Showing 36001 words to 39000 words out of 241571 words

Chapter 13 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14712

"Ina sane da iskancinsu ko kayan abincin da take kawowa Alhaji abinci ware shi ake ba a wanke ake mai da mata yan iskan Yara zaku yi akan abincin ku."
Ni dai ban ce kome ba, haka yarinyar ta dawo jikinta yayi sanyi, ta ce min. "don Allah kiyi hakuri, wallahi Hajiya Shuwa ce tace idan muka kula ki zata saka a kore mu,." "Ba kome." na wuce abina, haka na hada kullun zafin garin yasa kafin wani lokaci har ya tashi, na daura farfesu sai shinkafa da miya, haka nayi masar tass na gama aikin sannan na yi duk abinda ya dace na koma dakina nayi wanka, ina gama wanka ana kawo kayan cefenrm abincin sallah, haka na fito ana shan ruwa na jera musu kayan abincin sannan na koma daki nayi sallah. Ina idarwa Nabila tana shigowa ta kawo min abinci na hada mata abincin cikin gida aka tafi da shi nace mata. "don Allah ki zo na baki aiki mana." "Tow!" Haka ta kai ta dawo na bata aiki kayan yin cake ne da donut. Tana kawo min na bata masar Harira ta kai mata, wato tun da nayi sallah isha na shiga kitchen ban fito ba sai karfe daya da rabi,don har sun watse wurin takwas Deen ya tafi sha daya Mahmoud ya tafi ni daya kamar mayya nayi aikin nan, har da miyar abincin sallah duk rage aikin. Ina fitowa na same su a parlour shi da sa'adi ban kalli inda suke ba na wuce. Daki ashe ina shiga daki ta wuce kitchen din ta dibi Cake da donut. Kamar an aiko ni na fito na samu zata fita na saka hannu na amshi abuna babu kunya ta wuce ta bar gidan don dama shi ya tashi daga parlour shine zata shiga ta kwashe min wahalata. Haka yasa da na maida na rufe kitchen din na wuce daki nayi wanka na kwanta.


Asuban fari na tashi da aiki ina da babban kurfo na fito da shi na daura tuwon shinkafa, haka na cigaba da aiki har gari yayi haske aka fara tafiya Idi. Ban je ba domin aikina amma naji haushi ina tuka tuwo ta shigo sanye da Hijab fari sol, tana gyara zaman madubinta. Fitowa yayi sanye da farar shadda tass, sau daya na kalle su na cigaba da aikina, haka suka fita. Kafin su dawo na gama tuwon na kwashe na dauki na cikin gidan na kai na hada da kayan abincin da nayi da zobo, ni ba waya ba domin ina ji a lokacin bikin aka sace min nawa, ina zaune ina kallon abincinsu Mama. Wurin karfe sha daya sai ga Mudan ban san lokacin da nayi ta murna ba. "Kai Aunty Baby sai kace mun shekara bamu hadu ba." "Kira min Mamana!" Kiranta yayi muka sha waya har da kukana. "Kasan Allah kafin gwamnan a wurina sannan bari na duba daki zan baka kudi ka sayo min waya kayi welcome back din layina. Sai ka kawo min jibi." Haka na hada mishi abinci ya ci na bashi dubu sha hudu. "Kai Aunty Baby ana rike waya irin su Samsung kina kawo kudin me torching." Shigowa suka yi da abokanshi. "Sannunku!" Ko inda Mudan yake bai kalla ba, "Ni dai ka saya min koma meye." "Gaskiya Aunty Baby ba zan saya miki waya me torching ba." Ya fada yana mikewa, a lokacin muke gaisawa dasu Mahmoud, na koma kitchen na hada mishi abincin Mama. " Ni dai don Allah ka sayo min sannan akwai katin dan kasana a wurin Mama kayi welcome back da shi!"


Sai da ya tafi na koma cikin, na fara kawo musu abincin ina jerewa sannan da na gama na koma dakina na barsu, dake ina gamawa nayi wanka na saka atamfa me ratsin fari, "Aunty Ummu kizo Abba yana kiranki!" Farin mayafi yafa fito, idanun Mahmoud yana kaina. "Amaryan mu na ga kwalliyar nan, kuma na biya da sahalewar Tafida!" Tsaki tafida yayi yana faɗin . "Banza ka daina haɗa ni da yarinyar nan!" Yana gefe bai ci abincin ba, kallon Mahmoud Deen yayi, yaga yadda yake murna. Sai yaji ya rena Tafida sam bai san ciwon kanshi ba. Ina shiga cikin gidan kowa na tsaye Abba ya cewa Nabila. "Dauko mata kujera!" "A"a Abba nan ma yayi!" "Zauna dai!" Haka na zauna ina kallon namar. "Wancan na daron naki ne, ke daya da danginki. Babban daron kenan. Wannan kuma na tafida ne duk yadda yaso yayi da shi. Sai akwia kai da fata za a gyara a kawo miki. Salamatu bata goran sallah ta da kuma na tukwaicin abincin sallah." "Ai kuwa Alhaji yarinyar nan bata jin bata nime wani a tayata aiki ba kawai sai ganin tuwo muka yi." Inji Hajiya Kaltuma tana fada. "Mace ce ai, kuma ta nuna daga inda ta fito ba a koya mata son jikin irin nasu Farida ba!" Inji Hajiya Salamatu."Allah yasaka da alkhairi na gode Abba, na gode Mama na gode Umma. Sannunku da aiki sannunku da kokari Allah ya jibanci alamarinku!"
"Amin Ya Allah!" Duk suka fada , na mike aka biyo ni da kayan naman nan, na nuna inda za a ajiye min na koma daki na cire kayana na shiga aiki da chopping butch. Ina cikin aikin ya shigo kamar zai yi kwallo da kayan shi da sa'adi ce, "saka hannu ki dauka muje." Ta tafasa bance musu ba balle ta kone, suka dauki namarshi suka tafida da shi. "Don Allah ayi ya yi kyau domin zan tafi da shi ne wa abokan aikina!" Sai anan na fahimci. Ashe zai koma ne, ni dai nawa na raba kashi uku na soya nayi dambu, sauran naman na saka a firji kwana biyu aka dauka ana aikin layya ranar na biyu Mudan yazo min da na gida, na zuba mishi nashi da na su Mama har da danyen nama, ya kai musu na bada nasu kulsum.
Su Deen sun shiga na zuba musu nama da cakes, tunda Deen yaci tafida yazo musu da wanda aka mishi har ya fara dumm, ya cewa Tafida."waye yayi maka wannan aikin? Gashi yana son lalacewa!" "Bari nima dazun da naci naji ya fara yauki!" Na flat din gaban Mahmoud ya daukan yana sakawa a bakinshi. "A ina kuka samo wannan?" "Ji dan iska Ummu ce ta bamu!" Mahmoud ya dauke naman ya zuba a aljuhun wandonsa, cire namar yayi ya bar musu a wurin yana jan tsaki, wani dabara ce ta zo mishi ya juye na ta ya tafi da shi ita kuma.tasan yadda xata yi dasu. Bai kuma bin ta kansu ba. A daren da zai tafi ya shiga kitchen din ni nazo shan ruwa na samu yana juye min nama na. Inda yake ban kalla ba dake babu kunya a ranshi ya juye washi gari ya bar garin babu ko sallama.


Bayan tafiyar shi na fito na dauki namar nan don har dambun ya juye ya tafi da su ban ce kome ba tow me zance nasan a can zai rabawa abokai ne tun da naji yana faɗa mata. Haka na nutsu na gyara wanda aka mishi ya dawo hayacinsa na juye a roba na bashi zan na miya da shi. Kannena sun zo min yawon sallah, har a cikin gidan anyi musu alkhairi. Bayan tafiyarsu na cigaba da yadda na saba.


Bayan tafiyarshi na samu sassauci, domin dai babu shi. Amma yan uwansa mata sun tsane ni. Wata na daya cur Mahaifiyarshi tazo. Wayyo Allah na matar nan tana da kirki. Tunda taxo a cikin Yaranta babu wnada ya tab'a kawo abinci domin ta ci gashi tazo da kanwarsu Sabirah. Haka na ware mata kulla masu kyau, ina saka mata abincin. Yadda na daukaki lamarinta yasa ta kasa boye soyayyarta a gare ni,.ban san waye ya gaya masa ba amma ya kirani ta wayar Mahmoud ya kawo min wayar, yadda yake zagina da cin mutuncina bai saka ma jira ya kashe wayar ba. Na kashe na bawa Yara suka kaiwa Mahmud din. Kwananta goma ta tafi, bayan na mata abinda na ga xan iya domin Hajiya Kaltuma ta gaya min cewa. "Ki kyautata mata don Allah, tana bukatar kulawar Yaranta amma kamar wanda aka shiga tsakaninsu ai kin gani Dakyar suka zo ganinta." Na kwana ina juya lamarin nan tausayinta ya cika min rai. Shi yasa da zata tafi har da turmin zani na hada mata kala biyu nace mata inji Tafida ya kira wai na bata. Murmushi tayi irin na manya yasan Yaranta basu bata ba, tasan Yadda ya kullace ta ba zai bata ba. Amma haka tayi ta godiya, na bata dubu goma sabira na bata kala uku a wanda Mama tayi min, tow Allah na tuba Ina da sutura kamar me, domin Sif dina har babu inda xan saka kaya.
Haka muka yi ta turawa sai da na kwashi wata hudu sannan ya dawo a lokacin abincin mu ya kare saura kaɗan ne. Dama baci yake ba ciyar da mutane ya bani damar nayi da shi. Sai da na gama nazarin yadda xan yi zan gaya mishi da ya fito zai fita nace mishi. "Hmmm kayan abinci ya kare fa!" Kankance idanunshi yayi yana faɗin. "ina ruwana? Ni na ajiye ki? Idan kin so ki yi sata ko ki bi maza ki ciyar da kanki, ko kuma ko tafi wanda ya aure min ke ya baki abinci." Duk yadda nake kokarin danne zuciyata amma sai da tayi rauni na zuba mishi idanu. Kafin na koma daki na zauna....


#500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


13
Na jima kafin na iya hadiye kome na kira Mama, domin nasan tana da kayan abinci. "Ummu Hadiyya!" Kuka ne ya tunkuro min na d'aga kaina sama ina hadiye kukan na ce mata. "Yaya Aliyu ya bani kudin cefane, shine nace a ware kayan abinci!" "Ina kika kai kayan garanki?" Ta tambaye ni a rude, hadiye kukan nayi na ce mata. "Kin san yana can Abuja ne tow ya ce shi ba zai dauki kayan garana ba, gara ya bani kudi na saya mishi. Kin ji ba wai na kayan garan ba ne, Yawwa mama ki hada min da garin dan wanke." Jim tayi kafin ta ce min. "Shi kenan zan turo miki sai ko bani kudina don kin san bana son wasa da dukiya. Yawwa akwai kudinki da Babanki ya baki na rike amma dai naga rikewar bai da wani amfani a wurina Uwani zata kawo miki."
"Tow shi kenan!" Na fada mata, a hankali naji damuwata ya kare, amma kuma yanayin da nake ciki bana jin damuwar zata kare min. "Assalamualaikum! Aunty Baby gashi nan!" Ta ajiye min abinci murmushi nayi nace mata. "Nabila na gode, yau bana jin dadi ne shi yasa ban daura abincin rana ba." "Ayya haka ne!" Daga nan ta fita, ina zaune a wurin domin kunya nake ji na fada kayan abincinmu ya kare, wurin La'asar sai ga Mudan da Uwani sun kawo min kayan abincin. "Ku saka min a kitchen, zan kai store!" Zama Uwani tayi tana faɗin. "Aunty Baby baki da lafiya ne?" "Zazzaɓi nake ji!" "Gashi inji Mama!" Ta mika min kuɗi. Na duba dayawa na cire dubu uku na bata,.sannan na bawa Mudan ma ina kokarin mikewa Tafida ya shigo yana jin su Uwani na gaishe shi ya ki amsawa. Kamar ma bai ji ba ya wuce. "Jaraba kai Mudan muje kafin ya fara mana koran kare!" "Allah ya yaye miki!" Na fada ina rakasu har bakin gate, na dawo parlour na ganshi zaune a wurin kudina yana kallona. "Kin fara satan ne?" A hankali na kai hannu xan ɗauki kudin ya rigani dauka. "Ko ba tambayarki nake ba?" Nan ma shiru nayi ina Kallonshi. "Bakinki baya magana ne?" Na juya xan tafi ya ja rigana sai da ya yage ta gefe. Mikewa yayi yana kallona, hadiye yawu nayi na ce mishi."ka kyale ni don Allah!" Tura min kuɗi yayi yana faɗin. "Karbi kazamin kudinki waye ya sani ko abokan hulda ne suka turo!" "Zaka maimaita haka a gaban Ubangiji!" Buge min baki yayi yana hayayako min. "Wallahi idan baka daina kokarin dukana ba zai gayawa Alhaji domin ni ba baiwarka bace!" Na rab'a gefenshi ya finciko ni ya dawo da ni gabanshi. "Idan na zane ki uban me zaki yi?" "Ai kaji abin da Mamana ta fada maka zata ramin, ka gwada ka gani." Ganin yadda nake maganar da kwarin gwiwa yasa shi ture ni na fadi kan kujerar parlour. Haka na cigaba da ganin kayan bakinciki domin kuwa saboda mugunta karo yawan mutanen da suke zuwa cin abincin yayi.


Na rasa yadda zan dakatar da haka amma ina kamar zuga shi nake, haka nake hakuri da shi, ban tab'a gayawa kowa ba domin nasan wata rana sai labari. Ana haka Mahmoud ya sako ni a gaba da zuwa, sai ya san Tafida ya fita zai zo zauna a parlour wai yana kallo, sannan duk abin da zan dafa haka zai rena ya ce shi abu kaza zan yi mishi, na gaji da haka ranar ya same ni akan tsini ya ce min. "Ummu yau ina son Dan wake da dafaffen kwai!" " ba xan yi ba." Na fada ina me shigewa dakina, domin nima yau taliya naci d miya, tunda na shiga daki ban kuma fitowa. Sai da naji ana doka kofar dakin na fito ina kallon Tafida ne. "Zo ki wuce ki daura mishi dan wake da kwai!" "Garin Dan wake na ya kare kuma baka yi cefenen ba!" Na fada ina me juyawa dakin ya ci kwalar rigana ya fito da ni. "Wuce kafin na tattakaki!" Buge hannunshi nayi, Mahmoud din ya ce. "No kyale ta na saka Sa'adiyya zata min!" Yadda ya fada a sanyaye zaka ɗauka wani abin arziki ne, a kan idanunshi Tafida yayi ta cin mutuncina. Yana gamawa suka fita na koma dakina, haka yayi ta hada ni rigima da Tafida shima bai gane ba, ga cikin gidansu an hade min kai idan na cire Hajiya Kaltuma da Hajiya Salamatu, suma harkan su ya ishe su basu san meke faruwa ba.
-
"Yanzu kai Tafida tsakani da Allah zancen Mahmoud ka dauka har kake iƙirarin sake Ummu saboda taki gaida Umar ko Abubakar ko?" "Ban gane ba?" Ya fada idanunshi bude. "zaka gane idan lokacin ya kure maka, ka rabu da Mahmoud ka kula da matarka Tafida wallahi idan ka gyara alakarka da Ummu sai kafi kowa moran aurenka Tafida kada lokaci yayi kace kana niman masu tayaka." "Bana son haka Allah ya min tsari da niman wani alfarma a wurin wancan yarinyar baka mummuna me kamar da yan kasan wuta." "Eh tafi wnada ya gagarawa Iyayenshi alfarma ya zauna da ita haka!" "Deen gorin tarbiyya xaka min!" "Na gaya maka ka dakatar da shigar Mahmoud gidanka ka sanshi kuma kasan waye shi akan mata, ni wallahi ko kai da na yarda da kai zai yi matukar wahala na kyale ka kana shigar min gida. Balle har ka zauna da sunan kallon ball. Manzon Allah yayi alƙawarin baya tare da mazan da basu kishin matansu idan kana son ka zama daya daga cikinsu Allah ya baka sa'a "
"Yanzu kana nufin zaka iya hana ni shiga gidanka?" "Wallahi ba zan tab'a barinka ka zauna a parlour mata ta ba, domin kai abinka ka rena baka dauke shi da daraja ba shi wani yake son ko yayya ne ya samu."
"Ina ruwana kai idan taso na shiga gidan na same ta da kato akanta wallahi zan iya kauda kai na wuce." "Wacce irin kiyayya kake mata ne Aliyu?" "Kawai na tsaneta ne daga kasar zuciyata." Mamaki ya kama Deen jin furucin Aliyu, "tow Allah yasa kada kayi tunanin cutar da ita!"tsaki yayi ya bar office din Deen.


Satin shi biyu amma na sha azaba kamar idan ya tafi kada ya kuma dawowa. Bayan tafiyar shi da kwana biyu ne sai ga Aunty Maryam da Rukayya, ita Aunty Maryam bata da matsala sosai kamar Aunty Rukayya, tunda suka shigo muka gaisa sama-sama suka fita sannan suka bar min yaransu ban yarda nayi abinda Yaran zasu yi kuka ba. Yadda na saka musu abinci haka suka yi kaca-kaca da parlourn ban damu ba kayana ne dai na kwashe kada a lalata min. Haka suka gama harkansu suka tafi cikin gidan. Ban san me ke faruwa a cikin gidan ba, sai da Abba ya turo a kirani na je na samu an taru a parlournshi na gaida su. Na nime wuri na zauna. "Alhamdulillahi." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya fara da addu'a, "Daman abin da yasa na tara ku Aliyu bai da lafiya, na tura dan abokina ya duba shi yana asibiti." *Allah yasa ya mutu!* wani bangare na zuciyata ya furta haka, kamar ana ji ni, na rike bakina. "Ummu zaki tafi ke da Umar." Ban iya d'ago kai ba, haka na cigaba da sunkuyar da kai har aka gama taron. Kafin na tafi Hajiya Kaltuma ta turo min kayan cefene. Nayi miya sannan na soya kaza tare da dambu nayi mishi, sai cin-cin da cake. Domin ita ta sani nayi haka ina tsoron kada nayi ace wani abu. Haka kwana biyu a tsakanin muka wuce abuja, da gaske bai da lafiya abin mamaki Deen da Mahmoud mun same su a can, jikina yayi sanyi domin yadda ake son shi. Bai da lafiya sosai, domin baya gane wanda yake kanshi. Deen ya ce na zauna a asibitin ba zan koma gida ba, shi ya kai min kome na gida. Tunda Mahmoud ya ga na zo yaki tafiya ya tare a gidan baki daya a tunaninshi zan dawo gidan ya samu kaina. Sai aka yi rashin dace Deen ya harbo jirginshi, haka na cigaba da zama har tsawon kwanaki biyu, ya fara dawowa hankalinsa. Sannan suka bar garin tunda ya ganni yake wani haɗe rai. Ni kuwa ko a jikina tunda na fahimci ni ne baya bukata. Kwanansa uku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login