Showing 42001 words to 45000 words out of 241571 words

Chapter 15 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14706

ba, amma yadda yake gaya min magana yasa na kauda kaina kamar bana jin shi, Sa'adiyya da ta rigamu dawowa ita da Mahmoud suna parlour muka shigo. Daki na shige ban kalle su ba, na kwanta don na gaji sosai. Washi gari da sassafe naji motsin ana jan akwati. Ban fito ba sai sha daya gidan babu kowa na fito daga ni sai riga da wando na barci da na saka da asuba, na fere dankali na fara soya naji ana buga kofar gidan da kirana. "Amarya!" Da sauri ba saka hijab da yake jikin kofar kitchen na fito. "kin manta ne?" "Na gaji ne har nayi barci ." "Shirya mu tafi!" "Ban karya ba!" "No need zan miki takeaway!" Haka na shirya sannan na saka doguwar riga da mayafi na nad'e kaina, muka fita ita ce ta kai ni har inda zamu yi taro na kwana uku. Tana kai ni ciki tace zata kawo min abinci. Ta tafi ta cika alkawarinta, ana fitowa tana mika min abinci. "Kin san na makara muje na ajiye ki!" Haka ta kawo ni gida, "ki zo muci mana!" "A'a na gode!" Ta tafi ina shiga cikin gidan, hadiye yawu nayi domin Mahmoud na gani zaune ya zuba min idanu. Wuce shi nayi na nufi dakina, ina shiga na rufe kofar na zauna tare da fara cin abinci na. "Ummu Hadiyya! Ina son ki bani damar miki bayani yadda zaki fahimce ni, Ummu ina kaunarki ni bana son muyi kazamar alaka ki amince min na tsaya miki, Aliyu ya sake ki mu gina rayuwarmu na jima ina niman mace irinki." Idan gidan zai amsa tow na amsawa Mahmoud ya gama haukarshi ko waje wunin ranar ban fito ba, washi gari da safe ina fitowa na ganshi zaune daga shi sai gajeren wando, dakin na koma na zauna. Can ina zaune na ga abin bana kare bane zan tafi wurin taro na fito nayi abin karyawa haka ya zo ya tsaya a kaina yana ta min magana ban kula shi ba, abin da nayi niyya da ya sake yayi min wani shirme man gyada xan watsa mishi. Sai bai fara ba, har ya bar wurin na gama kome na shirya na fito zan tafi Tina ta zo muka tafi a bakinta najin Aliyu da shugaban kasa sun yi tafiya zuwa Morocco. Haka yasa na fahimci shi yasa Mahmoud yake damuna, kuma da alamu tafiyar ya sati guda ce, don haka tana kai ni nace mata. "Ni naga gidanku yafi kusa da nan, me zai hana kawai na dawo gidanku da zama kafin mu gama taron!" " Da gaske?" "Allah da gaske!" "Tow shi kenan!" Nayi haka ne domin gujewa sharrin shaidan, ana tashi muka dawo tare ta jira na kwashi kayana muka bar gidan, dana san gida daya muke kwana wallahi da ban zauna har haka ba, haka na koma gidansu Tina da zama ban tab'a ganin mutane masu mutuncinsu ba, sun girmama ni da mutuntatta ni, kannenta da Yayunta da matan yayunta kamar su goya ni, abinci kuwa dani ake girkawa Yarbawa karshe ne a girki sai suka ga nima ba a bar ni a baya ba, ai kuwa suka shiga cewa Ayawo a bude mana restaurants a garin nan, a wurin taron ma Ni daya ce yar arewa. Haka muka yi taron kafin muka fara zuwa girki, anan na ga Hajja yar Shehun Borno, ai kuwa ta ji dadi domin tana cikin alkalan gasar. Kowa na gabatar da kanshi nima na gabatar da kaina da inda na fito. Cikin jin dadi ta ce min. "kenan ke yar borno ce amma nasan yan borno turare aka sansu da shi, ba abinci ba." Cikin girmamawa na ce mata. "Dukka muna da shi turare da abinci!" Murmushi tayi tana mana fatan Alkhairi, tunda muka fara gasar girkin nan bana barci, ina kiran Mama tare da tambayarta, sallah dare kuwa na kara akan nada, girkin zai dauke mu kwana sha hudu. Ashe Mahmoud ya kira Tafida ya gaya mishi bana dawowa gida, da kamar zai ce ina ruwanshi sai yayi tsaki yace mishi. "Tana tare da Tina k zauna abinka kafin na dawo!" "Wallahi na zata wani wurin ta tafi!" Tsaki yayi yana faɗin. "Tow ina ruwana taje duk inda yayi mata ita ta sani ba ni ba." "Ban gane ba!" Kamar wanda aka tsira mishi allura ya fara magana, har da rantsuwa ko kato ya gani akan Ummu zai iya dauke kai don ba zai ji kome ba don baya kaunarta gara mutuwa sai dubu da zaman da yake da Ummu. "Tow ka sake ta mana tunda abin ya kai haka." "Ba zan sake ta ba domin Alhaji zai iya tsine min albarka. "Ita kuma bai dame ka ba idan ta bi wani namijin?" "Ita ta sani tunda yar talle ce ta saba da tsalle tsallensu da maza a waje kai ka dame ni!" Kashe wayar yayi murmushi Mahmoud yayi ya nufi dakin Ummu da ya ɓalla dazun, ya dauki bra dinta da pant, dinta ya runguma yana me sakawa a fuskarshi kamshin turaren miski yake shaka. "Kamar yadda kamshin nan yake Allah yasa kome na jikinki haka yake Aliyu na rantse da Allah sai na baka mamaki!"


Kwananmu tara Tina ta gaya min zai dawo ranar, daga wurin gasar gida ta kawo ni, ina shiga gida Babana ya kira ni yana tambayata ya nake da abinda nake yi, na gaya mishi akwai me kai ni, "ki turo account dinki zan turo miki zakkar da na cire ne na ware miki naki!" "Babana na gode in sha Allah zan turo!" Muna gamawa na tura mishi, ashe a can gida Maiduguri ana saka gasar mu bayan sallah isha, yan uwa da abokan arziki, kowa yana gani a tv NTA Maiduguri suna sakawa, wanda hajja ta dauki nauyin shi tare da Maggi star. Wasa wasa Yan uwa Aliyu abin bai musu dadi ba, domin gani suke ban cancanci shiga gasar ba, Shuwa kamar ta mutu don bakinciki, Abba kuwa ana isha yake dawowa yana me zama a jikin tv, yana kallon girke-girken.
Sai bayan Isha Aliyu ya shigo gidan, tunda na ce mishi. "Barka da hanya ka dawo lafiya?" "Da ban dawo ba zaki ganni?" "Ayi hakuri! Masifatu!" Inji Mahmoud yana shigowa cikin gidan, basu wuri nayi na koma kitchen, ina dafa jollop din taliya, ina gamawa na zuba a kula na barshi a kitchen din na shige dakina. Bayan ya huta ne ya fito ya samu Mahmoud ya dauki abinci ya baza a tire, har ta fara ci. "kai bana son iskanci, gidana ne zaka zo ka juye abinci kana ci sonka!" "Ai naga baka damu da girkin ta bane shi yasa na juye idan kana so Bismillah!" Ba musu ya sauka ya fara ci ko cokali bai dauka ba, haka suka cinye ya nufi kitchen ya dauki tukunyar ya juye sauran ya fito suka cinye. Washi gari na fito na kwaba fanke, na koma daki kafin karfe shida ya tashi na koma na fara soyawa ina gamawa na dama kunu na tafi wanka. Nasan Mahmoud baya nan, sai dai ina fitowa na samu an sha kudin saura kaɗan a kasan kofi, fanke kuwa na rantse da Allah daya aka bar min. Raina ya b'aci haka juya abincin nan aka juye tas yau kuma an kara min haka. Haka yasa ban ce kome ba na kira tinah na ce ta zo min da abinci don Allah. Da abincin tazo min muka wuce wurin gasar na karya a motarta.
A hankali na fahimci wannan abin da ake min ya fara yawa, daga ni sai Tafida a gidan bayan shi ko Mahmoud naga baya nan yazo da alamu ya tafi gida, kwatsam Ranar asabar da safe na gama soya kosai, na shiga daki na fito ko ya dauka wanka na shiga kawai na zo na samu ya zauna yana cin kosan da kunu sauri sauri yana gudun kada na kama shi, juywa nayi dakin na barshi ya ci. Yana gamawa na ji motsin ya bar gidan. Tun daga lokacin ban kara yin abu iya cikina ba, sai na yi dayawa amma bai gane ba idan nayi dayawa sai ya kwashe ya tafi da shi, ranar da muka gama gasarmu, da ranar wani kunu nayi wanda ake yi da shinkafar tuwo, madara kilo, kimba, kanunfari, citta, da manshanu da sugar. Domin a cikin kwanakin nan da kuma yi ni daya ce ban maimaita abinci ba, kuma yau da nayi wannan bakiɗaya hankalin Alkalan yayi kaina. Tunda na wanke shinkafar tuwo na zuba da ruwa me yawa, sannan na zuba kayan kamshi kafin na barci yayi ta nuna ina ganin ya nuna sosai na bude na kara dama shi, sannan na kara masa ruwan dumi ya sake. Na rufe shi kafin na dauko garin madaran na fara zubawa ina damawa, sai da ya hadu tas sannan na sauke na zuba sugar na juya shi, sannan na zuba a yan kananun bowl da cokali na zuba manshanu a kai ba jera inda kowa zai dauka. Tunda na gama na wanke kayan na koma gefe ina goge hannuna. A yau aka bamu damar magana tare da nuna mana inda zamu zauna, Alkalai na cin abincin mu, suna mana tambaya. Wani dan china da yake cikin alkalan ya ce min. "Wannan abincin naki ban tab'a ci ba sai yau! Sannan dayawanku da kuka tsallake zagaye na biyu kun sake maimata girki ke kuma tunda kika fara baki maimaita ba me yasa haka!"
Rike abin maganar nayi na sake murmushi, sannan na fadi sunan makarantar Yar shehun Borno inda na samu diploma a girki abin da suka koya mana da kuma ni kaina tun ina shekara goma nake koyan girki , sannan muna yin abincin sayarwa wanda a rana guda muna abinci sama da kala biyar zuwa shiga, haka yasa na kara sanin yadda zan kaucewa maimaici. Sannan na gaya musu iya abincin gargajiya da nayi ba arewa ne, ban dauko wani abu daga kudu ba, masa, dan wake, sinasir, kindirmo da dambunshi, tuwon alkama, fumkasau, dambun cus-cus, biski, da sauransu. Karshe na rufe da wannan girkin. Sun jinjina min hadin aka fara fitar da sunayen wadanda suka yi nasara ban kawo zan yi nasara ba, haka yasa ana gamawa hira damu aka fara kiran waɗanda basu yi nasara ba ana basu shaidar kwarewarsu, a cikin mu goma aka sallam shida, ya rage saura huɗu. Na hudun sha fara kira aka bata kyauta. Sannan aka kira na uku namiji ne, sai na biyu na miji ne, sai gaba na ya fara bugawa. Lokacin da alkalan suka kira na biyu zuba min idanun suka yi yadda na kasa nutsuwa, na rasa waye zai tsaya min a lokacin. Tina ce ta fito wurin ta rike hannuna. Hawaye ya zubo min. "ba gani a tare dake ba, zaki iya na gaya miki yanzu zasu kira ki!" Lokacin da suka kira suna na, kawai ban san lokacin da na zube ina me sujada ba, domin sun tabbatar da cewa idan nayi nasara akwai wasu kamfanoni da zasu dauke ni nayi musu talla sannan akwai gasar girki na duniya a garin dubai wanda za ayi December, ni ce zan wakilci Nijeriya da jahar Borno. Yadda nai sujada nan ina tashi da kuka na tashi Tina ta rike min hannu muka je aka bani lambar yabo da kuma kyautar miliyan biyar. Kuka nake idan na tuna irin kokarin Mama akan girkin. Sai na rasa abin cewa haka aka tashi taron.
"Kai shegen sama ina ka boya ne?" "A wannan lokacin da yarinyar nan tayi nasara ya dace ace kai ne a gefenta, amma Tafida ka barwa Tinah matsayinka, Haba Aliyu Haba Aliyu me yasa ne haka? Me yasa ko ina sai ka nuna baka kaunar Ummu, me tayi maka da zafi haka? Aliyu Allah yana sonka ne ya baka Ummu amma wallahi muna nan dayawa da muke addu'ar Allah ya bamu mata nagari, Aliyu har cikin raina nake son zamanka da ita, yanzu ka ga yadda take kuka tana bukatar wani a gefenta iyayenta ko mijinta, amma ta rasa kowa sai wata da bata hada kome da ita ba zata tsaya mata abin nan duk Najeriya ake kallo haba Aliyu abokan aikina dayawa sai da suka fadi cewa ina mijinta yake ba an ce matar aure ba ce, haba Aliyu, don Allah don soyayyarka da Annabi Muhammad ka saketa kaji ka sake ta don Allah tayi wani auren ko zata samu wanda zai kula da ita!"


Nan ya hau fada tare da gayawa Deen cewa. "Ina da nayi tafiya na bar mata Mahmoud ya na kaita wurin tattarawa tayi ta koma gidansu Tina shi yasa na barta da Tinan!"
"Mahmoud ka barwa Ummu yana kaita wurin ? Tafida anya mutane ne aka haifeka? Kai da kanka kasan Mahmoud ko bunsuru ya ganshi ya barshi shine zaka ce ka bar mishi yar mutane Innalillahi, gara da ta bar gidan Allah ya mata albarka ya bata yadda zata yi amma tabbas Allah sai ya saka mata domin nayi Imani da wanda rayuwata da mutuwata take hannunshi Mahmoud ya mata akunyaci yasa ta bar gidan Wayyo Allah kai dai Allah ya wadaran halinka, duk amintatta da Mahmoud ba zan bar mishi ajiyar mace ba kai mace ko ta kare balle macen mutum ba zan barwa Mahmoud ba, kai bari na gaya maka ko macen alade ba zan taba barwa Mahmoud ba balle macen bil adam wacce ta hada sura da zati irin na Hadiyya wallahi ba zan bar masa ita a gida ɗaya ba ko a mota daya ba zan bari ba, kayi a hankali da rayuwa idan kasan fitar rana baka san inda zai fadi ba.......
500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


15
"Wallahi baka yiwa kanka da rayuwarka adalci ba, kasan waye Mahmoud? Koda yake ba mamaki kai da shi kwarya sama ce ta daki na kasa, amma nasan haka kawai ba zan barwa Mahmoud diya mace baliga ba, idan baka sonta fine amma barin Mahmoud a jikin mace baliga masifa ce kuma na gaya maka gaskiya tunda kai dan banza ne!" "Ya ishe ka zagina!" "Hmm wata rana zaka yi kuka da fatan Ummu ta saurare ka." "Allah ya min tsari kada ya nuna min wannan ranar ya raba ni da mugun ji da mugun gani!" Duk wani masoyina ya kirani a waya anyi min fatan Alkhairi, na rasa inda Deen ya samu number na sai gashi ya kira har da fatan alkhairi. Haka na samu damar shiga cikin mutane, a wannan lokacin na ga kokarin shi na yarda ya kai ni irin tarurruka da aka yi ta yi akan nasarar da muka samu, sai dai abin da ya fara damuna yadda kiri-kiri yake gaya musu ai kawai girkin na iya amma ai kaina babu kome a cikinsa sai yadda ake abinci.
Kusan sai naji abin ya fara fitar min a rai, ya zamana ko taro ne bana son zuwa sai ya saka ni a gaba da dariya. Ana haka kwatsam tafiya ta kama shi Maiduguri, ya tafi da safe da yamma sai ga Mahmoud tunda na ganshi ta window naki bude kofar, yayi kiran duniyar nan naki budewa nayi kamar ma bana gidan. Kawai ya kira Tafida ya gaya mishi ai yazo bana nan. Aikuwa ya fara fada kamar ya shigo wayar.
**
Deen yana jinshi bai ce kome ba, saukar wayarshi yayi ya turawa Mahmoud sako. *Kabar gidan Tafida kafin na shiga wurin Mahaifinsa na gaya mishi yadda kake kokarin niman Yar Mutane!* Sakon na shiga ko minti ɗaya ba ayi ba sai ga kiran Mahmoud. "Zan ci abu kazan-kazan Ubanka Ni zaka mayar dan iska nace maka ina niman matar aure ne!!" "Kai ka sani idan kaso kada ka bar wurin sauran Alhaji zai ji da shi." Ya kashe wayar. "Kai da waye?" "Ni da wani dan akuya ne da yake bin matar wani jaki shine na mishi kashedi ya biyo ni!" "Shi mijin dakikin ina ne da yana zaune wani na niman Matarshi?" "Ai bayi da banbanci da maloho irinka, da ka bar Ummu Hadiyya a abuja har wani yana ce maka matarka bata nan? Anya Tafida tsinuwar Annabi ba zai kama ka ba kuwa? Tow zan gayawa Abba domin iya adalci nayi maka ina tsoron kada wata rana wani ya keta alfarmarta saboda kai " "ban gane ba kana nufin Mahmoud yana niman Ummu?" "Ni na gaya maka? Rufa min asiri wallahi ban isa ba!" "Lashe bakinshi yayi yana faɗin. "Tow shi kenan!" Kwananshi biyu a Maiduguri da zai dawo tare da Deen suka zo saboda akwai wani workshop da zasu yi, tafida yaso ya sauka a gidan amma yaki, ya ce." Zan na zuwa cin abincin dare dai!" Da haka kuwa aka bar zancen, an bawa Tafida kaya amma yaki ikon Allah da Deen ya shiga yin sallama da Abba ya bashi kayan ya zo min da shi. Nayi murna domin kusan kayan Mama ce ta turo min, haka na gyara abuna na cigaba da mana girki. Kullum na kira Babana ko Abba nasiha suke min tare da tambayana ko akwai abinda nake so, nace musu a'a babu kyautar da Abba yake bani har mamaki yake sani jin ga Babana ma haka, Mama itama nayi hakuri na zauna . Baba Bulama shima ba karamin kokari yake ba, abin da na kara fahimtar iyayena da na Tafida suna son mu zauna a inuwa guda amma shi fa yaki sam yaki maganar a zauna.
Haka lokaci ya tura har muka fara kusantar watan azumi, wanda yasani jin kamar nayi kuka don ina son nayi azumi a Maiduguri, haka muka fara azumi ranar da aka ɗauki azumi daya ranar ya shigo dakin ya ce min. "Ke ki shirya Babanki ya ji zan tafi Umara ya biya miki!" "Babana?" "A"a Babana!" Ya fada yana watsa min harara, haka na saka hijab muka tafi aka mana kome har da passport,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login