Showing 234001 words to 237000 words out of 241571 words

Chapter 79 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14709

sani amma bakiɗaya ya daina ganin farin Ummu bakinta yake gani kamar duhu, ya gaji ya rasa me ke damunshi, idan ya fita yana jin sauki kamar ya dawo ya dauke ta su tafi amma idan ya dawo sai yaji gidan ya mishi kunci, kawai ya gaji da ganinta, a watannin bayan mantawa yake da ita, musamman da ya rage shekara daya da wasu watani su gama tenure din nan, bai da nutsuwa baya barci, a lokacin da zai yi barci ya dace yayi sallah sai dai ya tsinci kanshi da barci, sallah lokaci biyar yanzu baya samun yinta, wani bin sai tsakiyar dare yake rama salollin kanshi.....( Wannan labarin rashin sallah akan lokaci na Tafida wallahi naji a bakin malamai uku, Malam Jafar Allah ya mishi rahama, Malam Albani ya fada shima, Malam tijani Yusuf guruntum ya fada dayawa Governor's na arewa basu samun yin Sallah cikakken a rana, duk lokacin da ka rasa sallah babu abinda ba zai faru da kai ba, Allah yana nutsar da duk wanda ya kiyaye sallah, amma an wayi gari sallah tana cikin abin da bamu yinta akan lokaci Allah yasa mu dace)78
Na zata rabuwa da Tafida zai zame min tashin hankali, sai nayi dace Mahaifina bai min magana ba, Mama da ta ji labarin abin da ya faru, ta wanke kafarta ta har gidansu Tafida ta ce maza Abba ya kira mata Tafida ya kawo mata Junior. Ba dauki lokaci ba, sai ga Fanna ta kawo Yaron, amsar Yaron tayi ta bar gidan, tare da fadawa Abba magana daya tak. "Da alamu Tafida bai san kabilar da yake aure ba ko? Allah ya bashi sa'a ya sake Ummu." Abin ya d'agawa Abba hankali, ya kira Tafida muryan shi na rawa ya ce mishi. "yan uwanka, sun kashe mahaifiyarku ko? Ni kuma kana son kashe ni, Tafida wani zunubin nayi maka da kake azabtar da ni akan aurenka? Me yarinyar nan tayi maka ka ce tafi gidans? Laifi ne haihuwar wato? Tafida me nayi maka da zafi?" Yadda Abba yake kuka abin ya tab'a shi rai. "Kayi hakuri Abba!" Iya abinda ya iya fada kenan. Sannan ya ya kashe wayar, tunda abin nan ya faru, bai gayawa ko Deen ba amma ya ce mishi yana cikin tashin hankali, shi kuwa Deen ya cigaba da mishi addu'a. Kuma koda ya tafi wurin Malam Zailani baya kasan iyalanshi sun kai shi jinya Cairo, wannan tashin hankalin ba karamin tab'a su yayi ba. Duk wannan abin da ya ke faruwa, Deen bai sani ba sai da Abba ya gaya mishi. Zuwa Tafida idanun yayi, gashi party dinsu sun matsa lambar sai ya sake fitowa, shi kuwa kamar wanda ake bude mishi kai, ya ce shi ba zai iya ba. Don dole suka tsayar da wani, domin Tafida yaki kuma yaki bada hadin kai.


A wannan yanayin ina gidan Babana Mama ta kawo min Junior, nayi farin ciki amma nayi kuka, ta bani hakuri da daurawa kanta laifi, domin ita take kidanta tayi rawanta, ni kaina na fada mata cewa. "Mama nima ina da laifi, tunda ni na kasa hakuri na jira abinda Allah zai yi damu, na shiga damuwa kika mai dani, a yanzu duk abinda zai faru bana fatan na koma gidan Tafida." "Idan rabon bai kare ba, zaki koma Tafida ba sake ki yayi ba, har yau kina nan da aure shi, don haka ki kara hakuri wata rana kamar ba ayi haka ba." Haka yasa na kasa magana nayi shiru, kwananta Daya ta koma Maiduguri. Na cigaba da kula da kaina da Yarona, yarana suna hannun Fanna bani da haufi akanta, ko ina nan ko bana nan.
---
Lokacin da Asiyah ta gayawa Mahaifiyarta, Tafida ya rabu da ni, murna tayi ta yi tana faɗin ai dama tasan haka zai faru matuƙar Ummu na gidan Asiyah ba zata yi daraja ba, murmushi Asiyah tayi ta ce mata. "Darajar me ya rage min? Bayan na rabawa karti kaina? Bayan na lalata rayuwata ta hanyar cire mahaifata da ya lalace, ina iya cewa Allah ya bani aron rayuwata ce saboda na gaya miki cewa bani da mahaifar da zan haihu, bani da lafiyar da zan ɗauki ciki. Bani da lafiyar da zan zauna ma kula da namiji idan kun yi baka ne don ku raba tafida da Ummu baku min adalci ba, ina lallabashi ya zauna da ni amma kuka saka ya rabu da Matarshi wallahi Allah ba zai bar mu, ba me yasa Allah ya bani aron rayuwa da mutuwa nayi da duk Ummu bata ga wannan tashin hankalin. " "Dalla yi min shiru, yan uwansa da Hajiya Kaltuma suka saka aka korata bani ba ce, ni dai sanadi na musu, inda na dauki wani shirt shi da na gani a wurinki, ranar da yazo baki abinci ya b'ata, kika gaya mishi akwai kayansa ma a cikin wardrobe, kuka saka rigar a washing machine. Kaltuma da Maryam suka bukaci na basu wani abu daga Tafida na dauka na basu tunda ita Ummu ba harkanta muke shiga ba, shine dalilin da yasa ya juyawa Ummu Baya amma ba mu ne muka mata asirin ba, danginsa ne." Dafe kanta tayi da yake mata wani irin juya. "Kin san inda aka yi asirin?" Ta tambayi Mamanta. "Iyace tayi?" "Ko kan gawata kika zo Allah ya tsayar damu a karkashin alarshinsa ya mana hisabi" daga haka ta kashe wayarta, bata tab'a sanin kiyayyar da akewa Ummu akan Tafida ya kai har haka ba sai yau. Maryam ta manta da nata matsalar tana yaki akan matsalar wani.


***
Maryam
Wato matsalar wani me dadin gani, Maryam tunda ta faɗi sai ta raba Ummu da Tafida haka bai mata ba, sai da tayi ta shiga da fita, domin tayi imani da Allah ko zata yi yawo tsirara haihuwar Uwarta da Ubanta sai ta raba Tafida da Ummu, sai aka yi dace Kaltuma tazo mata da the same goal zasu buga suna haka Turai ta kawo musu dauki, wannan abin ya ƙara musu kwarin gwiwa yarda da cewa, tabbas hadunsu zai bada abu me muhimmancin, kawai suka yi ta shiga da fita. Sai dai tunda suka yi wannan aikin kamar sun raba kansu da nutsuwa ne, anyi aikin akan idan Tafida ya rabu da Ummu tow ta lalace tayi ta abin kunya, sai gashi Abin kunyar na farko shine Sa'adiya tana yawon banza wani bin tafita sai tai kwana biyu bata dawo ba, Itama Naziha yarinyar ta lalace. Duk abinda suke Rukayya tana kallonshi domin tun da Maryam ta dake ta, wani kusa ya karceta a hannun damarta take ta jinya, duk da maganin da ake amma hannun kamar ya lalace, yanxu tana ta bin Umar a waya akan yazo ya ga halin da take ciki ta je gidan Abba yaki barinta ta ganshi. Ita kan ta tuba, jin haka Umar ya kira Deen ya gaya mishi. Bai so ba amma haka ya zo ya kaita asibiti aka dubata, sannan aka tabbatar da hannun ya lalace, za a yanke shi ne. Garin Bakinciki da kuka tayi ta tonawa Maryam da Kaltuma asiri. Da wani abin da kowa ya ji sai ya zubar da hawaye. Cikin kuka ta ce mishi."Mutuwa Hajiya ba mutuwa ce kawai ba, abincin da aka hanata ci Maryam tayi ta bata saboda Kaltuma ta gaya mata Hajiya tafi son Tafida da mu, ta cigaba da bawa Hajiya abincin da aka hana tana zuba mata sugar a cikin tana bata kayan zak'i!" "Zaki iya faɗar haka a gaban kowa?" Gyada kai tayi tana kuka. "Me zai hana kuwa? Bayan na rasa hannuna me xan yi da ya wuce na tona musu asiri!" "Tow Ummu fa?" Nan ta gaya mishi abin da ta sani akan Ummu ita kan Ya roka mata gafarar Ummu. Domin tasan tayi mata ba daidai ba, Deen gidansu ya kai Rukayya ya ajiye ta, sannan ya wuce wurin Tafida ya saka mishi record. Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Yanzu babban tashin hankalin, Abba domin ta iya saka Maryam aikata haka tow babu wanda ba zata saka ba." "Eh Abba ya ce a barta, Maryam kuwa ka kyaleta duniya ta ishe ta, an jima zamu tafi gidan Abba mu gama da case din Kaltumah." Gyada kai yayi. Bai san shirin Tafida ba.
** Maryam kuwa tunda ta fahimci abin da suka yi ya dawo kamar kan Yarta ce hankalinta ya tashi, tayi ta bin Malamai a karya amma ina, fatar da mugun bakin da tayi tayiwa Ummu ya dawo kan Yarta, domin yarinyar tayi wani irin lalacewa, sannan a wannan yanayin Itama Hajiya Kaltuma tana can tana niman sadiya a wani gidan yan iska ta same ta, anyi party wai tasha abu bata biya ba, aka mata shegen duka suka watsar da ita waje..haka ta dauko yarta tana fadar me yasa take son kashe ta ne. Har suka iso gidan, anan ta hadu da Maryam ta gaya mata ita fa ta gaji da abin da yake faruwa. Yarta ta lalace.. "Nima baki ga yadda na dauko Sadiya ba ne?" "Ni bansan wannan ba muje a karya asirin!" "Bayan mun jefe shi ruwa me tafiya ya tafi.da shi ko Aljanu ba zasu iya dawowa da shi ba balle mu mutane!" Ai kuwa Maryam ta fara bala'i da masifa, Hajiya Kaltuma ta rufeta da duka, jin hayaniyar yasa Sadiya tashi daga motar ta fito yana maye, hannunta ɗauke da kwalba. Tana zuwa sai wuyar Hajiya Kaltuma. Jini ya tartsatsu a ko ina, Ihun Maryam da zuwan su Tafida a kusan lokaci guda ne, haka yasa shi aka rufa kan Hajiya Kaltuma aka wuce da ita Asibiti, ita kuwa Saadiya dariya take tana faɗin ku bar ni na kashe ta. Itama Maryam Tafida da kanshi yasa security suka wuce da ita Headquarter na yan sanda, ajiyar zuciya Abba ya sauke, ya ce . "Alhamdulillahi Ubangiji na gode da ka kawo min karshen azzalumai." Cikin gidan suka shiga aka zauna ana tattaunawa. Sannan suka ji kome da Rukayya ta ce. "Allah ya kyauta ina Naziha?" "Bamu san inda take ba!" Haka aka yi ta niman yarinyar, amma bata nan babu ita babu labarinta.
***
Naziha.
Abin da take yana damunta, haka yasa ta gudu gidan Ubanta amma ya kore ta, bata tsaya nan ba ta tafi gidan wan Babanta suka kore ta, Unguwar su Ummu ta wuce. Ta same Mama ta ce tazo wurin Ummu ne, Mama ta ce mata ta futa ta bata wuri bata san inda ummu take ba. Rike kafar Mama tayi tana faɗin. "Ba tsoron fita nake ba, idan na fita zan cigaba da bin maza da mata ne, ki kai ni wurin Aunty Baby don Allah! Ko sunanta na kira bana jin ihun da ake yi a kaina don Allah Mama." Kallon yarinyar Mama tayi tausayi da soyayya irin ka uwa tasan ba wayonta ya kare mata Yaranta ba, Allah ne kawai ya kare mata yaranta yasa ta ce. "Wani irin abu kike ji?" "Ji nake kamar ana ce min na.tafi nayi ta bin maza babu wani abu, Mama idan na ga mace sai naji kamar don ita aka yi ni." Ta fada tana kuka, kasa magana Mama tayi, kafin ta ce mata. "Zaki iya zuwa Biu?" "Eh!" Nan ta gaya mata har gidansu Ummu, sannan ta kira Ummu ta haɗa su, kuma mama tayi.mata bayani ai ko Ummu ta ce ta je zata biya kudin motar.


***
Ummu
Tunda Mama ta gaya min Naziha, zata zo naji bakiɗaya jikina yayi sanyi Mama ta kara gaya min halin da yarinyar take ciki, na gayawa Babana, fita yayi can ya dawo ya ce min. "Akwai wani malami a nan baya na gaya mishi ya ce a bari ta zo!" Gyada kai nayi, har bayan isha bata zo ba, sai wurin karfe tara na dare ta iso, kusan yadda yan iska suke kunnen Naziha hujin ya kai biyar, hancinta akwai karfe, gefen bakinta ma haka asalin karamar yarinya ta zama irin wannan abin. Murmushi tayi tana zama, kayan jikinta wasu tsinannun kaya ne. Haka aka bata abinci, ta ci sannan tayi wanka dake dakina ni daya ne, kuma Babana ya gyara min. Ciki ta shiga yayi wanka a ban dakina, na bata kaya ta saka. "Kin yi sallah?" "A'a!" Na ajiye mata hijab, na cigaba da kula da Junior. Bayan ta idar na.bata abinci taci sannan ta kwanta ta fara barci. Bargo na lallubeta da shi, sannan na koma na kwanta.
Wurin karfe daya.
Kamar a mafarki nayi ta jin nishi, kasa ƙasa da karan wani abu kamar ana kiran waya. Lalubar wayata nayi na haska ina jin kar'ar, naziha ce ya bude kafaffunta sama tana goga wani abu a gabanta ban san lokacin da na yarda wayar hannuna ba.. jikina yana rawa, bata fasa ba wani irin ajiyar zuciya take saukewa lokaci zuwa lokaci alamar ta samu nutsuwa kafin naji tana kuka. "aunty Ummu kiyi hakuri, wallahi idan banyi ba, hauka zan yi." Ki shiga kiyi wanka ." Me zai saka na kyamace ta ina.ta je ana koranta, tasan da kowa ta tsallako gare ni, washi gari da wannan abin na tashi, don tun daren nayi adabo da barci, na tashi akan nawa Yaran ashe idan ka haihu bakai ba barci ba kai ba zagin dan wani ba kai ba lalata tarbiyyar dan wani ban fahimci haka ba, sai akan Naziha ban gane haka ba sai da Naziha ta zo da ciwonta, nasan tana son ta bari ne, tana son ta tuba, tana son ta gyara alakarta da Allah, tana son gobenta yayi kyau ne....79
Idan aka ce maka a duniyar nan abubuwa na faruwa kada ka yi mamaki, amma kuma idan ba kai ba ci kowa ba sai Allah ya kawo maka dauki, wannan shine rayuwar da muke ciki, koda gari ya waye Naziha taki sake jiki da ni. Har muka karya, ina kallonta, wanka na saka tayi muka fita zuwa gidan Malam mai almajirai, tunda muka isa gidan, jikinta ya kama rawa tana son ta gudu. Rike ta nayi wani almajiri yayi murmushi yana faɗin. "Ai ba zata iya guduwa na sake ta." Sake ta nayi ai kuwa ya yinkura zata gudu ta dawo ta zauna sai ga zufa na karyo mata, tun ba ayi kome ba, ko kafin ta fara amai,.zuwa wani lokaci Malam ya zo, ya kalle ta cikin lallashi ya ce mata. "Ya na ga daga zuwa kun zubar da makaminku, kenan zaku tafi ne?" Gyada kai tayi ya ce mata.."da kyau! Me yasa duk haka yake faruwa?" "Mahaifiyarta ce ta tura mu jikin Ummu Hadiyya bayan an bamu jini sannan aka bamu gaban taure muka ci!" Gyada kai yayi yana faɗin. "Hajiya kin ji abin da ya faru! Gaskiya ban san yadda xan warware wannan tashin hankalin ba, domin ke aka nufa suka dawo kanta." "Don Allah ka taimaka Baba Malam, zaka iya." "Eh xan iya amma asirin da aka mata na meye me kuke sakata ta aikata?" "Bin maza da mata!" "Saboda me yasa saboda kawai Uwarta da wasu mutanen sun tsani Ummu!" "Alhamdulillahi kinji!" "Eh a karya yarinya ce, laifin mahaifiyarta bai dace ya shafe ta ba." Shiru yayi yana kallona. Aljanun suka fara magana. "Maryam ta shirya ganin bayanki, keda Yaranki gashi yarta tazo wurin ki sani ba iya ita ɗaya ba ne da bata sonki da Tafida, duk abinda yake faruwa da sanin kishiyarki ita bata da yadda zata yi ne, na rantse da Allah. Ni iya aikomu aka yi sai aka yi rashin dace kina sallah dare mun yi mun yi mu shiga jikinki amma abin ta ci tura kuma a ka'idar idan haka ya faru, muna komawa inda aka turo mu ne, wasu sun shiga jikin ɗaya yarinyar ita kuma wannan mun samu tana cikin tsoro da abinda ya faru da ita, sai muka shiga tunda bamu da inda zamu zauna. An rabo mu da matsuguninmu!" Ban kara razana ba sai da naji suna ta bankad'o magana daga abin da suke aikatawa. Tsoron Allah ya shige ni, na kasa ko kwakwaran motsi. Kawai na auri Tafida ake son na lalace shine Allah ya dawo musu kaidinsu ta kan Naziha da sadiya.


Ban kara razana da lamarin nan ba, sai da na ji tana ihu, na kan.saadiya sun dawo kanta suka shiga surutu, da fade-fade anan na fahimci ka ga dai mutum amma kabarshi a inda yake, kafin suka tattara suka bar jikin Naziha, tare da cewa matukar ba aure tayi ba, zasu na waiwayarta domin sun samu yadda suke so a jikinta. Hada magani na Islamic yayi da hayaki, ya kuma bamu shawarar a aurar da ita idan an samu miji, domin aljanun ture suna da matukar biyayya akan abin da aka saka su musamman idan an shayar dasu jini.
***
Tafida yana office aka ji ihun Asiyah, Fanna ce ta fito ta nufi bangarenta, Asiyah itama Aljanun basu kyaleta ba, suka yi ta buga kanta da bango har ta suma zuwan Tafida kuwa kamar jira suke tayi wani tsalle ta cakume shi, tana faɗin. "Duk saboda kai, saboda kai saboda kai kawai, saboda kai Ummu ta fi karfinmu Ummu ta fi karfinmu." Nan ta shiga fadar abinda suka aikata, rike kanshi yayi tashin hankalin da yake ji yafi gaban kwantacce, haka ya kwace kanshi ya bugata da kasa, bai damu da ko ta mutu ko tayi rai ba, fita yayi ya kira Deen, ya gaya mishi halin da yake ciki,ko minti goma ba ayi ba, yazo aka kaita asibiti, daga can ya kira Uwarta ta zo ta dauki Ummu.
Ajiyar Deen ya sauke, yana faɗin. "An sake Maryam fa, Rukayya an yanke hannunta, ka duba su idan ka samu lokaci." Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon gefen hanya ya ce mishi. "Basu ne matsalata ba, a farko na roki Allah ya bani mulkin alumma, amma ban tab'a tunanin yadda xan roki Allah ya bani ikon rike gidana ba, Allah ya so ni da nabi shawarar ka da na saki Ummu da yanzu ban san me zan yi ba, yanzu shawo kan Ummu ta dawo wallahi ban san ya zan yi ba nasan ni mugu ne mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login