Showing 33001 words to 36000 words out of 241571 words

Chapter 12 - YAR MACE Complete Document hausa novels by Mai Damu.txt

24 Dec 2024

14748

muka karasa parlour inda, matar tana da kirki tunda ma shiga take ajiye min abinci da wanda na sani da wanda ban sani ba, haka da zan dawo na samu an hade min su cas na dawo dasu. Gabana ne ya fadi ganinshi zaune a parlourna ya daura daya akan ɗaya, dauke kai nayi na nufi kitchen na ajiye abin jikina yana bani kamar ya biyo ni ban gama tunanin haka ba naji ya shake min wuya da hijab dina. "Idan na kara ganin wannan mummunar fuskar naki a waje da sunan kin je gaida Abba sai na lahanta miki shi yadda ba zaki more shi da dadi ba! Kina jina!" Ya daka min tsawa. "Eh na ji!" Na fada ina kokuwa da numfashi. "Wawuya kawai!" Ya juya yana me fita, zubewa nayi a wurin ina rike wuyana, wani irin kuka ya zo min wanda ban kawo zan iya shi a yau ba, kuka nake. Sai da na gaji na mike zuwa dakina. Ina zaune a wurin naji ana ta magana sama-sama, fitowa nayi ina kallon ikon Allah. Kayan garana ake fita da shi buhun-hunan shinkafa da duk abinda aka kawo min ina kallonshi yana fitar da shi. "Kina da abinda zaki ce ne?" Juyawa nayi daki da sauri. Sai bayan fitarsu na fito zuwa kitchen din na samu buhun shinkafa daya kwalin taliya biyu sai jakan simo da sauran tarkace. Hawaye ne ya zubo min. Ina cikin gyara kitchen din aka kawo kayan cefene, ma zauna na fara gyarawa zan saka a firji sai gashi tare da Yarinyar nan, "Ya Tafida kayan abincin nan ina ga sai mun kai shekara bamu nemi abinci ba, gaskiya kana ji da Kuma sosai."
"Hmm! Shiga ki raba kayan ki kai mata rabi." Haka ta shigo tana me bangaje ni. "Ya Tafida kace ta matsa min. Dama ina yar talle da samun irin wannan kayan!" Hadiye yawu nayi na koma gefe sai da ta dibi kome sama da rabi sannan ta fita da shi tana wani shegen dariya. Sauran na dauka na saka a firji, na fito da kayan aiki na fara kokarin daukar girki. "Su fooder za a fara dafa su kaji babu a gidan Uwalle da Uballe!" Inji Yarinyar kenan, sai na rasa bakin magana, ban kulata ba ta shigo kitchen din. "nan gidana ne, Yayun tafida da shi Tafida ni suke burin na aure shi!" "Tow ni ina ruwana! Wannan matsalar naku ne ba nawa ba." Kada ku dad'a kada ku kara, yarinyar nan ta fita tana ihu tare da fashewa da kuka. Ta nufi bangarensu, ba ita ba hatta Tafida da Uwarta suka tawo. Tana kuka kamar ranta zai fita, "Me kika mata?" "Me na mata kamar ya?" Na tambayi Mahaifiyarta da ta min tambayar. "Nace me kika mata?" Ta daka min tsawa. "Tow dama nayi mata wani abu ne? Ni ban mata kome ba gata nan!" "Ke Sa'adiyya me ta miki?" "Marina tayi tare da cewa har abada ni da Tafida sai dai naga nesa!" "Marinta kika yi?" Matar ta shigo zata rufe ni da duka, Hajiya Kaltuma da bamu san da zuwanta ba tace. "Kul Hindatu shuwa, kika sake kika tab'a musu yar mutane sai kin gane Alhaji Muhammad Jadda baya wasa da duk abinda yake na shi." "Amma Hajiya baki ga rashin kunya tayi ba, taya don iskanci zata mari Sa'adiyya har tana cewa wai ba zan tab'a auren sa'adi ba? Na bari ne Hajiya ta gama nata nayi mata nawa wallahi sai kin gane baki da hankali, wawuya wacce iyayenta suka gaji da ita." Yadda yake cin zarafina ya sani zamewa kasa. "Tow wallahi xan gayawa Alhaji abin da kake aikatawa hauka ne abin har ka isa ka zagi iyayen kai ba a gaji da mugun halinka ba, mara kunya wanda bai san darajar iyayenshi ba" yasan Hajiya Kaltuma bata da dad'i itama, "kuma kema Shuwa zan gayawa Alhaji ya muku iyaka da gidan tafida ." Haka tayi musu tas suka fita ta kuwa gayawa Abba, ranshi ya b'aci ya kira Abban tsakiya mijin Hajiya Shuwa ya buga mishi kashdi wanda ya sa shi dole ya gargadeta.
Ashe al'amarin ya zaga ko ina na yan gidan, ranar da na cika sati Aunty Rukayya tazo da Yaranta. Ina kitchen ina wanke kayan abincin da Tafida da Sa'adiyya suka b'ata domin bayan gama fadar Abba, tafida yazo har dakina, ya murde min hannuna sai da yayi ƙara, ya ce min. "Ina son na illata ki ne? Tow wallahi ki nisanci Abbana idan kika kara barin yayi min magana akanki, zan baki abinda ba zaki iya amsa ba!" Ya tunkude ni na fadi goshina ya bugu da karfen gas dina, ai kuwa ya fashe. Tun ranar da naga haka na rufawa kaina asiri, ina dauke kai akan me suke yi, idan na fito na same su a parlour rufawa kaina asiri nake na shige dakin naki fitowa ai ba hauka nake da zan yarda ya fara saka hannunshi a jikina ba, ta ko wani hanya niman yadda zai ci zarafina Sa'adiyya take. Shi kuma biye mata yake kamar bai da lissafi.


Na gama wanke kayan kenan naji Muryan yara, na fito kawai yaran nan suka fasa ihu tare da fita da gudu, ban san me ya faru ba amma dai zan ce abin ya bani mamaki, can sai gasu Aunty Rukayya da Tafida da Sa'adiyya,dauke da wani yaro da ya fadi yana kuka Yaran suka koma bayan Tafida. "Ke mike musu?" Kasa magana nayi ina me jin wani iri abu a raina. "Me tayi muku?" "Kama tayi mana da zombies shine muka gudu!" Wani irin dariya suka saka tare da nuna ni, Sa'adiyya har da yin alamar yadda zombies suke tafiya tana dariya. "Eh dama tayi kama da zombies don ma she always look ugliest!" Kaina a sunkuye hawaye na zuba min kamar an bude pampo......
#500
8130269641 Abdulrahman Ramlat Manga Opay
Shaida biya a turo ta wannan numbers din.
+2347035133148
Or
+2348130269641'YAR MACE....🌺



*Mai_Dambu*




Paid book


12


Duk da naki karatun boko, hakan ba yana nufin ban san me wasu kalmomin turanci ba ne, hada na d'ago kai ina kallonsu. A hankali na juya zuwa dakina, na rufe kofar na cigaba da kuka. Suka cigaba da dariyarsu, can ina zaune naji yana buga kofar dakin tashi nayi na bude kofar ina kallonshi. "Uban waye ya baki izinin rufe min store din gidana?" Hadiye yawu nayi na rab'a gefenshi ya firgo ni. "Ba magana nake miki ba?" "Zan je na bude ne!" "Good!" Haka na bude ya shiga ya kwalawa Aunty Rukayya kira. "Aunty Ruky!" Shigowa tayi ta wuce ni zan fita Yaranta suka shigo suna daya Yaron yana ganin glass cup din da na wanke kawai ya dauka yana fadawa daya Yaron. "Ayman dauka mu sha ruwa a cikinsu;" "A'a sai dai mu fasa muji ko na gaske nan!" Kafin na ankara sun maka kofinanan da kasa shi kake tuss, suka kuwa kwashe da dariya suna faɗin. "La da gaske ne fa! Dauko sauran!" Nayi maza na tare su. "A'a kada ku kara domin zan muku bulala!" Na fada ina d'aga su. Ai kuwa Yaran suka saka ihu. Ban kula su ba na saka kayana a sama. "Wai don Allah me suka miki ne?" Inji Aunty Rukayya tana me cika bakinta da kayan garana, ashe diba mata yake yi har da kayan abinci. "Kayana suke fasa min, taya zan kyale su." "Lallai ma har kin samu bakin magana, kayan da waye bai san cewa Abba ne." "Wannan kayan hatta tsinke Uwata ce ta saya min, don haka ba xan bari a lalata min su ba." "Tafida kazo Matarka tana min rashin kunya" fitowa yayi ya mika mata wani bokiti cike da kayan duk abinda suka diba. "Me ya faru?" Nan ta labarta mishi abin da ya faru. Ganin ban kula su ba ina gyara inda kwalbar ya fashe, yasa shi kamo jelar gashina bakiɗaya ya d'ago ni. "Kika ce kayan Uwarki ce ya saya miki? Ko an gaya miki ban san Abba ya ce kada a kawo ki da kome ba ne." Irin kallon da nake mishi yasan ba kallon tsoro ba ne kallon kiyayya ce zalla. "Dani da kai ita, duk zamu hadu a fadar Allah kuma fadar karshe, Allah zai bin min hakkina kamar yadda zai fara hisabi daga kan dabbobi zuwa kan mutane!" Kamar wanda na gaya mishi wani magana me zafi ya sake Ni yana kallona, na gyara zaman hular kaina. Janyo glass cups din yayi ya fasa su bakiɗaya. "Kina da abin da zaki iya ?" Girgiza kai nayi, "wata rana tarihi zai maimaita kansa in sha Allah!" Na fada tare da nufar kofar dakina, ban san ya aka yi ba ni dai bude idanuna nayi na ganni a parlour Abba, bayana yana min wani azabar zafi. "Me ya faru?" "Sannu Ummu Hadiyya,.sannu Yaron nan Allah ya baka lafiya." Kokarin tashi nayi amma na kasa haka na koma na kwanta. Abin da na iya tunawa shine kamar an buga ni da kofar dakin da zan shiga daga nan ban san kome ba. "Kin tashi!" Abba da ya fito dakinsa ya fada min. " me ya faru?" Na tambaye shi. "Kaltuma d'aga idan zata iya zama!" Dakyar na tashi zaune dakin ya cika bakiɗaya har da Hajiya Salamatu. "Nura kai da Saleh ina son ku zama shaida Hindu ta fitar min da yarta a gidan. Sannan idan na kuma ganinta a cikin gidan nan kotu ce zata raba ni da ita, na biyu Tafida ba xan maka baki ba amma in sha Allah, sai ka zo nan kana rokon nayi maka alfarma a karo na biyu ina dauke kai. Na uku daga yau kada na kara ganin kafar Rukayya da Yaranta bakiɗaya a cikin gidan nan sai idan ni ne na bukaci haka, wannan shine hukuncina wanda haka bai mishi ba yana da damar kai ni kotu!" Sannan ya juya yana kallon Nabila ya ce mata. "Allah ya miki albarka da kika ga kome a idanunki, Ubangiji ya saka ki a cikin amintattun bayinsa." "Amin Alhaji!" Inji Hajiya Kaltuma, sannan aka watse. Rike ni Nabila tayi na koma bangarena bayan Abba ya bani hakuri, a hanya take gaya min abin da ya faru. "Na shigo na kawo miki sakon Inna kawai na ga Sa'adiyya ta tokare ki ta baya sai da kika bugu da kofarki, ga kuma Aunty Rukayya da kayan abinci shine na koma na kira Hajiyarmu tazo ta gani ta kira Abba, sannu." "Yawwa!" Tun da na koma na gyara gidan na kwanta ji nake kamar na bar gidan domin na gaji a yan kwanakin nan da nayi, ba karamin kullata na Tafida yayi ba.


Satina biyu layya ya karato, ban yi wani zumudi ba, ina dai zaune ne amma bana jin dadin rayuwata. Idan na shiga cikin gidan hatta yan aikin gidan basu kula ni ko na gaishe su basu amsawa, sannan ban da Hajiya Kaltuma da Inna babu me shiga harkata. Ana gobe arfa Alhaji ya kirani na je na gaida shi domin tun da na fara girki na ware wani kula me kyan gaske ina kai mishi abinci, ina shiga na samu abincin rana da na kai yake ci. Hajiya Salamatu tana gefenshi. Cikin nutsuwa na gaida ita. Ta amsa sama-sama. "Barka da hutawa Abba!" "Yawwa Ummu Hadiyya! Ga wancan kayan ki dauka na sallah ne, jiya na bawa Salamatu ta sayo miki!" A hankali na kalleta na ce mata. "Allah ya saka da alkhairi Mama, Ubangiji ya duba bayanki da gabanki na gode sosai." A yau na ga murmushinta, tana faɗin. "Amin Ya Allah!" Na dauki kayan ina jin wani irin dad'i na d'ago kai idanuna cike da kwalla na ce mishi. "Ni ne da godiya Ummu ni ya dace nayi godiya ni zan miki godiya!" "Alhaji na fara jin kishin yarinyar nan ka ware ta a cikin Yaran gidan nan!" Kallonta yayi kafin ya ce mata.."ke kanki kin san Aliyu yana niman mace da zata iya hakuri da shi ko? Ke kanki kin san Sharif da Alfah sun fi Aliyu saukin kai ko? Ke kanki kin so da Sharif ne ya samu Ummu saboda nagartatta don haka ki bar ni nayi mata godiya." Tabbas taso da Sharif ne ya samu Ummu domin haka kawai taji yarinyar ta mata amma kasancewar basu shiri da Tafida ta gargadi Yaranta babu ruwansu da Ummu kada taji wani abu ya fito baya. Amma yau yadda ta ga farin ciki a idanun Yarinyar yasa take jin yarinyar tayi mata, amma ba zata shiga hidimarta ba. "Na gode sosai!" Na mike na bar musu wurin suka yi ta hira sama-sama. Wurin Hajiya Kaltuma na shiga na nuna mata, ta tayani murna sannan na kaiwa Inna itama murna ta tayani, kafin na wuce bangarenmu takalman mutane na gani da sallama na shiga Deen ne sai Mahmoud da Oga da kanshi. Gabana ne ya fadi na gaisu sannan na wuce zuwa dakina. Ina cikin dakin na ji yana faɗin. "Ke!!!" "Tafida meye haka ina laifin Ummu?" "Uwar wa ta haifa!" "Mutumtawa na da dad'i!" "Kai dai ka cika tsugudidi!" Fitowa nayi ina kallonshi. "Babu abinci ne?" "Akwai!" Na fada ina nufar kitchen din. "Amma me yasa ka mai da gidanka kamar wani Barack?" "Bana son iyayi da ka gudu baka zo bikina ba, ban maka magana ba na maka uzuri ne yanzu kayi min maganar banza zamu doku ne!" Abincin na zuba na shiga kawo musu dama tuwo ne miyar egusi, na kawo ina jera musu har na gama zan tafi ya ce min. "Wai dama kin dafa ba zaki bani bane?" "Kayi hakuri!" "Mtseew!" Dukar kafadarshi Deen yai yana faɗin. "Ka kula ita rayuwa ba a mata haka!" Haka na barsu suka cinye abincin shi bai ci ba, ganin yadda suke santi ya shi mikewa ya fita can gidan Hajiya shuwa ya amso abinci a parlour ya ga Sa'adiyya ware idanu yayi yana faɗin. "Saadi yaushe kika zo?" Tura baki tayi tana faɗin. "Tunda dama na hanaka sakewa da matarka shi yasa har nayi laifi na zata nayi abin da zai faranta maka ne ashe ban sani ba nice nake ta hauka." "Ya isa ki yi hakuri idan na dawo zamu yi magana! Abincina na zo dauka!" Cikin kwarkwasa ta dauko mishi abincin ya dauka ya fita da shi. Har zuwa parlourn. "Tafida kira min Ummu wannan abincin wallahi ta cancanci na biya shi." "Ke!!" Ya kara kwala min kira, haka na fito ina faɗin. "Gani nan!" "Ga dan iskan da yake kiranki!" Ya nuna Deen shi kuma yana cin jollop din shinkafa, "Hajiya Ummu ga shi ba yawwa!" "A'a na gode!" Na ki amsa tsaki yayi yana faɗin. "Kasan yaran matsiyata haka suke." "In sha Allah ba zan kuma zuwa gidanka ba idan zaka cigaba da cin mutuncinta." "Tow Allah ya baka hakuri." Haka suka ajiye min kudin har da Mahmoud na dauka na wuce ina jin b'acin rai. Haka suka yi hira har lokacin sallah yayi suka fita na shiga kitchen din na yi jallop din cus-cus sai sauce din kayan ciki. Na ajiye a kitchen din. Ina sallah la'asar naji hayaniyarsu ban fito ba sai da naji ya fara kwala min kira da ke, na fito ina kallonshi. "Bar kallona da idanun kamar na Mayu Mahmud ne yake jin yunwa akwai abincin?" Hadiye yawu nayi ina gyada kai, na shiga kitchen din na dauko katon kula na ajiye musu. "Ke wai haka zasu na cin abinci ko dan irin ruwan sanyi babu!" "Kayi hakuri!" Na fada na rasa ne xan musu kawai sai na duba firji din na ga babu kome, na fito waje tare da cewa. "Babu kayan haɗin zobo ne shi yasa ban yi ba!" "Ni zan nimo miki!" Kai mishi duka Deen yayi ya mike. "Hajiya Ummu bani list na sayo!" Haka na shiga daki na rubuta mishi, na kawo tsaki Tafida yayi yana cigaba da kallonshi. Fita yayi bayan minti talatin sai gashi dauke da kaya niki-niki, na ware fruit din na markadesu na tacce, sannan na dauki sugar da na narka shi yayi ja kaɗan na zuba, kafin na rufe shi ina me kawo kankara na zuba a kai. Na dauka na kai parlourn na ajiye musu. Ashe wai kallon kwallon suke tsakanin Real Madrid da Barcelona! Ni dai na barsu nan na dawo dakina. Kafin karfe bakwai na dare sun cinye abincin. Haka suka bar gidan, da safe da zai tafi masallaci ya buga min kofa "ke jiranki nake!" Fitowa nayi. "Yau anan zasu sha ruwa saura ki musu kwauron abinci!" "In sha Allah haka ba zai faru ba!" Tsaki yayi ya fita. Ina idar da sallah na fito na wanke shinkafar tuwo na barta a kwando, na gyara gidan nayi wanka na shiga daki, karfe daya na rana na ji anata hira fitowa nayi na ga Aunty Maryam ce, yaronta nata buga remote din tv a kasa yadda basu ce mishi bari ba, nima ban ce mishi bari ba. Na gaishe ta amma taki amsawa na wuce kitchen na fara aiki, Yaron ya shigo yana kallona ya kai hannunshi tare da ɗaukar wuka. "Kai Amir ajiye wukar nan!" Ya faɗa.."yau muguntar ce ta motsa ba zaki ce mishi ya ajiye kada ya jima kanshi ciwo ba!" Amsar wukar nayi na ajiye na cigaba da aiki, kullun tuwon masata na juye a bokiti na fito da ita tare da saka hijab. Na shiga cikin gidan. "Hajiya Barka da ibada Nabila bata nan ko?" "Kina son wani abu ne!" "Dama masa zan yi!" "Harira!" Me wanke-wanken gidan.."Na'am Hajiya !" "Karbi bokitin ki kaiwa Ummu markade!" Wani irin kallon banza tayi min kafin ta ce mata. "Hajiya ina aiki!" "Kina aiki?" "Eh!" "Yayi kyau daga aikin ki wuce gidan Ubanki!" "A'a Hajiya ba ayi haka ba, inji Tabawa. "ke amsa kuyi hakuri Hajiya, Ummu kema ki yi hakuri Maza amsa ki tafi!" Ko furucin da Hajiya Kaltuma tayi amfani da shi yasa bakiɗaya suka razana, fitowa Hajiya Salamatu tayi tana tambayar Hajiya Kaltuma, ta gaya mata ai kuwa ta hade rai tana faɗin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login