Showing 84001 words to 87000 words out of 241571 words

Chapter 29 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14731

ya kara kira Mama ta dauka anan ne ya fara jin wani abu yana faruwa, gaishe ta yayi tare da kashe wayar, sannan yana tsaye Deen ya kira shi yana gaya mishi, ga masu taimaka mishi shiryawa su zo, ya ce tow. Yana zaune tunda ya fito wanka yake mamakin meke faruwa. Haka suka shigo security suka musu iso aka kawo wanda ya taimaka mishi ya shirya, abin ka da dan gaye kin saka babban riga yayi asalima kayan kamar dinki senetor outfits aka masa. Yana sakawa kayan suka mishi das, kasancewar kayan blue black ne sai ya fito da Asalinsa da kyawun surarshi. Lokacin da ya fito wani kwarjini yayiwa ilahirin masu take mishi baya, yana tafiya suna bin sa har inda motarshi yake, Deen ya kira cikin sanyin murya ya ce mishi. "Bangaren Ummu a kara gaya mata shi don Allah, ba don na kai ba a saka abin bukatar Yara yadda zasu sake." "An gama You're his Excellency!" "Ka kira ni da Tafida ko Aliyu zai fi min wannan sunan." Shiru Deen yayi yana nazarin muryanshi kafin ya ce mishi. "Kana lafiya kuwa?" "Ina fa Deen na kira Ummu tun jiya Mamanta take dauka ban san me ya faru ba don Allah ka bincika min!" "An gama angon Ummu mijin Sa'adiyya!" Shan mur yayi yana me kallon gefen hanya har suka isa office, cikin satin bakiɗaya bai zauna ba sai ranar Juma'a da Abba ya kira shi, ya tafi har gidan bayan sallah juma'a yan unguwarsu kuwa cika suka yi suna kallonshi. Shiga yayi gidan domin ya saka an tsayar da motar daga dan nesa da gidan ne. A hankali ya zubawa tsohon bangarenshi idanun, yana tuno wasu lokuta da yake zuwa ya samu tana aiki a wurin, haka kawai yaga kamar tana zaune tana wanki, kurawa wurin idanun yayi yana ƙara jin wani abu yana taso mishi daga tafin kafarshi wanda ya janyo mishi kaikayi ba tare da yasan dalilin ba, har tsakiyar kanshi. Lumshe idanu yayi rabonshi da mace tun ranar da Ummu ta fara nakuda, yasan shi ya zungure mata haihuwar, domin yasan wunin ranar tana kwace dakyar take aiki, amma ya nace cikin dare duk da yadda take magiya da gaya mishi cikinta yana ciwo da maranta, ya shafawa idanunshi toka, y biya bukatarshi saboda son rai. "Ya dai?" Mahmoud da ya shigo gidan ya tambaye shi, "lafiya lau!" Ya nufi cikin gidan Mahmoud yana biye da shi, da wasu manya-manyan foodflask, gaida Tafida ake yana amsawa a nutsu har cikin parlour Abba, ya zauna yana gaida Abba da Yayunsa. Mahmoud ya gaida su tare da ajiye a Abba kular abincin yana faɗin. "Gashi nan ba yawa na gidan gona na ne na saka aka yankasu." "Allah yayi albarka, na gode Mahmoud!" "Bari na gaida Inna!" Ya fita waje, Abba ya bi Mahmoud da idanun yana mishi addu'a. Kallon Tafida yayi yana faɗin. "Ya aiki da alumma?" "Alhamdulillahi Abba!" Ya fada yana murmushi. Mika mishi Mug yayi da dafaffen madara yana faɗin. "sha wannan kafin kaci wani abu!" Amsa yayi yana faɗin. "Abba amma naga damina bata yi ba!" "Eh daga Yola aka kawo min." Ya kurba yana gyad'a kai, "Naji labarin ka kama aiki? Tow Allah ya baka sa'a yasa ka fara da hannun dama kenan!" "Amin Ya Allah!" Ya fada, kallon Abubakar da Umar sannan ya ce musu. "Ko waninku zai kira min Saleh da Matarshi da yar rikonsu?" Mikewa Umar yayi ya fita ya kira Samha ya gayawa mata sakon Abba, da gudu yarinyar ta fita, can kuwa sai ga Shuwa da mijinta tare da Sa'adiyya, bayan Abba ya a buɗe taron da addu'a ya ce musu. "Tafida ga Sa'adiyya yau da safe tazo tana rokon na kiraka ka maida ta dakinta, tayi kuskure don Allah ayi hakuri." Gyada kai Shuwa tayi tana faɗin. "ayi hakuri dai Alhaji a kara hakuri ni ban san me yasa bata jin magana ba, amma zan yi magana da Kanina Ubanta ya tsawatar mata domin ai aure ba abin wasa ba ne balle miji irin naki mijin marainiya, yadda take bawa Tafida hakuri tare da Uwarta shi kuwa ya ce musu. "Abba na ji sai dai ku zama shaida duk ranar da ta kara zagar min Yara wallahi na gama aurenta domin igiya ukun zan sake bakiɗaya na gaya muku gaskiya." "In sha Allah haka ba zai faru ba!" Inji Shuwa tana share idanun. Domin yanxu ne ya dace ta janyo Tafida jikinta, ya kara moranshi sosai. Haka Abba ya haɗa su yayi musu nasiha, Tafida yana ta jira yaji Abba ya kira komensu da Ummu amma shiru wannan abin ya d'aga mishi hankali, "Abba Ummu fa?" Ba Sa'adiyya hatta shuwa sai da ta girgiza tana jin wani irin bakinciki yana lallubeta. "Ummu?" Abba ya tambaye shi, sai kuma yayi murmushi yana faɗin. "Zata dawo amma ba yanzu ba, ta baka damar cin amarcinka kafin ta dawo!" "Innalillahi wainnalihir rajoun, Abba." "Hindu ki hada mata kayanta idan zai tafi zasu tafi tare." "Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, mun gode sosai." Ta mike tana hararan inda Tafida yake, tana fita Abba ya wanke shi tas akan kuma ko bayan ranshi bai yarda ya tirsassa Ummu ta dawo gare shi ba sai dai idan ita ta bukaci haka, kuma idan ta ce ba zata zauna da shi ba ya sawwake mata, " idan kuma naji labarin ka kara kiran iyayen Ummu da sunan su mata magana ta koma ban yafe maka ba har abada!" Jin haka ya sashi jan bakinshi yayi shiru, amma Allah ya gani Abba ya mishi iyaka da Ummu, yana zaune a wurin har aka yi mangariba shi kan sa bai san me yake ji ba, bayan isha suka bar gidan ranshi a dagule, ya kira Ummu babu labarin wayarta ma baya shi, haka yayi ta trying. Alhaji Saleh da ya koma bangarenshi ya gayawa Hindu abin da ya faru. Ai kamar su tika rawa, nan ta kara jan Sa'adiyya a jiki ta gaya mata abin da zata yi. Haka suka iso gidan tunda suka fita a motar take hango daya side din da ya sha gyara ko ake kan gyaranshi ta ce mishi. "Can wurina ne?" Wani matsiyacin kallo ya watsa mata ya wuce, haka ta bishi tana faɗin. "Ina magana ka ki kula ni ko na kira Abba na gaya mishi abin da kake min ne?" Banza ya bawa ajiyar ta domin yana mata kallon mahaukaciya wacce bata da cikakken hankali da nutsuwa. Ganin hankalinta daya da na akuya ya tsaya tare da juyawa ya nuna mata daya side din bai kai inda ake gyaran kyau ba, ya ce mata. "Can naki ne." "Ni ne zan zauna a can da bai da bambanci da akulkin kaza, karya kenan wallahi!" Zuba mata idanun yayi kamar zai magana sai ya kuma wuce bangarenshi ya bude da sallama ya shiga, haka ya biyo shi itama, juyawa yayi yana kallonta kafin ya ce mata. "Ko zaki fita!" "Ni ba fa xan tafi can ba, haka kawai ina gani wuri me kyau ace na koma wancan me kama da kangon na zauna." Zuba mata idanu yayi, ya juya ba tare da ya ce mata cikanki ba, haka ya wuce ciki ya rufe kofar, yanayin tsarin gidan akwai babban parlour da ya hada sassan uku, sannan shi kanshi zai iya shiga kowani bangare ba tare da ya fita ba.


A can babban kitchen aka fara shigo da abinci ana jerawa a parlour, lokacin Tafida ya fito alamu yayi wanka ya sauya kayane, waya yake cikin yanayin damuwa ya ce mishi. "Ok kawai ka same ni a office, zai fi dacewa da maganar amma zaka iya zuwa ba matsala. Yana zaune a parlourn aka kira shi ana gaya mishi yayi baki. Ya ce musu. "Su shigo!" Kashe wayar yayi yana kallon Sa'adiyya. "Ki wuce bangarenki bana son Magana!" "Karuwa za'a kawo maka da kake tsoron kada na ganta?" Lumshe idanu yayi yana jin maganar, kafin fitowarsu Abba yasa shi yayi mishi alƙawarin duk abin da Sa'adiyya zata yi, tow kada ya tab'a lafiyarta, ko yayi wani abu idan har ya iya zama da ita tow shi yasan me zai iya mishi. "Tashi ki tafi, ina da baki ne." "Babu inda zani na gaya miki." "Ok!" Haka kuwa ta zauna kyam, yana murmushi ya dauki wayarshi ya kira Number Shuwa. "Hindu!" Yadda ya kira sunanta babu girmamawa yasata harzuka. "Ki gayawa yarki da alamu tana shirin miki kafar angulu don haka ki gaya mata ko kuma wani Babban al'amari ya faru!" "Bata wayar!" Sakawa yayi a handsfree! "Tashi don ubanki yar iska mara kunya, ke wacce irin mutum ce? Kina ganin yadda kowa yake lallaba Ummu ke ba abin koyo ba ne a wurinki! Wallahi na rantse da Allah wani abu ya kara faruwa sai na miki rashin mutunci." Mika mishi wayar tayi tana faɗin. "Zan tafi to!" Ta fita a kofar suka hadu da Mahmoud, dauke kai yayi yana wuce ta, Tsaki tayi tana me kallon Deen da yake murmushi domin shi dai yarinyar nan bai ga wani abun burgewa a tare da ita ba, ikin hura mata kai ya ce. "First Lady, ya ake ciki ne yaushe zaki fara aiki?" Yake tayi domin tana mugun ganin girman Deen ta ce mishi. "Sai lokacin da Habibi ya amince!" "Tow Allah ya nuna mana." "Amin Ya Allah!" Ta juya tana tafiya ita nan ga yar gayu, shi ganinta yake kamar wata yar tasha. Dariya ce ta so kwace mishi ya shiga bangaren Tafida ya samu duk suna kan table shi suke jira, yana zuwa ya kalli Abincin. Fruit ya diba yana sha a nutse yana faɗin. "Ni fa fruit ya ishe ni, ba zan kara cin abincin gidanka ba, sai Ummu ta dawo haka zai saka na zo naci abinci hankali kwance."🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 76


*Mama*
Abin duniya ya dame ta, don haka ta yanken shawaran zuwa biu ko boye Ummu babanta yayi domin yanzu ta fara gajiya da tafiyarta sati daya babu labari idan har Tafida ya cigaba da kiranta zata iya abin kunya duk yadda ya kai da ganin girmanta. Haka yasa ta shirya ranar asabar ta nemi iznin a wurin mijinta, ta wuce Biu gidan Yayarta ta sauka, tana me niman wuri ta huta. "Hadiza meke faruwa ne? Wancan satin Kabiru yazo akan yana niman Ummu, nace mishi bata nan yaki yarda sai da ya shigo da kanshi, abin ya daure min kai!" Zaro idanun tayi zufa na karyo mata. "Da gaske Ummu bata nan garin?" "Wallahi bata nan, domin ni da shi haka muka yi ta bin gidajen Yan uwa da abokan arziki, amma babu labarin Ummu!" "Innalillahi me na aikata? Kada dai Ummu saboda matsalar aurenta ta gudu?" Ta fada tana hadiye yawun tashin hankali. "Ban gane ba, wani abu ne ya faru?" Nan ta labarta mata yadda Ummu take ta kin komawa gidanta, cikin takaici da bakinciki Mama Lami ta rufe ta da faɗa, kamar zata dake tana me nuna mata sakarcinta na kin bawa Ummu damar fadar abin da yake damunta. "Shi ba ga shi can da Matarshi ba, ke da yake sallamamiya ce shine zaki tilasta mata ta koma dakinta, bayan ita tasan Meke faruwa a gidanta." "Tow ya zanyi zan bar Ummu ne ta cigaba da zama aurenta ya mutu, yaron nan binta yake yana bata hakuri!" "Naci Uwar hakuri na kwana, ke dai wallahi baki da hali ace Danka ma ba zaka iya taimakawa rayuwarshi ba, kin zama kyandir kashe kai haska wasu, a gaskiya Ummu bata dace da Uwa irinki ba domin a madadin ki zame mata sanyin idaniya kin zame mata tashin hankali, ki saurare ta ma abu ya gagara. Idan da sauran Yaranki ne zaki saurare su, shi yasa ake cewa Ina son Yarana eh na yarda ina sonsu idan naki su ina da wanda ya fisu ne, shi yanzu ba yana tare da iyayen shi ba ke kuma kin kora naki dawa. Idan Allah yasa aka ganta ta dawo wurin Ubanta ta zauna ai shi bai gaji da ita ba, ke da kike gudun abin kunya kada ace yarki ta kaso aurenta kina bin bayanta, su da suke fadar me zasu baki? Duk wanda yayiwa ƙaddaran wani dariya ya jira tashi ƙaddaran amma karfi da yaji kin saka yarki ta bazama duniya don Allah meye ribar haka? Meye amfanin abin da kuka aikata!" Yadda take fadar sai ga Mama har da kuka wiwi. "Ki gane wani abu duk abin da zaka yi mutane sai sun rena maka, mafi alkhairi kayi wanda Allah zai yarda da kai, kada saboda abin da wasu zasu fada muna tauye hakkin Yaranmu, mutane basu fasa fadar abin da suka yi biyayya ba, tun fil azal suke faɗa kuma haka zasu rayu akan fadar duk abinda yayi musu don haka wannan ya zame miki izina akan masu irin halinki, ita Allah ya huci zuciyarta ta dawo gida, domin ita aka yiwa laifi dole mu tsaya mu jira dawowanta." Mama Lami tayi fada sosai kuma laifin Mama ta gani da Mama bata nuna ta gaji da Ummu ba ai babu inda xata.


Haka lamarin ya rincabe, daga gidan Mama Lami gidan Baban Ummu ta nufa, nan ma babu labari anan Mamawo tayi ta mata faɗa da yar nasiha akan abin da ya faru, wanda bata boye musu ba shi kan Baban Ummu barin su yayi ya koma dakinshi abin duniya ya dame shi, bai taɓa danasani irin na yau ba, yaki yarda ya fito bar Mama ta bar gidan, Mamawo ta shiga dakinshi ta ganshi zaune. "Malam hakuri zaka yi, in sha Allah Ummu tana kyakkyawar hannun."


Kwanan Mama daya ta bar Biu, tun mota take share kwalla, domin har ga Allah tayi babban kuskure.
**
*TAFIDA*
Dakyar suka gama meeting din da suke ga ganawa da mutane da kuma zuwa majalisar jahar da zai yi, babban damuwar shi Deen da ya ce mishi Akwai matsala, domin Deen yana zuwa gidan bai yarda ya shiga cikin ba, Uwani ya kira ya tambayeta Ummu. Shiru tayi kafin ta ce mishi. "maganar gaskiya Ummu babu wanda ya san inda take? Har yau da nake maka maganar nan ana nimanta!" Shiru yayi kafin ya ce mata. "ban gane ba kina nufin Ummu an nime ta ba a ganta ba?" "Eh wallahi wayarta ta bari a gida kawai!" "Yaran fa?" "Hm tana tare da Yaranta!" Shiru yayi kafin ya jinjina kai yana faɗin. "Na gode! Amma gidansu Tafida an sami labarin kuwa?" "Eh tow naji Mama tana cewa an gaya Abbanshi amma ban sani ba ko shi yasan abinda yake faruwa, ni nasan wacece Aunty Baby ba zata tab'a barin mijinta haka kawai bayan ta jima bata yi aure ba, kawai akwai abin da aka mata ne." Lumshe idanu yayi yana gyada mata kai. "Abubuwa dayawa, amma kuma lamarin mata da miji sai Allah, kada mu zake su babu kunya!"da wannan suka yi sallama, tun ranar juma'a yake son gayawa Tafida amma kamar Mahmoud yasan akwai wani abu a kasa ya tattare yana nanikewa Tafida, haka shima Tafida kamar ya zare saboda tashin hankali. Shi kanshi Deen ya rasa yadda zai fuskanci Tafida da zancen kawai sai ya share shi ya nime labarin da kanshi, sannan Deen yayi kokarin bibiyar duk wani tasha da hotonta amma babu labarinta. Bayan sallah isha ba tare da sanin kowa ba, Tafida ya ja Motarshi tare da zuba kashedi kada abishi. Kai tsaye gidansu Ummu ya nufa, babu wanda ya san shine don an dauke wutar unguwar babu haske, shi kanshi bai ji dadin yadda yake tafiya a cikin duhun ba, bai ce kome ba ya nufi gidansu Ummu garin wucewa cikin rashin dace ya fada kwata, Wayyo Allah cikin wani tashin hankali da dimuwa ya mike yana jin wani irin wari da hamami, kamar zai yi amai haka al'ummarshi take rayuwa? Waye wakilin mazabarsu waye dan kwangilar. Haka ya wuce wurin Motarshi yana me barin unguwar, government house ya nufa, yana shiga ya hadu da Sa'adi, bai ko kalleta ba ya wuce side dinsa yayi wanka ya kai sau goma. Kafin ya daina jin warin da yake yi, daki yayi ya fito, yana zama ya ƙara kiran layin Ummu yana jin wani irin abu, har lokacin wayarshi a kashe. Kiran Deen yayi cikin gajiya ya ce mishi. "Deen meke faruwa ne?" Shiru Deen yayi kafin ya ce mishi. "Ka je gidansu Ummu ba zan iya baka labarin nan ba, domin laifinka ne kome Ummu tayi ba, da baka mata abin da kayi ba da yau kana cikin nutsuwa bayan abin da kayi bai isa ba sai da ka hada ta da iyayenta. Alhamdulillahi sai ka je ka ji me ke faruwa nayi ina yina sauran ya rage naka!" Jininshi ne ya fara tafasa yana ji kamar ya bude idanun ya ga gari ya waye amma ina ya kasa wannan hakurin, Kiran Number Baba Bulama yayi cikin sanyi jiki yake gaishe shi duk da rawan da jikinshi yake, "Baba meke faruwa ne? Kusan sati biyu ina niman Ummu bata daukar wayar, don Allah wani abu ya faru ne?"
"Aliyu bamu ga Ummu ba, sannan abin tashin hankalin bamu san inda take ba. Muna da yakinin Ummu tana cikin amincin Allah, amma kafin yau meye tsakaninta da kai da taki dawowa gidanka? Yarinyar nan tana gabana tsawon shekaru bata tab'a kafewa bata son abu ba sai akanka ta ce bata son gidanka ban san me ka mata ba, amma koma meye ba zamu daura maka laifi ba domin kuwa bata gaya mana ba"
A hankali yaji tsoron kada dai Ummu tana rike da duk abinda suka faru ne yasa taki dawowa daga karshe ta gudu,, wani abu yaji ya daki zuciyarshi tunda yake bai tab'a jin tsoro irin na yau ba, idan dai Ummu zata hukunta shi da laifin da yayi mata ne tow kuwa kwananshi ya kare, muryan shi na rawa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login