Showing 219001 words to 222000 words out of 241571 words

Chapter 74 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14744

tsinkewa. "Eh Asie!" "Allah ya mata rahama!" Tace a hankali, sannan ta sauka a motar ina kallonta tana share hancinta, dake Tafida yana tare da Deen, bin bayanta nayi har parlournta. Kwanciya tayi tana nishi, jini na fitowa daga hancin. "Ko zamu je asibitin ne?" "Ko munje basu cire min ciwon ba, ko mun je ba zasu hanani tafiya ba, don Allah kada ki tsane ni kin ji. Ya Aliyu ya gaya min cewa yana tausayina , amma so da kaunar da yake zuciyarshi naki ne ke daya akanki ya san so da ciwo!" A ranar na fara jin juyayyen kalmar so da ciwo! A madadin ciwon so ba shi da magani! So da Ciwo! Na furta ina kallonta. "Kin san ma'anar haka?" Rike hannunta nayi nace mata. "Bar ma'anar nasan So da ciwo! Domin bakiɗayanmu muka raye ne akan so da ciwo! Ina sonshi amma ina cutawa, yana sona amma bai gaza fuskartar damuwa da ciwon rai ba. Kina son shi amma ciwon sonshi ta kassaraki, bayan kina ganin kamar damar ki ce na ki samu soyayyarshi. Amma ciwo ya shiga tsakanin."
Murmushi tayi tana girgixa kai ta ce min. "Ban yi miki musu ba, amma na samu abin da nake bukata na kuma samu kulawar da nake nima, Aliyu ya damu da ni ya kula da ni, ko yau na tafi na samu mutum daya a gefena. Kin san ma'anar so da ciwo? Duk soyayyar da za a baka matukar makusantanka basu baka damar shaƙar iskan yanci ba, har abada ba zaka tab'a samun soyayyar nan ba, daga farko rayuwata an samar da ita ne ta wani lalataccen matsaya, na rayu lalace gatar da nake da shi na rasa shi, domin na lalata kome, da hannuna na kassara lafiyata, saboda soyayyar da ake min babu Cutarwa a cikin shi a baya fa, amma a yanzu ina son a soni, a kula dani, a ririta ni na zama matacciyar tsiron da bai da banbanci da babu shi!.idan soyayyar da Hajiya tayiwa Tafida shine zunubin da yake bin shi, lallai na yarda so da ciwo, idan soyayyar da Tafida yake miki shine zunubinki lallai so da ciwo, idan soyayyar da Mahaifiyata tayi min! Shine zunubina lallai so da Ciwo, ciwon da bashi madadinsa sai mutuwa....
*So da Ciwo*72


"Kin more kin ji dadinki, Allah ya baki mahaifiyar da ta san kukanki tasan damuwarki, haka yasa na kara fahimtar baki san yadda rashin nagartaccen asali yake ba, zunubi zunubi ce imma ka aikata laifin, imma wani naka ya aikata ni dai na san na aikata kuma na yarda ni mai laifi ce,na cutar dake kuma na zalince kaina da hannuna, sai dai ina jin kunyar na d'ago kai da sunan ki yafe min, don nasan ba yafe min zaki yi ba." Wannan maganar ta daure min kai ta sani jin wani irin abu ya tsaya min a rai, tausayi da kaunar Yarinyar ya dirsu a zuciyata, ban sani ba ko don ban iya tashin hankali yasa nake jin kamar na yafe mata ko don duniyar bakiɗayanta ba kome ne a cikin ta ba, yasa naji ba zan iya kallonta a cikin wannan yanayin ba, tayi ta fama da ciwo yasa na mike da sauri. "Zaki tafi amma kada ki ce mishi bani da lafiya!" Ta fada tana murmushi, nima gyada mata kai nayi, na fita. Sai da na shiga bangarena na fashe da kuka, me yasa? Me yasa? Me yasa kome yazo min a hakan? Nayi kuka nayi kukan da har ya shigo ya samu ina kukan, zama yayi a kusa dani yana kallona. "Kin shiga bangaren Asiya ne?" Gyada kai nayi ina kallonshi. "Haka take fama da jinya?" Murmushi yayi yana me jingina kanshi yana kallon sama. Buga kofar aka yi bai yi magana ba, sai Ni ce nace a a shigo!" Rukayya ce da Maryam, sunyi zuru-zuru, a wulakance suke kallona. "Tafida kofar bangaren Hajiya a rufe yake." Tashi yayi ya zuba musu idanu. Murmushi yayi ya ce min. "Ki shiga dakinki, ki duba wurin kayan Yaran nan, na wurga key din bangaren Hajiya kawo min sannan ki gyara kayan da kika ga a wargaje!" Gyada kai nayi ina faɗin. "Tow!" Na tashi, kallonsu yayi da kyau ya ce musu. "Hajiya itace kashin bayan zamanku a nan, ni ban haife ku ba ni kaninku ne, idan kun shiga ku tattara kome na ku, ku koma gidan Abba kada ku yarda gobe na ganku a gidana domin Hajiya na hakura yanxu bata nan bana jin zan iya shaƙar iskar da kuka fesar." "Tafida!" D'aga mata hannu yayi yana faɗin. "Kin manta ne? Ko kin manta kuna tsaye akan kalamanku na, kashe Hajiya nayi saboda mulki?" "A'a wallahi bani ba ne Yaya Abubakar ne!" "Wallahi sai kun bar min gidana!" Yadda ya kafe haka har na kawo key ya amsa ya cilla musu, ya kuma ce musu. "Awa daya ku bar min gidana ko na dauki doka a hannu!" Jin haka yasa Maryam ta juya yana kallona. "Zaki gani!" "Ba zan ga kome ba, domin kullum ina da mai Addu'ar Allah ya kare ni, kiyi kokarin fahimtar kema Uwa ce, idan kika cigaba da bina da sharri zaki shiga uku!" Daga haka na juya ina kallonshi. Haka suka fita bakiɗaya ma sun fita a rayuwarmu,domin a ranar suka bar gidan. Suna isa gidan Abba suka gaya mishi Tafida ya kore su, shima ya ce musu. "Idan har Tafida zai iya koranku saboda masifar da take bibiyarku tabbas gidana babu masaukinku, ku tafi na yafewa Abubakar ku, in sha Allah sai Allah ya saka mishi sai kun gani a ƙwaryan cin tuwonku!" Haka suka juya suna ji suna gani suka bar gidan. Tsohon gidan Hajiya da take Unguwar Abubakar suka koma akwai kome a gidan, abinci ne babu kawai.


***
Mahmoud kuwa bakiɗaya ya rasa lafiyarshi, domin kuwa yana raye ne amma bai da banbanci da mamaci, Ammyn kan Lagos, domin abin ya so tab'a mata ƙwaƙwalwa, shi yasa ta tafi da ita. Jinya Ammyn take mai ciwo da tashin hankali domin kuwa a cikin yan fashin nan bakiɗaya babu wanda bai kwanta da ita ba sai Hakim, sannan babban tashin hankalin shine cututtukan da suka mata dabaibayi, domin bayan ciwon infection me mugun ciwo, ga cutar zamani da suka daura mata. Haka ya tab'a garkuwar jikinta. Ammyn bata da lafiya sosai,yadda Hamdiyya take kuka domin gani take kamar Mahaifiyarsu ita ta amshi zunubin mahaifinsu da Mahmoud, sune da laifi ita ce da amsar hukuncin, wannan tashin hankalin kawai aka bata da shi amma bata iya ko barci. Haka tayi ta jinya.


Mahmoud da aka sallame shi, barin garin yayi domin idan ya cigaba da zama zai iya mutuwa, don koda yaushe gani yake Hakim Ummu bata gama sake shi ba, akwai abin da zai kara samunshi.
**
Ummu
Bayan wata uku
Wanda yayi daidai da shekaran daya da hawan Tafida mulki. Duk da kuwa yana fuskartar kalubale, amma da sauki duk da yan adawa ne, sai dai lokaci zuwa lokaci ana sake rumors akan shi ɗan shan jini ne. Yau da ya cika shekara daya a mulki wanda yayi dai-dai da cikan Yarana shekara daya suma, Asiyah ce da ta matsa aka dauko su tun jiya da Yaran sabirah, da suka dawo bayan rasuwar Hajiya. Suna wurinta domin tana bala'in son Yara, akwai wani abu da na kara fahimta Asiyah yar gayu ce idan ka cire shiririta, akwai wasu tarurrukan da yaje tare da ita, kasancewarta girman yola ce kuma yar gayu ce, yasa idan tana magana da turanci wanda yabi jikinta da harshenta sai ka ɗauka yanga take, a yadda ni da tafidan muka sakata a rayuwarmu sai yarinyar kome ya zo mata da sauki, kamar ba kishiya ba, domin ko zuwan mahaifiyarta tayi ta zugata tana zaginta, amma taki yarda da abinda Mahaifiyarta ta kawo mata kayan asiri kallon kayan tayi tana faɗin. "Ni da bani da wani burin da ya wuce na koma ga Allah ina mai takawa da tsoronshi zan.sake komawa baya? Mamana nasan cewa mahaifina boka ne, amma kuma bana jin zan kara yarda na sauka akan hanyar da Aliyu da Ummu suka daura ni, ki tafi da abinki bana bukata don Allah koda zaki ji labarin Mutuwata ki min addu'a, ki ce Mahaifina ya tuba ya daina abinda yake yi." "Ni zaki gayawa kin daina ? Bayan ta wannan hanyar aka samo miki tafka, lallai Asiyah ni zaki kunyata? Tow na barki da su Tafida!" Ta saka kai ta bar gidan, babu nadama a tare da Asiyah ta kawo kayan ta jibge a gabana. "Kin gansu duk kayan mallaka ce, ni da nake jin na kusan komawa ga Allah me zanyi da wannan? Kai ina a konasu!" Ta kuma fitar da shi waje ta bawa security mata da suke gidan, aka tafi aka kona su. Zuwa tayi tana kallon cikina. "Allah yasa Little me ce a cikin nan naki!" Ta fada tana murmushi. "Koda yake na ji, ance suna yana effecting ko? Kawai a saka mata suna Amatullah!" "Saboda kawai ranki ya miki dadi a saka Amatullah!" "Eh mana y'ata ce idan namiji ne a saka sunan Abbanmu na biu!" Tun lokacin rasuwarsa da yazo bayan addu'ar Uku Ya kawo mana abubuwa yarinyar nan bana sani sai dai ya ce min takira shi, haka Mama take gaya min Asiyah tafi Sa'adiyya domin tana kiranta. Kai hatta yan uwana sai da ta saba da su, karewa idan muka dauka cewa take . "Nifa idan na mutu ban yarda wani ya tab'a gawata ba daga Mama sai Aliyu kema ban yarda da ke ba, kada ki min bita da kulli dukar kabarin kishiya." Murmushi nake mata, Asiyah mutum ce kawai na kasunta bai hanata farin ciki ba, duk da a wanann satin ta dawo daga Abuja ganin likita, sam taki yarda ta nuna min sakamakon har shi mijin, kuma da ya tuntubi Likitanta cewa yayi a barta kada a dame ta.
Bayan la'asar cikina ya fito sosai, na fito a hankali na ga anata gyara gidan ana kawata shi. "wai me ake yi ne?" "Ana shirin birthday dinsu twins ne. Tana tsaye sai bayani take tana nuna inda bai mata ba. "Allah gani gare ka." Na furta yana tsaye kamar wata model sanye take da wani palazzo sai riga da ya wuce cinyarta amma an kame shi daga cikinta, dama gata kamar kara. Ta saka hular da ya dace da kayan takalmin kafarta baki ne, Dora tana mata bayani. "Madam idan kin gama bayani a dauko miki madaranki!" Juyawa tayi tana faɗin. "Me ya kawo me ciki nan? Ni bana son ana show a bata mana dress code dinmu da wani abu nan kamar tulu!" "Kinyiwa kanki mtseew!" Na ja tsaki ina barin wurin, kafin karfe shida biyar an gama, ni ban san lokacin da aka shirya taron ba, ashe tun tana Abuja tayi kome nata, shima Tafidan da yake ya zama irinta har da bata kuɗi don barna. Ana tsaka da hidimar Fanna ta shigo da jaka, wai ashe har Tinah aka gayyata. Sake baki nayi ina kallon munafunci irin na mutanen da nake tare da su, tinah bata shigo min ba ta tare a wurin Asiyah kasa hakuri nayi domin naji haushi ina shiga na samu har da su Mama da Hajiya Salamatu da Inna da Hajja Ganaah, sake baki nayi ina faɗin. "Yau naga ikon Allah, sai ku zo ku tare anan!" "Ke Malama Bama gayyar mai ciki oya je ki sauya kaya, za a zo a miki kwalliya ko Tinah!" "Hey Aunty Baby!" Juyawa nayi na bar parlourn suka saka dariya. Ina komawa na zauna a parlourn, naki tashi da kanshi ya zo ya zauna a wurina. "Duk wanda kika ganshi a wurin, tausayinta yake ji, domin duk ta gaya musu bata da lafiya! Kuma zata iya mutuwa kowani lokaci. Ummu kada ki ji haushi kuce zata rabaki da kowa ne a'a' ba haka ba ne, kin san a yanzu haka tana raye ne da magani da kuma ikon Allah, shine dalilin da yasa taki gaya min. Ummu kin ga takardanta da aka turo min dakyar." Ya nuna min har da stamp da aka mata na lamar kowani lokaci zata iya tafiya ya barmu!" Sai na rasa meke min dadi. Da taimakon shi na sauya kayan jikina amma naki makeup, sannan na fito muka hadu a wurin, an kashe kudi itama ta kashe kudi, don ma Tafida yana zuba mata kudi duk wata aka bashi albashinsa, haka kawai idan ya samu allowens zai bamu kudi masu bala'in yawa. Sannan a wata ukun nan da muka yi na kara fahimtar waye shi da kuma me yasa ka a gaba, al'ummar jahar Borno suna alfahari da shi, anci an gyatse sannan ta fitar da wani takardan da ta ajiye tace musu. "Wadannan takardun nawa guda uku ne, daya na same kyauta ce a lokacin wani raka oga da nayi Abuja, ta sanadinsa na samu, shi yasa zan barwa marayun da nake rike dasu. Koda bana raye na su ne. Wannan shi yake bani duk wata za a kai gidan marayu a taimakawa Yaran da suke gidan Marayun nan. Wannan na uku tsawon rayuwata na tara kudi, amma wannan na barshi ne wa Yarana Mufid da Mufidah. " tashi tayi tana kallon mutanen wurin, akwai dadi da farinciki ka samu wanda zai rike hannunka, musamman Miji kamar Tafida. Sannan ka samu kishiya Irin Ummu Hadiyya da gaske kafin ka samu zai bada wahala, amma for me is okay domin nayi dace." a hankali take magana tana faɗin. "A cikin wata uku da muka yi bayani rasuwar Hajiyarmu, a Write story about my life da mijina da kishiyata! Amma wannan ba karshen bane wannan shine mafarin! Ummu tayi kokari amma Mahaifiyar Ummu itace jarumar, sai dai behind the corner akwai Deen da wasu bayan Deen, nayi fatan da zan rayu na tsawon shekaru sama da hamsin zan bada labarin mijina da yadda na aure shi, by connection, nayi rayuwa a past dina, amma a present dina bana tunanin xan yi dogon rayuwar da nayi a baya!" Yadda take magana tana dariya yana saka mutane nishadi, amma ga ni da Tafida tsinkar mana zuciya take, d'ago kai tayi tana faɗin. "A duniya bana tunanin za a sa samu wanda yayi choosing good path kamarshi, ba koyi sadauakrwa da juriya, idan ka ji mutum ya ce hakurinsa ya kare dama can ba hakuri yayi ba, i learn this words ta wurin mother in law na, Hajiya A'isha Aliyu, Maman Ya Aliyu, Hajiya ta ce min, Ummu tana da mutunci sosai, Ummu tayi mata abinda Yaranta basu mata ba, a lokacin da tarasa kowa Ummu ta mata adalci ta kula da ita kamar na. Tace kiyi hakuri da Ummu bata da yawan magana amma zata kula dake kamar nata, Ummu ta koyawa Tafida yadda zai kula da kowaye a tare da shi, shi Yasa yau muke moran shi wannan aikin Ummu Hadiyya ce, ta amma ba dukkan ba ne aikinta Mamanta ita ce abin jinjinawa, ina mika godiyata ga Mamanmu." Kasa da kai Mama tayi tana share kwallan da yake zuba mata .. (Allah da gaske ni gaskiya labarin nan kuka yake saka ni 😭)73


Asiyah tayi magana masu nauyi, dariya tayi tana faɗin. "Ya Aliyu ka rike Matarka, domin itace sirrinka, dangi irina da sauran lady's like me muna kyasa namiji readymade ne saboda bamu san yadda Matarka tayi kokarin gina gidanta ba, we are always looking for what we want not what she build! Hmm, ba zaku gane yadda mace take kokarin gina mijinta da gidanta ba, kawai mu wurga musu rayuwa mu shiga." Murmushi tayi ta d'aga kofin hannunta. "Ina maka fatan Alkhairi bakiɗaya rayuwarku. Ina sonka daga baya amma nasan bai zama dole ka biya ni son da nake maka ba, amma kuma ina jin kamar na samu yanci. Na gode sosai da zuwa taya mu murnar zagayowar ranar haihuwar yan biyu da cikan Ya Aliyu a shekara daya na zama gwamna!" Sannan ta koma ta zauna aka cigaba da cin abincin, kowa yana yabawa da halinta. Kallonshi nayi da yayi shiru yana kallona. "Yan mata!" "Na'am!" Na amsa ina kallonta, tana hira da su Mama. "Allah ya bata lafiya mai daurewa!" "Amin Ya Allah!" Ya fada yana rike hannuna muka karasa har inda suke muna gaida Mutane. "Tafida kai da Asiyah kun kwace min Yaran ko?" "A'a Asiyah ce wallahi!" "A'a' kaji tsoron Allah Daadi kai ne kace na dauko su kana missing dinsu ko Aunty Baby!" "Ba ruwan Ummu cikin wannan maganar ke kika dauko su!" "Ni ban dauko su ba, a tambayi Matori gashi can!" Aka yi ta dariya ana hira cikin nishadi, kafin aka watse. Shi da ita suna rungume da yaran ni kuma na ja cikina nayi bangarena, wanka nayi na kwanta. Shigowa dakin yayi yana kallon yadda na kwanta. "Ina suke sun kwanta ne?" "Eh sun kwanta nace bari na zo nayi miki sai da safe!" Murmushi nayi ya sumbaci cikina." Yana shafa cikin ya kashe min hasken dakin ina kallonshi ya fita, na lumshe idanuna, barci yayi gaba da ni.




Washegari.
Tinah tazo muka wuni da ita, sai dai kuma naji dadin yadda ta bawa Asie kyauta da abubuwan karuwa ya min dad'i. "Aunty Baby ya dai?" "Me nace?" Na tambaye ta cike da kosawa yarinyar nan bata ji ina sake mata zata fara saka ni magana. "Wai tambayarki nake kawai ya kike jin gullin babyna!" Tsaki nayi bance mata kome ba, domin bana son Magana ita kuma kamar dama niman hanyar surutu take yi, don haka ta cigaba da tsokanata, ina mata murmushi Tinah dariya take, kwanan Tinah uku ta koma da tsaraba me yawan gaske, sannan muka cigaba da kula da Asie wacce kullum sai ta saka mu a damuwa domin kullum gaya mana tafiya zata yi, don Allah kada wani dalilin mara tushe ya lalata zamanmu. Bana ce Asie tafi ni kaunar zamana ba, amma tabbas ina son zaman gidan mijina duk da kuwa nasan waye shi, kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login