Showing 99001 words to 102000 words out of 241571 words
Chapter 34 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
wani shafi na musamman!" "Kai don Allah rufe ba shi muke bukata ba, kawai kamo min wancan dan iskan!" "Yallabai ya kwashe min kome a bankina!" " zan dawo dasu amma ka sani sai ka fanshe su!" Ya koma kan Smarty. "Yaron yana cikin Maiduguri state University." "Taya ka gano haka!" "Wayarshi Samsung series X ce, sannan location dinsa a bude yake." Wasa wasa Sai ga Yaron nan ya kamo dan banza, Deen ya tura sako tun da ya fara bayani, har da hotonshi aka binciko! "Yallabai me yasa ba za a saka hukuma ba?" Inji Jabir Adam, "Hukuma ta kama shi zata mishi dukar mutuwa ce, ni kuma ina son na ganshi ne zai gana da me girma Gwamna! Sannan daga yau kun zama team na musamman! Shugaban Team din kai ne, zaku yi aiki da mai girma Gwamna a office dinsa. Dakyau Mazaje kun yi abinda ya dace." "Mun gode sosai sir!" "Matukar zasu yi aiki a special team! Me ya dace da ku?" "Dark web!" "Daga yau kuyi kokarin saka idanun akan socila median Mai girma gwamna! Kun gane MD? Ku zaku zame masa security ne a duk lokacin da haka ya faru, ina bukatar bayani, albashinku zai fara ne daga ranar ashirin da daya ga wata MD su baka number account dinsu. Ka turo min kamar yadda nace wannan team ya zama sirri ko abokan aikinku bana sonsu sani, idan ka sake naji labarin Dark web ya fito." Murmushi yayi yana faɗin kad'a hannunshi.
Ajiyar zuciya ya sauke yana faɗin, "Yanzu dai lahu a gare mu, mu kame harshen mu da zukatanmu fitar da sunan team din nan daidai yake da ka kwabe wando kayi tsirara!" "Inji MD, dake kusan matasa ne shine magidanci sai suka yi na'am da kome kuma dama basu dayawa su goma ne.
*
*Ummu*
Kiran wayata da turo min sako kala kala yasa na fara jin kamar zan mutu, a lokacin Mahira take gayawa Mama da ta shiga wurinsu domin Ummi ta dawo da Taima, sakamakon jin jajjircewa Mama a kaina, sai ta ga ashe ita ma irin kuskuren Mama.take shirin aikatawa. Shine ta kira Mama take gaya mata halin da ake ciki, suke tattaunawa ita kuma Mahira ta fito tan gaya musu abin da ya faru. Ai kuwa akan kafarta ta shigo dakin ganin yadda na cusa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka me cin rai. " idan suka kashe ki Yaranki ne da asara. Kashe wayar ki bani!" Cikin kuka na nuna mata wayar da na buga da kasa. Dauka tayi ta saka a wardrobe. "Mahaifinki Bai tab'a zina ba,.nima ban yi ba har abada ba zaki yi ba kuma ban zagi masu yi ba addu'ar shiriya nayi musu gaya min me zai saka ki yi? Idan duniya bata yarda dake ba ni na yarda dake." "Nima na yarda da Mata ta......🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
D'ago kai nayi ina kallon Tafida da yake tsaye, yayi wani irin rama, cikin kuka na ce mishi. "ka tafi ka tafi bana son ganinka ka tafi don Allah, mama ki gaya mishi don Allah ya tafi bana son ganinshi." Na fada ina kuka don na gaji, takowa yayi har gaban Mama ya zube akan gwiwarshi. "Nayi mata laifi, na hantare ta, na cutar da ita na wulakantata, nayi mata cin zarafin da ban sha'awan ko makiyana a mishi. Mama gaya min me zan yi don na fashi kaina a wurin Ummu? Nayi kuskure nayi kuskure nayi kuskure nayi kuskure. Na rantse da Allah Sarkin sarakuna, nayi mata kuskure." Bakiɗaya sai jikin Mama yayiwa wani irin sanyi, ta kira sunan shi a hankali kafin ta ce mishi. "yau da ka gaya min kayi kuskure na yarda kana bukatar Ummu, amma kayi hakuri yan uwanka basu bukatarta!" "A'a Mama ni nake auren Ummu ba su ba, Mama ni zan zauna da Ummu ba su ba, Mama don ni daya Allah ya halicci Ummu Mama don Allah ki bani ita a karo na biyu, da kanki zaki bada shaidar haka!" "Kayi hakuri Hajiya Aisha ma tazo nace mata tayi hakuri Ummu Hadiyya bata da baki idan na barta da danginka zasu kashe min ita ne." Kasa zama yayi ya kasa tsaye. Ya kara zubewa a gaban Mama ya ce mata. "Na rantse ba zan kara barin Ummu tayi kuka ba na rantse!" Ya fada yana haɗa hannunsa wuri guda. "Ka je zan duba lamarin!" Kallona yayi ya ce. "na rantse ba zan bari ko kud'a ya tab'a ki ba!" "Kana haka ne domin buƙatar kanka, ka gaya min bani da amfani a gare ka balle ga rayuwaryka, Mama idan na koma ma." "Ki min shiru!" Mikewa nayi na bar su yanata magiya, ban daki na shiga na zauna tare da fashewa da kuka. Abun ya min nauyi yadda yake bada hakuri sai naji ba zan iya jure ganinshi haka ba, a ban dakin na zauna har na daina jin muryanshi, kafin na fito ban samu Mama a dakin ba, alola nayi na gabatar da sallah.
*Shuwa*
Shuwa ce ke kaiwa da komowa take ta kira Malaminta ya fi sau goma daga jiya zuwa yau amma dan iska yaki ɗauka, kallon Sa'adiyya tayi kamar zata zage ta. Sai kuma ta fasa cikin takaici ta rufe ta da duka tana faɗin. "Ni zaki kunyata? Ni zaki ci mutuncina ki tafi har gidansu kishiyarki, zaki tafi ki ci mutuncinta dake yar iska ce ke! Tir da halinki." Ta fada tana haki ranta yayi bala'in b'aci domin bata zaci maganar da Makamin ya fada bogi ba ne sai yanzu. "Na rantse Hajiya Aisha ba zata tab'a moran Yaranta ba, na rantse da Allah musamman Aliyu!" Yadda take cika baki zaka rantse da Allah zata aikata ko idan tayi wani abu zata samu nasara. Ita kan Sa'adiyya kuka take da takaici tana jin tana ganin zata rasa Tafida.
*Tafida*
Dakyar Deen ya kawo shi domin yaki kawo shi, ya ce mishi ya fuskanci matsalarshi ya ajiye batun Ummu, amma ina zuciyarshi ta gama nauyi, kwantar da kai yayi yana dafe kanshi da yake bala'in sara mishi, "Deen ina ga zan rasa Ummu har abada, Mahaifiyarta taki dawo min ita, Deen ya zan yi?" "Kayi hakuri! Abin da nake gaya maka kenan, kowani mutum da nashi amfanin yau ga Ummu da bata da wani amfani a gare ka, kana son ta dawo gareks amma abu ya ci tura, Ummu da kake renawa ita ce Allah ya nuna mata maka itama mutum ce kuma baka san iya baiwar da Allah ya mata ba, Tafida wannan ya zame maka izina." Hawaye na zuba mishi ya share yana faɗin. "Deen ka zage ni ko ba kome ya ji a raina ina da me gaya min gaskiya, Deen a ce kaf yan uwana babu wanda ya damu da halin da nake ciki sai Hajiya da Abba suka damu da ni, kowa kanshi ya sani sai dai nayi musu hidima, Deen ya zan yi? Kowa kansa ya sani."
"Tun farko kai ka nuna Ummu bata da amfani a rayuwarka, da ka ja ta a jiki yan uwanka ba zasu mai da kai abin da suka
mai da kai ba, sun mai da kai wawa kowa ya more ka ya koma gefe, Tafida ina jin haushin yadda babu wanda ya tab'a tambayar Ya Yaranka sai su zo da nasu yaran fisabiilillahi wannan wacce irin rayuwa ce, wato idan na fahimci wani abu kawai babu me son kayi gaba gara ka zauna kana bautarsu. Kayi hakuri yan uwanka ne dole yasa nake magana!" Haka ya mai da shi gidan Hajiya, nasiha da Hajiya tayi ya mishi tana nuna mishi muhimmanci yarda da ƙaddara yasa shi samun nutsuwa ya kwana a gidan, washi gari Deen ya zo daukar shi don yace zai koma office. Haka ya koma office zuciyarshi babu sukuni, idan ka ganshi sai ka zubar da hawaye. Alfarma daya Mama ta mishi. Duk ranar Juma'a ta ce yana turowa ana daukar mishi Yaranshi suna wuni a wurinsa.
Abba kuwa jin labarin abin da ya faru, akan kafarshi ya maida Sa'adiyya. Yace ai babu saki babu yaji, bayan komawarta Hajiya turai itama ta ce Asiyah ta koma gidan da zama yadda zata na taimaka mishi, shi kuwa ganin haka yayi amfani da Asiyah don cusguwa Sa'adi. Yadda yake fita da ita ko ya ce mata ta fito su zaga gidan, wannan abun ya fara damun Sa'adi kamar zata yi hauka. Ai itama ta ji yadda mata suke ji, nan ta fara zirga-zirgan kai kara nan ma Abba ya ce tayi hakuri aiki Asiyah take taya Tafida,ai lokacin Ummu da take mata haka bata kawo kara ba haka ta shanye itama ta koya daga Ummu, bakin ciki yasa ta jin kamar zata mutu, a bangaren Tafida ya rungume lamarin rayuwarshi domin ya fahimci Ummu bata da iko da kanta sai abin da Mahaifiyarta ta ce mata, Hajiya ma tana zuwa kullum ta gaida Ummu sannan ta roke ta alfarman yaushe zata dawo. Bata iya magana sai dai tayi ta wasa da yatsunta Hajiya bata sare ba.
*Ummu*
Zan iya cewa Mama tayi tsaya akan kalamanta, kuma ta tsaya min sai dai a kwanakin nan Mahmoud ya matsa min da zuwa, yau ne zuwan shi na biyu don haka naki fita, Mama tace min. "Ba naji ance Abokin Babansu Mufidah ya zo ba?" "Kyale shi Mama da Yaya Deen ne zan fita wannan na tsani ganin fuskarshi ma!" "Hmm idan muka sako ya kawo ki fa?" "Mama babu sakon da zai kawo min domin." "Ba kyau wulakanci, tashi ki je abokin Tafida ba abin wulakantawa ba ne!" Ban so ba haka na fito na same shi sanye da babban kaya. "Malam me kake bukata da ni?" "Malama Ummu ina sonki, kuma ina me baki shawara ki rabu da tafida domin ba sonki yake ba, amfani da ke zai yi ya wuce abinshi! Sannan ya cigaba daga inda ya tsaya kada ki manta, yan uwanshi basu sonki ni kuma duniyata a bude take na so ki." Murmushi nayi sannan na ce mishi. "Ko mutuwa Tafida yayi bana fatan na auri wani na shi balle kai, don haka ka b'ace min da gani mara kunya mara tsoron Allah, Allah ya tozartaka kamar yadda tab'a min aurena, Allah ya kunyata ka, kamar yadda ka kunyatani." Daga haka na bar shi tsaye ranshi a b'ace. Bai kara zuwa ba sai dai yana yawan turo min sako bana gogeda na shiga tara su domin zasu min amfani.
*
Yan uwan Aliyu sun dauka da zafi, sosai fiye da yadda ake zaton, sai kananun magana suke har da wanda basu daki daya suma sun dauka da zafi abin da ya kawo haka zuwan watan azumi da ya gabato, A tunaninsu Tafida zai sake bakin aljuhu sai suka ga wannan lokacin shiru suke ji, Abba ne ya musu rabonshi, a wannan azumin ya biyawa Hajija da Abba Umara, Sai Inna da Hajja Ganaah ya ce su je can su ta mai da larabawa maza mata, mata kuma maza, sai abincin sadaka da ya kaiwa Mama da kanshi ranar da aka kai azumi biyu, ranar a gidan ya sha ruwa.da zai tafi ya dauki Mufid da bai yi barci ba, ya fita da shi, "Ko zaki zo ki karbe shi!" Kallon Mama nayi naga tana nata hidimar ban amsa ba, sai da ya kara maimaita maganar ta amsa da cewa. "Ka je zata zo" fita yayi ta zuba min idanun. "Ki je!" Tashi nayi na saka hijab din sallah mama na fita, a zaure ya tsaya. "Bani shi tow!" "Zan baki shi don Allah ko zaki raka ni nan wajen ba nisa!" "A'a babu inda zan je!" "Please baki nayi zamu je ki gaida su don Allah!" "Babu inda zaki ka rufa min asiri kada ka ja min fada a wurin Mama!" "Ok na fahimce ki idan Mama bata gari zaki iya raka ni kenan!" "A'a Tafida ka rabu da ni kada ka kara cillani cikin matsala." "Ok ba zaki.je ba!" Ganin yana jan maganar na juya xan koma cikin gidan ya riko hannuna. "Ki fahimce ni ina bukatarki a kusa dani!" "Ni dai don Allah ka kyale ni!" Mika min Yaron yayi sannan ya tako gabana yana fadin. "Allah ya huci zuciyarki! Don Allah ki dawo dakinki!" "Ka tafi wurin Mama babu ruwana!" Haka na bar shi tsaye rashin da zuciyarshi kewa suke. Ya rasa yadda zai yi kamar yayi hauka, haka suka bar gidan washi gari ya aiko Deen da shaidar zuwa Umara, tayi murna sosai amma indai don kome ne gaskiya ba zan koma ba haka ta gayawa Deen ta cigaba cewa. "Ina son Tafida ya gane yan uwan shi basu bukatar Ummu idan ya dage karshe rayuka zasu B'aci kaga ba zan yarda a ci mutuncinta ina gani ban dauki mataki ba, da ace yan uwansa suna sonta da zan hakura."
Murmushi Deen yayi kafin ya ce mata. "Mama a wannan duniyar ma, Manzon Allah har ya gama rayuwarshi dai da aka samu wanda suka ki bin shi duk da sun san gaskiya ya kawo musu, Mama idan kika ce lallai sai wasu sun so Ummu baki yiwa Tafida adalci ba, amma Ummu yarki ce kina da iko akanta amma ki sani a kasa yaushe addu'ar zabin alkhairi muke fata, nasan yanzu Tafida yayi laushi wallahi ba Ummu ba wani ma ba zai wulakanta ba, kuma ba zai tab'a bari a wulakanta ba, Mama zuwa yanzu ta dace ki gane darajar yarki a wurin Tafida shi gwamna ne, wanda ake mishi tayin mata a kullum.amma ya hakura da bukatarshi yana jiran Matarshi daga gare ki, amma a haka ki ce na zata koma ba, duk abin da kika ji ba a kai wanda na gani ba, amma yau naga tarin soyayyar Ummu a idanun Tafida, na ka kauna mara iyaka a cikin kwayar idanunshi, na san Allah yake da ikon sauya mutum ba mutum ba, sai dai a wannan karon Allah ya bawa Ummu sa'a ta sauya Tafida. Ummu ta sauya Tafida ta sauya tunanin shi da duniyarshi, Mama idan kika bincike ta itama tana bukatar mijinta hakuri ne da kawaici irin naki da kika tarbiyyarta da ita a kai Mama ki gane ba kowa ba ne a duniyar nan lallai zai soka wanda suka so ka ka musu halaccin mai da musu soyayyarsu ko da bayawa ne."ba ita Maman ba hatta ni sai da Deen ya kashe min jiki da kalamanshi, a hankali ya mike yana mana bankwana, hankalina ya tashi amma haka na boye damuwata a raina na kuma yi alkawarin ba zan kara zubda hawayena ba, duk yadda tayi daya ne da Tafida zan zauna ba da Yan uwanshi ba.....🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76
Bayan na shigo gidan Mama tayi ta kiran Yan'uwa da abokan arziki tana gaya musu abin da ya same ta na alkhairi. Kafin wani lokaci mu ma gidanmu kowa yasan Mama zata umara, amma maganar gaskiya bata ce kome akan komawa gidan Tafida ba, ban san waye ya gayawa Dangin Tafida kawai sai ga kiran Maryam koda na dauka ina jinta. "Wato asirin da Maman Samha take cewa kun yiwa Tafida gaskiya ne ko? Tow wallahi ku dawo da takardan Umaran da ya baku ko na.baki mamaki." "Maryam ni bana faɗa a cikin azumi idan kun cika yan halak ku hana Tafida yau zuwa shan ruwa, sannan ku ce kada ya zo yaci abin da na dafa mishi domin kuwa zan saka mishi, makale mata, manne mata, dan katafi, mallaka, tare da bita zai zai, ku hana shi zuwa fa domin idan ya sha ruwa zan bashi kafi shayi ma." "Ummu kin ci Abu zan Ubanki tsinanniya yar matsayata!" "Eh na yarda aje a haka, yanzu ya dace ku kwantar da hankalinku duniyar sannu wanku ba zai tab'a cika ba sai da jinin Baburawa, Allah Sarki bawan Allah ya gano inda arziki sai rawan kafa yake, idan na kore shi ta tafi gida likitoci su ta saka mishi ruwa, ku tanadi maganin hawan jini matukar na dawo sai dai wasu baku ba, mtsee!" Na kashe wayar ina jan tsaki, kallon Mama nayi da take tsaye a bakin kofar dakin. "Ni bana son tashin hankali Ummu, Tafida yan uwanshi ba zasu barki haka, fitinarsu tai yawa, ki kira min Deen ya zona fasa zuwa Umaran." "Mama bafa su suka biya miki ba, shi ya biya miki taya zaki mai da kyautar da yayi miki bayan Allah baya son haka, idan yan uwan Tafida ne ba zasu fasa ba haka suke, hassada da kyashi halinsu ne!" "Ke kina son Mijinki?" Kaina a kasa na rasa amsar da xan bata, dai nayi shiru don nasan babu amsar da xan bata. "Nace kina son Mijinki ne?" Ban yarda na amsa mata ba, murmushi tayi sannan ta fita, ajiyar zuciya na dauke ina jin kamar na tsira. Ina kwance bayan azhar ya turo min sakon. _Ummu xan zo na sha ruwa!* gyada kai nayi kamar yana ganina, tashi nayi na nufi tsakar gida. "Mama Babansu Mufidah zai zo shan ruwa!" Juyawa tayi tana kallona. "Ko kiranshi kika yi?" "A'a wallahi ban kira shi ba." "Ki shiga store akwai kayan abinci, ki daura mishi duk abinda ya dace!" Abinka da an kwana biyu ba a shiga office ba, na shiga store din na fara aiki, kamar me domin akwai gas me kai hudu, tunda na shiga da Mufid a bayana, Mufidah tana bayan uwani Yarana sun yi wayo don ma naji Mama tana fadin Allah ya raba ni da kunika domin alamu ya nuna kazamin goyo nake. Wato ina goyo ina period, kafin a fara azumin nan sai da nayi kwana huɗu ina wanka aka fara azumi haka na nufi idan aka kusan gama azumi ma xan kara yi, ina gyara wanke