmata ya shiga tambayeta me ke saka mata fushi da jin rigima, ta tambaye shi akwai ciki ne ya ce babu ta ce "amma tana haila ko?" "Eh ta fara tun shekaranjiya!" "Shima yana tunzira mace!" Taya ta gaya mishi abubuwan da suke kawo saurin fushi. Ya mata godiya ya kashe wayar.


Ina kwance aka turo min sakon.
_Kamar yadda kika yiwa Sa'adiyya sanadin cikinta In sha Allah Yaranki da kike alfahari da su sai kin rasasu in sha Allah_ wannan abin ya tashi hankalina. Da sauri na kwashe yaran na nufi bangarenshi cikin kuka na zube a gabanshi. "me yasa ka dake ta, me yasa Aliyu yanzu Yarana zasu amshi abin da basu aikata ba Wayyo Allah na, ya zan yi da rayuwata ne, tunda na tsallake maganar mama na biyo ka nake fuskarta tashin hankali.." amsar wayar yayi yana kallon rubutun. Kafin ya kira layin malam Zailani. "Baba Malam!" "Haidara na mutane Madina!" Ya sake murmushi yana faɗin. "Wani abu ne?" A hankali ya kara gaida shi kafin ya gaya mishi kome, dariya Malam yayi yana faɗin. "Ummu uwar matsorata, kyaleta kada ka nuna mata akwai babu wani abu, in sha Allah babu wanda ya isa ya same ku, idan ka ga wani abu ya faru ka saka cikin kaddaranku ce!" Dariya Malam yake yana kara zoyalarsu" domin shi dai bai ga abin tashin hankali ba, don haka ya ce mishi. "Gobe ayi yanka a raba sadaka! Akwai jarabawa bawa a daure a karba da hakuri haka shine cikar imani, Allah ya muku albarka sannan Ali kayi bincike da kyau, ka kuma gyara zamantakewarka da iyalinka haka zai sama kama nutsuwa amma abin sai godiyar Ubangiji!"...........


```All spicess
Jollof mix
BBQ mix
Thyme plus
Garam masala
Curry powder```






```Special zobo
Special yaji
Spice kuli kuli
Miyar kuka
Miyar kubewa
Special daddawa```




```Garin masa/sinasir
Garin alale da kosai
Garin kunun tsamiya
Garin kunun aya```
*Shin ko kun san kayan kamshin da kayan zobo tare da duk wani dangin kayan abincin gargajiya da Ummu take amfani yana samuwa ne ta wurin Shaharariyar me kayan kamshi na AIDA spicess! Ina mata yan yayi ina masu abinci na online kayanku ya tsinke a gindin kaba, ga Hajiya Aida special spicess tazo mana da kayan girki na gargajiya da na zama kai Jama'a wata miyar sai a makota! Na gwada sauran ku gwada ina jiranku! Za a iya samun Aida spices ta wanann number:+234 806 968 1068 Whatsp siyan na gari mai da kudi gida! Hajiya ki zama yar gayu me sauki ne amma girkin yan gayu dai da Aida spicess*🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


"Ka gyara mu'amalarka da yan uwanka, akwai waɗanda ka manta da su a cikin yan uwanka, munyi magana da mahaifinka, yana da kyau ka janyo su a jiki kada ka nuna bambanci a tsakaninsu. Ayi sadaka domin ita maganin masifa ce duk wasu fitittunnu." "In sha Allah!" Inji Tafida, kashe wayar yayi yana kallona da nake kuka kamar an aiko min da mutuwa. "Ya Isa haka, ki je ki kwanta." D'ago kai nayi na zuba mishi idanu. "Kasan me suka ce?" "Gashi nan a rubuce, sannan idan kika razana haka yana nufin wani yana bibiyarki kenan!" Gabana ne ya fadi sai yanzu lissafin ya zo min Mahmoud, hannuna dukka biyu na saka a bakina. Wasu irin hawaye ne suka shiga wasan tsare a idanuna taya aka yi su Maryama suka zo nan gidan? Taya Mahmoud ya san ina tare da Tafida? Taya ya san ina gidan nan? A hankali na mike xan fita bayan na wauci wayata. "Tow me yasa kike kashe ni da wannan shiru da kukan naki ne? Me ye nayi miki da na cancanci kyautar azaba daga gare ki? Kin san yadda nake ji a raina a idan na ga ruwan hawaye na zuba a idanunki? Kin san yadda nake kuntatta a dalilin kukanki? Gaya min meye zan yi ki daina muka?" Ya fada da karfi yana girgixa ni. "Kai laifintu tuni hukuncin laifin nake amsa? Ban san yadda zan gaya maka ba amma da ciwo, da zafi da kuna ka bude idanunka a cikin tashin hankalin da nake ciki, ban aikata kome ba amma saboda mutum daya kullum da zullumi nake kwana saboda shi gani nake wata rana zaka iya juya min baya, nemi rabuwa da kai ba sai don dalili daya dalilin da wata rana zai iya kashe ni har mutuwata don Allah kada ka tambaye ni mai ya faru domin bani da Ansarta, sai dai daga ranar da ka tsinci gawata ka zurfaffa bincike domin tashin hankalin barina da kayi kowani kare da doki yana tozartani!" Da sauri ya sake ni cikin wani tashin hankali, muryan shi na rawa ya ce min. "Me ya faru? Me aka miki!" Durkusawa nayi ina sauke wani wahalallen ajiyar zuciya, saboda kirjina da yayi nauyi." Zan kwanta" na fada ina dafe kirjina, daukata yayi ya kwantar da ni, sannan ya kalli yaran da suke kananan kuka,Sagir ya kira sannan ya kira Kaninshi Sharif a karon farko a rayuwarsa y gaya mishi abin da zai mishi, juya kaina nake ina jin kamar numfashina zai iya daukewa na fara yunkurin tashi. Ta d'aga ni, ya zaunar da ni sannan ya tafi ya dauko min doguwar riga, domin kayan jikina kananunne. Yazo ya saka min a kan rigar sannan ya rufa min bargo, ina kwance a kishingide Sagir ya iso, ruwa ya saka min tare da allurai, kafin ya zauna yana tattaunawa shi da Tafida. Suna cikin haka Matori ya kira shi yace ga baki sun zo, "su shigo!" Hajiya ce Tafida ya dauko domin shi bai san waye zai dauko a wannan lokacin ba, kowa so yake ga bayanshi."Innalillahi wainnalihir rajou! Meke damunta?" Kallonta yayi kafin ya mike yana bata wuri ta zauna ya kalli Sharif. "Sharifai!" "Na'am!" "Ya Ummun da jiki?" " sauki sosai! Na gode sosai!" "Ba kome xan tafi!" "Da wuri haka? Dama akwai aikin da xan baka ko kana da free time?" "Ba damuwa Tafida!" "Yawwa muje!" Haka suka fita ya bashi sakon sannan ya tafi dama sadaka ce da yanka. Ya bar gidan yana godiya, kallon agogon hannun shi yayi kafin ya kira mahaucin da yake aikin yankan gidan Abba ya gaya mishi abin da yake bukata, sannan ya tura mishi kudin da Tafida ya turo ya mishi kuɗin da yawa, ya kuma rubuta a cikin sakon, *Ba yawwa ka sayi kankana da sauran!* Saniyar miliyan daya zai saya Tafida ya tura mishi miliyan biyu da rabi! Kiran wayar shi yayi ya ce mishi. "Saniya daya ka ce kuma ka turo!" "Kada ka damu ka saka mai da sauran sannan ka sha kankana domin nasan tun Muna yara akwai soyayya da kankana?" Murmushi yayi yana faɗin. "Kudin yayi yawa!" "A cikin albashina ne ba a cikin dukiyar al'umma ba!" "Alhamdulillahi Ubangiji ya ƙara dafa maka!" Daga haka suka yi sallama. A bangaren Tafida tunda Hajiya tazo shima ya narke bai da lafiya hararanshi tayi ta mai da hankalinta kan Ummu.
**
*Mahmoud*
A can ranar da yayi yunkurin yin fyade wa Ummu akwai wani abu da ya aikata da ya zame mishi majidadinsa! Kafin Ummu ta fito ya dauki wayarshi mai kiran Black berry, ya saita shi yadda zai ɗaukar mishi duk abin da ya faru. Haka yasa shi duk fadar da suka yi jan towel din Ummu da yayi ya ga tsiraicinta, yana nad'e cikin videon ya san Ummu ko zata mutu ba zata tab'a bashi kanta ba. Amma idan yayi amfani da videon yasan abin da yafi kanta sai ta bashi. Haka yasa kafin ya tura mata sakon ya fara kiranta yana faɗin. "ki duba wayarki na ga baki Whatsp na turo miki wani sako!" Bayan ta gani ya ga babu al'amarin ta kuma a online bayan ta ga sakon, sake tura mata yayi da abin da ya sake jifata cikin zullumi. Murmushi yayi yana faɗin.."Duk inda kika tafi kika dawo Ummu wannan dukiyar sai na tab'a naji yadda kike kema!"


***
*Ummu*
Wannan lokacin nafi sha'awaar mutuwa da rayuwata, sai nake ganin kamar barin umarnin Mama da nayi yasa ni nake fuskarta azabar rayuwa haka. Bude idanun nayi ma ganni a dakinshi. Yana zaune a gefena hannunshi cikin nawa. "Ya jikin naki?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login