Showing 207001 words to 210000 words out of 241571 words
Chapter 70 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt
yasa Mama shiru. Har kasa ya durkusa ya gaishe ta yana kallon inda nake ganin na mike zan tafi cikin daki ya ce min. "Ya jikinki? Kina Ansar magani kuwa?" A fusace nayi cikin daki, "Ke Ummu!" Mama ta daka min tsawa. Dawowa nayi na tsaya musu a kai kerere! "Zauna baki ji yana gaishe ki ba ne?" "Meye matsalata da shi? Yayi harkan gabanshi nima nayi nawa!" "Allah ya shirya ki!" Sannan Mama ta amsa mishi suka gaisa kafin ta bashi labarin gobe xan tafi maganar gasar abincin da za ayi. Murmushi yayi yana faɗin. "Allah ya bada sa'a yasa a dace." "Amin Ya Allah!" Kanshi a sunkuye yana kallon kasa. "Mama ina su Mufid?" Aasiya ta tambaye ta, kunnena yana waje ban san lokacin da nayi tsalle na fito na kwashi Yarana, duk da basu ganin fuskata, amma na watsa musu harara. Na wuce dakin da Yarana. "Tow Mama zamu wuce!" "A gaida gida!" "Gida zai ji" daga haka suka fita. "Baka ce mata kome ba, ka koma ka ce ka mai da ita don Allah!" Bai kulata ba har suka isa motar, tana rokon ya koma cikin gidan ya ce ya maida Ummu amma yaki kulata.
Wato ni Tafida zai wulakanta ya dauki min Matarshi zuwa gidanmu? Don gani yar iska, bakin cikin da na kwana da shi Allah kaɗai ya sani sai na rama wulakancin da ya min don wallahi ba zan yafe ba, wannan ai cin fuska ce. Kwafa nayi na juya ina me jin karan takaici, sako ne ya shigo min ina dubawa na ga shine. Kamar na ruga mishi zagi amma wannan ba tarbiyyar Mama ba ce, duba sakon nayi naji kamar na saka hannu a kai na fasa ihu. Lallai ma Tafida ya rena min hankali. *Kiyi hakuri! Wallahi ban san zuwanta zai b'ata miki rai ba da bamu zo ba, yarinyar tayi nadama!* Bakincikin wannan sakon yasa ni tura mishi da cewa. _Kaje Allah zai saka min tunda cin mutuncin bai isa ba sai ka kawo min matarka gidanmu na gode!_ sai kuma ja rushe da kuka, domin wallahi raina yayi bala'in b'aci, kuka nake ƙasa ƙasa, sai gaza fahimtar kishi ne ko takaici ne, domin Tafida ya bala'in b'ata min rai, haka yayi ta turo min sakon ban hakuri amma naki kula shi karshe kashe wayar nayi, ranar nayi barci cikin wahala. Washi gari ina tashi na nufi inda kayana yake na dauki towel naje nayi wanka da alola, ina fitowa sallah na gabatar na zauna a wurin har gari yayi haske. Sannan Mudan yazo ya wuce da ni Airport. Abun mamaki a airport din na same shi. Tare da Asiyah da alamu suma tafiya zasu yi, babu abinda ya dame ni da su. Abuja muka nufa tare. "Aunty Baby!" Banza nayi musu na cigaba da abin da nake. "Kin ga ki kyaleta bata son magana!" Ina lura da ita ta wani kanta a kafadarshi, dauke kai nayi ina jan tsaki kasa ƙasa, a wurina yau ta zame min ranar b'acin rai, domin dai abin da suke yi yana bala'in sosa min rai. Tashi nayi zan wuce ban daki , kallonta yayi ya ce mata. "Gyara zaman ki zata wuce!" Ba musu ta gyara na wuce abina, koda na shiga ban dakin sai naji ina ma da na zauna anan ɗin wallahi har mu sauka. Can dai na hakura na dawo, sai dai nayi ba zan kara saka idanun akansu. Domin kada Tafida ya dauka kishinsa nake ji, koda na dawo na zauna ba yabo ba fallasa ta min magana na amsa sama-sama, sannan na zauna har muka dauka tana yi tana saka ni cikin maganarta, bana biye mata sai dai na share su, muna sauka na samu tinah tana jirana, yadda na tsare ta da idanu sai da ya bata dariya "Iyawo Aliyu irin wannan muzuran!" Share ta nayi kawai na wuce gaba tana bina a baya, d'aga musu hannu tayi, domin su da sauran lokacin tafiyarsu ko ni zan je na huta ne saboda ba zan iya zaman airport ba. Muna isa na lura da yadda take dariya na gano chat suke da Tafida hade rai nayi ina hararanta. "Ka ga kada ka hada ni fada da Iyawo!"
Haka tayi ta min tsaya ina share ta, kafin na sake nake bata labarin abin da ya faru. "Ummu kin ce baki son Tafida meye na kishi akanshi?" Kamar xan yi kuka na gaya mata abin da suka min jiya. Share zancen tayi kawai tana mika min bowl shake da fruit, ina ci ina kallonta. "Ummu!" Mika min wasu takardu tayi, tana faɗin. "Duba min wanene yafi miki kyau!" Amsa nayi ina dubawa. "Wannan tafi kyau!" "Ok makarantar girki ce ake son a gina a Maiduguri, amma ba a samu malamar ba shine nace ko zan miki magana ne sannan zai hada da shagon sayar da abincin bakiɗaya." Ajiyar zuciya na sauke ina jin wani irin abu a raina na ce mata. "Anya ba wani bane ya biya kike min hanya haka?" Dariya tayi tana faɗin. "No ina son ki tsaya da kafarki ne, yadda babu wanda zai ce kina jiran tsammani! Ummu Hadiyya ko don hidimar da da kika min zan biya wannan kyautatawar!" Sai naji na kasa magana bakiɗaya, muna nan har lokacin tafiyarmu yayi. Karfe goma na dare.
***
Maiduguri
Ance dare mahutan bawa, amma ga wasu mutanen wannan ne lokacin aikinsu. Domin cikin kwarewa da sanin kan aiki yau suka dirka gidansu Mahmoud.....
🚫 LITTAFINA NA KUƊI
500₦
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641
Yan uwa Yan Nijar ga na ku inda zaku yi payment din: +227 84 50 64 7667
Kafin yau! Jiya kenan Yayar Mahmoud da Yaranta mata biyu, mai suna Hamdiyya sun zo daga lagos, kasancewar sun jima basu zo ba mijinta dan Damaturu ne, ita kan ta Banbanta da Iyayenta domin halinta daya da Rayyan. Hamdiyya tana da matukar kirki da sanyin hali, amma bata daukar reni haka yasa tun fil azal suke faɗa da Mahmoud, har tana nuna mishi abin yake ba kyau ya daina kafin lokacin ya kure mishi akwai wani zuwan da tayi da yar aikin Yaranta, Mahmoud ya kama latsa Yarinyar Allah ya taimaka ta kama su, Amma sai aka juye laifin akanta na zuwa da yarinyar wai ba mamaki yar iska ce tazo zata lalata musu tarbiyyar D'ansu. Su akansu, sun san Mahmoud bai da mutunci amma haka suka rufe abin musamman Ammyn da take cewa bata haifi dan iska, tayi masu aiki dayawa amma Mahmoud ya yi sanadin barinsu gidan wasu yayi musu fyade wasu kuma bai musi ba, Allah kaɗai yasan irin bakincikin da ya cusawa iyayen Yara, wannan kenan..
Dirkowa Tango, daya daga cikinsu Oga Hakim, ya bude gidan, bayan ya sumar da me kula da gidan, sannan ya rufe suka shiga babu sand'a ko tafiya a hankali, basu yi magana ba amma daga takunshi zaka fahimci kosasun mutane kamar wasu shanu, raba kansu suka yi wasu suka yi bangaren Ammyn suka taso ta. Bayan sun ɓalle kofar gidan, wasu suka wuce bangaren Mahmoud, suka shiga shi kan Matar Mahmoud bata rufe ba domin Oga Hakim ya gaya mata matukar ta rufe sai ya rabata da rayuwarta haka yasa bata rufe ba, ta bar kofar a bude. Koda suka shiga cikin gidan, sun same ta zaune domin bata yi barci ba, sai Mahmoud da yake ta sharar bacci, amma ta daure hannunshi da kafarshi, sai bakinsa da ta saka salitep ta rufe gam, kunna wutar dakin suka yi. Oga Hakim ya ja kujeran mirror ya zauna yana murmushi. "Ina kudina?" Bude drower din ta tayi ta ciro wata jaka, ta ajiye a gabanshi sannan ta zube akan gwiwarta. "Oga Hakim ga shi nan!" Murmushi yayi ya ce mata. "Akan kudina ba laifi ba ne, zan iya karba tunda babu abin da nake ganin mutuncinsa sama da kudi, kuskuren da kika yi auren dan iska da bai san darajar na gaba da shi ba. Wanda bai dauki Amanar abota da zuciya daya ba. Da ace ya mai da hankali ya rike amanar abotarsu tun na yarinta, da wani magana ake ba wannan ba. Amma yau zan nuna mishi yadda ake rashin mutunci ganin idanunsa." Ya kalli Yaranshi ya ce musu. "Ku yi waje da shi!" "Tow!" Duk sauran fuskarsu a rufe yake, shi ɗaya ne fuskarsa a bude wacce kana gani kasan zai yi rashin mutunci, domin kuwa fuskar tasha fetching kamar kwarya zani, daya daga cikin yaranshi ne ya wake Mahmoud da mari, sai da ya farka domin ya zaci da katako aka mare shi. A lokacin aka shigo da su Ammyn, parlour aka zube su a tsakar parlourn.. "don Allah ku dauki kome ku kyale mu?" Dariya Oga Hakim yayi ya ce musu. "babu abin da zan dauka a gidan nan, sai dai zan yi abin da na ga zan iya. Kwanaki d'anki yayiwa Yarinyar da tazo aiki nan ciki kuka kore ta?" Murmushi yayi ya kalli Yaranshi kafin ya ce musu . "Ya ma sunan Uwar Yarinyar?" "Yahanasu me mana aikin abinci!" "Thank you Rainbow!" Ya kalli agogon hannun shi ya cigaba da cewa. "Kuka ce sharri ta mishi! Bayan ga video abin da ya faru. Shi d'a ita kuma baiwa ce saboda ta zo niman abincin da zata ci ko? Haka ne kafin yau wacce yarinya ce ma yayiwa Fyade ta mutu wurin haihuwa?" "Atika Oga! Kanwar Bobo!" Wanda aka nuna da sunan Bobo ya gyara zaman bindigarsa. "Hajiya kin tuna da kakarsu tazo kika kore ta?" Wani irin kuka Ammyn ta fashe da shi tana girgiza kai, "Taya ka samu videon abin da yayiwa Matar Tafida?" "Hmm mutumin nan dabba ne yafi a kira shi da dabba acikin dabbobin ma mara amfani kai ko alade yafi dacewa da a kiran da ita." "Sana'armu fashi da makami, sai dai muna kyautata alakarmu da mutanen da basu da shi kuma suke da karamin karfi, na san wacece matarka tun kafin ka aureta, saboda na biyo bayanka na saka ta kare kanta yadda zata shiga jikinka! Bayan aurenku muka daura akan inda ka fara. Baka tuna fuskar ta ba ko?" Shiru yana yana motsi kafin Bobo ya kwad'a mishi mari sai da ya fadi. "Na so na maka adalci na kyale ka, amma na fahimci dole na dasa maka abun da ka dasawa mutane dayawa." Ya juya ga Hamdiyya da take kuka rungume da Yaranta. "Matar mataimakin controller na custom ko? Mijinki mutumin kirki ne, sau uku yana min Alfarma na shigo da motocina arewa, Mun san halacci, Jazu kaita wancan bangaren da Yaranta, ka rufe su domin muna cin haramtacciyar abinci ne ba ma haɗawa da halataccen abinci, Uban Yaran mutimin kirki ne,.mun yi gwagwarmayar a wani lokaci, amma bai tab'a lakatar wata mace ba. Idan muka tab'a ta Allah ba zai bar mu mutsira ba kamar kullum!" Ya fada yana mikewa. "Ni dan kasuwa ne da nake shigowa da motoci, sana'ata kenan sai kuma bayan fage ina bashi da makami waye ya sani? Waye ya damu da ni? Amma na damu da mutanen da suke buƙatar taimakona, Hajiya sai hakuri akan idanunki Mijinki da d'anki suke tabargaza baki tab'a hanawa ba, haka yasa karamin danki ya bar gida, zaku yi mamakin yadda aka yi nasan kome a'a nima na turo mutumina yayi min aiki, ai ba ku kadai bane masu lissafi, Baka gane fuskar ta ba ko? Ka tuna Wafiyya?" Wani irin rikice yayi yana kallon Saubai'a yana ja da baya. "Ka san me kayi ai? Bayan haka ka saka makarantar ta kore ta bayan ka lalata mata rayuwa kai da mahaifinka kuka lalata mata sauran damar da take da shi ka tuna ta? Wannan kanwarta ce Saubai'a a'a Affiyah fansa ba zata yiwu ba saboda kana tare da Safiyyudeen da Aliyu Tafida ba zasu bari a cutar da kai ba zasu baka kariya a matsayinka na amininsu! " Juyawa yayi yana kallon Baban Mahmoud. "Kai da kanka ka lalata d'anka bayan kasan haka kayi ya ƙoƙarin boye laifinka bayan kasan cewa abu daya muke yi! Bari ka ga yadda ake gudanar da hisabi a duniya domin kayi naka muma zamu yi na mu." Janyo Ammyn suka yi. Ihu Mahmoud yake suka kwashe da dariya, "Jazu kai kace Uban kake bukata je kayi kodumo da shi!" Su rai goma sha biyar nan haka suka yi layi akan Ammyn, Mahmoud yayi bakinciki kamar zai mutu yayi ihu yayi kukan ya buga kanshi yayi kome. Yana kallon Matar shi Saubai'a tana murmushi, hawaye na zuba mata. "Kaji yadda ake ji, Yar uwata ta rasu ta bar duniya da bakin cikin abin da ka aikata mata,mun rasa kowa na mu bayan rasuwar Mahaifiyarmu, dama Mahaifinmu ya jima da rasuwa, domin ta rufa mana asiri Mamanmu tayi ta sana'a, ka kunsa mata bakin ciki biyu ga ciki ga kora, ita kanta ta fada fyade ka mata, haka bai maka ba kayi bibiyar rayuwarta har sai da ta mutu hankalinka ya kwanta, ka godewa Allah da ban kashe ba domin Abokan da ka ci amanarsu sune suke kare ka, yanzu babu kowannensu a tare da kai. Ai Tafida ya gaya maka ba zai maka kome ba ka zata tsoronka yake ji kada ka kara fitar da hoton matarshi a'a yasan Allah baya bariin hakkin aure ka tab'a ya bada damar an.tab'a naka. Nayi Imani da Allah fansa ya shigo da ni rayuwarka amma ko da wani abu ya shiga tsakaninmu ka yarda kai ne sanadi." Ga Ammyn da Babanshi cikin mawuyacin hali domin Jazu gay ne, sau tari idan suka je fashi tow shi abin da yake yiwa maza da mata kome, yadda suka tozarta Ammyn yasa ya daina gani sosai, alamar zai suma. "Ku tale min Dan iska!" Oga Hakim ya fada yana mikewa, yana zuwa ya saka kafarshi da katon takalmin shi me kama da dutse ya daki gaban Mahmoud sai uku anan ya zube sumamme. "Zaki zauna ne ko zaki zo muje!" Hawaye ta share, ta ce mishi. "Zan bika!" Ta fada tana shiga dakinta, ta dauko akwatinta ko inda suke bata kalla ta bi bayansu. "Ina zaki daga nan?" "Zan je na dauki Little Wafiyya na tafi da ita inda zamu zauna babu wanda zai dame mu!" "Na ce Taj ya baku takardun shaida barin kasar ya baki?" "Ya bani!" Ta fada tana kallonshi. "Nan babu tsaro sana'ata na kasada ne da wasa da rai, idan na samu lokaci zan na zuba duba ki da Wafiyya!" "Na gode sosai!" Mika mata jakar kudin yayi yana faɗin. "Na ki ne dama, kada ki sake yarda ayi amfani da ke don cin amanar wanda ya yarda dake, na san ba don kina buƙatar fansa ba, ba zaki yarda nayi ruin dinki ba. Ki kula da yarinyar nan sosai kada ki yarda ta nime wani abu ta rasa, idanuna yana kanki." Daga haka kowa ya kama gabashin, Hamdiyya suka bude ta kafin suka tafi abinsu. Bayan tafiyarsu, ta fita zuwa bangaren da ta samu iyayenta cikin wani irin mugun hali, ihun niman taimako da a gaji tayi ta yi, babu wanda ya fito a cikin daren kamar zare sai da asuba ne, aka ta kawo musu ɗauki. Tare da nufar asibitin da su, Hamdiyya bata taɓa tsintar kanta a cikin tashin hankali da bala'in irin na daren jiya zuwa yau ba, Yaranta ma kuka suke su a kaisu wurin Babansu kawai ba zasu zauna ba. Karfin imani yasaka ta iya zama asibitin domin gani take zasu iya biyo su asibitin, ta girgiza iya girgiza, mijinta kuwa ta kira shi ya kai sau dari, ce mishi take yazo. Karfe shida na yammacin ranar Alhaji Abbas ya rasu domin kuwa abin ya tab'a shi sakamakon abin da aka mishi dayawan mutane da suka san halinsa basu fadi maganar alkhairi akanshi ba, sai bayan sallah jana'sarshi Mahmoud ya farka, labarin ya karad'e ko ina na garin Maiduguri, har a jarida an fashi sun shiga gidan tsohon Kwamishina.
A lokacin da Hajiya Kaltuma ta ji labarin, tafi kowa murna domin Mahmoud shine mutum ba farko da zai fara bada shaidarta. Haka yasa ya ta nufi asibitin bata samu ganinshi ba, har washi gari. Deen da ya samu labarin ya kira Tafida ya gaya masa, hankalinsu duk a tashe duk da abinda Mahmoud yayi basu manta da abotarsu ba domin kuwa sun yi kokarin sakawa a kare shi kada a sake farmakarsu. A ranar da suka cika kwana uku Deen ya iso, yana asibitin karshe da bai yarda da Asibitin ba, domin ya ga wani da bai yarda da shi ba. Wato Jazu haka yasa aka mai dasu asibitin da yake cikin fadar gwamnatin kasar, wanann lokacin likitoci suka tsaya akan shi sosai.
***
*Ummu*
Kasancewar na kwana biyu ban shiga kitchen ba, haka bai saka na manta da yadda ake rike ludayin miya ba, nayi matukar kokarin ganin nayi kome yadda ya dace, sai dai ma yasan tsayuwar da nake yana haifar min da ciwon kafa da gajiya, haka yasa kafin wani lokaci na gaji, idan na koma masauki gajiya nake a daddafe nake sallah na kwanta. A hankali kwanakin suka ta tafiya, har muka samu sati uku kafin muka gama, cikin ikon Allah da yadda na tsammaci lamarin domin yawan gajiyar da nake yasa nake ta zuwa ta biyu ko ta uku, a kullum sai nayi baya. A ranar na karshe ne muka yi aikin kamar babu gobe haka yasa ni jin kamar ba jikina ba, ina gamawa na tafi ban dakin da yake wurin nayi ta amai. Na gaji sosai, a hankali naji kamar jiri na daukata zama nayi na rufe idanuna, a hankali naji an dauke ni sama. Idan idanuna bai min karya ba Tafida nake gani. A hankali na lumshe idanu na gyara kwanciyata a kafadarshi. Hawaye na zuba min. Tun farin abin yake bibiyarsu, sai dai wani abu da ya lura Ummu tayi rauni Ummun da ya sani ba ita ba ce, yana hango gazawa da rauni a tare da ita, haka yasa koda ya samu Asiyah ta ga likita, ya bar